← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 163 OF 227

Sashe 163

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A tsorace ta miƙe ta je ta rage volume ɗin, shi kuwa Harleen ya ajiye laptop ɗinsa a gefe ya jawo waya ya fara latsawa. Daidai lokacin Ammie ta sauƙo ƙasa. Kallo ɗaya tai wa ƴan sandan ta ɗauke kanta tare da ƙarisawa in da su Faryan suke, ta zauna a saman sofa tana mai da kallonta a kan Rimsha da jikinta ke ta faman kermar tsoro.

"Ku wasu irin dabbobi ne? Baku ji ana magana ne? Kuna wasa da wuta ko? Hukuma ce a gabanku!!". ACP ya faÉ—a a kadarance. ÆŠaura kafa É—aya kan É—aya Faryan ya yi, ya jawo Rimsha jikinsa yana faÉ—in. "Baby zo ki ga me kawarki ta rubuta mun, wai tana sona saboda ina kama da daddynta". Ya faÉ—a yana murmushi.

Rimsha dai hankalinta sam bai kwanta ba, tana tsorace da Æ´an sandan nan, kallon wayar kawai take yi, amma hankalinta baya jikinta, hasalima bata ga me Seraphina É—in ta rubuta ba.

Wani irin tsawa ACP ya daka masu. "Ku dabbobin ina ne nace? Kun san zan iya jefaku a cell ko?".......... Jikin Rimsha ne ya tsananta kerma, ta ƙara ƙanƙame Farya. Ammie ce ta ce. "Faryan naga alamar wannan Seraphina ɗin tana burgeka, ka fara biyewa Rimsha ko?".

Murmushi Faryan ya yi. "Ammie yarinyar ta haÉ—u fa, kin ganta kuwa, kamar ki sace ki ajiye ki yi ta kallo, kyakkyawar gaske ce"........ Cikin zolaya Ammie ta ce. "To ya tsaya a iya haka dai, kada ka bari Abbanka ya jika"...... GabaÉ—aya Khaiza'an's family sun mance da wasu Æ´an sanda, sun baiwa banza ajiyarsu.

A fusace ACP ya sake cewa. "Lallai dikkanku sai kun yi danasanin wannan abin fa kuka aikata!"...…... Miƙewa Faryan ya yi, ya nufi kitchen yana faɗin. "Ammie bari in duba idan waɗan nan robot ɗin sun kammala abinci".

"Faryan zo mun da ruwa mai sanyi". Harleen ya faÉ—a yana É—aura kafa É—aya bisa É—aya ya cigaba da dannar waya. Watau idan kana neman shahararrun Æ´an rainin wayau to ka zo gidan Abba, takaici ne zai kasheka.

"Rimsha je ki ɗauki mun Americano na da na baro a ɗaki in karisa shanyewa". Ammie ta faɗa tana kallon Rimsha da tsoro ya gama cikata, dan dik family Abba ita kaɗai ce matsoraciya. Gagara miƙewa ta yi, ta kankame Faryan da ya dawo ya zauna a kusa da ita yanzu yana miƙawa Harleen ruwan da ya ɗauko mashi. Riko hannunta Faryan ya yi, tamkar zata yi kuka can ƙasa ta ce. "Uncle, I'm very scared"......... Ƙasa sosai yai da murya wajen cewa. "Don't fear anyone except ALLAH, get up and go bring what Ammie sent you to get".

Da gudu ta miƙe ta nufi sama tana waigo ƴan'sandan da suka yi kasaƙe suna ganin ikon God...... Harleen ne ya ce. "Kai Faryan kara gudun Ac ɗin nan ka zo mun da small chop".

Ai a ƙule ACP ya ce. "Me kuka ɗauki kanku ne ahalin Khaiza'an? Dame kuke taƙama ne?"....... Dik cikin parlon babu wanda ya ɗago ya kallesu bare su tankasu, sai ma cewa Harleen yai. "Faryan zo mun da bluetooth". Watau ya toshe kunne kada su dame shi.

