← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 177 OF 227

Sashe 177

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jinjina kai Leo ya yi alamar kwarai kuwa. "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, ina ake son Æ´an Avaris su sanya ransu? A hukuma azzalumai, a shuwagabannin azzalumai, a makaranta azzalumai, a kasuwa azzalumai, a asibiti azzalumai, a koina azzalumai, ina suke son jama'a su sanya ransu? Wa suke son su kaiwa kukansu ya tsaya masu?"..

A taƙaice Leo ya ce. "ALLAH, shi kaɗai zasu kaiwa kukansu kawai, amma basu da wata mafita, a ko'ina akwai gurɓatattu"....... Vash ya ce. "Basa tsoron mutuwa"........ Zaynish ya ja dogon tsaki game da cewa. "Sun manta akwai mutuwar ne ai, sun manta akwai ranar da zasu tsaya gaban ALLAH su zayyana dik abin da suka aikata".

Noor dake ƙoƙarin haɗe guys ɗin can ya ɗauresu da belt ɗinsa da ya kwance ne ya ce. "Ni fa ina son addinin nan naku, saboda naga akwai adalci sosai a cikinsa, kome zaku faɗa bisa adalci kuke faɗa".

Ai da sauri Leo ya ce. "Are you sure kana son shiga?"....... Kai ya gyaɗa a lokacin da yake ɗago guys ɗin ya saɓa a saman shoulder ɗinsa. "Ina son shiga, bro kyawawan halayenku sun ratsa zuciyata, ibadarku, komai naku akwai kyau, ina son shiga"........ Da sauri Zaynish ya ce. "A'a to sauƙe waɗan nan mutane ka karɓi shahada yanzu".

Jinjina kai Leo ya yi tare da sauƙe mutumin da ya ɗauka a ƙasa, ya zo ya rungumi Noor yana faɗin. "Ba zamu iya jiran sai mun isa sansani ba, yanzu kawai ka furta shahada"..

Ba karamin daɗi Noor ya ji ba ganin suna ta murna dan zai shiga addininsu, aikuwa hakan ya ƙara mashi kwarin gwiwa, sai ya sauƙe mutanen, Leo da Zaynish har suna haɗa baki wajen karanto mashi shahada, ya maimaita, ya ALLAH, su kaɗai suka san irin daɗin dake ransu, rurrungumesa suka yi, Vash mai karnuka ma zuwa ya yi zai rungumesa Noor ya ja da baya yana faɗin. "Bro, ba da dogs ɗin nan ba, ka bari sai mun koma sansani ka".

Murmushi Vash ya saki yana ja da baya. ALLAHU AKBAR, yau Noor É—inmu ya zama musulmi, ya rabb, yau ranar murnace a garemu mu team NOOR.

Haka suka kwashi mutanen, a lokacin 5 na asuba ta yi, gari ya fara haske, kai tsaye suka ƙarisa wajen sansaninsu, cikin dabara suka shiga sansanin, in baku manta ba ai fitar sirri suka yi, kai tsaye tantinsa Leo ya ce su kai mutanen, already biyu daga cikinsu sun mutu, ɗaurin goro yai masu ya barsu a ciki.

Ya fito da sauri ya nufi wajen tekun nan dan ya yi wanka su yi shirin sallar asuba, lokaci ya yi, while a daidai lokacin ita ma Arya ta fito dan ta je ta yi wanka, ita tana son yin wanka a lokacin da jama'a suke barci, dan yana son shiga gefen tekun nan wajen ƙorama ta yi wankarta, bata son shiga toilet ɗinsu na nan sansani.

Zuciyarta cike da tinanin su Leo basu dawo ba, dan ita tasan basa nan, ta damu sosai, kai tsaye cikin tabkin wajen ƙoramar ta nufa, hannunta rike da soap ɗinta and gel, ta ratayo towel ɗinta a wuya, while tana sanye da pjs a jikinsa, su V dik suna barci, saura sojojin wasu suna wajen wutar da suka hura, wasu kuma suna cikin tantunansu.

