Sashe 57
Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bari in warware maku wani abu, dan bana son kwakwalwarku ta shiga ruɗani sosai, ainahin ruɗani yana gaba, to idan kuka fara rikicewa tin yanzu kwakwalwarku da wuya ta iya ɗaukar ruɗanin gaba, shiyasa yanzu zan warware maku wannan rikicin kam, idan na so kara rikitaku ba zan warware maku ba, sai dai in ce maku Leo da Zayra'an suna zama a wani gida ne daban, hakan zai nuna maku kamar basu da alaƙa da IRON FIST, kada ku manta CRYSTAL PALACE tana da gidaje dayawa, dan haka ba lallai Leo ya zauna da IRON FIST gida ɗaya ba idan na so rikitaku, sai dai ba zan so ku rikicen ba! Dan haka mu je ku ji su waye su na hakika tin yansu kafin mu shiga ainahin ruɗani.
IRON FIST su da a farko suka kasance jiga-jigan jami'an da AZURE ta yaye a shekarun baya ya aka yi suka rikiɗe suka zama terrorists? A lokacin da Lion ya je ɗaukar Leo a Barrack ai na faɗa maku shi ɗin babban jami'i ne da Azure ta yaye ko? To ya aka yi suka rikiɗe zuwa ƴan ta'addan da duniya ke nema? Meyakefaruwa ne?. Kamar yadda kuka ji ne! Leo kanin IRON FIST ne amma ba tare da yasan su ne IRON FIST ɗin ba, kuma kamar yadda kuka ji, IRON FIST jami'ai ne da AZURE ta ya ye. Akwai babban dalilinsu na rikiɗewa su koma terrorists a idanun duniya, da farko fansa suka shiga ɗauka, sun ga akwai dalilai da dama da zai sa su cigaba da abin da suke yi shiyasa suka cigaba bayan gama ɗaukar fansa, in taƙaice maku labari su ɗin ba terrorists kai tsaye bane, duniya ke kallonsu a matsayin terrorists, amma su ɗin Earthsentinel.
Yes confirm ana basu kwangilar kashe rai, kuma suna kashewan, amma su sun san irin waɗan da suke kashewa, wai kun san kai tsaye su waye su kuwa? Ba zaku taɓa gane karatun a yanzu ba, dan dik yadda kuke tinaninsu sun zarce nan, su ɗin faɗa suke yi da duniya gabaɗaya ba iya ƙasarsu ba, suna da kaifin kwakwalwar da gudun aikinta ya zarce gudun bullet ɗin sniper gun, sun yi gagarumin zama dan tinanin mafita ga duniyarsu, a nan suka gane daga in da matsalar duniya na farko ta samo asali, watau idan suna son gyara a farko dole sai sun kawar da demokraɗiyya daga idon duniya, sun cire sonta da aka cusawa al'umma, idan ba haka ba, babu abin da zai gyaru a duniya!. Shiyasa suka sayar da ransu gabaɗaya.
Dik waÉ—an da suke bin mulkin demokraÉ—iyya a cewarsu juya mutanen ake yi ba raÉ—in kansu suke bi ba, dan haka demokraÉ—iyya ita ce abin da zasu fara kawo karshenta, idan waÉ—an nan Team ukun suna tinani kuma suna hasashen abubuwa zaku zaci ba mutane ne ke magana ba, saboda ALLAH ya basu baiwar da hasashensu yake zamana gaskiya, a kullum da hasashensu suke aiki ba da bincike kai tsaye ba, yes suna binciken, amma dan su tabbatar da hasashensu suke yi, kuma suke samun nasara.
Takaitaccen tarihinsu, sun taso ne su ukun nan, tin suna yara, da guru da Lion basu san iyayensu ba sai dai iyayen Champion kawai, sun rayu cike da son juna, tin suna yara idan ka taɓa ɗaya daga cikinsu haɗuwa suke yi sai in da karfinsu ya kare, amma a hakan kada ku zaci basa faɗa! Kunga Lion da Champion mugun faɗa suke yi idan ta kwaɓe masu, guru ne ɗan ba ruwana, shi ne kuma mai sulhuntasu, idan suka ɓata Champion ya tafi ɗakinsa yaki kwana da Lion, in ya je ya gagara yin barci, shi ma Lion ya gagara yin barci, abin dariya sai Lion ya ce da guru ya je ya lallaɓa Champion ya dawo su shirya, shi fa Lion ɗin ba zai je ba, dan dikkansu suna ikirarin ba zasu taɓa furta kalmar sorry ba a rayuwarsu, dan haka ba zai cewa Champion sorry ba.
Idan guru ya je ya lallaɓa Champion ya dawo fa sai dai ya samu waje ya zauna saman gado, babu mai cewa wani kala, a haka zasu yi barci cikin jin daɗin zasu kwana waje guda, washegari faɗar zata kare, dan suna tashi daga barci zasu fara yi wa juna magana, to haka suke har suka girma, yanzu haka in ta kwaɓe masu suna iya gwabza faɗa, guru ne middle man a cikinsu mai sulhu, kuma kun san zafin zuciya da zafin zuciya idan ta haɗu dole ake samun haka, ga su da kafiya, halinsu iri ɗaya, ba wanda zaka tankwara a cikinsu ya tankwaru, kowanne idan ya yi magana ɗaya ya yi ne, kunga dole a gwabza idan ra'ayi ta banbanta a kan abu. Guru dai yana nan kamar Manassa, komai normal ne a wajensa, ya fisu hakuri, kuma shi yana iya control zuciyansa, shiyasa basa faɗa da shi, kuma shiyasa shi ne mai lallaɓasu ya masu sulhu, amma waɗan nan biyun, da Lion da Champion, balai, ai in aka samu saɓanin ra'ayi abin baya kyau jama'a, faɗarsu gara faɗar dawakai, amma su in ta kwaɓe sai sun yi damaging na komai a wajen da suke, su jiwa kansu ciwo, kuma su yi fushi da juna, amma su gagara barci idan ba tare ba.
