← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 227

Sashe 102

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na Lion ya sha kitso kalba a wajen Aryan, ya ɗaure mashi gashin nasa yai mashi tuntu da jelar, kitson tai masifar kara mashi kyau na gasken-gaske. Shi kuwa Aryan arabs hair garesa, kada ku manta shi bakuraishe ne, gashinsa irin dark blue ɗin nan mai sheki wanda zaku zaci ma baki ne in baku kallah sosai ba, gashin ɗan daidai ne a kan nasa, bata wuci zuwa bayan wuyansa ba, yadda dai gashin larabawa yake, yana kwance luff yana wani irin sheƙi, ga wasu gajeru guda biyu da suka zubo mashi ta gaban goshi sun yi nannaɗa sosai, while na bayan kuma suna kwance kuff sun yi bayan wuyansa. Ya ALLAH idan kuka ga Aryan ko, yadda yai gyaran gashinsa tamkar shararren ɗan soyayya, ga dikkan alamu yana cikin soyayya!.

Shi kuwa guru ba zan ce komai a kansa ba saboda yana sanye da nose mask, yana zaune gefen bed rike da waya yana latsawa.......... Bayan Aryan ya bar wajen Seraphina ya fita ne ya wuce office É—insu bai je wajen Abba ba, daga office ya dawo gida, ya rufe sim É—insa da su Abba suka sani ya buÉ—e na iya nasa da su Lion, shiyasa Seraphina ke ta faman kiransa number a kashe.

Bayan sun kammala shiryawa suka É—auko haÉ—aÉ—É—un nose mask É—insu suka sanya, irin nose mask masu rufe har saman hancinsu É—in nan ne, iya kwayar ido zaku gani, and dikkansu hat suka sanya a kansu dan shi ne ya dace da shigar tail coat.

Wani irin diamond watch mai bala'in tsadar gaske suka ɗauko iri ɗaya, a tare suka fara sanyawa a hannunsu, sai dai su sun kammala sanyawa na Lion kuma ya zame ya faɗi ƙasa a ƙoƙarinsa na gyara botirin tail coat ɗinsa na wajen hannu dake ƙoƙarin fita.

Duƙawa Aryan ya yi ya ɗauko agogon, sai wani irin kyalli take yi. Tamkar jiya basu doka faɗa kamar zasu kashe juna ba, haka ya kama hannun Lion ya zura mashi agogon tare da sanya mashi maɓallanta, sun yi masifar kyau, suka ɗauko half covers shoes suka sanya a kafafunsu launin baki kalar hat ɗin kansu. Sai tashin daddaɗar kamshin perfume na kamfanin su Noor suke yi.

A jere suka tsaya a tsakiyar É—akin kamar wasu guards, guru dake zaune a gefen bed ne ya kwaso masu wayoyinsu wanda dik bala'in mutum ba'a iya bin diddiginsu. A tare suka jera zuwa waje, cikin zafin nama suke taku dake nuna tsantsar jarumta a tattare da su.

Cikin tsadadden motar Aryan suka shiga, dan basu cika fita da motar Lion or na guru ba, dayawan lokuta dana Aryan suke fita. Suna fitowa harabar side ɗinsu sai ga wasu jiga-jigan jami'ai guda biyar sun biyo elevator sun sauko zuwa in da suke, ashe a hawan dake ƙasan nasu benen jami'ansu na SSO ne, suna tare da su dan basu tsaro na musamman, sun ki yarda su zauna gida ɗaya da jami'an ne saboda su ne IRON FIST, idan suna tare da su za'a iya samun ɓacin rana saboda jami'an SSO akwai basira.

Da yake sune manya cikin hukumar SSO ba ta yadda za'ayi a barsu babu masu basu tsaro shiyasa suka kama masu benen ƙasan nasu dan kada gwamnati ta zargesu. Abin da yasa yanzu ma ba'a zargansu saboda an san su jami'ai ne dake buƙatar sirri na musamman, shiyasa idan suka yi wani abin ba'a zargansu.

