← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 227

Sashe 37

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Manyansu sun ji daÉ—i sosai. Daga nan suka nufi masallaci, bayan sun yi sallah suka yi lunch sannan suk nufi class. Yau an koya masu karfin gudun kowani bindiga, illarsa, dalilan da yasa yake kwacewa a wasu lokutan, goge dattinsa, cansa wasu sassa nasa, da faidar kowacce, kowacce lokacin da ya dace ayi amfani da ita.

Sun ɗauki awa biyu a class ɗin kafin su fito su sake komawa wajen horon harbi, dai saiti shi ne babban abu a fagen yaki, in baka da saiti ma kana iya harbin kanka, dan haka dole ka kware sosai. Daga wajen saiti da yamma suka wuce wajen horon hannu, dan ƙara gwada kwanci, suka yi gym na yamma sosai zuwa karfe 7 suka tashi horo. Masallaci suka nufa, bayan sallar mangrib and Isha'i suka nufi rooms ɗinsu.

Vash and Zaysh a tare suka jera zuwa yaronsu a maimakon su koma roon ɗin nasu. Noor and Leo kuma ɗaki suka koma, Leo ya je yana shafawa Noor magani a bakinsa da ta kumbura sosai. Sai sannu yake yi mashi, Noor sarkin son jiki tuni ya kwanta mashi a jiki har da kukan shagwaɓa, yau ya tuna da su Aunty Lusi, yadda yake yi masu ya hau yi wa Leo yau, shi kuma ya daure yana ta biye mashi, dan Noor ya shiga ransa matuƙa.

A gefe guda kuwa su Arya bayan sun dawo da school sun yi lunch V ta ce zata tafi wajen daddy, da sauri Arya ta hanata ta hanyar cewa su je su buga basketball a wajen game É—insu. Ba dan ta so ba ta yarda, kuma babu rabon haÉ—uwarta da Noor nan kusa!.

Arya ta raba masu team, suna sanya sportswear iri ɗaya kaunin milk color. Arya ta ɗauki basketball ɗin nasu suka nufi wajen wasanninsu. Katafaren fili ne da GAT yasa aka ƙawata masu shi, kayan wasanni ne kala-kala a cike a ciki, akwai wajen football, basketball, snooker, har wajensu whots akwai, kwallon kwando da komai dai.

Raba kansu suka yi team biyu, Arya da Manassa, Angelie and V. Akwai wasu zaratan sojoji dake tsaron wajen wasan, suna tsaitsaye tamkar saƙaguna suna satar kallonsu Arya. Ga shi sportswear ɗin nasu guntun wando ke zuwa tsala-stala cinyoyinsu dake wani irin glowing, very soft. Daga sama rigar tasu mai ƙaramar hannu ce, kayan dai yai masu kyau sosai.

Da suka fara ball É—in dik in da suka yi idanun sojojin nan a kansu yake, musamman V da ko'ina yake cike dam, ai tana tashin kan mutane. Cikin nishaÉ—i suke wasanninsu cike da kaunar juna, Arya dai ta yi wa V wayau ta hanata zuwa ganin masoyi Leo.

A can cikin barrack kuwa zama Vash and Zaysh suka yi a saman wasu kujerun dake arear wajen horonsu. Suna zama Zaysh ya ce. "Bro kasan akwai mata a training É—in nan?". Da sauri Vash ya amsa da. "Yeah, three days ago na haÉ—u da wata kyakkyawa a kusa da Senior staff side".

Shiru Zaysh ya É—an yi kafin ya ce. "Ni kuma almost a month ago, mun yi karo da wata, kuma tin time É—in ban sake ganinta ba"......... "Bar zancensu kira mana Ummie mu gaisa, na yi kewarta, jiya bamu yi waya ba"....... Watau idan kana da kyan hali kowa nemanka zai dinga yi!.