ÆŠaya daga cikin Æ´an'sandan dake baya ACP ne ya ce. "Kufito mana da Muhammad Khaiza'an, shi muka zo tafiya da, in kuma baku fito da shi ba zamu bincike gidan gabaÉ—aya, kuma ba zamu ragawa kowannenku ba, dik zaku tsinci kanku a bayan kanta!". In a harsh way ya faÉ—a yana wani zazzare masu ido, bai san nan gidan dik tantirancinka sun fika iyawa ba, kuma su ba duka ba zagi, kai bama magana zasu sanya zuciyarka bugawa ne.

"Wai ba daku muke magana bane?!!". ACP ya faɗa cikin ɗaga murya wanda ya sanya Rimsha dake sauƙowa yanzu ta razana ta saki plate and cup na hannunta ya faɗi ƙasa ya tarwatse, Americanon ya malale a ƙasa. Jikinta na rawa ta ɗago da kai ta sauke kallonta a kan mugun watau Harleen, dan tasan ko kowa bai yi mata magana ba shi sai ya yi saboda bala'insa daban ne a gidan nan bayan Aryan.

Ga mamakinta sai ta ga ya harareta ya ɗauke kai bai yi magana ba, take ta haɗiyi yawu gwad jikinta na ɗan kerma. Tana ƙoƙarin raɓawa gefen glass ɗin ta isa wajen Faryan ACP ya damki hannunta tare da sanya mata pistol gun ɗinsa a forehead ɗinta, a dake ya ce. "Ku fito da Khaiza'an ko in fasa kanta!!". Wai irin zai razanasun nan.

Miƙewa Ammie ta yi tana faɗin. "Ku kawo mopper a goge Americanon nan, sannan ku zo da tsintsiya dan kwashe glass ɗin, Faryan bari in ɗan kwanta in huta". Ta kai karshen maganar tare da nufar sama, ta raɓa gefen ACP ta yi wucewarta........... Saura kaɗan Rimsha ta saki fitsari a wando saboda tashin hankali, jikinta ya tsananta kerma, kallonta a kan Uncle Faryan dake girgiza mata kai alamar kada ta tsorata.

Harleen kuwa ko a jikinsa yana cigaba da cin small shop da Faryan ya shigo mashi da shi, suka baiwa bansa ajiyar su ACP, kuma ga shi su ACP É—in suna shakkar shiga cikin É—akunan gidan su duba ko Abba yana nan, su da kansu sun san da wuya idan Abba yana gidan, amma sun jajirce sai Khaiza'an's family sun kulasu.

Ganin babu sarki sai ALLAH ne yasa suka ce zasu tafi da Rimsha, idan har suna sonta Khaiza'an ya kawo kansa station. Still dai babu wanda ya kulasu, ACP ya kamata suka nufi waje. Take ta fara kuka hawaye bibbiyu.

Suna fitowa harabar side É—insu sai ga motar Aryan ya danno kai, sun dawo da Abba, an je an gyarawa Abban karafunan kafafun nasa. Tin Aryan bai gama parking ba Abba yasa hannu zai buÉ—e kofar motar saboda ganin Rimsha a hannun Æ´an'sanda ya É—aga mashi hankali. "Abbaaaaaa......" Aryan ya faÉ—a yan jan sunan.

Harara Abba ya dalla mashi kafin ya buɗe mota ya fita, da alama har yanzu bai huce ba, Aryan kuma babu alamar zai karɓi wannan umarni, ba zai yarda ya auri Aunty Lusi ba. Fitowa Abba ya yi, yana dogara sandarsa ya isa gaban ACP. Da karfi Rimsha ta fara ƙoƙarin kwatar kanta ta nufi Abba, amma ACP ya ƙanƙameta, bai saketa ba.

Lokaci guda kuma ya saketa a razane yana kallon Aryan dake tinkarosu tamkar wani zaki, gabaÉ—ayansu babu wanda hantar cikinsa bai kaÉ—a ba, ACP har da haÉ—iyar wani yawu da karfi gwad. Da gudu Rimsha ta nufi Abba, tana zuwa ta faÉ—a jikinsa, riketa ya yi yana cigaba da kallon Æ´an sandan.

