← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 201 OF 227

Sashe 201

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dr Kamal ya amsa da. "To ai dama dole sojojinsu su zamana basa tsoron mutuwa, yaki kawai suka sani, to mutane ne wanda sun taso ba su san komai ba face horon da aka basu, babu uwa, babu uba, babu ƴan uwa, shiyasa zasu iya fito na fito da kowacce ƙasa, basu san daɗin iyaye da ƴan uwa bane, basu san daɗin rai da rayuwa ba, abu ɗaya suka sani shi ne su kashe ko a kashesu".

Jinjina kai Dr Mark ya yi. "Haka ne, dayawan manyan ƙasashe haka suke yi, shiyasa duniya take tsoronsu take tsoron sojojinsu, sojojinsu basu tsoron mutuwa, hasalima basu san me daɗin rayuwa ba bare su ji tsoron mutuwa, ba kana gani dik a wajenmu suke sayan jarirai ba, a renesu su zama sojoji, shekaru 17 zuwa 18 ya isa na renonsu".

Shi dai Dr James ko ƙala bai sake ce masu ba tin da ya ce sayar da yaran zai yi a mayar dasu sojiji tin da eggs ɗin suna da karfi matuƙa, shi saboda yasan komai sai bai shiga hirar ba, su Dr Kamal ne ba komai suka sani ba, amma shi ya jima da sanin cewa manyan ƙasashe basu cika amfani da ƴan kasarsu matsayin sojoji ba, suna sayen jarirai ne su renesu su kuma horar dasu, so yasan komai.

A gate É—insu suka tsaya suka yi knocking, da sauri wani guard ya zo ya buÉ—e masu. Ciki suka shiga Dr Kamal and Dr Mark suna cigaba da hiransu.

Lokaci guda suka tsaya cak a lokacin da suka shigo parlo. Slowly Dr James ya sauke kallonsa a kan sister Zinta dake zaune saman sofa ta buga uban tagumi tana ruwan hawaye, while sister Maya na rarrashinta.

Wucewa Dr Mark ya yi tin da shi bashi da wani business dasu, ya nufi É—akinsa abinsa. Kallon juna Dr Kamal and Dr James suka yi. A tare suka tako zuwa in da suke, bai yi magana ba, hannun yasa ya É—auki Zinta cak suka wuce room É—insu.

Sai faman tirjewa take yi tana faÉ—in ya saketa ita kam. Bai direta a ko'ina ba sai a saman gadonsun, a lokacin 5 na asuba ta yi. Fashe mashi da sabon kuka ta yi, zama a gefen gadon ya yi tare da jawota jikinsa yana kokarin rarrashinta.

Ai tana zuwa jikinsa sai ta ji karnin jini, kun san shi wani shegen abu ne da baya ɓuya dik da suna cire kayansu su sanya na aiki a jikinsu, amma sai ya kama fatansu ƙarnin, bare ma ace jinin ɗan mutum, shiyasa suke yin wanka idan sun gama zaluncin nasu ai.

Ta yi mamakin jin karnin jini a jikinsa, amma sai ta kawar da tinanin da cewa. "Ni ka sakeni"....... Saketa É—in ya yi yana faÉ—in. "Menene yafaru kike wannan kuka haka? Yaushe kika tashi daga barci?"........ Tana turo baki ta ce. "Ina ka je? Wajen sister Lazy ko?". Tana dallah mashi hararar da bata san tana yi ba ta yi maganar.

Wani irin dogon ajiyar zuciya ya sauke, shi ya zaci ma wata matsala ce babba, nisawa ya É—an yi. "Baki ga mu uku muka dawo bane?"...... Tana kallonsa bata yi magana ba..... "Mun je duba babys É—inku ne basu da lafiya, akwai babyn da hancinsa yake bleeding shi ne muka je basu magani da taimakon gaggawa, ai kinga ma dikkanmu muka fita a tare ko?".

Ajiyar zuciya ta sauke, sai yanzu ta gane dalilin dayasa yake karnin jini, watau babys ɗinsu ba lafiya har da mai bleeding, jinin ya taɓa shi kenan, to yanzu zuciyanta ya yi sanyi. Tafukanta tasa ta rufe fuska tana ɗan murmushi ga hawaye a fuska, wani irin kallon kauna ya bita da shi, har cikin ransa ya ji mugun daɗi ganin tana kishinsa.

Dogon hancinta ya ɗan ja game da cewa. "Bari in yi wanka in shirya zuwa office". Ya faɗa yana miƙewa.... Da sauri ta ce. "My Dr nima zan fita aiki yau, ina son ganin babys ɗinmu"...... Kai ya jinjina mata game da cewa. "Ki shirya to mu fita a tare". Cike da murna ta tashi, jiya da bata ga jariran nan ba dik ta damu.

After some hours.

Rike da hannunta suka fito parlo, yana sanya da kayan aikinsa, ita kuma kayan da ya bata shi ta sanya, doguwar riga zuwa gwiwa, ta kamata sosai a in da ta fito mata da shape na jikinta matuƙa.

A parlo ya isko su Dr Mark sun shirya, sister Maya ta yi wanka ta nufi sashin gidansu dan shiryawa zuwa aiki. Gaba Dr Kamal and Dr Mark suka yi, Dr James and sister Zinta suka rufa masu baya.

Suna shiga sashen asibitin ya saki hannun district Zinta game da cewa. "Jeki wajen babys ɗinku, anjuma ina zuws"...….... Tin da suka shigo sauran nurses ɗin suke ta faman kallonsu cike da mamaki. Ita kuwa ko a jikinta, ta matsa ta yi hugging ɗinsa game da sumbatar gefen cheek ɗinsa. Kama nata kumatun ya yi shima ya sumbata kafin su yi sallama ta wuce ta bufi SECTION D.

