← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 227

Sashe 49

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

One thing da na manta ban faɗa maku na, su Noor ba musulmai bane, nasan zaku ce Noor sunan musulmai ne ai, kada ku manta ni na yanke sunan nike ce mashi Noor, amma sunansa Nooriel, dan haka ba musulmai bane, shiyasa idan Leo yana ce mashi kada ya ji tsoron kowa face ALLAH baya wani ɗaukar abin serious, dan tin farko bai yi imani da ALLAH ɗin ba, amma zamansa da Leo a yanzu yasa sosai yana jin cewa zai iya musulunta, kuma yana jin cewa lallai ALLAH shi ne mahaliccin kowa da komai, Leo bai taɓa ce mashi ya musulunta ba, yana dai yin ibada a gabansa, a haka kuma abin take shiga ransa, kun san addinin musulunci da shegen daɗi, ba sai ance maka zoka shiga ba, in dai ana ibadar a gabanka dole ka yi sha'awarta sai dai in son zuciyarka zaka bi!.

Sosai ya kwarara mashi gwiwa, bai rabu da shi ba har sai da ya tabbatar ya kore mashi wannan tsoro, sannan dan ma ya kara karfafasa sai yasa ya kira V a yanzu su yi magana, saboda a cewansa idan ya kirata zai kara kwarara kansa. With his full confidence ya danna mata kira, yanzu baya jin tsoron komai.

Kira ɗaya ta ɗaga, har lokacin tana zaune a balcony, ta ci kuka har ta ƙoshi, dan a tinaninta shikenan ya ji cewa ita ƴar GAT ne ya rabu da ita, ta yi ta nadamar faɗa mashi gaskiya da ta yi, har idanunsa suka yi jajir suka ɗan kumbura.

Tana ɗauka ta fashe mashi da wani sabon kukan, dan zuciyarta a kusa take. Ɗago eyes ɗinsa ya yi suka kalli juna da Leo, hararansa Leo ya yi kafin ya koma ya kwanta tare da jawo bargo ya rufe har kansa. Ajiyar zuciya Noor ya sauke, slowly ya sauƙa daga gadon, da sauri ya fita zuwa balcony wai kunyar Leo yake ji.

Tsayuwa a wajen ya yi tare da manna wayar a kunnensa, ya zura hannunsa ɗaya a aljihu kafin a sanyaye ya ce. "I'm so so sorry for the delay in responding to your message, wani ɗan abu ne ya ɗauke hankalina"...... Haba lokaci guda ta ji tamkar an sauƙe mata dik wani nauyin dake kanta jin cewa ba daina yi mata magana zai yi ba, amma dik da haka sai ta cigaba da kukan dan ta kara ratsa zuciyansa da kyau.

"Please stop crying! Yana taɓa mun zuciya"........ Cikin kuka ta ce. "Ni dai ka rarrasheni in kana son in yi shiru"..... Yadda ta yi magana voice ɗinta ya huda zuciyansa sosai, har wani ɗan shock ya ji, one side smiling ya ɗan saki kafin a cikin ransa ya ce. "Yau ga shi a hannun rigimammiya, wai ya rarrasheta kawai, to shi ko ta ina ya iya rarrashin ne ma?".

A fili kuma sai ya ce. "Okey me kike son in yi yanzu kenan?"...... Tana turo baki tamkar tana a gabansa ta amsa da. "Ka mun kalamai masu daÉ—i"....... "That's all?"....... Kai ta jinjina tare da cewa yeah. "Okey, get ready to accept my cool and sexy words".

Da sauri ta ce. "Done, I opened all my ear, I'm listening now!". Ta faɗa har tana tuntuɓen harshe...... "See her, rigimamma kawai, wai I'm listening, har kina haɗe words, kece auta ko?".... Kai ta gyaɗa tare da cewa. "Kamar kai ba, nasan kaima ai kai ne auta"...... "Who told you?"........ "Aunty Lisa". Ta bashi amsa a taƙaice. Ɗan girgiza kai ya yi cike da mamakin yadda lokaci guda Aunties ɗinsa suka aminta da ita, har da bata labari.

Jin ya yi shiru yasa ta fara jansa da hira da salon soyayyarta mai melting heart har bai san time da ya saki jiki ya shiga biye mata ba, suka raba dare suna hira, dan ko da su Arya suka dawo room ɗin bata daina wayar ba, sai da daddynsu ya shigo ne ta ɓoye wayar ba tare da ta katse kiran ba, Noor na jin dik abin dake wakana.

Yau da yake yana da baƙi bai zauna hira da su ba, sai ya yi masu goodnight ya fita kawai. Su Arya suka tattaro laptop ɗinsu suka shiga aiki dan gyara kwarewarsu, ita kuma V ta cigaba da wayarta da heartbeat ɗinta. Sai around 3 na dare sannan ya ce su kwanta dan da safe zai wuce US, akwai sammako kenan a gabansa. Kada ku manta tsakanin Avaris da US ba nisa, suna kusa sosai.

Abin ku da sabon soyayya, sam bata so su yi sallama, ita ko kwana zasu yi a haka a shirye take, amma ta hakura dan girmama buƙatarsa, suka yi sallama ba tare da ya yarda ya furta mata kalmar so ba, dik hiran da suka yi bai yarda ya furta kalmar ba, ba wai dan bata yi mashi ba, no, kawai dai ya ce tukun nan, sai ya gama sanin wacece ita da yadda take gabaɗaya. Ita ma bata damu da ya furta mata ba, a cewarta a hankali zai furta ba sai an ce ya yi ba, dan haka da suka zo yin sallama ma ce mashi ta yi take care, goodnight and have a nice dream, bata kawo zancen love ba, amma tana kiransa da heartbeat.

