← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 227

Sashe 21

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko kaÉ—an Leo bai kalli in da yake ba, amma da ya fahimci Noor baya son faÉ—uwa ne yasa ya kama hannunsa sai ya juyar da hannun nasa ya rike Noor É—in da karfi suka fara gudu sosai a tare, hakan ya yi mugun karawa Noor kwarin gwiwa ba kaÉ—an ba.

Lamarin da ya yi mugun baiwa su Zaysh mamaki kenan, how comes Leo zai kama Noor? Kai kamar a mafarki?. Shi kuwa Leo ganin Noor ya dage sosai ne yasa ya kara kankame hannun nasa.

Abin da ba'a taɓa ba wai Noor ya zo na farko, sai yau shi da Leo su ne farkon isa wajen, tsalle ya dinga yi yana murna tamkar wani karamin yaro, kamar ma bai gaji ba fa, dik kuma daɗin Leo ya taimaka mashi ne yasa bai ji wahalar gudun ba. Shi kuwa Leo robar ruwan da aka ajiye masu a wajen ya ɗauko tare da ɓalle bakin ɗaya, tin da ya kafa a ɗan bakinsa bai zare ba sai da ya sanye tas, ya yi jifa da robar, sannan ya sake ɗauko wani, ya ɓalle ya sha rabi, zai rufe rabin Noor ya karɓa ya kafa a bakinsa, tas ya shanye, sai murmushi yake yi ya zo na ɗaya, a ransa yau ya ɗanɗani irin farincikin da ake ji a dik lokacin da aka yi nasara, sai ya ji yana sha'awar ya yi ta yin nasara a rayuwansa. Da bashi da wani tunani a gaba a rayuwansa, amma dalilin wannan abin Leo yasa ya fara tinanin cigabansa.

One by one matasan dik suka iso wajen. Wasu sun iso a tare da Captain, wasu a bayansa. Yau babu wanda bai iso a kan lokacin ba, bayin ALLAH sun fara saba horon ne. Captain bai bari sun huta ba, yana isowa ya ce maza su shirya su kama hanya, ya nuna masu wani hanya a wajen, ya ce su je.

Ba musu suka kama hanya, da sauri Noor ya bi bayan Leo, a kusa da shi ya tsaya, dik in Leo ya cire kafa a wajen shi kuma zai sanya. A haka suka isa wajen wani katafaren yashi mai kama da ruwa, irin yashi mai mugun laushi dake lumar da abubuwan nan ne.

Waro idanu suka yi suna kallon wajen cike da mamaki. Muryan Captain ne ya katse masu kallon nasu da cewa. Zaku rarrafa daga farkon yashin nan, ku yi iyo a cikinsa ku fita ta other side É—in. Zazzare idanu suka yi, gabaÉ—aya horonsu ya canza fa, yanzu dik girman yashin nan zasu yi iyo a ciki? Kai, lallai yau gwiwowinsu zasu cire, da matsala gaskiya.

Suna can suna tunanin mafita Captain ya fara kirga masu lokaci, ga shi ya ce mintina 10 kawai garesu, wanda bai fito a 10 mins ba zai faro. Cikin zafin nama suka faffaɗa, dayawansu sun ji sabon wahala, dan a tunaninsu karamin aiki ne, sai da suka faɗa suka ji lumewa ƙasa suke yi, suna ƙoƙarin ɗagowa amma ƙasar na sake yin ƙasa da su.

Still Noor yana kusa da Leo. Sai dai bai fargaba ya ga Leo É—in ya fara yi mashi nisa, hakan yasa ya kara zafin nama ya matsa kusa da shi. Da Leo ya ga haka sai ya kama hannunsa da kansa, suka fara iyo a tare, yadda kuka san a cikin teku suke........ Note kowani horo da nufin yinsa da kuma dalilin, ba in da ba'a turasu kama masu laifi, dan haka dole gwiwar kafafu da hannu su yi kwari!.

A wannan karon ma Leo, Noor, Unays, Zaynash ne suka yi farko-farkon fitowa. Ya ilahi suna fitowa, wani irin daÉ—i da Noor ya ji, bai san lokacin da ya daka tsalle ya rungumi Leo yana murnushi ba. Da karfi ya ce. "Thank you so much brother, I really love you".

Haka kawai Leo ya tsinci kansa da tsananin farinciki ganin yadda Noor yake murmushi saboda shi. Ganin Leo bai amsa shi bane yasa ya sake shi yana kara faÉ—aÉ—a murmushinsa. A daidai lokacin su Vash suka fito. Cike da farinciki Noor ya ce. "Brothers na shiga sahun Æ´an farko".

Zuba mashi idanu Vash, Unays, Leo and Zaysh suka yi, suna ta mamaki yadda yake murya. Shi kuwa yau ya gane watau zuwa na É—aya fa duniya ne, akwai mugun daÉ—i, kai kanka a farinciki na musamman zaka tsinci kanka.

Shi kansa Captain farinciki ne ta lulluɓe zuciyansa, sai ya guduri niyar faɗawa Leo ya ja Noor a jiki tin da idan suna tare yana zagewa ya yi nasara, dan suna son ya yi nasara. Da wannan tunani a ransa ya haɗa kan waɗan da suka yi nasara suka nufi wata hanya, waɗan da ba su nasara ba kuma ya kyalesu tare da sauran sojojin dake wajen kan su mayar da su su sake!.

Wani katafaren fili aka kaisu a yau ma, sai ya raba su team by team, bari mu É—auki team room number 1 and room 2 mu yi bayani a kansu. Captain ya yi gyaran murya tare da cewa. "Room 1 kune a matsayin zakwakuran sojoji kun zo kama manya Æ´an'taadda a filin daga, team room 2 act like gangster now, room 1 ku kama room 2 ba tare da kun kashesu ba, ku gwada dabarar yaki mu gani".