Da yake wajen akwai duhu saboda duwatsun ƙoramun, sannan gari bai waye sosai ba, dan 5:20 ne a yanzu, so hakan yasa bata ga Leo ya cikin ruwan ba. A saman wata karamar dutse ta tsaya, ya cire pjs ɗin jikinta kaf, ta ware dogon silky ash hair ɗinta da ya kai mata har ƙugu, ya rage daga ita sai wani ƙaramin vest zuwa cibiya wanda bashi da hannu, daga ƙasa pant fari tas mai kyau.

Zama ta ya bakin dutsen tare da sanya dogon kafarta dake É—aure da diamond chain mai kyau a cikin ruwan, ita tana saka chain da waist beat dan kwalliya, amma su V basa sakawa. Ajiye kayanta da towel É—in a saman dutsen ta yi, ta ajiye su gel É—inta ma.

ÆŠan rintse idanu ta yi tana faÉ—in shiiii alamar ruwan da sanyi, sai kuma ta É—an ja tsaki game da cewa. "Ko ina su sir Nirash suke? Sun samu nasarar abin da suka je nema? Ina masu fatan cin nasara". Ta sake jan tsaki tare da datse idanunta, da sauri ta faÉ—a cikin ruwa tana faÉ—in shiii sanyi.

Dik abin da take yi a kan idanun Leo, amma ita bata farga yana cikin ruwan ba, da yake yana can tsakiya. Linƙaya ta fara yi yana juyi a ciki tana jin daɗin ruwan............ Nima na juya alƙalamina dan ba'a kansu kawai zan ƙare page ɗin ba, zamu dawo anjuma mu ga ya zasu kaya a cikin ruwan nan, ga Noor ya musulunta, Zaynish da yankar wuƙa a hannu, ga haɗaɗɗun karnuka guda biyu da muka samu, ga waɗan nan miyagun da muka kama, kai ga-ga ɗin ma yawa me da shi fa. Bari dai mu je mu dawo.

--------------------------🔥
CRYSTAL PALACE.

"Daddy please talk to me, baka da lafiya ne?". Tamkar zata yi kuka ta yi maganar. Hannunsa yasa ya laluɓo nata hannun, ya ƙanƙame cikin nasa, can ƙasan maƙoshi ya ce. "Stop crying kada abin ya mun yawa kin ji my Cherry?".

Ajiyar zuciya ta sauƙe, da kyar ta iya cewa. "Daddy na bari, amma ka faɗa mun me yake damunka ne, baka da lafiya ne?"....... Ɗan matse hannunta a cikin nasa ya yi, yana ɗan lumshe idanu ya ce. "Ban taɓa maraicin uwa ba sai yau, ban taɓa jin zafin rasa Ummiena ba sai yau, my Cherry please ina son farinciki na musamman ta ɓangarenki kin ji?". Ya faɗa tare da juyo da jikinsa ya kwanta a miƙe.

Hannunta É—aya ta É—aura a kan lion chest É—insa. "My gentle chaos, zan yi dik iyawata wajen ganin na wanzar da farinciki a tattare da kai, yanzu dai faÉ—a mun baka da lafiya ne?". Ta kai karahe tana É—an sunkuyo da kanta a kansa kaÉ—an, ta É—an É—aura goshinta a kan nasa......... Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Lafiyata lou, kawai ina cikin damuwa ne, na tina Ummieta".

"Daddy na yi alƙawarin sanyaka farinciki tamkar yadda Ummie take sanyaka"......... Ɗan miƙewa ya yi, ya koma yai kwamciyar ruf da ciki, ya ɗago kansa suna kallon juna, zallar madarar kaunarta ne kwance a cikin kwayar idanunsa, in a low way sosai ya ce. "Are you sure?". Ya faɗa yana ɗage mata gera guda. ALLAH sarki har ya mance me Abba yai mashi, masoyiya ta kwantar mashi da hankali.