Wayansa ya je ɗaki ya ɗauko ya dawo, yana kunnata saƙon Ummie na shigowa. "Koman dare idan ka samu lokaci ka kirani". Shi ne abin da saƙon ya ƙunsa, haka kawai ya ji faɗuwar gaba, cikin zafa ya laluɓo numberta ya danna kira.

A lokacin tana zaune saman kujerarta da ya gama shan wahala, dama ba wani qualityn kirki ba. Kiran na shigowa ta yi gaggawar É—agawa, muryanta na rawa ta ce. "Hello"........ Sai da ya ji kirjinsa ta buga kafin ya amsa da. "Ummie lafiya?".

Kuka ta rushe mashi da shi, da kyar cikin kuka ta iya cewa. "Zaynish na shiga uku, yayanka aure zai kara, ƴan uwansa sun ce ya kara aure tin da ni bana haihuwa"....... Ɗan waro idanunsa a kan face ɗin Vash ya yi, idan ransa ya kai miliyan to ya ɓaci, a duniya babu abin da ya tsana irin ya ga tashin hankalinta, yau da yana da dama babu wanda ya isa yasa mijinta ƙara aure, amma bashi da shi, innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Da kyar ya saita natsuwansa tare da cewa.

"Ummie ki yi hakuri ki yi shiru mu yi magana kin ji?"....... Da kyar ta iya amsawa da. "Na gagara dannewa ne, Zay wai fa ƴar wannan gwaggon nasu masifaffiyar zai auro! Wannan yarinya mara kunya da ka taɓa wankawa mari lokacin da ta ce zata dakeni, ita fa suka ce ya aura! Wai ni me na yi masu ne? Meyasa suka tsaneni? Na yi wani laifi ne? Zay kada ka ɓoye mun, ka faɗa mun tsakaninka da ALLAH me laifina in gyara!". Tana kuka tamkar ranta zai fita.

Miƙewa tsaye ya yi, ya ɗan matsa gaba kaɗan dik da Vash baya jin yarensu, amma shi mutum ne mai son sirri da mugun zurfin ciki, yasan ko a yanayin maganarsa Vash zai fahimci wasu abubuwa.

"Ummie baki da wata matsala, ki natsu, kin manta kece kike ce mun ALLAH na jarabbatar mutanen kirki ne? Kin manta kece kike ce mun a kowani hali nike ciki kada na manta da ALLAH ne? Yanzu ki rufe idanunki, ki ambaci sunan ALLAH sau uku a jere kafin mu cigaba da magana"....... Shi ma dauriya ce kawai yake yi, amma zuciyansa tamkar zai fasa kirjinsa ya fito waje.

Cikin kuka ta amsa abin da ya ce, cike da yaki da yarda da ALLAH ta rufe idanunta ta ambaci sunan ALLAH sau uku a jere, take ta ji zuciyanta ya yi sanyi, dik wani raÉ—aÉ—i ya kau, nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tare da sanya hannu ta goge hawayeta. A natse ta ce. "Nagode wa ALLAH da ya bani É—an uwa kamar kai".

Ajiyar zuciyan shi ma ya sauke kafin ya amsa da. "Nafiki farinciki idan na tuna kece Æ´ar uwata"...... Kara nisawa ta yi tare da cewa. "To na yarda, yanzu dai ka bani shawara É—an uwana"....... "To shikenan, yanzu dai so nike ki kwantar da hankalinki, ki natsu, sannan ki bani aron kunnenki"........ Gyara zama da kyau ta yi, ta kara sauke ajiyar zuciya kafin ta ce. "Ina jinka rabin raina".