Dukkansu gidan baya na motar suka shiga, jami'i ɗaya ya shiga driving seat, sauran jami'ai huɗu suka tada mota guda wanda ya kasance nasu ne dama, already suna da motoci guda 3 kasancewar su 12 ne ke tare da su. Yanzu Aryan ne ya ce jami'ai 5 su zo su tafi, shiyasa basu sauƙo su dikka ba, and dikka jami'an suna sanye da black suit, sun saje da guards dan ɓadda kama.

Aryan ya umarcesu da su wuce da su wuce kai tsaye izuwa airport dan ba zasu ta fi da jet É—insu dake saman benensu ba, kun san kowani bene a CRYSTAL PALACE a sama kololuwa akwai wajen saukar karamar jet wanda yadawa daga cikin manya a CP É—in suna da jirgin kansu wanda yake sama a fake, daddyn Noor ma yana da shi, su Lion suna da shi.

Kai tsaye airport aka wuce da su, jirgi suka hau sai Washington. Suna dira a Washington jiga-jigan motocin jami'an SSO dake wajen already sun yi wa airport ɗin diran mikiya, ta ko'ina kaki ne ke shawagi, an turo masu sojoji, ƴan sanda, har da fighter jet ta sama dan tabbatar masu da tsaro. Ƴan jaridu sun cike airport ɗin tab, ta ko'ina sai snapping ɗinsu pic's ake yi.

Dik kansu kansu a ƙasa a lokacin da suka fito daga cikin jirgin, kowa yana burin samun damar ganin faskokinsu, amma sunki bada dama. Da gudun gaske jami'an SSO suka zo suka yi masu zobe suna sara masu, ga wasu jami'an da suka jera layi tin daga wajen bakin marfin jirgin har izuwa wajen motar da aka tanada masu, rike suke da manya-manyan bindigu waɗan da basa saɓa saiti.

Wargima waje yake samu, domin kuwa babu ɗan jaridan da ya iya keto tsakanin jami'an SSO ya isa wajensu Aryan wai ya ce zai masu tambayoyi, sun dai ja gefe suka masu hotuna har suka shige cikin motocin da aka tanada masu. Da gudun gaske jami'an SSO suka shiga nasu motocin suma, a tare aka tada motocin, a jere suka fita airport ɗin suka nufi white house da su, watau fadar shugaban ƙasa. Yau suna da wani zazzafar meeting ne da manya-manyan kakin dake faɗin ƙasar.

Sunan wannan meeting É—in ma National security high command meeting. A secure intelligence & defense operations room na white house za'ayi meeting É—in.

Meeting ɗin zai fara ne da misalin karfe 12:00 AM na dare kenan, zasu kammala karfe 4:00 AM, gab asuba kenan, yanzu kuma 11:30 suka isa airport, daga airport zuwa fadar shugaban ƙasa zai ɗaukesu 20 mins, zasu shiga a kan lokaci kenan.

Waɗan da za'ayi meeting ɗin nan da su sun haɗa da shugaban ƙasa, ministan tsaro na ƙasa, CDS watau Chief of Defence Staff, COAS, CNS, CAS, NSA, DG, GOC, FOC, AOC da sauran manya dik zasu hallara.

Kowa yasan yadda gidan gwamnatin ke da tsaro da tsari ga haɗuwa, ba sai na tsaya ɓata lokacina wajen yi maki bayani ba. An ƙawata ɗakin taron nan sosai da sosai dan ɗakin yana cikin wani ɓangare na Presidential Villa ne, wall na ɗakin mai tsawon gaske ne, CCTV ta ko'ina, rundunar tsaro ta musamman dake kai komo a arear yadda kuka san cewa idan an barsu zasu iya hana mala'ikan mutuwa ketawa ciki ya ɗauki rai! Babu alamar imani ko wasa a tattare da dik jami'an dake wajen!. Wurin yana da drone surveillance sama da counter sniper system a ko’ina.

