← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 227

Sashe 55

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ke fa to?". Rimsha ta tambaya. "WaÉ—an da ya kawo mun last two weeks ma kinga basu kare ba, kawai wannan zan baku ne"........ Hannu Rimsha ta sanya ta É—auki guda biyu ta bar saura kwali huÉ—u, dama shidda ne..... "Daddyn nan naki yana sonki sosai". Cewar Rimsha. Uhm kawai ta ce tare da kwasan saura ta baiwa su Aana, daga nan ta koma gefen bed É—inta ta zauna tare da fito da littafanta zata fara karatu.

----------------------------🔥

To ku zo mu bi kowani jami'i daga cikin matasan jami'an mu zuwa gidansu mu ga ya suka isa ne? Ya rayuwarsu a gida bayan horo kafin su koma barrack. DaÉ—in abin ma dai dukkansu a Crystal Palace suke except Zaynish, dan haka haÉ—a kayanmu zamu yi, zaman Crystal Palace yakamamu, dole in kama mana gida É—aya haya dani daku masu karatu, kumu je mu bararraje a can, hawa gomar dik zan kama mana, kowacce ta zo mu haÉ—u ai an zama dangi, to na yi gaba sai kun zo.

CRYSTAL PALACE.

MUHAMMAD KHAIZA'AN'S HOUSE. Idan baku fahimta ba gidansu Vash kenan. Gida ne mai É—auke da family guda bakwai, Muhammad Khaiza'an da matarsa, Æ´aÆ´ansa maza guda uku, Faryan, Dr Aryan da ya je É—aukar Vash a barrack, sai Harleen, sai Vash da Rimsha. Vash mahaifinsa shi ne babban yayansu Dr Aryan, ya rasu ne, mai bi mashi shi ne mahaifin Rimsha wanda momyn Rimsha ta yi breaking heart É—insa ya rasu.

Nasan yanzu kun gane karatun, da Vash da Rimsha ƴaƴan wa da ƙani ne, mugun Uncle ɗinta da kuke ji tana ambatar nan ba kowa bane face Aryan, ya tsaneta saboda ya fi kowa shaƙuwa da daddynta kafin mom ɗinta ta shiga rayuwansu ta rabasu da shi na har abada. A dalilin rasa mahaifin Rimsha yasa Muhammad Khaiza'an ya karfafa dokar haramta soyayya a zuri'arsa, dama can ya haramta auren soyayya, a dokarsa sai dai shi ya zaɓa maka mata, a cewarsa auren soyayya dik yaudara ce, dik yadda aka yi a lokacin samartakansa an taɓa yaudaransa.

Haka yaransa suka tashi basama soyayya, mahaifin Vash da Mahaifiyarsa ba auren soyayya suka yi ba, Abba Muhammad Khaiza'an ne ya haÉ—a auren, kuma suka zauna lafiya har ALLAH ya basu Vash, sun koma ga ALLAH sanadin haÉ—arin jirgin sama da ya yi sanadin rayuka da dama. Shi mahaifin Rimsha bijirewa mahaifinsa ya yi, suka kullah soyayya da mahaifiyarta tin a school, ya kafe lallai shi ita zai aura, ba yadda Abbansa bai yi ba, ya ce wlh idan ba ita ba kashe kansa zai yi, cikin fushi Abba ya amsa da ya je ya aureta amma shi babu ruwansa, kuma ba shi zai nema mashi aure ba.

Sai da su Arya suka dinga rokansa, sannan ya hakura ya nema mashi aurenta, daga karshe dai ta ci amanarsa, ta haifi Rimsha tana jaririya ta ajiye mashi ita ta tafi bayan ta kwashe mashi makudan kuɗaɗe, ko shayar da yarinyar bata yi ba, Abba ya yi takaicin hakan, ya dinga faɗa, a lokacin kuma daddyn Rimsha ya yake jiki ya faɗi yana faɗin shi a kira mashi matarsa, har lokacin bai daina kukan sonta ba, daga nan Abba ya ce ko bayan ransa bai yafe ƴaƴansa su yi auren soyayya ba, wai sai auren haɗi, ya zaɓa maka da kansa, ya aura maka a kawo maka ita ɗaki kawai!