Shiru suka yi suna tunanin ai ba'a koya masu wannan horon ba. Tamkar Captain ya gane me suke tinani sai ya ce. "Ba'a yi maku practical a kan abin da ba'a koya maku ba, a cikin horon da kuka yi akwai wannan, ku fara zaku fahimta".

Shiru suka sake yi, basu taɓa sanin dik wani rarrafe ko lankwashe-lankwashe da ake sanyasu wani nau'i ne na dabarar yaki ba, su sun ɗauka kawai dan jikinsu ya yi kwari su yi karfi ne, shiyasa suke ganin ai ba'a koya masu ba.

Filin yana da maɓoya sosai ta yadda gane mutun abu ne mai wahala, akwai tankuna da drones na tsofaffin bayan motocin yaki. Captain ne ya ce. "Room 2 you have two run now, room 1 ku kuma ku yi shirin kai wa gangsters farmaki".

Room 2 ne suka fara kallon juna, to su da ba Æ´an ta'adda ba ya za'ayi su iya acting kamar su fisabillilahi? Basu san an koya masu salon Æ´an ta'addan bama, dan wani lokaci kafin ka kama É—an ta'adda sai ka maida kanka irinsa shiyasa ake koya masu irin salonsu.

Wasu empty pistol gun Captain ya baiwa su Leo a matsayinsu na waÉ—an da suka zo kama gangster's.

Sauran sojojin kuma ya ce dik su koma baya, bari room 1 And 2 su gwada aiki.

Baya su Leo suka juya har sai da ƴan room ɗin su Unays suka ɓuya, sannan ne Captain ya ce su juyo. A natse ya ce. "A nan wajen zaku gwada kaifin ƙwaƙwalwa mu gani, ku kama ƴan uwanku ba tare da bindiga ba, kuma kada ku bari su dakeku, sai dai ku ku dakesu, amma ban da dukan da zasu ji ciwo".

Kallon juna suka É—an yi, Zaysh ne ya ce. "Brothers let's walk slowly kamar yadda muke tafiya a daji yayin fitar da kanmu, muna tafiya a hankali dan kada mu bugu da itace ko wani dutse".

Kallon juna suka É—an yi, sai Leo ya wuce gaba, bayansa suka biyo, hannu ya É—aga masu wanda yasa suka tsaya, da hannu ya yi masu alama da su rabu ba tare da ya juyo da kallonsa a kansu ba. Baya Captain ya koma tare da rungumo hannaye a kirji, shi da sauran sojojin suka zuba masu ido.

Sanɗo suka fara yi rirrike da bindigun da aka basu. Rabuwa suka yi kowa ya kama laluɓe, a yau kowa kaifin kwakwalwarsa ta kwacesa. A yayin da suke zuwa su kuma su Unays suna kara ɓoyewa ne. A hankali Leo yake tafiya har ya shiga bayan wasu matattun motocin yaki da wasu kwantaunars, a nan ya ɗan tsaya shiru tamkar mai tinanin wani abin, sai kuma ya ɗan rintse idanunsa tare da kasa kunne sosai.

Lokaci guda ya waro idanunsa waje, cikin zafa ya juya gefensa tare da sanyawa Unays dake laɓe bayan wata mota bindiga a kai, da numfashin Unays ya yi amfani wajen gane yana wajen, kun tuna horon da aka basu a daji na su dogara da numfashin juna? Ashe ta shiga kansu da kyau.

Yana sanyawa Unays bindiga ya yi zafin namar damkoshi ta wuya-wuya suka fito harabar wajen, daidai lokacin Zaysh ya fito da nasa ya kama shi ma. Wani irin dogon ajiyar zuciya Captain ya sauke alamar ya ji daɗi, saura Noor da Vash dake laluɓe. Kun san da cewa Noor yana da bala'in kaifin ƙwaƙwalwa, ga shi dai baya son horon, amma wlh ya naɗi komai a kansa. Dan haka shi ma da numfashinsa yai amfani wajen kama shi, yana fitowa shi ma Vash ya fito ya kama nasa.

A tsakiyar wajen suka tsai tsaya kusa da Leo. Da ido Captain yai amfani wajen cewa room 2 su kwaci kansu. Ai suna gane karatun suka juya suna fuskantar su Leo gaba da gaba, kafin Leo yai wani motsi Unays ya ɗaga kafa yai ball da bindigar da Leo ya nuna shi da shi, sama bindigar ta yi, tana dawowa Unays ya caɓeta tare da nuna Leo ɗin da ita yana wani irin murmushi wai irin ya yi nasarar nan.

Ɗan buɗe idanunsa Leo ya yi yana ɗan mamaki, dan shi bai zaci su Unays zasu kwaci kansu ba. Sai kuma ya ɗan fiske. Unays kuma mamaki yake yi yadda aka yi kafafunsa suka yi sama sosai, watau horon rarrafen nan tasa kafafuwansu sun kara kwari matuƙa, lallai kuwa gaskiyar Captain ne an koya masu dabarun yaki a cikin wannan horo su ne basu ankara ba.

Matsar da bindigar saitin forehead ɗin Leo Unays ya yi, yana cigaba da wani irin murmushi. Cikin zafa Leo ya ɗan kauce tare da yin ƙasa kaɗan, ya kama hannun Unays mai rike da bindigar, ya murɗe hannun baya, ai bai san time da ya saki bindigar ya fasa kara ba. Kasa ta faɗi.
Chapter 21 · 0% Book details