Ba a amfani da wayoyi ko internet na jama'a, dik hanyar sadarwan wajen tana military grade encrypted satellite line.

Su kansu jami'an da za'ayi zaman da su kafin su shiga cikin É—akin sai da scan na farko, na biyu voice ID da aka shiryawa na'urar already, na uku badge code da ake basu ana saura minti É—aya meeting. Yanayin tsarin É—akin meeting É—in ba'a magana, dan É—akin round ne ba kamar sauran É—akuna ba, an yi haka ne kuma dan kowa ya dinga kallon juna.

Ga wani haɗaɗɗen tangamemen table launin black oak a tsakiya, an zagaye shi da kujerun masu laushi launin baƙi, kowacce tambarin rundunar ko in ce maku kowacce hukuma kamar soja da Air Force kunga ba ɗaya bane, to kowacce kaki da chair ɗin babban General ɗinta da zai wakilcesu a wajen an manna tambarin kakinsu a jikin kujerar da zai zauna, ga sunan hukumarsu a jikin ɗan karamin signpost a gaban kujerar tasa a saman table ɗin.

Sannan a gaban kowani babba na kowani kaki akwai LED screen panel dan nuna bayanan sirri, bayanan sirri suna fitowa daga secure satellite intelligence feeds mafi aka sari. Sannan akwai babban smart board mai 80 inch a ta gaban ɗakin dake ɗauke da taswirar gabaɗaya ƙasar, daga kudancin kasar har arewacin ƙasar.

Sannan ga hologram table a tsakiyar table É—in nasu, wanda ke iya nuna tsarin harin 3D simulation. CCTV da ke É—akin an saita shi ta yadda ba zai É—auki sautin komai ba sai dai hoto, an haÉ—esa da jammer system.

His excellency yana da matsayi na farko a kan kujerar farko da aka tanada na musamman, dik da tsananin tsaron dake wajen hakan bai hana kasancewa yana tare da security aide É—insa dake tsaye a bayan kujerarsa tamkar sassaken gunki ba.

Daga jujerarsa sai na Ministan tsaro, dan haka komai ya kammala, su Aryan na shigowa É—akin his Excellency ya shigo shi ma, yana shigowa kuma aka kulle kofar babu wanda zai sake shigowa.

Wani irin musulmin natsuwa ɗakin taron ya yi, daga nan zaku fahimci manyan kai ne a wajen, kuma zaratan maza ba ƙananan kwari ba.

Bayan kowa ya ɗan natsu ya sauke numfashi, masu buƙatar shan ruwa sun sha daga cikin ruwan da aka jera a gaban kowannensu, hankalin kowa ya natsu, sai Ministar ɗin tsaro ya miƙe tsaye tare da gyara mic dake saitin gabansa, a natse ya gabatar da dalilin wannan zama da suke yi dik karshen wata, ya kuma gabatar da buƙata daga office ɗinsa, ya shinfiɗe dikkan rahotonnin da ya tattara daga hannun wasu manyan jami'an ƙasa da kuma wasu ƴan majalisu da dai sauransu.

Bayan ya kammala gabatar da komai da shaida ne. Chief of Defence Staff watau CDS wanda shi ne general security strategy, ya miƙe ya kora nasa jawabin, baya ga shi dik Chiefs na Runduna kama daga COAS watau Army, CAS Airforce, CNS Navy, SSO da dai sauransu sai da suka yi nasu jawabin, a jawabin su Lion guru ne ya yi, dan Lion da Aryan basu motsa ba saboda ransu dake jagule, kun san IRON FIST da kaifin ƙwaƙwalwa, tuni sun gano maƙaryatan cikinsu, shi ne nan ransy tai mummunar ɓaci, idan suka ce zasu buɗe baki ko zasu motsa a wajen zasu iya tarwatsa komai, shiyasa shirunsu ya fi masu alkhairi.
Chapter 102 · 0% Book details