← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 227

Sashe 9

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Meyasa ake hanasu wayoyinsu a lokacin horo? ana hanasu wayoyinsu ne saboda abu biyu, na farko dan kada su fitar da sirrin irin horon da ake yi masu, watau su ɗauki video ko hotuna, shiyasa da wuya ku ga video ɗin yadda ake ainahin horar da sojoji, ainahin horonsu ba wai tsallake dutse, ko gudu or iyo cikin ruwa ba, ainahin horon ɓoyesa ake yi matsayin sirri, sai ka shiga zaka sani, zan rubuta yadda rayuwar sojoji suke a gaske da dik wata wahalar da suke sha da komai dai, ba zan rage komai ba! Zaku san su waye soldiers ba sunansu da kuke ji kullum ba, akwai abin da zan ɗan sakaya, abu na biyu da yasa ba'a basu waya shi ne zai ɗauke masu hankali daga kan horon da suke yi, musamman karatu da nazarin makamai da suke yi, yana ɗauke masu hankali. Dan haka kada ku manta da na faɗa maku ni zan barsu tare da wayoyinsu ne saboda labarina ya tafi mun yadda nike so, bana son abin da ba haka ba in saka maku shi tin da baku sani ba sai ku ɗauka gaske ne, shiyasa na faɗa maku ba'a basu wayoyi ni ne kawai na basu fatan kun game?!

-------------------------🔥

ARVASH ne ya ce. "Wannan wani irin ƙara ne ya tashi mutane ba lokacin tashi ba?".

ZAYNASH ne ya kalli ARVASH idanunsa dik barci ya ce. "Awww kai nan baka san gidan soja ka zo ba ne kake tambayar me ya tasheku yanzu? Tab lallai ma, watau lokacin tashi bai yi ba, to ai a wannan gidan babu zancen lokacin tashinka, ba kamar gidanku bane da zaka yi barci lokacin da ka ga dama ka tashi lokacin da ka ga dama, nan lokacinsu zaka bi, dallah tashi ka yi abin da za yi yanzu, karfe biyar da rabi za ka fara karɓar horon, GIDAN SOJA GIDAN WUTA kake!! Kai baka karanta a document na biyu da aka bamu bane?".

Ɗan turɓune fuska Noor dake jinsu ya yi yana ɗan miƙa kafin ya ce. "Ni wallahi daddynmu ne ya matsa mun gabakiɗaya akan wannan aiki, wai na taso cikin mata, na taso a rago shi ne fa kawai ya ce sai na shiga aikin soja, gaskiya ni barci bai ishe ni ba". Ya faɗa tare da koma ya kwanta.

ZAYNASH da yake kokarin fitowa ƙasa daga gadonsa ne ya ce. "Kwanciya ko? Hhhhh yaro man kaza, kwanta bari Captain ya shigo cikin ɗakin nan sai ka gane annabi isa ba ɗan ALLAH bane manzon ALLAH ne, sai yafi maka sauƙi ka tashi da kafarka ka je wajen training akan ka bari ya zo ya same ka".

Yana rufe baki VASH ya karɓa da cewa. "Kyaleshi, idan Captain ya shigo zai nuna mashi a GIDAN SOJA GIDAN WUTA yake ba a gidansu ba". Ya faɗa tare da dirowa kasan gadon ya nufi in da ya kasance toilet ɗinsu.

Kwanciyansa Noor ya koma yayi yana cewa. "Bazan tashi yanzu ba, sai anjuma, dik abin da zaku yi sai dai ku yi, ba Captain ba komawa zai zo sai nayi barci na, a gidan mu karfe takwas nike tashi, dan haka sai takwas É—in ta yi zan tashi". Ya faÉ—a tare da jawo bargo abinsa.

A cikin ƙasa da mintuna arba'in da biyar suka yi wanka suka shirya cikin ƙananan kaya yanda zai musu daɗin karɓan horo, sannan suka fito, suna fitowa suka nufi inda ya kasance masallaci, a nan suka yi sallah sai dai kafin su fita sun yi ƙoƙarin tayar da Noor daga barci, amma yaki tashi, ya ce su barshi, haka suka rabu da shi, dan a gidan soja dama ba'a taimakon juna ai a lokacin horo, barin mutum zaka yi jikinsa ya gaya mashi.

