← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 118 OF 227

Sashe 118

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai tsaye elevator suka nufa. Suna tafiya Seraphina sai shagwaɓa take zuba mashi, shi kuwa yana ta faman biye mata. Kai tsaye katafaren shopping dake sama suka nufa dan yin shopping gobe Monday zata fara zuwa schoo nan school dake cikin CP ɗin yai masu registration ita da Rimsha, ya sake haɗasu makaranta ɗaya kenan. Wannan karon ya ɗaura ɗamarar saka masu ido da basu kula ba tare da ya bari sun san yana sanin dik abin da suke yi ba!.

Suna shiga ya samu waje ya zauna tare da ce mata ta je ta É—auki dik abin da take so. Da sauri ta wuce ciki tana murna, har da cewa wai zata sayi breziyya, dan Rimsha ta faÉ—a mata ita dai tana sakawa, kai waÉ—an nan yara sai Aryan ya yi da gaske wlh, idan ba haka ba akwai aiki, ita Rimsha yanzu 14 years take, kunga ko ta sa bra ba matsala, amma Seraph 13 É—in ma da sauran watanni huÉ—u kafin ta cika, ace ma tana da 13 years, wai dik abin da Rimsha ta yi sai ta yi ita ma, kai wannan yarinya, ita ma Rimshar akwai iya shege da komai ta yi sai ta faÉ—awa Seraph É—in.

Shi kuma ya fito da wayansa, yana fito da waya sai ga Faryan da Rimsha sun shigo shopping ɗin suma. Ai ba ƙaramin mamaki Aryan ya sha na ganinsu ba, yanzu ya zai yi?.

Yasan dole Rimsha zata haɗu da Seraphina, and yasan ƙaramin aikin Seraphina ce ta ce zata kawota ta gaisa da daddynta, dama jiya a wayan da suka yi ya ji Rimsha na ce mata ALLAH yasa daddynki ba mugu bane irin uncle Aryan, ya dakeni babu abin da na yi mashi, ba dan ina son family ɗin daddyna sosai ba da na gudu na bar gidan, kuma ba dan Abba ya ce daddyna ya fi son uncle Aryan a kan kowa ba da wlh na cewa uncle Aryan ALLAH ya isa ban yafe ba, wlh ba dan ina son uncle Aryan kamar yadda nike son daddyna ba da na yi sallah na roki ALLAH ya sakamun a kan abin da ya yi mun, amma ba zan iya yi mashi mugun fata ba, zan dinga yafe mashi kome ya mun dan ALLAH ya yafe mun nima, kuma ina kallonsa kaman daddyna, dan wlh yana kama da daddyn nawa sosai kamar an tsaga kara.

Yana jin Seraph ta amsa mata da. "Gaskiya uncle Aryan ɗin nan naki azzalumi ne, ni na ji ma na tsanesa, amma ba komai watarana shi ma zai yi aure ya haifi yara, za'a rama maki, ki kyalesa, kuma ki dinga addu'a, mammy ta ce wai idan ka faɗawa ALLAH damuwarka zai biya maka buƙata".

To tin da suka yi wannan hira yasan sai Seraph ta ce Rimsha ta zo ta ga uncle ɗinta ba bugu bane. Aikuwa ya zame mashi dole ya gudu. Miƙewa ya yi da sauri ya fice daga super market ɗin, ya tsaya can nesa da wajen yana kallon kofar shiga.

Aikuwa yadda ya yi hasashe ne, sun haÉ—u kuwa a wajen sayan underwears. Suna saki kara game da rungumar juna, sai dariya suke yi kamar wasu zararru, cike da mamaki Rimsha ta ce. "Dama a CP gidanku yake?"...... Seraphina ta ce. "Sunan wajen nan kenan CP?".

Kara rungumeta Rimsha ta yi tana amsa mata da e. Ai Faryan baya ya koma yana kallonsu cike da mamaki, sai dai kuma tin da ya kyalla ido ya ga Seraphina zuciyarsa ta amsa, a ransa yake jin ya samu irin kalar zaɓinsa.

Sai da suka gama rungume-rungumen junansu sannan Rimsha ta ce. "Uncle Faryan wannan ita ce Seraphina É—in da nike faÉ—a maka". Ta dawo da kallonta a kan Seraph. "My star lady ga uncle É—ina dake kaunata shi kaÉ—ai, wanda nike baki labari".

Seraphina tana É—agowa ta kallesa sai da ta ji faÉ—uwar gaba, domin kuwa jini ba karya ba, kamannin Aryan ta gani, har kamar zata ce daddy sai ta ga wannan bai kai Aryan tsawo da cika ba, da farko zata ce la mai kama da daddy, sai ta tina yadda suka yi da shi a kan hoto, dan haka sai ta fasa magana game da cewa. "Good evening Uncle Faryan".

A natse ya amsa mata, ai sai da ya yi magana ta kara tabbatar da kamannin, dan har voice É—insu yana shige. Daurewa ta yi bata nuna komai ba, ta ja Rimsha suka shiga cikin shopping, bayansu Faryan ya bi amma daga É—an nesa, daga karshe ya samu kujera ya zauna, dan ya lura yawonsu a cikin wajen nan ba zai kare ba.

Suna tsaka da yin shopping ne wani haÉ—aÉ—É—en guy ya tare masu gaba, matashi ne É—an kwalisa, yana sanye da wasu shaggun pop dress, gashin kansa sak na Noor É—inmu. Ba kowa bane kuma face uncle É—in Noor wannan uncle É—in nasa guda É—ayan.

