← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 171 OF 227

Sashe 171

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Take wuƙar ta fasa mashi tafin hannu dan bai sanya hand gloves ɗinsu na aiki ba, janye wuƙar baya mutumin ya yi, hakan yasa ta kara pasa tafin Zaynish. Kafin DOL su motsa sai ganin wasu jiga-jigan mutane huɗu suka yi sun bayyana kewaye da su, suna sanye da bakaken kaya na manyan ɓarayi, suna wani irin haki, da alama gudu sosai suka yi kafin su cim masu.

Siririn tsaki Noor ya ja tare da cewa. "Ku zo da wuri mu baku a jikinku muna son komawa kafin gari ya waye"....... Zazzare wuƙaƙen hannunsu mutanen suka yi, miƙawa Vash igiyar karen hannunsa Zaynish ya yi, ya sanya hannu ya tsaga rigar jikinsa gida biyu, ya ɗaure hannunsa dake zubar da jini, har lokacin haske wata tamkar kamar rana yana haskasu.

Komawa baya Vash ya yi ya jingina da jikin wani ƙaton dutse dake wajen, ya barwa mazajen AZURE filin su fafata shi kuma ya rike karnuka. Haɗe bayansu Zaynish, Noor and Leo suka yi suna kallon mutanen.

Kansu mutane suka yi da wuƙaƙen, hakan yasa suka dare suka rabu. Wani irin faɗa suka fara gwabzawa na nuna banbanci kwarewa, sai dai sun yi mamaki ganin mutanen sun iya faɗa irin wanda ake koyawa sojoji.

Mutane su huɗu, su kuma su uku haka suka fara gwabzawa. A tare mutane biyu suka yi kan Noor shi kaɗai, kaucewa wuƙar da suke ƙoƙarin caka mashi ya fara yi, while shi kuma Leo ya kwace wuƙar nasa mutumin ya jefar, sun fara faɗar hannu, wani punch Leo ya kai mashi a bayan kunne wanda yasa ya yi baya-baya ya faɗi ƙasa.

Ganin ya faɗi ne yasa ya daka tsalle, ya taka wani dutse dake kusa da Vash, ya ƙara tsalle game da juyawa ya daki ɗaya daga cikin masu kawowa Noor hari da wuƙa, a wuya ya dakesa da ƙafansa, sai ga mutumin ya faɗi ƙasa. Dafa shoulder ɗin Leo Noor ya yi, ya daka tsalle ya taƙa ɗayan mutumin a fuska da waɗan nan shaggun tauraran takalman nasu, baya-baya ya yi ya faɗi ƙasa.

Dafe shoulder ɗin Noor Leo ma ya yi, ya daka tsalle tare da juyawa ya taka mutuminsa da ya taso yanzu yake ƙoƙarin nufosu, watau ya farfaɗo daga punch da ya sha...... Da karfi Leo ya riko waish ɗin Noor tare da ɗaga shi sama, Noor ɗin ya ware kafarsa ɗaya ya kaiwa mutumin da suke faɗa da Zaynish duka a gefen wuya, wannan duka ɗaya ba tashi Noor yai mashi, dan wannan shegen takalman nasu ya daki maƙogwaron mutumin wanda yasa ƙashin wajen ta ɓalle, kun san takalmansun nan ba karamar taurice da ita ba.

Zaynish bai iya faÉ—a da mutumin sosai bane saboda yankar da suka mashi a hannu, so da hannu É—aya yake faÉ—a shiyasa Leo ya taimaka mashi ta hanyar É—aga Noor ya daki mutumin.

Yana sauke Noor ɗin ya yi tsale ya yi backtorn ya taka ɗayan mutumin da ya taso yanzu a kai sai da ya koma ya zube a ƙasa. Tsalle Noor ya yi ya taka tsakiyar bayan Leo dake duƙe, ya ware kafafunsa ya daki guy da ya sake miƙewa a ciki, hakan yasa guy ɗin ya sake komawa ƙasa, ya durƙusa kan gwiwinsa yana nishi sama-sama tamkar yana son sumewa ne.

