← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 227

Sashe 31

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A yanzu dikka matasan sun haye ginin da salon Leo, Captain ya sanyasu suka dinga maimaitawa har na tsawon awa É—aya, sai da suka saba sosai, a karshe ma kusan a tare dikkansu suka haye saboda an kware ya bi jiki.

Daga nan aka wuce da su wani ɗaki mai matuƙar duhu dan a masu mental stress training, ɗaki ne da ko yatsanka ba zaka iya gani ba saboda tsananin duhu, haka aka rufesu a ciki na tsawon wannan lokaci, ga ƙara na harbi bindigogin dake tashi kusa da wajen, so ake yi a koya masu natsuwa a lokacin tashin hankali da wahala, su natsu su nemawa kansu mafita mai kyau, da yake kuma dikkansu natsastsun matasa ne sai aka samu abin da ake so, dan dik harbin nan da ake yi suna zaune hankalinsu a kwance, wasu ma hiransu suke yi, to kunnuwa sun saba da harbin bindigar ne ai!.

Bayan awa Captain ya fitar da su aka wuce da su wajen da zasu yi rescue run. A nan ma ana koya musu wata dabara ce na yadda za su ceci abokanansu a lokacin yaƙi. An sanyasu sun sanya kaya masu nauyi a jikinsu, sannan su ɗauki abokin horonsu da suka yi kamar sun ji ciwo ba zasu iya tafiya ba, kamar an harbesu a kafa, Captain ya ce su yi gudu da su a bayansu na tsawon mita 500. Amfanin sanya kaya mai nauyi a jikinsu shine, a lokacin yaki zasu ɗauki bindigunsu, ga tarin alburusan dake waist ɗinsu, suma masu nau yi ne, sannan su ɗauki ƴan uwansu, kunga dole su sanya kaya masu nauyi yayin wannan gwaji.

A wannan karon Leo yaki É—aukar Noor, dan ya ce ya yi mashi kaÉ—an, bashi da nauyi! Dan haka sai ya ce Juraiz na É—akinsu Unays ya zo. Ba musu ya je dan shi ma yana mugun yin Leo ba karya, dik wanda ya ce baya son Leo sai in hasada wlh, Juraiz kuwa bashi da hasada dan haka yana yin Leo!.

A bayan wuya ya É—aukesa, Vash ya É—auki Noor, Zaysh ya É—auki Ameer na É—akinsu Unays, shi kuma Unays ya É—auki wani katon matashi a room nasu yake shi ma, shi ne cikon na huÉ—unsu, suka yi ready, Captain na cewa go suka danna da gudu. Dikkansu su babu wanda ya faÉ—i, hakan na nufin zasu iya cetan abokansu a wajen yaki. Sosai Captain ya dinga sanyasu maimaita wannan horo, saboda yana da mugun muhimmanci a tattare da su!.

Bayan kammala wannan, suka yi sallah suka yi lunch sannan suka shiga class, a ajinsu na yau an koya masu yadda ake haɗa bindiga cikin ƙanƙanin lokaci, ka shirya shi ka sanya bullets, sannan aka koya masu yadda ake goge bindiga idan ta yi datti, aka karantar da su me bullet! Me karancin gudun da yake yi a second, me karshen gudunsa a second, daga nan aka koya masu yadda ake rike kowacce bindiga. A class yau an sha artabo, dan ba kowa ya iya rike bindiga ya yi harbi ba, wasu idan bullet ya zo fita tafiya suke yi da bindigar gabaɗaya su faɗi kasa. Kun san da cewa in bullet ya zo fita da karfi jan bindigar yake yi? In baku sani ba yau kun sani, sai mutum ya jajirce ya rike da karfi in ba haka ba su wuce tare da bullet ɗin, karfin bala'i ne da fitar bullet, baku ga har wani hayaki yake yi idan ya zo fita ba?.

Captain da kansa yau ya sha dariya yadda aka basu ƙananan bindigu su gwada harbi, sai dai Captain ɗin ya ga sun wuce tare da bindigar sun faɗi ƙasa, bullet ya jasu. Abin mamaki Noor bai faɗi ba, bullet bata ja shi ba, dik da bindigar koyar harbi daban, na yaki daban, amma ko na yakin aka bashi tabbas ba zata jashi ba, dan shi ɗin renon Leo ne!.

Captain ya yi mamaki sosai, wai Noor ne da jarumta haka!....... Bayan sun kammala wannan class suka wuce wajen horon magana da ido, kullum sai an koya masu shi, saboda yana da mugun amfani a wajensu, yakamata ace suna da silent words wa juna!.

A yanzu horar da su yana yi wa Captain mugun daÉ—i, saboda babu ragwaye babu mai sanya shi ciwon kai!...... Basu suka tashi horon yau ba sai karfe 7 kamar da aka saba. Suka yi sallar mangarin and Isha'i, suka yi dinner sannan kowannensu ya koma room É—insa.

Suna shiga suka hau yin wanka. Bayan sun yi shirin kwanciya kowa ya hau neman gida. Shi kuma Leo ya kwanta ya ɗauko book ɗinsa yana bitan karatun da suka yi ɗazun, yana jinsu suna ta hira da gida ko a jikinsa. Da suka ishe shi sai ya ce dik su kashe wayoyinsu ko ya karɓa ya fasa! Daga magana ɗaya bai sake ba dik suka kashe wayoyin nasu saboda tsoronsa da suke ji.

