← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 227

Sashe 84

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan GAT ya katse kiran ajiye wayar V ta yi tare da miƙewa ta fito wajen tantin nasu, magrib ta kawo kai, rana ta faɗi. Can ta hango sojoji sun kunna wuta a wajen tantin su Noor, kuma dayawan sojojin suna wajen, ajiyar zuciya ta ɗan sauke tare da juyawa zata koma ciki kenan sai ji ta yi ta bugu da kirjin mutum.

Slowly ta ɗago kai suka kalli juna, a ɗan shagwaɓe ta ce. "Zaka fasa mun kai ne my Romeo?"...... Cikin zafa ya jawota jikinsa ya rungume, ajiyar zuciya ya sauƙe kafin ya ce. "I missed you over my Juliet"........ "Miss you more, amma ina zaka je a daren nan? Duhu fa ya fara".

ÆŠan raba jikinsu ya yi tare da kai hannunsa ya É—an shafi tula-tulanta ta cikin riga kafin ya ce. "Na zo tabbatar da kinci abinci ne"...... Bin kirjin nata da kallo ta yi, suna mashi kwalele ta cikin riga shiyasa ya shafasu, É—an turo mashi baki ta yi kafin ta rike hannun nasa a cikin nata. "Ina da small chop a rucksack É—ina zan ci kawai". Ta bashi amsa....... "No, sojoji suna mana girki, yakamata ki ci abinci sosai". Tana É—an turo baki ta amsa da. "Zaka bani a baki?".

Kai ya gyaɗa mata alamar kwarai, da sauri ta faɗo jikinsa tare da cewa. "Let me remove my uniform, in canza sai na fito".......... Da okey ya amsa kafin ya raba jikinsu, ta koma ciki shi kuma ya wuce zuwa tantin da Leo yake a ciki. Ita dai Arya tin suka zo aiki take yi, bata huta ba, ƙoƙarin ganin sun yi abin da ya kawosu sun koma shi ne a gabanta ba shiririta ba, haka shi ma Leo, tin da suka zo bai zauna ba, yana ta ƙoƙarin ganin sun yi abin da ya kawosu sun koma, dan akwai gagarumin aiki a gabansu, mission 5 ba wasa ba, basu da lokacin ɓatawa.

Sojoji uku ne suka kunna wuta suna masu girki lafiyayye irin wanda ake masu a barrack, sauran sojojin 6 sun kewaye tantinan nasu da bindigu a hannunsu dan tabbatar da tsaro, saura sojoji 7 kuma suna wajen wutar da suka hura suna hira, banda su Arya su dikka sojoji 24 ne, ku ciri sojoji 4 na room one which's Leo, Noor, Zaynish and Vash, kunga saura sojoji 16, to ga bakwai suna wajen wutar da aka hura suna hira, ga uku wajen girki kunga goma, shidda na kewaye da tantinansu suna basu tsaro, lissafin ya fita daidai kenan, in da su Arya ne sojoji 28 ne a wajen.

Zaynish yana cikin tantinsu shi da Vash suna hira kan yadda mission ɗin nan zai kaya, tin da suka shiga basu fita ba. Amma after like 3h bayan sun yi sallar magrib and ishai, Leo ya jasu sallah, musulman cikinsu kenan, sai dikkansu suka nufi wajen wutar da aka kunna, suka ƙara ƙirare a ciki, suka zazzauna suna hira, amma ban da Leo a cikinsu, shi yana cikin tantinsa rike da waya yana chatting da Yah Aryan ɗinsa, da alama ya fi shaƙuwa da Aryan fiye da kowa.

Ita ma Arya bata fito ba, tana É—aki, su V ne dai bayan sun kammala abin da za su yi ita da Angelina sai suka fito, suka nufi wajen wutar, ita kuma Manassa a bakin tantinsu ta tsaya tana kallon yanayin wajen da hasken wata ke haska ko'ina.

