← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 162 OF 227

Sashe 162

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ƙule ya ce. "Yau mugunta kake ji da shi ne?"....... Ɗebo wani abincin Leo ya sake yi, ya shammacesa yana magana ya sake danna mashi a baki. Ai a miliyan Noor ya miƙe yana tufo da abincin waje saboda zafi. Da sauri ya dunƙule hannu zai kai wa Leo ɗin punch a kumatu Leo ya damki hannun nasa tare da ture plate na abincin gabansa, ya jawosa Noor ya faɗo jikinsa, yana ƙoƙarin damke wuyan Noor ɗin.

Noor ya juya ya rungumesa yana faɗin. "Wai ni yau me nai maka ne?". Shiru Leo bai yi magana ba, ya janye Noor daga jikinsa kawai yana ja mashi coily hair ɗin nan nasa. Wasa suka ɗan taɓa gwanin burgewa kafin Noor ya kwanto da kansa a kan laps na Leo yana faɗin. "Bro me na yi maka yau kuma?".

"Babu abin da ka mun, kawai ina son gwada maka ne, yadda ka ji wannan zafin abincin nan haka mace take, ka kiyaye"........ Awwa sai yanzu Noor ya gane karatun, ya ALLAH, watau Leo ba zai canza ba, halinsa É—aya da yayansa Lion, wai a haka ma fa Leo bai san tarihin iyayensu da irin cin amanar da ya faru ba, da ya sani kam ban dan me zai faru ba.

Miƙewa Noor ya yi yana faɗin. "Sauran mata ne suke saka mutu a zafi tamkar wuta, but my Juliet daban take da sauran mata, bari ma in je in ganta, goodnight bro"....... Da ido kawai Leo ya bisa ba tare da ya yi magana ba, miƙewa tsaye ya yi, har zai fita kuma sai ya ɗan dakata tare da juyowa.

A kusa da Leo ya tsaya, a kunne ya raɗa mashi cewa. "Kada ku nemeni, kuma kada ku zo mun ɗauki, yau ni da matata zamu kwana, yau zan yi dis virgin ɗinta, bye bro". Yana kai karshe ya miƙe da sauri yana ja baya, dan yasan sai Leo ya kai mashi duka ko damƙa.

Harara Leo ya bisa da shi, sai kuma ya sauke idanunsa ƙasa bai yi magana ba. Wucewa Noor ya yi ya fice waje. Kai tsaye tantinsu Arya ya shiga, yana shiga V dake kwance ta ɗago kai, ta ji kamshin perfume ɗinsa, Arya na zaune gaban laptop tana cin abinci. Tabbatarwa da cewa shi ne yasa ta miƙe zaune a tsakiyar mattress ɗin. Muryarta a dishashe ta ce. "My Romeo".

Bai yi magana ba, ya iso dab ita, hannu yasa ya ɗauketa cak, da sauri ta saƙalo wuyansa tana kwantar da kanta a gefen kirjinsa. Bai ce da Arya ko uppan ba ya fito waje da V, kai tsaye cikin tantinsa ya shige da ita. Bai direta a ko'ina ba sai a saman mattress ɗinsa, ya sauƙeta game da yunkurawa zai miƙe ya sauƙa.

Da sauri ta riko damtsen hannunsa, muryarta a raunace ta ce. "I'm so so sorry my Romeo, ba zan sake ba, na tuba"........ Dogon numfashi ya ja tare da sauƙewa a hankali. Can ƙasa kamar mai raɗa ya ce. "To sakeni"......... Sake shi ɗin ta yi tare da kwanciya a saman mattress ɗin, ta fashe da sabon kuka.

