← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 227

Sashe 19

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Komawa ya yi ya zauna tare da ciro wayansa daga aljihu, intently ya fara latsa wayar yana typing message. Ɗan zuba mashi idanu ta yi, sai kuma ta turo baki, take dara-dara violet eyes ɗinta suka cika tab da kwallah, a fili ta ce. "Where are you mammy? I'm so scared here, come and take me away from here". Cikin kwararriyar turancinta ta yi maganar, voice ɗinta ba dai daɗi da sanyi ba, ga zallar madarar shagwaɓa.

Yana jinta sarai, amma ko motsi bai yi ba, yana cigaba da latsa wayarsa. Ganin babu mai kulata ne yasa ta lallaɓa ta koma ta kwanta shiru. Kyakkyawar yarinyar karshen haɗuwa, gashin kanta light ash very silky haka, ga wani irin sheki da yake yi, violet eyes ɗinta dara-dara farare tas da su.

----------- silent for almost 40 mins ne ya biyo baya kafin wasu nurses guda biyu suka katse masu shirun ta hanyar shigowa. Ɗaya hannunta rike da wata ƴar CPH-note-b, ɗayar kuma hannunta rike da babban leda mai shaƙe da magunguna. A gaban bed ɗin suka tsaya, mai rike da magungunan ne ta miƙawa guy ɗin tana faɗin. "Here's her drugs, make sure she's taking it on time".

Hannu yasa ya karɓi magungunan ba tare da ya kalli in da suke ba, ita kuma ɗayar nurse ɗin miƙa mashi note-b ɗin ta yi, saƙon sallama ne, takarda ce mai ɗauke da sunan CRYSTAL PALACE HOSPITAL da sauran bayanan yarinyar, me dalilin kwanciyarta, kwananta nawa, kuɗin da aka cajesu, kai komai dai, a karshe time da date da aka sallameta. Sannan takardan nashi ne, dan idan ba mazauna CRYSTAL ba babu wanda yake da irin takardan, din in zaka kwanta jinya sai ka zo da notebook ɗin, a nan za'a cigaba da yi maka rubuce-rubuce har ranar sallama!.

Nan ma karɓa ya yi, ba tare da ya yi magana ba ya miƙe tsaye, gentle ya tako zuwa gaban bed ɗin. Hannu ɗaya yasa ya ɗauki yarinyar sai saman shoulder ɗinsa, bai bi ta kansu ba ya nufi waje.

Yana fitowa wasu jiga-jigan guards masu zubin gangsters su uku suka take mashi baya da gudu. Kai tsaye wajen wani dankareren mota ya nufa, tin kafin ya iso wasu guards madaka karti dake kusa da motar suka ɓalle mashi back door. Ciki ya jefa yarinyar kamar yaki, sannan ya shiga gidan bayan shi ma.

Da sauri suka mayar da door É—in suka rufe, da wani irin gudun karti suka nufi sauran motocin dake wajen, da gudun gaske suka ja motocin suka kutsa cikin C-P (CRYSTAL PALACE) Ita dai taga ikon God, sai kawai ta hau binsu da kallo, tam daina magana tin da har yanzu ba'a samu mai iya amsa mata ba.

Ɗaya daga cikin shahararrun ginin da ya fi ƙawatuwa a wajen suka nufa, shi hawa 10 ne kawai, sannan shi gabaɗaya glass nasa sky blue ne babu mix. A parking lot na gidan suka paka motocin, da gudu wasu kartin guards dake shawagi a gidan suka nufo motocin. Nasa suka fara ɓuɗewa kafin na kowa. Fitowa ya yi cikin zafin nama, yasa hannu ya ɗauketa sai saman shoulder ɗinsa, hannunsa ɗaya rike da drugs ɗinta.

Ita dai shiru kawai ta yi tana kallon ikon God. Kai tsaye elevator ya nufa, daga kan yadda yake tafiya zaku san lallai wannan shahararren gangster ne, tafiyarsa babu wasa ko sanyin jiki. Hawa na biyar ya haye. A wani katafaren parlo mai tsananin kyau ya dakata. Shiru ya É—an tsaya kamar na 1 minute, sai kuma ya nufi wani door dake fuskantosa.

Yana zuwa ya ɗan taɓa handle na door ɗin sai ga shi ya buɗe kansa. Wani katafaren sleeping door ne, katon bed ne kawai a ciki, yana shinfiɗe da wani haɗaɗɗen bedsheet na alfarma white kala, da one side sofa. Sai kofar toilet and balcony wanda dik da glass aka yi su kun sani.

A saman bed É—in ya direta tare da É—aura drugs É—inta a gefenta, daga haka ya juya bai sake kallon in da take ba. Parlo ya fito, kai tsaye ya nufi wani madaidaicin door dake fuskantar É—akin da ya fito.

Wani haÉ—aÉ—É—en dry kitchen ne a wajen, da alama babu kowa a gidan sai shi kaÉ—ai. Kyakkyawan pot ya É—auko daga cikin pot set É—insa, ruwa ya zuba a ciki tare da buÉ—e drawers na sama ya É—auko wani É—an karamain bottle, wani green leaf ya É—ebo daga ciki, ya zuba cikin ruwan pot É—in, sannan ya É—auko wani bottle na honey. KaÉ—an ya zuba zuman a ciki, ya kunna gas, a kai ya É—aura tare da nufo waje.

Yana fitowa ita ma ta fito daga room É—in da É—an gudunta tana faÉ—in. "Mammy I don't want to stay here, please come and take me away from here". Tana kuka sosai da hawayenta. Kallo É—aya ya yi mata ya É—auke kansa, sai ya nufi wani siririn hanya dake kusa da glass wall dining room dake cikin parlon.