Dirowa ƙasa Noor ya yi, yana dirowa Leo ya miƙe tare da dafa shoulder ɗin Noor ɗin, ya daka tsalle tare da ware kafafunsa ya sake kaiwa guy ɗin dake durkushen wani mugun duka a gefen wuya da kafarsa, hakan yasa guy ɗin yanke jiki ya faɗi baya numfashi.

Dirowa ƙasa Leo ya yi tare da fara karkaɗe hannunsa alamar sun gama da su dikka........ Vash ne ya cire bindigar dake wajensa yana faɗin. "Dik ku kashesu, ba za'a rasa mai sauran numfashi a cikinsu ba"........ Hannu Leo ya ɗaga masu game da cewa. "Ku kamasu mu koma da su sansani, ina zargin ta yadda aka yi suka iy faɗar sojoji, lallai ba ƴan ta'adda bane kawai!".

Noor dake haki kaÉ—an-kaÉ—an ne ya ce. "Ina zargin navy ne!"...... A natse Zaynish ya amsa da. "Tabbas na zargi hakan nima"....... Vash ya ce. "Okey kenan Navy sun san da zaman filin da muka je yau kenan?".

Leo dake ƙoƙarin zare belt na wandonsa ne ya amsa da. "Suna da sani mana, sun san komai, kawai sun mayar da kansu karnukan farautar manyan Avaris ne shiyasa basa ɗaukar mataki"..... Zaynish ya ce. "Okey, watau sun ga shigarmu wajen?"...... Kai Leo ya jinjina alamar yeah sun gani. Cike da takaici Zaysh ya ce. "Okey, Navy na gadin ɓarnar manya ƙasa ba wai su dakatar da ɓarnar ba, watau masu gadinsu suka mayar da jami'an?".

Jinjina kai Leo ya yi alamar kwarai kuwa. "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, ina ake son Æ´an Avaris su sanya ransu? A hukuma azzalumai, a shuwagabannin azzalumai, a makaranta azzalumai, a kasuwa azzalumai, a asibiti azzalumai, a koina azzalumai, ina suke son jama'a su sanya ransu? Wa suke son su kaiwa kukansu ya tsaya masu?"..

A taƙaice Leo ya ce. "ALLAH, shi kaɗai zasu kaiwa kukansu kawai, amma basu da wata mafita, a ko'ina akwai gurɓatattu"....... Vash ya ce. "Basa tsoron mutuwa"........ Zaynish ya ja dogon tsaki game da cewa. "Sun manta akwai mutuwar ne ai, sun manta akwai ranar da zasu tsaya gaban ALLAH su zayyana dik abin da suka aikata".

Noor dake ƙoƙarin haɗe guys ɗin can ya ɗauresu da belt ɗinsa da ya kwance ne ya ce. "Ni fa ina son addinin nan naku, saboda naga akwai adalci sosai a cikinsa, kome zaku faɗa bisa adalci kuke faɗa".

Ai da sauri Leo ya ce. "Are you sure kana son shiga?"....... Kai ya gyaɗa a lokacin da yake ɗago guys ɗin ya saɓa a saman shoulder ɗinsa. "Ina son shiga, bro kyawawan halayenku sun ratsa zuciyata, ibadarku, komai naku akwai kyau, ina son shiga"........ Da sauri Zaynish ya ce. "A'a to sauƙe waɗan nan mutane ka karɓi shahada yanzu".

Jinjina kai Leo ya yi tare da sauƙe mutumin da ya ɗauka a ƙasa, ya zo ya rungumi Noor yana faɗin. "Ba zamu iya jiran sai mun isa sansani ba, yanzu kawai ka furta shahada"..

Ba karamin daɗi Noor ya ji ba ganin suna ta murna dan zai shiga addininsu, aikuwa hakan ya ƙara mashi kwarin gwiwa, sai ya sauƙe mutanen, Leo da Zaynish har suna haɗa baki wajen karanto mashi shahada, ya maimaita, ya ALLAH, su kaɗai suka san irin daɗin dake ransu, rurrungumesa suka yi, Vash mai karnuka ma zuwa ya yi zai rungumesa Noor ya ja da baya yana faɗin. "Bro, ba da dogs ɗin nan ba, ka bari sai mun koma sansani ka".

