Sashe 210
Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Yanzu in ce gidansa za'a kaiki ko?"...... Kai ta ɗan jinjina kafin ta ce. "Abba ya ce ya ɗaukeni ya mayar dani gidansa, ban sani ba ko zai mayar dani"..... "Good". Seraphina ta faɗa kafin ta ce. "Ina fatan ya mayar dake gidansa, sis zamu yi nasara, tabbas uncle sai ya zama namu, trust me, zaki mallaki zuciyansa ko yaki ko ya so, ki shirya faɗa domin samawa kanki ƴanci, ki ganki mana, mace kyakkyawa, ga diri, ga komai, tabbas zaki iya samun zuciyansa cikin ƙanƙanin lokaci". With her full confidence ta faɗa.
Shiru Rimsha ta ɗan yi, sai take jin tamkar zata iya, sai take ganin kamar zata iya kallon face ɗinsa yanzu, zata iya yi mashi magana, bata taɓa yi mashi magana ba, bata taɓa kallon fuskansa da kyau ba, sai dai a sace ta window take kallonsa, ko in baya ganinta, magana wannan baya haɗasu, tsoronsa da take ji ya zarce yadda kuke tinani, amma yanzu tana jin kamar zata iya kiran sunansa a gabansa ta mashi magana, kalaman Seraphins sun ɗan shiga kanta sun hura mata kai.
Seraphina kuwa ta dage sai bata shawari take yi, ta dinga tunatar da ita littafin da suka karanta, yadda ake sace zuciyan namiji, dik Rimsha ta san komai, amma tsoron Aryan yasa ta mance komai. Sosai yau Seraphina ta sanyata gaba da shawari masu harfin da tasa ta fara jin kamar zata iya samun kan Aryan.
Sun jima suna hira har kusan mangrib, sannan suka sauƙo suka yi lunch a tare, suna kammala cin abincin sai ga message ɗin Aryan na cewa. "Yanzu ki dawo gida ina jiranki"....... Ai take hankalinta ya koma can, bare ma da ya ce yana jiranta, dik sai ta ji tana son ganin kanta a gida.
A gurguje ta miƙe tana sanar da Rimsha daddynta na jiranta, basu so rabuwa ba, amma haka suka hakura, Rimsha ta rakota main parlo tana cigaba da mata magiyar ta ɗan kara ko awa ɗaya mana, Seraphina ta ce. "My sis idan daddy ya yi kira zuciyata bata iya jira har sai na je na gansa, yana fa gida yana jirana, ki bari gobe ai zamu haɗe a school".
Dukan wasa Rimsha ta kai mata a baya tana faɗin. "Mara kunya, kalleta a wajen, ko kunyata baki ji kike rawan jiki kansa, wai ni me kika yi wa daddyn nan ne da ya mutu a kanki haka? Kullum yana gida tare dake". Cikin zolaya ta yi maganar tana murmushin da ya jima irinsa bai samu gurbi a zuciyata ba..... "Ai daddy ban yi mashi komai bama tukun nan, kin san yana taka mun burki, yana ɗan hanani wai sai mun yi aure, kin san me?". Ta faɗa tare da tsayawa a tsakiyar staircase na sauƙowa ƙasa.
Kai Rimsha ta girgiza alamar a'a bata sani ba. Cigaba Seraphina ta yi da cewa. "Daddy yana hanani nuna mashi love mai kyau sosai, ya ce sai mun yi aure, idan muka yi aure ko, daddy ba zai yarda ko waje ne ya fita ba, kullum zai zama yana gida manne dani, zan narka zuciyansa da soyayya"........ Shiru Rimsha ta É—an yi, a cikin ranta ta ce ina ma ace ta samu mai sonta sosai, wanda take so sosai ita ma, wanda zata zautar da shi da wannan tarin soyayya da ta iya, ta narka zuciyansa da kaunarta, ta mallaka mashi kanta. Nisawa ta É—an yi kafin ta ce. "ALLAH ya nuna mun aurenki da wannan daddyn dai kowa ya huta tin da kinki uncle Faryan É—ina, nima ki tayani da addu'ar ALLAH yasa uncle Aryan ya sakeni in samu wanda yake sona nike son shi, wanda zan zuba mashi dik wata soyayya da na iya, in zautar da shi da kaunata". Tamkar zata sa kuka ta kai karshen maganar
Dafa shoulder ɗinta Seraphina ta yi. "In Sha ALLAH my sister da uncle Aryan ɗinki zaki yi dik wannan kamar yadda nima da daddyna zan yi hakan, uncle Aryan zai soki, zai ƙaunaceki, zai zauce a kanki kamar yadda daddy ya mun, ki ɗauki shawarina da na baki please, zamu dace".