Da kallo ta bisa, a ranta ta ce ko dai baya magana ne?. A fili kuwa hawaye na cigaba da tsere a kan fuskanta sosai. Tana ganinsa ya yi amfani da remote wajen sauƙo da staircase daga sama, sannan ya haura sama abinsa ya kyaleta tsaye kamar wata doluwa.

Zaman dirshan ta yi a ƙasa tare da sanya hannayenta dikka biyu ta fara watsa kyakkyawan ash hair ɗinta tana cigaba da kuka. Lokaci guda kuma ta ɗan kwaɓe fuska tana ɗage hanci sama wai jikinta na tsamin datti, dan yau kwanakinta uku a asibiti bata yi wanka ba, kuma babu wanda ya yi mata, tin da suka kawota ma shi sai jita ya je, tana sume aka kaita, daren jiya ta farfaɗo tana kuka kenan aka yi mata alluran barci, bata tashi ba sai ɗazun. Farfaɗowarta jiya yasa aka kirasa a waya ya zo, tin kuma da ya fita wajenta jiyan sai yanzu ya koma ya ɗaukota da likitocin suka sanar da shi ta samu lafiya zai iya tafiya da ita.

Abin da ya sumar da ita kuma shi ne hayakin wutar da su Eagle suka kunna a gidansu. Wannan yarinya ba kowa bace face ƴar Dr Hushaima ALLAH jiƙan rai, da alama kuma wannan mutumi shi ne bahagon murɗaɗɗen mutumin da Dr ta taimaka dik da ban sani ba, hasashe nake yi, naga halinsu na rashin magana iri ɗaya ne da wancan, to wai ma su waye su ne?.

To yanzu dai mu É—an koma baya kaÉ—an dan mu ji ya aka yi yarinyar Dr ta tsira?.

STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥

ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥

PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.

4-11-2025.🔥

FIVE LIONS, FIVE MISSIONS, ACTION, DEATH OR LIFE, ADVENTURE, BRAIN GAMES, REDRESS, A BREATHTAKING LOVE THAT STEALS THE HEART AWAY.♥️🔥

E_____________5

Abin da ya sumar da ita kuma shi ne hayakin wutar da su Eagle suka kunna a gidansu. Mu É—an koma baya kaÉ—an dan mu ji ya aka yi ta tsira?.

A lokacin da Dr ta fita ɗakin da gudu ta nufi room na ƴarta a lokacin shi ma ya miƙe daga gadon, in baku manta ba ai bata yi mashi alluran barci ba, so idanunsa biyu, yana jin dik abin dake faruwa. Fitowa daga room ɗin ya yi ta hanyar dafa bango, dan jikinsa dik babu karfi ko kaɗan, da kyar ma yake iya motsawa, amma saboda yasan musifar da yake a ciki sai ya yi tinanin dik yadda aka yi shi ake nema yasa aka shigo gidan again.

Cigaba da tafiya ya yi har zuwa wajen staircase, zai taka stair ɗin kenan su Eagle suka banko parlo door. Ganinsu yasa ya fasa sauƙa, dan jikinsa babu wani karfin da zai iya kwatar kansa, sai ya matsa baya, a maimakon ya koma room ɗin can sai ya kara gaba, a nan ya ci karo da room na ƴarta, buɗe door ɗin ya yi ya shiga ciki.

Yana sanya kai daidai lokacin yarinyar ta farka, ta zauna a saman bed tana faɗin. "Mammy I want to dring water". Laluɓar hanya a cikin duhu ya yi izuwa wajen switch, sai da ya kusa kewaye room ɗin kafin ya gano switch ɗin. Kunna light ɗin ya yi, take haske ya gauraye room ɗin.

Da sauri Seraph ta É—ago kanta ganin haske tana faÉ—in. "Mammy a little water......". Bata iya karisa maganar ba ganin mutum a tsaye ga bandeji a hannu, bugu da kari bata iya ganin face É—insa. Wani irin razana ta yi tare da zazzaro voilet eyes É—inta a kansa.

Wani irin kallo ya bita da shi, wanda ita bata san yana kallon nata ba saboda nose mask É—insa, ga p-cap daga cikin hular jacket É—insa.

Cigaba da zazzare ido a kansa ta yi, tana kallonsa from up to down. A daidai lokacin ya ji motsin mutanen, a tinaninsa suna shigowa room ɗin ne, sai dai kuma a lokacin suka wuce da Dr zuwa ICU ɗinta. Jin motsinsu yasa ya daure tare da takowa izuwa wajen bed ɗin nata. Hannunsa ɗaya mara ciwon nan ya sanya tare da ɗaukar yarinyar, tana ƙoƙarin kurma ihu ya yi amfani da hannunsa mai ciwon ya rufe mata bakda tafukansa.

Wajen view ɗinta ya dawo, da kyar ya iya buɗewa, tana ƙoƙarin kwace kanta ya dake suka fita ta view ɗin, a saman wani ɗan dakali a wajen ya zauna da ita a jikinsa. Ƙoƙarin kwace kanta ta fara yi da iya karfinta, ganin zata iya ja su faɗi kasa tin da wajen ba wani mai faɗi bane, irin dakalin nan ne da ake yi na saman window ɗin toilet ko na ɗaki hakan nan ne, to a wajen window toilet suka zauna, ganin zata ja su faɗi ne yasa ya sanya hannunsa ya zame hular jacket ɗin kansa, ya ɗan kawar da p-cap na kansa gefe dan ta samu damar ganin idonsa, sai ya zame hannunsa daga bakinta ya ɗago haɓart suna fuskantar juna.
Chapter 19 · 0% Book details