A lokacin da su V suka isa waje dikka sojojin suna zaune a kusa da wutar saboda sanni, sojoji uku da suka yi girki sun zubawa kowa nasa, ƙananan sojoji sun bi sun rarrabawa kowa, Noor ya ɗauki na Leo ya kai mashi cikin tantinsa, while Angelina ta ɗauki na Arya da Manassa ta kai masu, haɗaɗiyar jolof rice suka yi, sun kware a iya girki sojojin, dan suna daga cikin sojojin da aka baiwa horon girki, shiyasa ma aka haɗasu da su.

A kusa da Noor V ta zauna a ƙasa saman farin yashin dake wajen, ta fuskanci wutar dake ci kaɗan-kaɗan tare da fara tsintar kirare ƙanana tana zubawa a ciki wutar ta kara ruruwa. Angelina kuma ta ɗan gefe ta zauna tana danna waya, hankalinta sam baya a kansu, chat ma take yi da aunty Lisa ɗinsu.

Sojojin sai hira suke yi, Juraiz da Unays and Ameer sai hira suke yi, ƙananan sojojin dake tsaitsaye a kansu dan ba mate ɗinsu bane waɗan nan 12 na bar 2 ɗin, Noor ne ya umarcesu da su zauna ayi hira da su, kun san shi yana da sauƙin kai, baya zafafa al'amurra, ya ce idan ba'a bakin aiki suke ba su rinƙa zama tare da juna, misali kamar yanzu da suke zaune ana hira ai ba a bakin aiki suke ba, dan haka babu wariya, ya umarcesu da su zauna.

Sun ji matuƙar daɗi, haka suka zazzauna cikin farinciki, nan dik suka haɗe suna hira. Dik bayan minti ɗaya sai Unays ya ɗago ya saci kallon Angelina, shi kuma Juraiz sai faman satar kallon V yake yi, ita kuma ta kurawa wuta ido tamkar mai wani tinani, sai da Noor ya ɗan ja dogon hancinta, ajiyar zuciya ta sauke tare da juyawa suka fuskanci juna, can ƙasa yadda kowa ba zai ji ba ta ce. "My Romeo zaka fara ko?".

Fakar idanun yaran nasu ya yi tare da jawota baya, ta dawo daidai da shi, ɗan zubawa juna ido na ɗan lokaci suka yi kafin ta zare kallonta tana ɗan murmushi. Da yake ta ɗan yi baya da wutar sai ya zamana haske baya haskasu sosai, hannu Noor ya kai ya ɗan matsa mata tula-tulanta yana ganin kwayar idanunta. Ɗagowa ta yi suka kalli juna kafin ta riko hannun nasa, ta fahimci wani abu da shi, yana balain son tula-tula, babu abin da yake taɓawa a jikinta irin kirjinta, kuma idan zasu haɗu sau dubu idan ya kalli face ɗinta sau ɗaya sai ya kalli kirjinta sau uku, ga su masha ALLAH da su, kai ka ce ta kai 18 years, sun cika ɓul-ɓul kamar an hura balo-balo, sannan ta sanya roba top da ya bayyanar da su sosai, dole hankalinsa ya tashi sosai, komai sai motsawa take yi, kawai ya daure ne.

Miƙewa Angelina ta yi, ta ɗan ja gefe tana amsa call na kiran Aunty Lisa ɗinsu da ya shigo yanzu. Binta da ido Unays ya yi yana haɗiyar yawu, dan tana cikin wannan shiga tasu dai mara kan gadon nan, watau wando guntu zuwa gwiwa, da roba top, amma ta ɗan ɗaura army jacket a saman kayan saboda sanyi, kafafunta sanye da crop, ita kuwa V haka ta fito babu jacket ɗin.