Miƙewa ya yi, ya cire uniform ɗinsa, ya rage daga shi sai shorts guntu wanda bai kai tsakiyar cinya ba, ga shi short ɗin ta matse shi sosai.......... Saman gadon ya dawo, yasa hannu ya ɗagota gabaɗaya ya rungume, sosai take ta faman shessheƙa, in a cool way sosai ya ce. "Ke baki san ke matata bace da zaki ce voice na wani is so sweet? Baki san cewa voice ɗina kawai zaki ji ki yaba ba? Kin manta ina sonki ne? Kin manta zan ji zafin in kika yabi wani ne?".

Cikin muryan kuka ta rungumesa taigtly kafin ta ce. "Sorry my Romeo it was a mistake, ba zan sake ba"....... Kai ya jinjina. "Is okay to, for now I forgive you, but in kika sake, you will lose my control and my happiness"...... Ƙara ƙanƙame shi ta yi tana ƙara ce mashi sorry.

Ɗago face ɗinta ya yi, ya haɗe fuskokinsu kafin ya haɗe bakinsu, ya fara bata hot kiss mai narka zuciya, ai ƙara shigewa jikinsa ta yi, ta fara shafesa tana turo mashi kirjinta, a gefe guda tana shessheƙa. Ai kwantar da ita ya yi, ya mata runfa da buɗaɗɗiyar kirjinsa, ya fara moving hands ɗinsa a jikinta, cikin salo ya fara ɓalle mata botiran sleeping dress ɗinta.

Ita kuwa ta ɗaura hannayenta a saman bayansa, tana yin sama da su, slowly ta dawo da shi ta gaba, kai tsaye ta damki magicstick ɗinsa. Ƴar ƙara ya saka mata kafin ya fara bata komai cikin zafa, dan ta kunna shi ne......... Romancing ɗinta sosai ya yi, ya rabata da kayanta dikka, daga ita har shi suka manta da a filin daga fa suke, yaki suka fito, ko da yake dama su basu ɗauki rayukansu a bakin komai ba, already sun sa a ransu mutuwa zasu yi anytime.

In a romantic way ya dinga binta da love and sexy words, ya É—auke mata hankali kafin ya yi yunkurin shigarta, ko me ya tina kuma sai ya fasa, ya kwanto jikinta yana mayar da numfashi, yana jin tamkar ana buga mashi guduma a tsakiyar kai. Hannu tasa tana É—an bubbuga bayansa kamar mai rarrashinsa, tana jin bugun zuciyansa na tsanantawa.

Shiru ya kwanta a jikinta, after like 10 mins, slowly ya miƙe, ya sauƙo ƙasa, kayansa ya mayar jikinsa tare da matsowa bakin mattress ɗin, ya tsuguna a gabanta, in a cool way ya ce. "I'm coming, ki yi barci, yau a tare zamu kwana". Yana kai karshe ya miƙe ya fita.

Yana fita bai zame ko'ina ba sai ta bayan tantunansu, a nan ya isko Leo, Zaynish, Vash suna tsaye, wayar hannunsa ya duba time 11 na dare ya yi, gaba Leo ya yi, suka rufa mashi baya, dik cikinsu Vash ne kawai yake rike da bindiga, su kam banda ƙananan wuƙaƙen dake jikin takalmarsu na aiki babu abin da suka ɗauka sai torchlight ɗinsu mai bala'in hasken nan.

Cikin tsakiyar dokar daji suka kutsa ba tare da sanin kowa ba, suna tafiya suna tattaunawa kan aikin da zasu je yi, ma'ana aikin da ya fitar dasu a daren nan. A can kuwa sauran sojojinsu suna zaune bakin wuta suna ta hira, while Arya na ta kokarin ganin ta yi aiki tuƙuru, Angelina ma ta dawo ta kunna laptop ɗinta tana duba gabas da dajin, dik da cikin duhu ne tana sauraran sauti da motsi, while Manassa na kwance rike da waya tana zubawa Vash tsiya, dan shi ma suna tafiya yana dannar waya ne, sai hakuri yake baiwa aljanarsa da ta ce zata kashe Manassa da ya kula.

