← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 227

Sashe 6

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Doka ta farko a GIDAN SOJA shi ne biyayya ga manyan Hafsoshi sojoji wajibi ne a kanku, bin umarnin manyan ba tare da gardama ba, ba shawara bace, wajibi ce! Ana buƙatar sojoji su kiyaye dokokin soja da na ƙasa bakiɗaya, abu na biyu shi ne shaye-shaye, an haramta amfani da miyagun ƙwayoyi da barasa a yayin aiki. An hana sata, cin hanci, fyaɗe, da sauran manyan laifukan da nasan kun sansu kuma kun karanta kundin dokokinmu, tunatarwa nike kara yi maku, dan a GIDAN SOJA dik wanda ya karya doka kun san sauran, to gargaɗi ne da jan kunne mai karfi a matsayin na sabbin sabbin ɗauka".
Ya ɗan ja numfashi kafin ya cigaba. "Sai doka ta gaba shi ne yin aure ba bisa ƙa'ida ba. Sojoji suna da ƙa'idoji kan lokacin da za su iya yin aure, misali, a wani lokaci baya an tsare wata soja da ta amince ta auri mai bautan ƙasa (NYSC) ba tare da izinin manyanta ba, aka tsareta a prison na soja saboda ta karya dokokin soja kan aure, nasan kun samu wanna labarin a document ɗin da aka baku, sojoji suna da lokacin yin aure wanda sai sun karɓi umarni daga sama! Ba raɗin kansu suke yi ba". Dakatawa ya ɗan yi yana mai da numfashi kafin ya cigaba da cewa.

"Horon fisika da na Ilimi wajibi ne a kanku, sojoji dole ne su halarci horo na jiki da na ilimi dan inganta kwarewarsu. Dole ne sojoji su kula da tsabtar kayan aikinsu da muhalli. Ana buƙatar sojoji su kasance a shirye dan kowane aiki a kowane lokaci. Yin ritaya daga aiki yana da tsari da dokoki da dole ne a bi. Sojoji da suka karya dokoki suna fuskantar shari'a a kotun soja dake cikin Barrack ɗin nan. Wannan shi ne dokokin GIDAN SOJA, fatan kun ji da kyau?". Ya kai karshen maganar yana rarraba idanunsa a kansu.

Nisawa ya ɗan yi kafin ya cigaba da cewa. "A yau zaku karɓi manyan allurorin da ake yi wa dik wani sabon ɗalibin soja na kariya da sauransu, cikin alluran da zaku karɓa sun haɗa da allurar rigakafin cutar tetanus da diphtheria Tdap, waɗanda ka iya zama haɗari ga rayuwar soja, wannan allura ana yi wa sojoji a lokacin horo na farko kamar ku kenan, idan aka yi maku yanzu kuma sai bayan shekaru 10 za'a sake yi maku. Allurar na biyu kuma shi ne rigakafin cutar hepatitis A da B. Alluran yana kare hanta daga ƙwayoyin cutar Hepatitis A da B. Allura na uku shi ne allurar meningitis, watau meningococcal vaccine, yana kare kai daga cutar kumburin kwakwalwa watau meningitis, abin da yasa za'ayi maku shi dan horon da zaku fuskanta, gujewa ƙwaƙwalenku su kumbura ko su taɓu. Sai Rigakafin zazzaɓin cizon sauro watau yellow fever, yana kare sojoji daga wannan cutar da ake samu a yankunan tropic, musamman a Afirka da kudancin Amurka, so aikin zai iya kaiku ko'ina, dole ayi maku wannan alluran". Ya dakata yana ɗan nisawa.

Commander ne ya karɓi zancen da cewa. "Waɗan nan su ne alluran da zaku karɓa a yanzu, dan haka ku shirya". Ya kai karshe yana dawo da kallonsa kan wasu zakwakuran sojojin dake gefe suna kallonsu, basu shiga cikin line ba, horarrun jami'ai ne ta ɓangaren harbi, basu da wasa.

"Ku shigo da surgeons generals and nurses yanzu". Captain ya faÉ—a a dake. Daddagewa sojoji biyun nan suka yi suka sara mashi kafin su nufi gate na hall É—in. Jim kaÉ—an suka shigo tare da malaman asibiti da surgeons brigadiers. Nan Captain ya umarci matasan sojojin nan da su gyara tsayuwarsu da kyau su kuma É—age hannun rigarsu sama dan dikka alluran a damatsan hannu za'a daddanna masu.

Haka kuwa aka yi, dik suka gyara suka tsaitsaya da kyau, nurses É—in nan suka hau bin line by line suka fara yi masu alluran. Abin ku da jarumai, tamkar ba jikkunansu ake fasawa a danna alluran nan ba, suna tsaye kyam tsabar ma sun sanya aikin a ransu.

--------------------🔥

A yayin da dikka wannan abin yake faruwa su kuma manyan zaratan general's na sojoji suna can cikin COMMAND HQ suna tattaunawa dangane da yanayin tsaron kasar Avaris, taro na gaggawa ne suka shiga. To mu leƙa Command HQ ɗin mana mu ga me suke tattaunawa, dan yana da amfani a garemu kwarai da gaske..

COMMAND HQ.
Ɗakin meeting na sirri na AZURE, bangon ɗakin ma Soundproof, common view bulletproof ne wanda babu wani bullet da zai iya fasashi, dik da ya kasance ɗaki ne mai matuƙar tsaro, amma an saka bulletproof glass sosai saboda tsaro, ga na'urorin leƙen asiri da ke bin duk motsi waɗan dake ciki da waɗan dake waje ko in ce tunkaro ɗakin.