"Me haɗinku da jikata? Me tai maku zaku kamata?". Abba ya tambaya...... Da kyar ACP ya saita natsuwansa game da ɗauke kallonsa daga kan Aryan dake gab da ƙarisosu kafin ya ce. "Lush family ne suka shigar da ƙara a kan Khaiza'an, batu ne na cin zarafin ɗan adam, ka tilasta masu yin abin da basa so, ka kawo kuɗi ka basu dan kasayesu, cin hanci kenan, kasan kuma corruption haramun ne a ƙasar nan"..….. Abba ya gane karatun, watau grandpa ɗinsu Noor ne da wannan ɗanyen aiki.

A daidai lokacin Aryan ya ƙariso wajen, fuskansan nan tamau babu alamar wasa, a dake ya ce. "A yaushe CRYSTAL PALACE ta yi lalacewar da ƴan sanda zasu iya shigowa cikinta?!"...... Shiru ƴan sandan suka yi, dan sun san ba kai tsaye suka shigo da nufin kama wasu ba, sun yi wa jami'an dake bakin main gate karyar cewa ziyara zasu kaiwa ɗan uwansu a Lush family, shi ne suka samu hanyar shigowa, dan jami'an bakin gate sun duba number Lush family dake jikin littafin CRYSTAL PALACE ɗin, sun kira table phone nasu, suna tambayi cewa suna da baƙi kala kaza ne? Dama grandpa ne ya ɗauki wayan, sai ya ce e suna da baki, shi ne fa suka basu hanya bayan sun cajesu basu ɗauke da komai sai bindigar aiki.

A tsarin CRYSTAL PALACE da yanayin tsaronta babu wani jami'in da ya isa shiga cikinta ya kama wani, babu wannan mahaluƙin, idan akwai mai laifi a cikinta to sai dai a tuntuɓi jami'an dake tsaron CRYSTAL PALACE ɗin, su da kansu zasu yi bincike, idan ya tabbata mai laifi ne, da kansu zaku kama shi, idan kotu ne su miƙa shi kotun dake cikin CRYSTAL PALACE ɗin, idan hukunci ya dace da shi su zasu yanke mashi, shiyasa na ce maku manyan kai ne ke zama a cikin CRYSTAL PALACE, akwai tsaro, dokoki da ƙaidoji, babu wani abin da ya isa zama barazana ga mutanen ciki, karfin ikon CRYSTAL PALACE ya zarce yadda kuke tinani.

Tsuru-tsuru ƴan sandan suka yi. Aryan ya daka masu tsawa, hakan yasa ACP ya ce. "Dama Lush family ne suka shigar da ƙasa kan Khaiza'an, shi ne muka zo tafiya da shi.......".

Bai iya ƙarisa maganar ba sakamakon gigitaccen marin da Aryan ya ɗaukesa da shi, wai Abba aka zo kamawa. In a harsh way Aryan ya ce. "Ba'ayi mahaluƙin da zai iya taka gidan Khaiza'an da suna kama shi ba!". Da farko Aryan ya so nuna masu ID card ɗinsa na SSO, sai kuma ya fasa, dan basu kai ya tsaya nuna masu waye shi ba, gara ya jibgesu ba'a matsayi nagaba da su a wajen aiki ba, su rubuta a tarihinsu farin kaya ya jibgesu.

Abba sarkin izza, aikuwa ya ce Aryan ya ƙara masu, dan shi an walaƙanta shi da har ƴan sanda suka shiga gidansa. Kallon Abba Aryan ya yi. "Abba ka je ciki kawai". A tausashe ya faɗa...... Hannun Rimsha Abba ya riko suna nufi elevator yana faɗin kada Aryan ya raga masu, ya masu hukuncin da gobe ko sunan Khaiza'an suka ji sai sun saki fitsari a wando.

Shi kuwa Aryan Abba na shiga ciki ya É—auki waya da nufin ya kira jami'an SSO dake benensu, sai ya ga wayar Lion ce a hannunsa, ya É—an yi mamaki, sai can ya tina ashe É—azun da ya kwanta jikin Lion suna hira wayoyinsu na haÉ—e waje guda, da ya tashi ne ya manta ya É—auki na Lion kenan, dama wayoyin iri É—aya babu abin da ya rabasu, sai ka kunna hasken wayar zaka ga wallpaper kowa da kalar tasa.
Chapter 163 · 0% Book details