Dik ya tashi hankalinsa, ya dinga bata hakuri, har da cewa shi tai mashi dik abin da zata yi mashi, amma ta kyale Manassa bata san komai ba, ita kuwa ta kafe lallai sai ta nakasa Manassa. V dai tana tantin Romeo É—inta kwance tana tinanin love moment da suka sha, dik ya tashi kanta da salonsa, idan ta tina his soft lips, his romance, his sexy words, ya rabb, sai ta jita a wata duniya na daban.

Shi kuwa Unays ya zage sai ya kafa gwamnatinsa a zuciyar Angelina, sai tashin kanta da love words yake yi, ita kuwa tana can tana tinanin yadda zata samu even contact É—in Zaynish ne. Uhm akwai dirama.

CRYSTAL PALACE.

4:30 na washegarin ranar da Abba ya kai sadaki, ranar Alhamis kenan.

Zaune familyn Khaiza'an's suke a parlo, Faryan, Harleen, sai kuma Rimsha dake zaune kusa da Faryan ta tada kai da cinyansa tana chatting da Seraphina, suna ta hira kan school, yau sun mayar da hankali kan hirar karatu ne ba hirar shirme ba, Rimsha tana son jan Seraphima ta musulunta, tana bata tarihin Annabi Muhammad (SAW)

Faryan yana latsa nashi wayan shi ma suna chat da Seraphina, dan bai hakura ba kuma ba zai hakura ba, while Harleen yana aiki a laptop ɗinsa, kun san Harleen pilot ne, matuƙin jirgin sama. Abba baya nan, sun fita da Aryan, ƙafa ta matsawa Abba sosai, kun san yana da problem na kafa, sai da aka dasa mashi karafuna, to dama dik karshen wata ana zuwa asibitin ƙashi a duba mashi, wannan wata bai je da wuri ba, kafar ta dame shi shiyasa ya kira Aryan a gaggauce suka tafi, dalilin kenan da yasa kuka gansa yana dogara sanda, matsalar kafa ce.

Knocking na door aka yi, hakan yasa Rimsha ta mike, a tinaninta su Abba ne ya dawo, ta nufi jikin door É—in, ba tare da ta duba camerar door É—in ba ta sanya fingerprint É—inta, kofar ta buÉ—e. Tana buÉ—ewa sai ga kaki sun shigo cikin parlon, Æ´an sanda ne su biyar, a gaba ACP ne da sauran yaransa.

Razana Rimsha ta yi, da gudu ta juya ta koma ciki tana faɗin. "Uncle Faryan police". Wannan magana da ta yi karaf a kan kunnen Ammie dake ɗaki tana shan americano, tana zaune saman sofa. Jin Rimsha ta yi kukan sunan ƴan sanda yasata ajiye americanon ta miƙe tsaye, tana sanye cikin arabian dress, ta yi rolling veil a kanta.

Ƙasa ta nufi tana ɗan sauri dan ta zo ta gani. Police a gudan Khaiza'an? Abin da ko a mafarki bai taɓa faruwa ba. A tsakiyar parlo ƴan sandan suka tsaya, ACP yana kallonsu Faryan ya ce. "Kai ina Muhammad Khaiza'an yake?"....... Dik cikin parlon babu wanda ya amsa mashi, saboda rashin yi masu sallama da basu yi ba. Cigaba da abin da suke yi suka yi tamkar basu san da halittar ƴan sanda a wajen ba.

Wani irin ƙasƙantaccen kallo ACP yai masu kafin ya ce. "Wai ba daku muke magana bane?"....... Ɗago kai Faryan ya yi, ya kalli TV dake magana, a ɗan natse ya ce. "Rimsha rage volume na TV ɗin nan, karen ciki na mana haushi dayawa". Kuma da gaske wani bakin ƙare na haushi a cikin TV ɗin.
Chapter 162 · 0% Book details