Kai kawai Rimsha ta jinjina, ita kaɗai tasan me a ranta, ita kaɗai tasan waye Aryan. Hannunta Seraphina ta ja tana faɗin. "Zo mu je ki rakani ni kam, daddy na jirana". Ta jata suka sauƙo ƙasa. Babu kowa a parlo sai Abba dake zaune saman sofa yana rike da sandarsa.
Cikin girmamawa Seraphina ta ce. "Abba zan koma"........ Kai ya jinjina mata. "Okey ki gaida gida sai na zo, ki faÉ—awa iyayenki fa ina nan zuwa mu gaisa".
Da okey ta amsa mashi, har zata fita ya kirata, kyautar wani kyakkyawan zobe ya bata yana faɗin. "First gift from your father in-law"........... Ni kam na ce Abba ya faɗi daidai, aikuwa shi father in-law ɗinta ne amma ta ɓangaren daddy Aryan namu ba.
Karɓa ta yi, diamond ring ne mai bala'in tsada, ta ji daɗi, a tsakiyar yatsanta ta sanya tana mashi godiya, yana kallonta ya ce. "Kin dace da ɗana sosai"..... Ita kam murmushi kawai ta yi game da wucewa tana kara yi mashi godiya.
A kofar parlo Rimsha ta tsaya suka ƙara yin sallama, sannan ta koma ciki Seraphina ya wuce, ko da ta dawo cikin parlo Abba baya nan, ta wuce room ɗinsa dan shirin zuwa masallaci. Sama ta haura ta nufi ɗakinta dan yin wanka ta yi sallar magrib
Benensu kai tsaye Seraphina ta wuce tana sauri sosai. Tana shigowa ta isko Madam a parlo. Oyoyo ta yi wa Madam game da zuwa ta rungumeta tana murmushi. Murmushi Madam ma ta yi tana faɗin. "An dawo?". Kai ta jinjina alamar kafin ta sake Madam ta miƙe da sauri ta nufi ɗaki tana faɗin. "Daddy na jirana".
Da kallo Madam ta bita tana murmushi. Tsayawa ta yi a kofar É—akin ta yi sallama saboda ya hanata shigowa babu sallama dik da take ba musulma ba. Bata jira ya amsa ba ta faÉ—o cikin É—akin.
Yana kwance a kan gado yana waya da guru dake ce mashi ya yi maza ya zo su yi shirin zuwa masallaci, shi kuwa ya ce yana É—akin matarsa idan guru ya isa ya zo ya fito da shi.
Da gudu ta haye gadon tana faɗin. "Na yi missing ɗinka over my gentle chaos". Ta faɗa game da manna mashi sumbata a cheek ɗinsa. Zuba mata idanu ya yi ya kasa ɗaukewa, yaga ta ƙara kyau sosai ne.
"Daddy na maka kyau sosai ne da kake kallona haka?"...... Shiru bai amsa mata ba. Hakan yasa ta sake cewa. "Ni fa taka ce, ka kalleni da kyau ka sake kallo, kayanka kake kallo, mallakinka ne". A shagwaɓe sosai ta faɗa.... Shi kam ya rasa waye yake koyawa Seraphina manyance da iya magana, dik ta gama goge mashi hadda.