So sun fita suka bar Leo a tsakiyar gadonsa yana zaune yana latsa wayansa, basu yi mashi magana ba shi ma bai yi masu ba!.

Sai dai ga mamakin su kuma shine ya riga su zuwa masallaci, a can suka iskoshi, da yake hanyar zuwa masallacin yana da yawa, sai suka yi tinanin kila yanke ya bi.

Karfe biyar da rabi daidai suka fito daga masallaci, suna fitowa gabaɗayansu suka nufin wani tapkeken fili, dama already sun sani ba yau bane farin zuwansu gidan soja, wata ɗaya da ya wuce sun yi cike-ciken form da zasu yi, sannan sun zauna na sati ɗaya a nan a nunnuna masu abubuwa kafin su koma su yi shirin zuwa karɓar horo, so sun san komai kuma yana cikin tsarin da aka tsara musu kafin a dauke su, ba saɓa lokaci! Babu wasa da aiki! Babu karya doka.

GIDAN SOJA GIDAN WUTA, WAI ME KUKE TINANIN ZAI FARU NE?. NASAN HAR YANZU BAKU FARA FAHIMTAR KOMAI BA, TO KU YI HAKURI KU CIGABA DA BIBIYA, NAN GABA KAÆŠAN ZAMU ISA IN DA ZAKU FARA GANEWA! YANZU FARKO NE SAI NA DAURE NA YI MAKU NAYANIN KOMAI YADDA ZAKU FAHIMTA! DAN GABA KU JI DAÆŠI!.

*Wannan littafi na ZAKUNA BIYAR tin daga page 1 na step 1 har zuwa karshen step 1 sadaukarwa ne ga mutanena na ƙasar Niger, ƴan Niger ƴan amana, ƴan Niger sun mun abin da ba zan taɓa mantawa da shi ba, Niger gidan karaminci da mutunci, gidan amana da kyautatawa, kai ƴan Niger baki na ya yi kaɗan wajen iya faɗan alkhairanku, kun mun na gani! Ban san da me zan biyaku ba shiyasa na yi maku wannan sadaukarwan, ALLAH ya kara maku lafiya da zaman lafiya, kwanciyar hankali da farinciki, jin daɗi da walwala mara yankewa har illarh Masha ALLAH, hakika ina kaunar mutanen ƙasar Niger kauna sosai mara misiltuwa, much love.*🌹♥️

STAR LADYN TAKU CE TA AMANA.🔥

ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥

PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.

2-11-2025.🔥

FIVE LIONS, FIVE MISSIONS, ACTION, DEATH OR LIFE, ADVENTURE, BRAIN GAMES, REDRESS, A BREATHTAKING LOVE THAT STEALS THE HEART AWAY.♥️🔥

E_____________3

5:30AM AGOGON AZURE BARRACK TA BUGA.

GabaÉ—aya matasan sun haÉ—e a filin nan, da yake akwai tsari da natsuwa sai dik suka shiga cikin layi mai kyau.

Kowannensu yana abin da yake yi, ZAYNASH and VASH hira suke ta yi da juna gwanin burgewa, tamkar sun jima da sabawa da juna, shi kuma NIRASH sai duba wata Æ´ar takardan hannunsa yake yi yana tsaye a can jefe bai shiga sahun layi da su ba.

Sai lokacin da Captain ya kariso wajen ne NIRASH ya nufo in da sauran matasan suke, a gaba ya tsaya tare da rufe takardan hannun nasa, da yake Æ´ar karama ce sai ya turata cikin aljihu, dik suka mayar da hankali kan Captain dake tsaye a gabansu.

------------------🔥

Yana tsaka da barcin da ta É—auko É—anÉ—ano da daÉ—i, har mafarkin sisters É—insa yake yi, ya saba kwanciya a saman laps É—insu yai barci har ya tashi ba zasu saukesa ba, yau yana kewa, gadon gidan soja bata yi kama da cinyar sisters É—insa ba.