While shi ma abin da ya ce mata kenan, have a nice dream like your beautiful face. Ta dinga murmushi jin ya yaba kyanta, a haka dai suka yi sallama, ta kashe wayar ta kwanta.

A yayin da dikka hakan ke faruwa shi kuwa GAT ya je sun sha hira da daddyn Noor dasu Aunty Lisa a room da aka baiwa daddy. Sai satar kallon Aunty Lisa yake yi, amma bai amayar da abin dake ransa ba. Dik in ta motsa a kan idanunsa ne, tin bata gane ba har ta fara ganewa, dan dik in ta É—ago sai sun haÉ—a ido, zata ga ita yake kallo, da farko bata É—auki hakan a komai ba, sai daga baya da ta ga kallon ya yi yawa sai ta fara jin wani tinani a ranta.

Da yake wayayyiya ce, ba kauyanci da shirme a kanta, sai ta ce. "Daddy I'm feeling sleeping"...... Daddy Noor ya amsa mata da ta je ta kwanta mana. Dan ta tabbatar da zarginta ne ta yi hakan, miƙewa ta yi tare da yi masu goodnight ta fito izuwa room da aka saukesu.

Tana fitowa ta É—an yi gaba kaÉ—an sai ta tsaya, shiru ta yi tana tinanin meyasa GAT yake kure mata kallo haka?. Bata dawo daga duniyar tinanin ba sai ganin mutum a gabanta ta yi yana faÉ—in. "Meyatsayar dake a nan pretty?".

ÆŠan firgita tai kafin ta ce. "Daddy me ya fito da kai?"........ Waskewa GAT yai da cewa. "Nothing, kawai zan je room ne"....... Ta gano saboda ita ya fito, amma ta nuna bata gane ba ita ma, ta basar tare da yi mashi goodnight zata wuce. Da sauri ya ce. "Let me escord you!".

"Thank you daddy". Cikin ladabi ta faÉ—a...... "Nevermind dear". Ya faÉ—a a lokacin da yake isa dab ita, da hannu ya nuna mata hanya ta wuce ya rufa mata baya, dik wani takunta a kan idanunsa har suka isa room É—in, har ciki ya rakata, a gaban bed ta tsaya tare da cewa. "Thank you daddy".

Kai kawai ya jinjina, ya gagara yin magana kuma yana jin kamar ba zai iya juyawa ya tafi ba. Ganin haka yasa ta ce. "Daddy akwai wani abin ne?". Kai ya girgiza mata alamar a'a babu, amma ya gagara tafiya. Da ta sake tambayarsa rasa me zai ce mata yasa ya ce. "Room É—in ya yi maku ne ko a canza maku?".

Dik wani take-takensa ta ganosa amma ta basar tare da cewa. "Ya yi sosai daddy"........ "Ba wata damuwa?". Ya faÉ—a a É—an dake. Kai ta gyaÉ—a zuciyarta cike da mamakinsa. "Goodnight". Ya faÉ—a tare da juyawa, da kyar ya iya daina kallonta ya nufi waje. Dab zai fita ya jugo dan ya saci kallonta, sai suka haÉ—a ido, ashe shi take kallo, da alama ita ma ta folawa haÉ—aÉ—É—en GAT namu, uba ga su V ai kun san ya haÉ—u.

Still goodnight É—in nan dai da yaki karewa shi ya sake ce mata kafin ya juya, hannu ta sanya ta toshe baki tana murmushi, dan dik ta gama ganosa. Nauyinta da yake ji yasa bai sake juyowa ba dan kada su sake haÉ—a ido, sai ya yi zafin namar ficewa, yana jin nauyinta sosai, musamman yadda take ce mashi daddy, yana jin kamar ba zai iya tinkararta da kalmar so ba!.

Yana ficewa ta daka tsalle tare da faɗawa saman bed ɗinta, a fili ta ce. "Ooooo, ta ko'ina ya haɗu, and ga shi so silent, saukin kai and natsuwa"....... Bata san su ya gwadawa saukin kan da natsuwar ba tin da akwai abin da yake so a wajensu, amma GAT na soja ina ya ga saukin kai, tab GAT fa? Lallai sunan kawai suke ji, mutumin da ganinsa ma kawai tashin hankali ne saboda bataliyar sojojin dake take mashi baya, amma dik ya takawa sojojin birki da umartansu su koma cikin barrack su bar kwaranni a gidan dan kada su firgita mashi abin kauna, amma ban da haka ai in yana gida zaku rantse da ALLAH dikka barrack ɗin ne a gidansa, dik ta in da ka juya kaki da bindiga zaka ga suna shawagi dan tsaronsa, sojoji sama da 30 ke gadinsa idan yana gidan, idan zai fita yana tafiya dasu ya bar basu wuci 10 ba a gida dan tsaro ga gidansa da family ɗinsa, kunga kuwa babu sauki wai ciwon arne, su dai sun ga saukin tin da ƙararrawar zuciyansa ta buga a kan Aunty Lisanmu!.

Haka GAT ya kwana da tinanin Lisa a ransa, while ita ma da tinaninsa ta kwana, taki faÉ—awa su Luna meke going, ta bar abin a ranta, washegari da sassafe suka hau shirin tafiya US, GAT bai fita office da wuri ba, ya tsaya tabbatar da cewa bakinsa sun tafi cikin aminci.
Chapter 49 · 0% Book details