Wurin yana da ƙofar shigowa ɗaya da kuma ɗakunan bincike guda biyu kafin a isa ciki. Kai bincike sosai fa ake yi kafin kowa ya shiga, ma'ana kafin manyan Generals ɗin ma su shiga, sai an binciki ID, fingerprint, retina scan. Sannan ga wasu jiga-jigan sojoji guda biyu masu rike da jiga-jigan bindigogi suna tsaye a ƙofar ɗakin ta ciki da waje, ma'ana biyu ta ciki biyu ta waje, sai ka rantse da ALLAH sojojin nan basa numfashi saboda yadda suka kame kam.

An kunna jammer na'urorin hana leƙen asiri, anti-drone radar, da surveillance 360 wacce ko yaya aka motsa dan leƙen sirrin cikin ɗakin sai an gano mutum, ko wata na'ura ka tura dan leƙen asiri jammer sai ta ganota. Daga nan zaku san ba ɗakin wasan yara bane a wajen! Kuma ƙananan kai basu zuwa wannan waje!.

Manyan Generals na zaune a saman chair na table dake zagaye da É—akin, irin round table É—in nan ne, sannan a saman tables É—in gaban kowani chair akwai sunan jami'in da zai zauna a wajen, wani É—an karamin sing post ne da sunanyesu.
Shugaban sojojin watau THE GENERAL OF THE ARMY THOMAS (G.A.T) yana zaune a tsakiya ta gaba, sauran Generals na a gefen dama da hagunsa bisa rank É—insu.

A tsakiyar round na table ɗin ga jagorar rubuce-rubuce, da sashen bayanan leƙen asiri, da kuma wani soja mai ɗaukar hoto da recording idan an buƙata. Ƴan jaridu basu isa shiga wannan waje dan ɗaukar bayanai ba, sai dai su jira a waje idan an fito wani daga cikin General ya faɗa masu ga abin dake wakana dangane da tsaro ga kuma irin tattaunawar da aka yi!.

Dikka dakakkun Generals É—in dake wajen suna zaune ne cikin ladabi da biyayya game da nuna alamar girmamawa ga GAT dake wajen, kama daga kan lieutenant general, major general, brigadier General, General, dik suna cikin wannan É—aki, kun san akwai bambanci tsakanin Lieutenant General da kuma Lieutenant, sannan akwai banbanci a tsakani Major General da kuma Major kawai, su waÉ—an da zaku ga General ya shigo cikin sunansu ana nufin su ne manya, misali Major General shi ne shugaban dik wasu Majors dake Barrack É—in, kun gane ai? Wannan General É—in na nufin mai wakiltan ko shuganan dikka Majors or Lieutenant ko dai wani runduna. Nasan kun gane nufina In Sha ALLAH.

Zama yana tafiya cikin ladabi mai tsauri, dan kowa sai an bashi izini kafin ya yi magana.

Wani kyakkyawan soja ne ya mike, hannu ya sanya ya buÉ—e taswirar kasan Avaris a gabansu. Katan taswira ne sosai wanda yake É—auke da dukkan sassa na kasar, da yankuna da dama sai dai kuma a wasu yankuna akwai alamar jan marks, hakan alama ce da ke nuna yankunan da yan ta'adda su kaiwa kawainiya, su ake wa wannan mark É—in.

Still wannan kyakkyawan soja da ya buɗe taswira shi ya sake buɗe wasu takaddu a saman table ɗin. Takardun ne da suka fito daga hannun sojojin amma ta fannin kwararru kuma gifted waɗan da suke kamar jami'an leken siri na ƙasa, su horo na daban ake basu, ba zaku fahimci irin jami'an da nike nufi ba, dan ba kowa ya sansu ba, su ɗin sirrin ƙasa ne, amma bari mu kutsa ciki zaku gane irin jami'an sirrin cikin soja da nike magana.

Duk wani soja da ke wajen a saman table a gabansa akwai coded notebook da pen da wani taswirar na manyan states na ƙasar, rahoton leƙen asiri, da hotunan jiragen yakin maƙiyan ƙasa da ƙasa, wannan kyakkyawan sojan ya sake budewa.

Bayan ya kammala buɗe su gabaɗaya sai ya koma saman kujerarsa ya zauna ya kame ƙam, dukansu suka kara natsuwa sosai. Cikin nuna tsantsar isa da girma G.A.T ya mike tsaye, yana miƙewa duka sauran sojojin suka kara nutsuwa sosai. Ɗan gyaran murya yayi cikin kwararriyar turancinsa ya fara magana a natse bayan ya kunna mic dake gabansa, ya kuma kunna recording system na sirri dan su ajiye tarihin kowane zama.

"Ina yiwa kowa da kowa barka da zuwa wannan taron, na san kunsan abinda ya tara mu anan, dan dik karshen sati muna yi, domin sanin halin da kasar mu take ciki da kuma sanin irin nasaran da muka cimmawa, kamar dai kullum zamu fara gabatar da abunda ya tara mu ba tare da ɓata lokaci ba, ina son bayanai daga bakin kowannenku, ina son jin wani nasara aka samu da kuma cigaba da muka kara samu a yankunan da ƴan ta'adda sukayi wa kasan nan kawanya".
Chapter 6 · 0% Book details