To a taƙaice kun ji su waye Lion ko, to bari ku ji waye Champion, kun tina Dr Aryan na gidansu Rimsha? Shi ne ainahin Champion, shiyasa da zasu je AZURE ƴan albarkan suka rufe fuska da nose mask, dan in dai GAT ya gansu sai ya ganesu, ai na faɗa maku shi ya horasu a lokacin da suke matasan sojoji, kunga kuwa tsab zai ganesu, dan Champion da Lion dik sun je AZURE a ranar, amma babu wanda ya san sune, guru ne bai je ba. Masu ta cewa kai yayan Leo ya haɗu matuƙa to yayan Leo dai shi ne Lion na IRON FIST, kuma dik da baku ga ainahin fuskansa ba yana sanye da nose mask wannan shi ne ainahin kamanninsu shi da Champion, kamanin da duniya take neman gani ruwa a jallo ta rasa.
Kun san kuwa tin da su Lion suka kuduri niyyar kawo karshen dik wata zalunci da munafurtan al'umma da ake yi dole ne dama a kirasu da ƴan ta'adda, dole ne a nemi ko da halin yaya ne yadda za'ayi a gama da su, an shafa masu bakin fenti cewa su ƴan ta'adda ne, an sanya dik wani ɗan ƙasa yana jin tsanarsu, dan su suna kisa ne bisa radin kansu ba dan a yaba masu ba, dan haka basa fitowa su sanar da al'umma cewa gurɓatattu suke kashewa, su kuma manyan duniya suna fitowa ne su nunawa al'umma cewa mutanen kirki IRON FIST ke kashewa! Yanzu kun gane dalilin da yasa kenan aka tsanesu kuma ake kiransu da ƴan ta'addar da duniya gabaɗaya take nema ko?.
Aikinsu na faɗa maku wa duniya gabaɗaya suke yi wa ba ƙasa ba, dan haka ko shugaban wata ƙasa ce yake aikata ba daidai ba suna kashesa ba sai iya na kasarsu ba!.
Yauwa yanzu kun gane dalilin da yasa Champion ya hana Rimsha shiga motarsa a school da ya je kenan ko? Saboda shi ne Dr Aryan, kuma ya tsani Rimsha kun sani! Ba da ainahin fuskansu suke fita ba in baku manta ba, shiyasa Rimsha bata ganesa ba, ai kun san da ta san shi ne ko kusa da motarsa ba zata zo ba, amma bata sani ba. TO A TAKAICE WAÆŠAN NAN SU NE IRON FIST, SAURAN BAYANI ZAKU JI A GABA.
Ga shi dai kuna gani an cusawa su Leo tsanarsu, an ce zasu yakesu a cikin FIVE MISSION da zasu tafi ɗin nan, to ALLAH yasa su yi sauran 4 mission ɗin lafiya, shi kuma na biyar ɗin dani da ku dik mun san abu ne mai wahala gano su waye IRON FIST, dik da cewa Leo yana da karfin hali da kaifin ƙwaƙwalwa ne irin na yayan nasa, amma babba kam babba ne a ko'ina, idan suka yi wasa Zayra'an zai gwada masu fifikon iya aiki, amma zamu ga yadda zata kaya kam. Ku baku yi mamakin yadda halin Leo and Lion yake kamanceceni ba kafin ku san su waye su? Baku yi mamakin yadda halin Vash and Champion suke kamanceceniya ba?.
Note, family ɗin Aryan basu san cewa yana ɗaya daga cikin IRON FIST ba, shiyasa ma ya yi karatun likitanci dan ɓadda kama, Ammie bata sani ba, haka su Faryan basu sani ba, to ku kaɗai na faɗawa, Dr Aryan Dr ɗin ɓadda kama dai shi ne Champion namu na amana, ko Seraph bata san ainahin kamanninsa ba, amma kunga ita Rimsha ta sani, watau a littafin nan akwai rikici ne na kin karawa, kai kun san me nike hangowa a gaba kuwa? Ban son rikicewar tai maku yawa ne, yanzu ai nasan kun gane karatun ko?. To mu koma kan labarinmu.
---------------------------
Kai tsaye room na yayansa ya nufa. Tsaye ya isko yayan nasa yana rike da waya tankar yana typing wani saƙo ne. Gado ya wuce ya zauna yana faɗin. "Brother tin da na dawo ban ga Yah Champion and Yah guru ba, ina suka je?"........... Yana rufe baki sai gasu sun shigo a tare, dikkansu yau da ainahin fuskokinsu, dan basa ɓoyewa Leo kansu a matsayinsa na ƙaramin ƙaninsu kuma ɗan zamisan da suke son rena ya zama bakin damisa kamansu wanda ko sun rasa ransu a wannan aiki sai maye gurbinsu, shi ne dalilin da yasa suka turashi AZURE, kuma shi ne dalilin da yasa Aryan ya tura Vash ma AZURE, dan su kansu sun yarda da horon AZURE, suna son renon kannen nasu ne su zama tamkar su, ta yadda ko sun mutu zasu karisa masu aikin da suka fara. YANZU WASAN ZAI FARA.
Amma fa still sun hana masu karatu ganin kamanninsu, dan kuwa suna sanye da nose mask dikkansu a yanzu ma, kuma daga yawonsu suka fito Æ´an albarka.