Kallonsa suka yi, take suka É—aure fuska, Seraphina ta ce. "Are you out of your mind da zaka tare mun gaba?"..... ÆŠan lumshe idanu ya yi kafin ya ce. "Yadda kike haÉ—aÉ—É—iya haka voice É—inki ma yake, kin dagi zuciyata"...... Da alama dik family É—in su Noor muggan Æ´an love ne, family É—in su Abba kuma sun raba jaha da love, kuna ga yadda uncle É—in Noor yake neman sace zuciyar Princess Teema taku ta amana, ga ji salon soyayya mai ratsa zuciya.

Tsoro ne yakamasu, da sauri Rimsha ta ja hannunta suka raɓa gefensa suka wuce, juyawa ya yi ya bisu da kallo, a ransa ya ce. "Ta haɗu, ko zan salwantar da dik abin da na mallaka sai na mallaketa, ita ce na gani a view na benen kusa damu ranar, kyakkyawan tamkar Seraph". Bai san sunanta Seraphina ba, ma'anar Seraph yana nufin kyakkyawan gaske mai haske kamar malaika mafi haske, shiyasa ya ce tamkar Seraph take, bai san kuwa Seraphina take ba.

Da iya gaskiyarsa ya faÉ—a cewa ko zai rasa dik abin da ya mallaka sai ya mallaketa, kun kuwa san familyn Noor ba dai kuÉ—i ba, akwai gumurzu, da alama kuma É—an soyayya ne, zai yi saurin sace zuciyar mace, su IRON FIST kun san basu iya soyayya ba, da sauki gaskiya, gara ma Aryan É—in ya É—an fisu, to zamu dai ga yadda wasan zata kaya, ga uncle Faryan ma ya ga Æ´ar baby Cherry Bloom É—inmu ya kamu.

Kutsawa ciki suka yi, a tare suka yi shopping, komai iri É—aya suka dinga É—auka, sun lodi kaya sosai, Seraph ta ce Rimsha ta zo su je ta gaisa da daddy É—inta, aikuwa ta ce to. Sai dai suna zuwa basu gansa ba, sun turo uban kaya niki-niki a cikin shopping bike. Mamaki ne yakamata, sai ta fito da wayarta ta hau kiransa.

Bugu ɗaya ya ɗaga, a shagwaɓe ta ce. "Daddy ina ka je?"........ Nisawa ya yi kafin ya ce. "Kin gama ne?". Da e ta amsa mashi....... "Okey ki bar kayan a wajen ki fito ki koma gida zan zo maki da su da daddare, wani abin ne ya taso mun na tafi"....... Tana turo baki ta ce. "To daddy ga Rimsha na haɗu da ita, tana son ku gaisa".

"Cherry ina aiki, watarana zamu gaisa da ita, ki yi abin da na ce see you later". Daga nan ya katse kiran, tana neman kira mashi ruwa, idan ya haÉ—u da su Rimsha ina na ga bakin yi wa Abba bayanin in da ya samo yarinya har yake zuwa shopping da ita? Ai da matsala.

Ɗan shagwaɓe fuska ta yi, tana kallon Rimsha ta ce. "My sister daddy wai wani abin ne ya taso mashi ya tafi, ya ce in bar shopping nawa a wajen zai dawo ya biya in koma gida"........ Rimsha zata yi magana Faryan ya rigata da cewa. "Ba damuwa ku bada kayan a haɗa lissafi sai in biya dikka".

Da okey suka amsa, tare suka tura kayan suka karisa wajen machine da zai buga masu lissafi, babu kowa a wajen sai wani machine, cikin machine É—in suka buÉ—e suka zuba kayan, baya suka ja suka tsaya, ya gama lissafa kayan tas, ya zuba masu kowanne da kedarsa, su bra leda daban, pant ledar daban, haka ya yi siling komai ya fito masu da shi ta other door É—insa, ga kuÉ—in kuma ya rubuta a gaban screen É—insa.

Faryan ya matsa ya miƙa card ɗinsa ya manna da jikin payment side na machine ɗin. Su kuma suka kwashi kayansu suka hau rabawa, kowacce ta ɗauki nata. A tare suka fito.

Rimsha ta ce sai ta bi Seraphina ta ga gidansu, aikuwa Faryan ya goya mata baya dan shi ma yana ganin ya yi kamu zai so sanin gidansu, ita kuwa sai murna yake yi ta masu jagoranci dan tasan hanya. Ai dafe kai Aryan dake tsaye a gefe yana kallonsu ya yi, shikenan Seraphina tana neman kwanto mashi ruwa, tin da ya ganta tike da kaya niƙi-niƙi yasan Faryan ne ya biya masu kenan.

Dole ya fasa bin bayan Seraph ya koma gidan Lion, dan in ya bi bayanta za'a samu matsala, amma sai da ya tabbatar ta shiga gida kafin ya nufi gidan Lion É—in. ......... E kam nima na ce asirin wani ya kusa tonuwa, Rimsha a gidansu Seraphina, tab, ai gobema zata dawo tin da yanzu tasan suna waje guda, kai kam Aryan sunanka sorry.

-----------------------🔥

WS-HOSPITAL. 🧠 🫀🩸🔥

Tin daga wannan rana sister Lazy ta dinga ɓata aikinsu Zinta, sai ta hanasu submitting results ɗinsu, ta ƙala masu sharri wajen Dr James, shi kuwa ya aminta, ya dinga sanya minus a aiki har tsawon kwanaki 30, daga nan ya ce rainin hankalinsu ya yi yawa, yasan maganinsu, ya kuma san kalar wahalallen aikin da zai basu su yi replacing waɗan nan 30 days da suka yi missing basu bada rahoto ba.

Yau takama Monday, dikka nurses na asibitin kowanne yana bakin aikinsa, Maya da Zinta ma suna nasu bakin aiki.
Chapter 118 · 0% Book details