← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 227

Sashe 45

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gab zasu hau elevator Champion ya tsaya, scorpion na kokarin yi mashi magana ya juya da sauri yana faÉ—in. "My phone, I'm coming". Bai jira amsarsa ba ya wuce ciki da gudunsu na terrorist. Sama ya haura tare da nufar wannan É—aki. A gaggauce ya buÉ—e ya shiga, kai tsaye wajen table É—in da suka zauna É—azun ya nufa, wayar ya É—auko tare da nufar kofar fita. Dab zai fita ya kunna wutar wayar.

Ganin jini a ƙasa yasa ya ɗan ja baya kaɗan, ya kara haska wajen da kyau. Tabbas jini ne, a ransa ya ce meyakawo blood wajen nan kuma?. ALLAH sarki jininta ne, dan a garin neman iskar shaƙa ta dinga buge-buge har bakinta ya fara jini. Ɗan bin jinin da light ya yi har izuwa wajen da take yashe a ƙasa bata ko motsi. Ɗan waro eyes ɗinsa waje ya yi, da sauri ya kai hannu ɗaya ya ɗauketa cak sai saman shoulder ɗinsa suka yo waje. Kai tsaye ya nufi kasa da ita. Sai cikin mota, kai tsaye ya ce su wuce CPH da ita, dan a bata taimakon gaggawa idan ma tana raye kenan.

Kun gane ne, ɗakin binciken nasu sun yi shi ne musamman ta yadda babu wanda zai iya leƙan asirinsu, ko ka samu nasarar shiga a sace ba da saninsu ba to 30 mins ya yi maka yawa ka baƙunci lahira ba tare ma da sun taɓakaba, haɗarin dake cikin ɗakin tamkar haɗarin dake tattare da su ne! Kun gane ai?.

Suna zuwa CPH aka ce ba za'a karɓeta ba sai da wannan notebook ɗin nasu na shaidar mazauna CP ne su. Champion ji ya yi tamkar ya harbe likitan dake mashi wannan jawabi, amma sai ya daure da cewa. Scorpion ya je ya ɗauko notebook ɗin a gida, a room ɗinta cikin drugs ɗinta. Da sauri ya juya ya tafi, yau ba dan Lion ɗinsu ne ya ce su kula da yarinyar kuma su bata kome take so ba da babu abin da zai hana Champion bai kasheta ya jefar da gawarta ba, dan ta cika karambani dayawa a cewansa.

Haka dai ya dinga tausan kansa har aka kawo note-b ɗin, ya karɓa ya baiwa likita aka karɓeta. In takaice maku sai da ta yi kwana biyu a sume bata san in da kanta yake ba sannan ta farfaɗo da taimakon ALLAH da taimakon likitoci, sai da ta sha ruwa keda 3, kamar ma za'a kara mata jini, sai kuma aka fasa, aka haɗa mata magungunar jini kawai.

After two days suka É—auketa suka koma gida, a cikin wannan sati Champion ya nema mata boarding school, ya shirya mata komai ya É—auketa ya jefata can ba tare da ya jira dawowar Lion É—in nasu ba, watau ft, yana kwance a gadon asibiti bai san in da kansa yake ba, saboda raunin da ya ji, ga shi ya rasa jini sosai, sai da aka kara mashi leda biyu, har yanzu dai yana fama da jinya.

To shi dai Champion ba zai iya jurar kiriniyar Seraph ba, shiyasa ya yanke nasa hukuncin, dan a kullum basa zaman lafiya a gidan, ta dinga kukar mammy É—inta, abinci sai an mata É—ure, idan ta fito suka haÉ—e da zakin nan ta dinga ihu tana suma kenan, dik ta hanasu samun peace of mind a gidan, dan haka ko dan hero (zaki) da take tsoro gara a bar gidan da ita!.