Murmushi Vash ya saki yana ja da baya. ALLAHU AKBAR, yau Noor É—inmu ya zama musulmi, ya rabb, yau ranar murnace a garemu mu team NOOR.

Haka suka kwashi mutanen, a lokacin 5 na asuba ta yi, gari ya fara haske, kai tsaye suka ƙarisa wajen sansaninsu, cikin dabara suka shiga sansanin, in baku manta ba ai fitar sirri suka yi, kai tsaye tantinsa Leo ya ce su kai mutanen, already biyu daga cikinsu sun mutu, ɗaurin goro yai masu ya barsu a ciki.

Ya fito da sauri ya nufi wajen tekun nan dan ya yi wanka su yi shirin sallar asuba, lokaci ya yi, while a daidai lokacin ita ma Arya ta fito dan ta je ta yi wanka, ita tana son yin wanka a lokacin da jama'a suke barci, dan yana son shiga gefen tekun nan wajen ƙorama ta yi wankarta, bata son shiga toilet ɗinsu na nan sansani.

Zuciyarta cike da tinanin su Leo basu dawo ba, dan ita tasan basa nan, ta damu sosai, kai tsaye cikin tabkin wajen ƙoramar ta nufa, hannunta rike da soap ɗinta and gel, ta ratayo towel ɗinta a wuya, while tana sanye da pjs a jikinsa, su V dik suna barci, saura sojojin wasu suna wajen wutar da suka hura, wasu kuma suna cikin tantunansu.

Da yake wajen akwai duhu saboda duwatsun ƙoramun, sannan gari bai waye sosai ba, dan 5:20 ne a yanzu, so hakan yasa bata ga Leo ya cikin ruwan ba. A saman wata karamar dutse ta tsaya, ya cire pjs ɗin jikinta kaf, ta ware dogon silky ash hair ɗinta da ya kai mata har ƙugu, ya rage daga ita sai wani ƙaramin vest zuwa cibiya wanda bashi da hannu, daga ƙasa pant fari tas mai kyau.

Zama ta ya bakin dutsen tare da sanya dogon kafarta dake É—aure da diamond chain mai kyau a cikin ruwan, ita tana saka chain da waist beat dan kwalliya, amma su V basa sakawa. Ajiye kayanta da towel É—in a saman dutsen ta yi, ta ajiye su gel É—inta ma.

ÆŠan rintse idanu ta yi tana faÉ—in shiiii alamar ruwan da sanyi, sai kuma ta É—an ja tsaki game da cewa. "Ko ina su sir Nirash suke? Sun samu nasarar abin da suka je nema? Ina masu fatan cin nasara". Ta sake jan tsaki tare da datse idanunta, da sauri ta faÉ—a cikin ruwa tana faÉ—in shiii sanyi.

Dik abin da take yi a kan idanun Leo, amma ita bata farga yana cikin ruwan ba, da yake yana can tsakiya. Linƙaya ta fara yi yana juyi a ciki tana jin daɗin ruwan............ Nima na juya alƙalamina dan ba'a kansu kawai zan ƙare page ɗin ba, zamu dawo anjuma mu ga ya zasu kaya a cikin ruwan nan, ga Noor ya musulunta, Zaynish da yankar wuƙa a hannu, ga haɗaɗɗun karnuka guda biyu da muka samu, ga waɗan nan miyagun da muka kama, kai ga-ga ɗin ma yawa me da shi fa. Bari dai mu je mu dawo.

--------------------------🔥
CRYSTAL PALACE.

"Daddy please talk to me, baka da lafiya ne?". Tamkar zata yi kuka ta yi maganar. Hannunsa yasa ya laluɓo nata hannun, ya ƙanƙame cikin nasa, can ƙasan maƙoshi ya ce. "Stop crying kada abin ya mun yawa kin ji my Cherry?".
Chapter 171 · 0% Book details