"So nike ki kara hakuri kan wanda kike dashi, ina ji a jikina wahalarki kaɗan ce ta rage, ki mai da komai ba komai ba, dik abin da za'ayi ki toshe kunnuwanki, ki rufe idanunki, kada ki taɓa nuna kamar kin san suna yi, ko ita yarinyar da zai aura kada ki taɓa nuna mata kamar kin damu, ki nunawa yaya kina supporting ɗinsa, zan tura maki kuɗi ku fara business, ki mai da hankali kan kasuwancinki, ki kuma cigaba da addu'a, ALLAH baya barci, kuma babu wanda zai baki haihuwa a duniyar nan face shi, tabbas kuma bai manta dake ba, amma dik da haka ki dage da addu'a, ki dage da tashi sallar dare, ki kai kukanki garesa, ki koma gefe ki huda ganye kina kallonsu, ina da tabbacin ALLAH zai dubeki da idanun rahama, sai warware mana dikkan matsalolinmu".

Sosai ta ji kwarin gwiwar kalamansa, amma sai ta ce. "A ina ka samu kuɗin da zaka bani in fara sana'a?"...... Bai ɓoye mata komai ba, ya faɗa mata kuɗin da Vash ya bashi, idan zai canza kuɗin ya turo mata sun kai 3M, jin kuɗin da bata taɓa ganin kwatansu bane yasa ta kiɗime, hankalinta a tashe ta ce. "Zay anya mutanen kirki ne kuwa? Kuɗi har miliyan uku zasu baka kyauta? Ni kam gaskiya ina tsoro, ka rabu da su to". Dik ta rikice.

Natsuwa ya yi ya kara yi mata bayani da kyau har ta fahimta, sannan ya ce zai tura mata 2.5 shi kuma zai bar sauran a hannunsa, ya ce ta samu sana'a mai kyau ta kama. Cike da murna ta ce mashi to zata sayi kayan gado da kujeru masu kyau ko da na 1m ne, dan ita ma ta sabonta É—akinta kafin amarya ta zo.

Na'am ya yi da wannan shawara tata, daga nan ya ce ta nemo account ta turo mashi zai tura mata, ta dai tsaya a kan sana'ar da zata kama sosai, kada ta yi wasa!. Ai mancewa da batun kishiya ta yi, ta dinga murna, har da dariya mai sauti, daga nan ya koma ya haÉ—ata da Vash, suka gaisa ta dinga yi mashi godiya cike da murna, mamaki Vash ya dinga yi a kan meyasa take yi mashi godiya har haka ne? Dan ya É—an hawa Zaysh É—an wannan kuÉ—i da bai wuci na kashewansu a wuni idan suka so ba!

Haka dai ya amsa da okey, daga nan Ummie ta yi masu addu'oin da ta saba, suka yi sallama, shi ma Zaysh suka yi sallama, ya koma ya zauna suka cigaba da hira da Vash.

---------------------🔥

Haka rayuwar matasan sojojin nan ya cigaba da tafiya har suka ɗauke basic training na tsawon watani, a nan manyansu suka ga room 1, room 2 zuwa room 3 suka da kaifin ƙwaƙwalwa da kwarewa, dan haka sai aka fara basu horon jami'an na musamman, misali kamar a Nigeria ce jami'an NDA haka, su jami'ai ne da kwarewarsu ya zarce yadda ake tinani, dan shi horonsu ma na shekaru biyu ake yi masu, amma a Nigeria horon yana iya kai shekaru uku, sai dai su AVARIS a shekaru biyu jami'i ya zama kwararre, basa ɓata lokaci kuma basa ɗaukar wasa. Dan haka su Noor suka shiga fagen horon jami'ai na musamman da iya gwabzawa a ƙasa da ƙasa, ga karatun da suke karɓa tamkar a school, har yau Unays, Zaysh, Leo basa shiri, kuma har yau Leo bai yafe dukan da aka yi wa Noor ba, sauran jami'ai sun yi passing out a watanni shidda nan, su kuma an matsa da su gaba, wani wajen da aka kaisu ba mai iya samun damar ganinsu, ko fitowa basa yi, barci a ƙurarren lokaci tashi a farkon lokaci, komai an ninka masu ukun na baya.

A ɓangaren su Arya ma hakan ce, sun dukufa a kan aikinsu babu kama hannun yaro, sun mayar da hankali sosai.
Chapter 37 · 0% Book details