Dik abin da take faɗe guru na jinta, dik sai ya ji wani iri, a ransa ya ce. "A dole a gidan nan su dinga rasa natsuwar Champion ɗinsu, ashe dole dik after 1 hour ya gudu wajenta, irin wannan shagwaɓa mai narka zuciya da kalamai masu zafin nan, ai komai taurin zuciyarka sai ta narka maka shi, ka ji wani irin shagwaɓa mai melting heart, ya rabb, gaskiya nima ina buƙatar irin wannan kulawa da soyayyar, wai tayi kewansa over"........ Ni kam na ce to malam guru irin wannan kula da soyayar dai a waje ɗaya ake samunsa, a wajen mace kawai zaka iya samunsa, matan da kuke cewa basu da amfani, to dik duniya macece kawai zata yi maka irin wannan soyayya da kulawar, yauwa gara ma ka dawo cikin hankalinka, ko ya kuka ce jama'a?.
Zare wayar daga kunnensa Aryan ya yi, a daidai lokacin take cewa Aryan. "Daddy yau naga soft lips ɗinka ya ciza red sosai, kamar in yi kissing ɗinsa fa". Tana murmushi mai kwantar da hankali ga shagwaɓa, ko kunyansa bata ji kwata-kwata, ta tsaresa da waɗan nan dara-daran violet eyes ɗin nata tana wani turo baki.
Katse kiran ya yi game da dallah mata harara kafin ya ce. "Ban ce ki dawo da wuri ba? Me ya sanya kika je kika yi zamanki a can?". Yana ɗaure fuska sosai ya faɗa, sai kuma ya miƙe zaune yana kallonta.
Ɗan turo baki ta yi, ganin babu alamar wasa a tattare da shi ne yasa ta sauƙo ƙasan bed ɗin, a gabansa daidai in da ya sauke fararen kafafunsa ta tsugguna, hannayensa ta riko cikin nata, cikin girmamawa da sanyin murya ta ce. "Ka yi hakuri daddy, ba zan sake ba, hira ce ta yi daɗi yasa na manta ka ce in dawo da wuri".
Ai gabaɗaya ta narka zuciyansa, ga girmamawa, ga soyayya kuma ga shagwaɓa, sai ya rasa me zai ce mata ma, ya tsareta da ido kawai, yana mata wani irin musulmin kallo mai narka zuciya.
"Please my whisper baby ka yi magana mana, na ce na zan sake ba, first and last i promise, ka ji nawan?". Tana turo baki ta faÉ—a, bata san dik ta rufe mashi baki ya rasa abin faÉ—e bane.
Wani irin musulmin ajiyar zuciya ya sauke game da riko hannayenta da ta kama nasa hannun da su. Ya ɗan matsa ƴan yatsunta cikin tafukansa har sai da ta ce wash......... Cikin wani irin low voice ya ce. "Komai zafin da na ɗauka sai dai in ban zo wajenki ba, komai ɓacin ran da nike ciki sai dai in ban haɗu dake ba, dik gudu suke yi, my cherry, kin san dik wata hanya da zaki bi dan ki faranta mun, nima yau zan sanyaki farinciki na musamman, jeki shirya, kada ki ci komai, yi wanka kawai ki shirya bari in yi sallar magrib da ishai ina zuwa in baki wata bazata".
Haɗaɗɗen murmushi ta sakar mashi game da miƙewa tana faɗin. "Thank you so much my gentle chaos". Ta faɗa zata wuce. Miƙewa ya yi rike da hannayenta, ya ɗan kura mata idanu kafin ya ɗan rage tsawonsa, ya ɗan sumbaci gaban goshinta kafin ya saki hannayenta. Suna bin juna da kallon kauna ya wuce ya nufi benensu dan ana gab da kiran sallar mangrib. Yana fita ita kuma ta faɗa toilet cike da begensa da sabon soyayyansa.
A tinaninku bazatan me zai bata?.
----------------------
IRON FIST.