← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 227

Sashe 97

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɗan ɗaure fuska ya yi, zai sake yin magana Lion ya yi saurin girgiza mashi kai alamar a'a, dan haka sai ya yi shiru, daga karshe Lion ya ce ya amsa da okey kawai, da hakan ya amsa suka yi sallama da Abba. Yana ajiye wayar Lion ya ce. "Uba wani bango ne da in babu shi babu zuri'a, ba'a ja da iyaye ayi nasara, ko nan gaba kada ka kuskura ka yi ƙoƙarin ja da maganansa, and okey zata rabaka da kowa lafiya"...... A duniya Lion yana kaunar daddynsa, yanzu haka maganar mahaifi da ya yi sai da idanunsa suka kaɗa suka yi ja, shi kaɗai yasan me yake ji a cikin ransa, ga Hoosainin daddyn nasa da ya renesa ma babu shi, wlh ba dan yana da karfin imani ba da ya jima da kauce hanya, dan dai tin da ya taso kalma ɗaya mahaifinsa yake yawan faɗa mashi shi ne dik wuya kada ya kuskura ya sauƙa daga turban koyarwa fiyayen halitta, mahaifinsa da second dad ɗinsa watau Hoosainin mahaifinsa sun jajirce wajen gina rayuwansa a kan turban musulunci, idan ya tina zai yi wani abin in ya tina tarihin Annabi Musa, Annabi Dawud, Annabi Isma'il, Annabi Isa, Annabi Nuhu, Annabi Muhammad (SAW) waɗan nan Annabawa tarihinsu daban yake, in ya tinasu sai ya fasa, dik wani gwagwarmayar da kake tinani ka sha a rayuwa to ko rabinsu ba ka kai ba. Annabi Nuhu ya fi dikkan Annabawa shan wahala a duniya, shekaru 950 ya yi yana wa'azi wa mutanensa, amma dik da haka suka ki musulunta, dik hakuri irin na Annabawa sai da Annabi Nuhu ya yi fushi ya roki ALLAH da ya halaka mutanensa, ALLAH ya ce ka kyara jirgin ruwan da zaka ɗauki ƙalilan ɗin mutanen da suka bika, saura zasu hallaka, imagine hakurin Annabi Nuhu, shekaru ɗari tara da hamsin yana masu wa'azi, amma daga karshe ma ce mashi suka yi mahaukaci ne bashi da hankali. Daga Annabi Nuhu sai Annabi Musa, ya sha wahala, ya azabtu kafin ya samu ya kwato mutanensa banu Isra'ila daga hannun mutanen Masar watau fir'auna, ya sha azaba bawan ALLAH nan, suka sha da kyar, suka tsallaka teku, amma me ya biyo baya? Yana cetansu daga azaba me suka ce mashi? Annabi Musa ya zo ya samesu suna sassaƙa gumaka, ya ce ya haka? Suka ce kai Musa mu fa ba zamu taɓa binka ba, ba zamu bautawa abin bautan naka ba, mu namu zamu sassaƙa yanzu! Imagine, mutanen da ka sai da ranka ka cecesu, ka wahala, ka juri yaki da dik wani barazana, babban mushiriki kamar Fir'auna ka kwatosu daga hannunsa, cikin kunci da azaba ya fito da su izuwa iskar ƴanci, amma me suka saka mashi da shi? Dik da haka bai yi fushi ba, ya cigaba da yi masu wa'azi, amma suka ki, sai wasunsu ne suka aminta, Annabi Isa, har ɓoye kansa yake yi a ɗaki saboda jefansa da kalmar mara uba da ake yi, bai yi wasa da yara kamar yadda kowani Annabi ya yi ba, ya rayu cikin ɗaki shiyasa ya taso baya son hayaniya kuma shiru-shiru, ya fuskanci ƙalubale da dama. Kai Annabawan ALLAH akwai hakuri jama'a, su ɗin karshe ne! Wani nan ko kyauta yai maka baka gode ba an dinga bala'i kenan, amma su ku duba, ALLAH ka bamu ikon koyi da su!.

So Lion yana mugun son daddynsa, baya barin mutun ya yi wasa da mahaifinsa, shiyasa ya takawa Aryan birki.

Miƙewa Aryan ya yi tare da cewa. "Ina zuwa, let me check them"..... Kai Lion ya jinjina mashi alamar to kafin ya ce. "Ka san yadda zaka yi da Abba, amma ko mutuwa zaka yi kada ka yarda da shiga cikin abin da ya shafi waɗan can halittu na mata, kasan dokar IRON FIST".

Kai ya jinjina alamar gamsuwa, sannan ya matsa kusa da Lion É—in, rungumar Lion ya fara yi, hannu Lion yasa ya É—an bubbuga bayansa alamar jinjina, sumbatar gefen kumatunsa Aryan ya yi, shi ma Lion sumbatarsa ya yi kafin su raba jikinsu da juna, ya matsa ya rungumi guru ma, suka sumbaci juna kafin ya fito. Kai tsaye benen su Seraphina ya nufa, dan ya duba ta tashi lafiya.

A lokacin da ya shigo tana tsaye a tsakiyar É—akin tana rike da waya, sam bata ji shigowansa ba, sai ji ta yi ya kwace wayarta. Da sauri ta É—ago da kallonta a kansa, ko da ya shigo ma sai da ya tsaya for good 5 mins yana kallonta, amma bata san ya shigo ba, sai da ya karewa surar jikinta kallo, tana sanye da shorts jeans zuwa tsakiyar santala-santalan cinyoyinta, daga sama Æ´ar riga da bata gama rufe cibiya ba mai dogon hannu kamar crop top haka, kun san shigarsu ai su, ba hankali aka sika ba, kafafunsa sanye da socks and bedroom crocs faro tas mai tsada.