Tana shiga taga ɗakin ya ɗan canza mata, durkutsawa sauran nurses ɗin suka yi suna ɗaga mata gaisuwa, fuska a ɗauke da fara'a ta amsa kafin ta ƙariso ciki, cike da mamaki ta ce. "Sister Nazy meyafaru? Ina sauran babys ɗinmu? Naga sun ragu ne".

Daidai lokacin sister Maya ta shigo, ita ma durkutsawa ƙasa suka yi suka hau gaisheta. Wacce aka kira da Nazy ce ta amsa da. "Aunty Zinta basu ragu ba, dama haka suke"...... Kai Zinta ta shiga girgizawa alamar a'a kafin ta ce. "Ba haka suke ba, gaskiya sun fi haka sosai ma".

Sister Maya da ta shigo yanzu ne ta ce. "Ai dama su 55 ne, na taɓa ƙirgasu a lokacin da muka fara aiki a nan"...... Jama'a ku ce wow, ku tafawa sister Maya!.

"Yauwa kin kirgasu ko?". Sister Zinta ta faɗa. Kai sister Maya ta gyaɗa alamar e kafin ta ce. "Gaskiya an ragesu, ha haka suke ba, waɗan nan ai basu wuci 30 ba a nan"....... "To mu kirgasu mu gani". Cewar sister Zinta. Na'am suka yi da zancenta, dan haka sai suka fara ƙoƙarin kirga babys ɗin. Suna kirgawa babys 30 ne ciff, kunga daren jiya ma sun ɗauki biyar.

Zazzaro idanu sister Zinta ta yi game da cewa. "Sister Nazy ina sauran babys ɗin?". A kiɗime ta yi maganar. Zazzare idanu dikka nurses ɗin suka fara yi, tsabar babu ƙwaƙwalwa a kansu wai basu san cewa an kwashi yara 25 ba, kuma kullum suna kwana tare da su su tashi da su.

Dage mata suka yi a kan lallai su basu san an ɗauki babys ɗin nan ba, su dai kawai suna yi wa yara wanka. Hankalin sister Zinta idan ya yi dubu ne ya tashi, cike da tashin hankali ta ce. "Bari in sanar da Dr James, kila su sun san in da yaran suke"...... Na'am suka yi da zancenta, dik hankalinta ya yi tsananin tashi, tana kiɗime, fitowa ta yi da sauri ta nufi sashin 3D, ita kuma sister Maya ta wuce ta ɗauki ɗan babynta da ta maye gurbin darling da shi wanda yake da rabon kwanaki nan gaba jiya 3D basu niƙa shi ba.

Tana ɗaukansa sai ta ji jikinsa da zafi, hakan yasa ta yi gaggawar ɗagowa tana kallon su sister Nazy da suma ita suke kallo, tambayarsu ta yi me ya sami babyn, nan ma idanu suka fara zarewa suma faɗin basu sani ba. Siririn tsaki ta ja game da saɓa babyn a kafaɗa ta fita izuwa office na Dr Kamal dan ta bashi ya duba mata lafiyar yaron.

Ita kuwa sister Zinta a kiɗime ta shiga office na Dr James, bata ko bi ta kan office ɗin PA sister Lazy ba, da sauri ta wuce. Tsaye ta iskosa yana ƙoƙarin cire coat ɗin jikinsa ya sanya surgical gown, dan akwai matar da aka kawo daga geferal hospital ɗinsu dake saman WS-HOSPITAL, in baku manta ba ai General hospital ɗin Avaris ce a samansu Dr James, su kuma suna ƙarƙashin ƙasa.

To an kawo matar ne zasu cire mata mahaifa, in baku manta ba a farko labarinmu da farkon ganinmu da 3D suna cirewa wata mata mahaifa ne, to ashe daga cikin wannan General hospital ɗin ake shigo masu da matan suke cire masu mahaifa sai a sake fitar da su. Idan mace bata da lafiya, in suka ce tiyata za'ayi mata, bayan anyi mata allura da sunan za'ayi mata tiyatar, in ta yi barci sai su sauketa ƙasa izuwa wajen 3D ta sihirtaccen hanyarsu, 3D kuma su yi mata aiki su cire mata mahaifa, idan sun gama su kaita wannan ɗaki d suke shirya drugs ɗin da suke haurarwa saman nan, fatan kun tuna ɗakin?.

Idan suka kaita wannan ɗakin suka ajiye to zasu yi wa babban likitan General hospital ɗin message, shi zai shigo da yaransa su ɗauketa su haurar da ita sama, sai a mayar da ita ɗakin tiyata na General hospital ɗin, su yi kamar su suka yi mata aiki suka cire mata cuta. Wannan mata da kuka gani a farkon labarinsu da 3D suka cire mata mahaifa ma ai daga wannan General hospital na Avaris ɗin ta fito, baiwar ALLAH bata sani ba kawai aka cutar da ita, aka shigo da ita wajen 3D bayan an yi mata alluran barci da sukan za'ayi mata ciyata a cire mata ƙarin mahaifa, shikenan aka kawota 3D suka rabata da mahaifarta.

Kun san wani abu? Ko hukuma zata shekara tana binciken General hospital ɗin nan ba zata taɓa samun wani abin zargi ba, ku lura da irin tsarin da aka yi mana, ɓarkar tana ƙarƙashin ƙasa, ko kin ce a wannan asibitin aka cire maki mahaifa wlh ba za'a taɓa yarda ba, saboda babu alamar abin zargi a wajen, ba wanda zai zaci cutarwar tana ƙarƙashin ƙasan hospital ɗin, sai ranar da ALLAH ya yi asirinsu zai tonu ne kawai za'a ga abi da ba'a taɓa tsammata ba.
Chapter 201 · 0% Book details