A taƙaice dai soyayya haramunce ga ahalin Muhammad Khaiza'an...... Kun san me mutane na? Wani diraman da za'a buga a cikin wannan ahali ba? Uhm sai shiru kawai, ku dai mu je ciki, ahalin haramta soyayya kenan, ko ya za'a kaya? Ga su dai da zaratan maza, su Vash da auren haɗi, jama'a you will love this part and laugh over.

Zaune Faryan and Harleen suke a parlo, kowannensu danna wayansa yake yi, matasa ne da basu rufe 30 years ba, yayansu Aryan shi ne mai 32 years. Sun yi nisa cikin abin da suke yi sai ga Rimsha ta sauƙo daga upstair, sanye take da silky pj's a jikinta, a lokacin da su Vash suka dawo daga horo Rimsha tana gida kenan, sun dawo hutu suma, kada ku manta a ɓangaren rayuwarsu a makaranta da rayuwarsu Lion na koma baya ne dan in faɗa maku yadda suka rayu, dan haka iya rayuwarsu ta makaranta ce muke baya, bana son ku rikice shiyasa na sake yi maku bayani!.

Ganin su Harleen a parlo yasa ta sha jinin jikinta, ta fasa zama tare da juyawa zata koma sama. A natse Faryan ya ce. "Rimsha lafiya zaki koma?"...... Idanunta a kan Harleen, muryanta na rawa ta ce. "Babu komai uncle"........ "Zo nan". Ya faÉ—a yana mata alama da hannu. In baku manta ba dama na faÉ—a maku uncle É—inta Faryan ne kawai yake sonta.

Jikinta na ɗan kerma ta karisa sauƙowa ta nufosu...... "Don't come here!". Muryan Harleen a kaifafe ya daki dodan kunnenta. Da sauri ta kalli Faryan da ya kirata, narai-narai da ido ta yi tamkar zata yi kuka. Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa. "Zo abinki, rabu da uncle Harleen ɗin nan da mugun halinsa".

Gagara motsawa ta yi, dan tana tsoronsa sosai, a gidan daga Aryan a waɗan da take tsananin tsoro sai Harleen. A daidai lokacin wani dattijo ya sauƙo ƙasan, irin dattawa masu kwarin nan ne, da karfinsa, yana rike da wata sanda mai kama dana mulki yana ɗan dogarawa, kafarsa ɗaya a ɗan karkace ne, karaya har biyu ya taɓa samu a ƙafa shiyasa yake ɗan ɗingisa kafar yake kuma yawo da sanda.

Hannunsa rike da wani littafi mai suna The Franklin scandal yana karantawa. Hannun Rimsha ya kama tare da nufar su Harleen, kun san da cewa shi ma a farko ya ki Rimsha? Ya ce sai dai a kaita gidan marayu, dan wlh Abba yana da mugun zafin zuciya, sai da Ammie ta dinga lallaɓasa, kun san uwa, ba zata so jinin ɗanta ya walaƙanta ba, ta dinga bashi hakuri tana tuna mashi faɗar ALLAH da yake cewa laifin wani baya shafar wani, sannan ne ya aminta ya yafe ya kuma rike Rimsha, da gidan marayu zai kaita.

A saman sofa kusa da Harleen ya zauna yana faɗin. "Harleen wai ba zaka daina takurawa jikata a gidan nan ba ko?"......... Shiru Harleen bai yi magana ba, sai ma yunkurawa da ya yi zai miƙe ya bar wajen kenan suka ji alamar motsin buɗe kofa. Dikkansu kai kallonsu wajen suka yi.