Ya yi nisa a cikin mafarkin da yake yi tamkar saukar aradu haka ya ji an takasa da wannan shegiyar takalmar tasu, da karfi Commander ya takasa har sai da ya faɗo ƙasan gadon. Ko a fuska kuka ga commander kuka ga Captain kun san Captain Onbish ya fi imani da tausayi, Commander ko kaɗan babu ALLAH a lamuransa, bakin mugu ne da ya ga jiya ya ga yau a GIDA SOJA, in taƙaice maku shi ya horar da su Captain Onbish ɗin ma! Kunga kuwa dole wannan ba zai yi tausayi ba!.

Ƴar kara Noor ya saka tare da waro idanunsa. Ganin mutum a tsaye a kansa fuska babu alamar annuri yasa yai mahaukacin razana, dan shi fa ya manta a GIDAN SOJA yake. Ihu ya kurma sai kuma lokaci guda ya ɗauke wuta ɗiff alamar ya kame ko ya suma, kar ku manta irin ciwon da yake da shi.

Daddynsa ya ɓoyewa GIDAN SOJA wannan batu, kuma magana ake ta ba dik kai ke zuwa wannan gida ba, kunga magana ake ta daddynsa na da daloli, dan haka ba zasu zurfafa ba!.

A maimakon Commander ya tausaya mashi ganin ya suma, sai ya sake sanya kafarsa ya take nasa kafafun yana ce mashi ya tashi ya fita wajen horo cikin ɗaga murya. Sai dai dik tsawar da ya yi a banza, dan Noor bai motsa ba. Hakan yasa ya ɗan duƙa a gabansa, nan ya tabbatar da ya suma. Siririn tsaki ya ja tare da kwalawa wasu jaratan sojoji biyu kira, dama tare suke bin ɗaku-ɗakuna suna tashin sauran basu tashi ba!.

Da wani irin gudu kamar gangsters waÉ—an nan sojoji suka shigo room É—in. Da hannu ya nuna masu Noor game da cewa. "Ku zuba mashi ruwa kafin ku É—aukesa zuwa wajen horo". BABBAR MAGANA, watau ba É—aga kafa babu tausayi!.

Da sauri soja ɗaya ya matsa kusa da shi, hannu yasa ya cicciɓesa sai saman shoulders ɗinsa. Shi kuma Commander ya fita zuwa sauran ɗakunan dan tabbatar da kowa ya fita. Waɗan nan sojoji babu tausayi babu tausayawa suka kai Noor wajen babban tap na barrack ɗin. A kan fuskansa suka kunna tap ɗin. Ai ruwan nan na taɓa fatansa a wani irin gigice ya farka yana ambatar sunan Aunty Lusi, da alama ta fi kula da shi a gidansu.

Janyesa daga wajen tap ɗin suka yi ganin yana neman sake rasa numfashinsa, suka tsayar da shi a kan kafafunsa, sai ƙoƙarin tangaɗi yake kamar zai faɗi. Sai dai yana waro idanunsa take ya shiga natsuwarsa, dan ganin waɗan nan sojoji yasa ya tuna ashe fa GIDAN SOJA yake, sai ya ji ya kara tsanan aikin fiye da yadda ake zato.

Basu bari ya samu damar tinani ba ɗaya ya daka mashi tsawar da ya sanya shi firgita, in a harsh way suka ce ya wuce wajen horo kafin jikinsa ya gaya mashi, bashi da zaɓin da ya wuci ya wuce da sauri, dan bai ga alamar wasa a wannan waje ba! Waɗan nan sojoji tsab zasu iya cinyesa ɗanye a cewansa.

Haka ya wuce zuciyansa na tsananta bugu da razana saboda tsawan da suka yi mashi ya tsorata sosai. Shi ko wanka bai yi ba, ga jikinsa a jike da ruwa, babu damar ya koma É—aki bare ya canza kaya!.

--------------------🔥
Chapter 9 · 0% Book details