Ash hair É—inta a gyare, ya sha gyara wajen Madam, sai sheki yake yi, ga wani irin fitinannen kamshin dake fitowa daga jikin gashin ga kuma na jikinta, sai kamshin ya bada wani kala mai É—aukar hankali. Sai da ya tsaya ya karewa jikinta kallo kafin ya shigo.

"Daddy kai ne?". Ta faÉ—a tana É—an murmushi. Harara ya dalla mata kafin ya ce. "Baby anya ba zan hanaki waya ba kuwa? Baki iya amfani da ita ba"..... Zazzaro eyes É—inta a kansa ta yi kafin ta ce. "Daddy me na yi kuma?"..... Ganin kamar zata faÉ—o jikinsa ta rungumesa ne yasa ya wuce saman sofa ya zauna yana faÉ—in. "Me ma baki yi ba? Haka ake amfani da waya ne? 24h baki komai sai pressing phone? On Monday zaku fara zuwa school, anya zaki yi karatun kuwa?".

Da sauri ta dawo kusa da shi, a gefen bed ta zauna suna fuskantar juna. "Please daddy kada ka rabani da wayar, i promise you that zan yi karatu sosai, kaga ai sss 1 zan shiga, dole in dage ko? Kuma dole sai da waya, and daddy ni karatu ma fa kawai nike yi da wayar, idan ka rabani da ita kaga karatuna zai ka baya tin da kamar lesson a gida nike yi da ita. Na yi alkawarin kula, zan warewa waya lokacin taɓawa daban, zan ware lokacin karatu"....... "Baby ni zaki yi wa kalaman yaudara?". Ya faɗa yana kallon idanunta a tsaitsaye, ga gashin idanun nata sun mimmiƙe, alamar kawai so take ta yaudaresa kada ya rabata da wayar, wai ita ma ta yi wayau, a haifeta a gabansu su sanya mata suna amma wai zata yi mashi wayau.

"Daddy trust me, kasan ai bana karya, kuma da gaske karatu nike yi a cikin wayar, and kaga wayar yana da amfani ko?"........ Miƙa mata wayar ya yi ba tare da ya sake cewa komai ba, dan Seraph tana goge mashi hadda yarinyar nan.

Karɓa ta yi har da sauke ajiyar zuciya, a tinaninta ta mashi wayau ya yarda da ita, cike da wayau ta ce. "Daddy tin ɗazun ma karatu nike ta yi da wayar fa, kaga yana da amfani na ce maka, kamar uncle ɗina mai mun lesson yake". Wai irin ta sake sanyawa ya yarda da ita sosai ɗin nan............ Shi dai ido kawai ya zuba mata yana mamakin yarinyar nan, bata san kome take a wayar yana ganinta ba.

Shammatarsa ta yi ta sake snapping ɗinsa pic har guda biyu bai sani ba. Sai dai tana ɗauka ya miƙa hannu ya kwace wayar tare da cewa. "Me kike yi da pics ɗina? Kin ɗau na farko bai isheki ba sai kin ƙara ne?"...... Ai a zabure ta miƙe ta faɗa jikinsa da nufin ta kwace wayar, tamkar zata yi kuka ta ce. "Daddy ni ban yi snapping ɗinka ba, give me my phone".

Shi kuwa ɗaga hannunsa sama ya yi yana kallon hoto, sai ya danna delete zai goge. Wani irin zabura ta yi game da miƙewa a jikin nasa zata kwace ta hanasa gogewa. Baya ya yi da hannun nasa, binsa ta yi dole sai ta kwace, idanunta sun cika tab da kwallar yaudara tana son karya mashi zuciya irin ya kyale mata ɗin nan.

Daidai kyakkyawan gefen face ɗinsa ta kwanto mashi da kirjinta tana miƙa hannu zata kwace wayar. Hannunsa ɗayar yasa ya tallabo waist ɗinta ta baya wajen mazaunanta, da ɗayan hannunsa kuma ya danna delete ya goge hoton, ya koma kan ɗayan ma ya goge. Take ta ɗauke wuta, tamkar ta yi sumar tsaye, shiru bata motsa ba. Sauke hannunsa ya yi, sai yanzu ya lura da yadda ta kwanto jikinsa. Take ya ji ya ɗan ɗauke wuta shi ma, a hankali ya ɗan yi ƙasa da ita yana jin tamkar kada ya raba jikinsa da matasan tula-tulan nata dake saitin face ɗinsa, amma ya ɗan yi ƙasa da ita.

Wai irin ta yi fushin nan ne fa taki motsawa. Dawo da ita daidai suna fuskantar juna ya yi, ya ɗan kwantar da ita gefe yana tallabe da bayanta da hannunsa ɗaya. Zubawa face ɗinta idanu ya yi, ta datse idanu tana hura kumatu, ga hawayen da suka cika mata ido sun fara zubowa, ta ji zafin goge hotunan da ya yi, ta ci alwashin turawa Rimsha hotun nan yau, amma ya ɓata komai, abin da ya fi bata takaici ma shi ne yadda ya ganota, yanzu tasan zai rabata da wayarta ne ko kuma ba zai sake yarda da ita ba bare ya bata daman zama da shi har ta samu damar ɗaukarsa wani hoto.

Shi kuwa slowly ya sunkuyo da kansa a kanta, a gefen wuyanta ya É—an kwanto da kansa, a hankali ya fara shakan kamshin shampoo na gashinta mai daÉ—in kamshin dake kwantar da hankali, sai ya rungumeta sosai a jikinsa, kawai ingiza shi zuciyansa take yi da ya yi kissing É—inta, gudun kada yai hakan ne yasa ya kwantar da kansa a gefen wuyanta.
Chapter 97 · 0% Book details