A natse Aryan ya shigo cikin parlon bakinsa a ɗauke da sallama, daga ɓangarensa ya fito, fuskan nan tasa tamkar hadari, a ɗaure tamau. Ai Rimsha na ganinsa ta watsa da gudu ta yi sama, dan ta san shi ko Abba baya iya dakatar da shi a kan tsanar ganinta da ya yi, a kan ya ja mata bala'i ya karyata gara mata ta gudu ai. Tana haurawa sama suka ci karo da Vash da ya tashi barci a yanzu, jiya basu taso da wuri ba sai mangrib suka baro AZURE, cikin dare suka iso, shi ne yake ta barcin gajiya, tin da ya yi sallar asuba ya mai da barci sai yanzu ya farka.

Tsawa ya daka mata game da cewa. "Baki da hankali ne kike yi wa mutane gudu a cikin gida haka?". Kara shiga tashin hankali ta yi, sai kawai ta fashe da kuma mai tsuma zuciya. Abinku da soja, to shi da zuciyarsa kamar dutse ina zata tsumu? Wani tsawan ya sake daka mata kan ta wuce ta bashi waje ko ya yi ball da ita. Ai tin bai gama rufe baki ba ta wuce da gudun gaske ta nufi room É—inta.

Siririn tsaki ya ja tare da wucewa ya sauƙo ƙasa cikin zafin nama....... Jama'a a irin wannan gida ta ya za'ayi Rimsha ba zata fi son zaman school ba?.

Saman gadonta ta faÉ—a tare da fashewa da wani kukan mai tsuma zuciya, tana jin tsanar kanta na ratsata, sai ta ji yau dai ta tsani mom É—inta da ta ja mata wannan tsana, ita me laifinta. Cikin kuka ta ce. "Ni me laifina? Me na yi maku? Ni É—aya nike da mom ne?".

Daga bakin kofa Faryan ya amsa da. "Baki da laifin komai Rimsha, kuma ba ɗaya kuke da ita ba, kawai zafin zuciya ce da riko irin nasu Yah Aryan, amma ki kara hakuri everything is nearing its end". Ya faɗa tare da shigowa ciki. A gefen bed ɗin ya zauna, da sauri ta tashi ta faɗo jikinsa tana rirriƙesa tare da fashewa da sabon kuka, cikin kuka take faɗin. "Uncle kai da Abba and Ammie ne kawai masu tausayi a gidan nan, su uncle Aryan har Yah Vash basu da tausayi, kowa baya sona, shi ma Yah Vash ba kamar da ba, a baya idan ina kuka yana rarrashina, amma yanzu sai faɗa da tsawa, haka da asuba da na bugesa ban sani ba kamar zai dokeni.......". Kukan da ya ci karfinta ne yasa ta dakata da yin maganar.

Cikin tausasawa ya ce. "Vash yanzu ya zama soja, dik wani sanyin halinsa ya tafi, sai kin yi hakuri da shi kin ji? Su Yah Aryan kuma watarana zasu gane baki da laifi su daina kyararki".

Cigaba da kukanta ta yi bata sake yin magana ba, dan jin zuciyarta take yi tamkar zai fashe ne.

A can parlo kuwa, Abba ne ya ce. "Aryan zo nan". Ba musu ya je ya zauna kusa da Abba, shi kansa Abban shakkar yi mashi magana a kan Rimsha yake yi, saboda ya san zuciyar Aryan shi ya gado, ga balain kafiya kamar kafurin farko, tin da ya furta ya tsani Rimsha fa dole su yi hakuri kawai su kyalesa, in ya juya baya juyuwa ne.

"Ina son ka kaini asibiti anjuma a duba mun karafunan dake kafata É—in nan, dan na fara jin canji". Abba ya faÉ—a ba wai dan hakan ya so faÉ—a ba, so yake yi ya taushesa ya ce ya rage tsanar Rimsha, amma kwarjinin É—an nasa yasa ya canza maganar.

STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥

ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️
🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥

PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.

https://www.facebook.com/share/g/1EUXbqsDjP

STEP 1________🔥

2025-11-17.🔥

FIVE LIONS, FIVE MISSIONS, ACTION, DEATH OR LIFE, ADVENTURE, BRAIN GAMES, REDRESS, A BREATHTAKING LOVE THAT STEALS THE HEART AWAY.♥️🔥
Chapter 55 · 0% Book details