Fitowa daga tantinsu Arya ta yi, ta nufi tantin da Leo yake a ciki. Excuse tai mashi ba tare da ta jira ya amsa ba ta afka ciki. Yana tsaye a tsakiyar É—akin daga shi sai shorts irin matsastsun nan, daga sama farar singlet ce, fita yake son yi zuwa wajen koramar can ya zuba ruwa a jikinsa, shi ko sanyin da ake yi ma baya ji.

Ɗakin nasa akwai light na sola bulb da aka sanya mashi, so hasken ta haska shi da kyau. Ai tana ɗaura idanu a kansa sa da ta ji gabanta ya faɗi, zuciyarta ta kaɗa, amma saboda karfin hali irin na yarinyar nan bata nuna ba, ta ɗan yi ƙasa da ido tana satar kallon kyakkyawan surar jikinsa, musamman golden hair ɗinsa da ta sha kitson kalba, ya ɗaureta yai tuntu da jekar kitson, gashin sai kyalli yake yi. Da yake ta bawa kofar shigowa baya ne sai ta kurawa tuntun gashin nasa ido tana yaba kyan gashin a ranta, amma dik da dare ne ta hango wani zane a bayan wuyansa ƙasan tuntun gashi kamar zanen fuskar wani abin, ta so gane menene amma ya yi nisa da ita, bata gani sosai.

Ba tare da ya juyo ba ya ce. "Menene?"....... Sara mashi ta yi kafin a dake ta ce. "Akwai motsi kilo mita 10 daga nan in da muke, ta yammaci"...... Shiru bai yi magana ba, amma har cikin ransa ya jinjinawa yarinyar nan da kwazonta, yana son mutum mai mayar da hankali a kan abin dake gabansa, ta É—an burgesa gaskiya, bata tsaya shirme ba, tin da suka zo take bincikar sassan dajin nan har sai yanzu da ta gano wani motsi, ko abinci bata ci ba.

Dogon tactical trouser É—insa ya É—auko, ko kaÉ—an bai damu dan tana É—akin ba, a gabanta ya shirya ba tare da ya juyo ba, ita ma da karfin hali bata fita ba tana jiran amsansa, kirjinta tamkar zai fashe saboda bugawa, amma karfin halinta ya zarce umarnin da zuciyarta ke baiwa gangar jikinta.

Lallausan t-shirt ya sanya a jikinsa fara kal, sai da ya kammala tsab sannan ya juyo, ba tare da ya kalleta ba ya wuce ya fita. Ajiyar zuciya ta sauke tare da dafe saitin kirjinta dake barazanar tarwatsewa, sai da ta É—auki second 10 sannan ta samu damar juyawa ta dallah wa bayansa harara, ta ja siririn tsaki kafin ta rufa mashi baya.

Kafin ta fito ya shige cikin tantin nasu, a gaban laptop É—inta ta iskoshi tsaye yana kallon alamar motsin dake wajen. A gefensa ta tsaya tana É—an É—aure fuska, ji take tamkar ta kaiwa wannan lallausan kumatun nasa cizo ko zata huta da takaicinsa. Katse mata tinanin mugutar da zata mashi da take yi ya yi ta hanyar cewa. "Babu yadda za'ayi ki iya É—auko sautin dake wajen ne?". Ya yi maganar ba tare da ya kalli in da take ba.

"Zuwa da safe zan yi ƙoƙarin hakan". Ta bashi amsa ciki-ciki. Juyawa yai ya nufi kofar fita, dab zai fita ya ce. "Ina buƙatar sautin dake wajen". Daga haka y fita. Sosai ta kara jin haushinsa, dik ƙoƙarin da ta yi ko ya yaba mata, bai yi ma kamar ta taɓuka wani abu ba, kai ALLAH wadaran halin Leo. Siririn tsaki ta sake ja tare da komawa gaban laptop ɗin tana hura kumatu game da tsuke ɗan baki, ta cigaba da ƙoƙarin ganin ta gano ke yake wajen.

-----------------------🔥

WS-HOSPITAL.
Chapter 84 · 0% Book details