A takaice ya ce dik su fito da littafansu su fara karatu! Wani irin harara Zaysh ya dallah mashi kafin ya fito da book É—insa, a ransa yana faÉ—in. "Sai ya dinga yi mana magana kamar shi ne ubanmu, ba za'ayi karatun ba tin da kai ka haifemu". A fili kuma dole ya fito da book É—in ya fara karatu, dan yasan Leo baya É—aukar wasa ko shirme, yanzu jikinsu zai gaya masu, ba duka ba zagi amma akwai horarwa! Ganshi da É—an banzan kwarjinin da yasa suke shakkarsa.

Haka É—akin ya natsu tsit suka fara karatu, suna jiran 11 ya cika su saci hanya zuwa wajen horon dare da suka saba!.

------------------------🔥

Sanye suke da sleeping dress mai zubin pj's launin maroon, sun yi matuƙar kyau, dikkansu kwance suke a saman beds ɗinsu, sun saki gashin kan nan nasu har ƙugunsu. Arya tana practical a kan karatunsu na yau, amma gabaɗaya zuciyanta yana kan tinanin Leo da yau tsawon wata kenan da haɗuwarsu, basu sake haɗuwa ba, amma ya tsaya a dikka zuƙatan yaran GAT, da tinaninsa suke kwana suke kuma tashi! Su kansu basu san dalilin tinanin nasa ba!.

Ta yi nisa cikin aikin da take yi na ƙoƙarin bin diddigi da kuma datsar wata camerar, shi ne karatun da aka yi masu yau. While ita kuma V tana can tana karance-karance labaran soyayya, a maimakon ta yi practical na abin da aka koya masu, ta tsaya biyewa soyayya.

Manassa tana nata aikin ita ma na fannin likitanci, while Angelina ta kashe laptop É—inta, ta ajiye shi a gefe, ta shiga bargo tamkar mai yin barci, wayarta ta kunna tana kallon film É—in batsa a wayar, ita kuma tata bala'in kenan, tin bata kai ko'ina ba akwai ta da son sharholiya, ta iya kallon film É—in batsa sosai, yanzu ba abin da bata sani ba, shiyasa ta matsu take son saurayi, ta ce sex zai yi daÉ—i tin bata É—anÉ—ana ba, wai a haka ma GAT yana mugun sa ido a kan yaran fa, amma ya yi sake idanunsu ya buÉ—e, wayayyu ne sosai, shiyasa uwa daban take, haka tarbiyarta ma daban yake, da uwar tana raye wasu abubuwan ba zasu yi shi ba.

Batu na gaskiya Angelina ta fisu buɗewar ido a ɓangaren maza da son romance, ita kuma V soyayya da shagwaɓa, har da cewa ita namiji ɗan shagwaɓa zata aura, wanda zai dinga yi mata kuka idan suna romancing juna, ita kuwa Arya cewa ta yi bata ga namijin da zata so ba, suma masu zancen mazan basu da hankali ne, dan haka tana hana su V zancen soyayya, while ita kuwa Manassa komai ma daidai ne, idan anga dama ayi soyayya, idan ba'a yi bama matsalar mutum ne, ita dai karatu ne a gabanta.

V dake ta faman sakin kyakkyawan murmushi ne ta ce. "Bloody i wish in samu masoyi like me yanzu, ku kashe juna da love and romance"........ Manassa dake aikinta ne ta amsa da. "Aikuwa da an yi shirme, saurayi irinki to waye zai rarrashi wani idan É—aya yana kuka? Nan in kika fara kuka sai daddy ya zo! Ai ke sai irin gangsters da basa dariyar nan ne zasu gyara maki zama".

Arya ce amsa da cewa. "Ke baki da wani aiki sai labaran soyayya ne? Ba zaki yi abin da zai amfani rayuwarki ba ko?"...... Turo baki ta yi kafin ta ce. "Aikinku kenan ai, ku baku san soyayya da shegen daɗi bane, ina zan ga jarumina, Angelie please ku nemo mun shi, zan faɗa mashi ina son shi! Ya zo in yi hugging ɗinsa, in yi kissing ɗinsa, huuuuuuu, I really like love and romance". A shagwaɓe sosai ta faɗa.

Siririn tsaki Arya ta ja tare da cewa. "For sure watarana wannan shauki ne zai gamasar dake! Ni sai na rasa a ina ma kike koyan wasu abubuwa"...... Manassa ce ta amsa da. "Arya, love fa akwai daÉ—i, there was a time da na kalli wani love film, they way suke son juna, I felt like ace ni ce".

Shiru Arya bata sake tankasu ba, saboda gabaÉ—aya gani take basu da aikin yi ne yasa, ita bata ga dalilin da zai sanya ta so wani namiji ba......... V ce ta katsesu da cewa. "Oh my God, bloody please ku ce masoyina a dik in da yake ya zo gareni". Ta faÉ—a idanunta a kan laptop É—inta tana rungumar Teddyn dake manne da kirjinta.

"Ga masoyin naki ai a jikin roba". A cewar Manassa. Wani irin haɗaɗɗen murmushi ta saki kafin ta amsa da. "Shi wannan ai special ne, nasan ba zan taɓa ganinsa ba bare har ya so yi, shiyasa ban saka a raina zan same shi ba, amma ba zan taɓa son wani kaman yadda nake son shi ba, hoooo look at his soft lips and his big-big sharp eyes, his hair, karshe ne shi ɗin".
Chapter 31 · 0% Book details