Tafukanta ta ware, kumatunsa dikka biyu ta tallabo, tana murmushi ta ce. "I'm very sure my gentle chaos". Ta faɗa tana ɗan matse kumatun nasa....... Zuba mata idanu ya yi yana jin wani irin tsantsar kaunarta na ratsa mashi zuciya, haɗe fuskokinsu ta yi, ko kunyar kallon cikin kwayar idanunsa bata yi, a shagwaɓe ta ce. "My gentle chaos ina sonka sosai".

Wani irin kallon kauna ya É—an bita da shi kafin in a low way sosai ya ce. "Love you more, from the button of my heart, love everything about, coz you're special".

Ɗan ɗagowa ta yi, ta sumbaci gefen lallausan kumatunsa, tana murmushi. Hannu yasa ya shafi soft cheek ɗinta game da lumshe idanu, a cikin ransa yana jin zai samu hanyar rabuwa da Rimsha, shi bama wai rabuwa da ita ba, bai damu ba dan bai ɗauketa mace ba, bai yarda matarsa bace dama, amma dai koma me yana tsoron ɓacin ran Seraphina sosai, shiru ya yi yana tinani, can ya tina why not ya haɗa guru da Rimsha? Saboda Abba yana da abu guda ɗaya, idan Rimsha da kanta ta same shi ta ce bata son Aryan lallai zai yarda ya raba wannan aure, hakan kuma ba zata faru ba har sai Rimsha ta faɗa son wani.

Da alama hanya ce ta haɗuwarta da guru wannan aure nasu, tabbas zai ɗauketa ya kaita gidansu, ta rayu a cikinsu matsayin sister ɗinsa, daga nan guru zai fara sonta, idan soyayyarsu tai zurfi Rimsha ba zata iya rabuwa da shi ba, tabbas zata faɗawa Abba bata son shi, shi kuma zai raba wannan aure nasu, daga nan shi kuma Aryan ɗin bayan ya saketa ya aura mata scorpion ɗin, tabbas zai wahalar da ita ta yadda ba zata taɓa jin son shi a ranta ba, hakan zai sa ta fara son guru da wuri ayi komai a gama. Lallai wannan shawara ta yi, tina haka yasa ya sauƙe dogon numfashi....... Lallai nima na shaida, wannan wata hanyace ta haɗuwar Rimsha da guru, ko kuma Lion da Rimsha ba........... 👀

Cikin zolaya ya ce. "My Cherry yanzu idan na ce mata biyu zan aura zaki yarda?"........ Zazzaro idanunta a kansa ta yi, sai kuma ta tamke fuska tamau. "No daddy, ni kaÉ—ai zaka aura, babu wani mata biyu!". Tana hura dogon hancinta ta faÉ—a, zallar kishinsa ya gani kwance a cikin kwayar idanunta tin ma bata san menene auren ba.

Kai ya jinjina tare da cewa. "Yadda kike son kawarki Rimsha É—in nan ba zaki yarda ku auri miji É—aya ba?"........ Siririn dariya ta É—an yi kafin ta ce. "Mijina ni kaÉ—ai ne, ita ma mijinta ita kaÉ—ai zata aura!". ....... "But why?". Ya tambaya cike da mamaki, dan ya zaci sai wacce tasan aure take kishin mijinta ai.

Hannu tasa ta rufe fuska tana murmushi game da cewa. "Daddy ba kace in daina maganar da bata dacen can ba?". Kai ya jinjina alamar haka ne ya hanata, ohk sai yanzu ya gane nufinta, watau ba zata yarda wata mace ta raɓesa har ya haɗa jiki da ita ba, lallai Seraphina ta wuci tinaninsa, miƙewa zaune ya yi, sai ya canza topic na hirar kafin ta jefa mashi wata maganar ta juya mashi ƙwaƙwalwa.

Ƙarisa hayewa saman gadon ya yi tare da kwanciya da kyau, ya jawo pillow ya ɗaura a kan kirjinsa, yana binta da wani irin narkakken kallo mai narka zuciya ya ce. "Ina jin kamar ke na rumgume ba pillow ba, zan yi barci kada ki tasheni".
Chapter 177 · 0% Book details