In kara takaice maku sai bayan zuwanta school da sati biyu Lion ya warke ya dawo, ko da ya dawo bai tambayi ina take ba, bai bi ta kanta bama, suka shiga sabon babi na aikinsu, dama gagarumin aiki ne a gabansu aka samu wancan matsala su Eagle suka farmasu, kungiyar su eagle sun basu aikin kashe wani ne suka ce ba zasu yi ba, dan su ba kowa suke yi wa aiki ba sai wanda suka yi ra'ayi, to abin da ya haɗa tsama a tsakaninsu kenan, su eagle suna ganin ai sun san sirrinsu sannan su ki yi masu aiki? Shi ne suka nufi kashesu, suka shirya zama da su, a wannan zaman ne Lion shi kaɗai ya yi attending har suka farmakesa, su Champion basu je ba, dan basu cika zuwa waje su ukun a tare ba. Kada ku manta suna da fuskoki da dama, su eagle ba da fuskan Iron Fist suka sansu har suka ƙulla harƙallah ba, da wani fuska ne, shi fuskan Iron Fist suna amfani da shi ne kawai idan zasu yi gagarumin kisan da zai jinjiga duniya! Fatan kun gane?.

Seraph dama Jss 1 take a school, Champion yasa aka kaita Jss 2, daga nan ta cigaba. In kara takaice maku har tsawon shekara biyun nan suka wuce, Seraph ta kammala Jss 3, tana da shekaru 12 kenan yanzu, Lion bai taɓa tambayar ina take ba, da alama ma ya manta da ita a duniya, amma Champion yana zuwa wajenta a school time to time, yana kai mata kayan abinci idan ya dedeci lokacin karewarsu. Amma ku zo mu ɗan bi rayuwarta a makarantar ko kaɗan ne mu gani kafin mu yi skipping.

GOLDEN ROOTS ACADEMY, shi ne sunan school da Champion ya sanyata. Boarding school ne wanda daga jss 1 ake fara kwana a makaranta zuwa Ss3.

Ranar da ya kammala shirya mata komai ya É—auketa a mota ya wuce kai tsaye da ita school É—in. A ranar sai kuka take yi tana tambayar ina zai kaita? Kuma ina mammy É—inta? Bai ko kalli in da take ba, yana driving cikin zafin jini abinsa. Tin da suka shararo titin da ya sadasu da school É—in ta yi tsit tana kallon hanya har suk shiga ciki, katafaren makaranta ce na gani na faÉ—a, Æ´aÆ´an manyan kai ne kawai a cikinta, shinfiÉ—aÉ—É—iyar titi ce ta ratsa ko'ina a school É—in. Kai tsaye parking lot É—insu ya nufa.

Yana parking ya fito tare da buÉ—e side É—in da take ciki. Sanin cewa baya yi mata magana yasa ta fito da sauri, jakarta dake ciki ya ciro tare da buÉ—e bayar motar ya É—auko echolac É—inta, ba tare da ya sake kallon in da take ba ya wuce gaba abinsa. Da sauri ta rufa mashi baya suka nufi office na director.

Yana zuwa ya wuce ciki kai tsaye, kafin ta karisa shigowa sai gani ta yi yana ƙoƙarin fitowa, zata bi bayansa wani kyakkyawan farin fata dake zaune a saman office chair ɗinsa ne ya dakatar da ita ta hanyar kiran sunanta. Da sauri ta dakata, alama ya yi mata da hannu a kan ta zo. Ba musu ta je, tana tafiya tana waigo Champion har ya kurewa ganinta.

Cikin harshen turanci director ya ce ta samu waje ta zauna bari Madam Rohisha ta zo ta ɗauketa su tafi side na ɗalibai!. Muryanta na rawa ta ce. "Uncle where is my Mammy? Do you know where she is? Will you take me to her?". A kiɗime take magana, ya fahimci akwai firgici da tashin hankali a tattare da ita, dik tana ruɗe, ga idanunta a kumbure luhu-luhu! Lokaci guda mugun tausayin yarinyar ya kama shi, miƙewa ya yi daga kujeransa ya dawo in da take, cikin tausasawa ya fara rarrashinta har ya samu ta ɗan natsu.

A daidai lokacin Madam Rohisha ta shigo bakinta a ɗauke da excuse, wata haɗaɗɗiyar mata ce, fara tas tamkar ka taɓa jini ya zuba, tana da ido masu zurfi da kyakkyawan dogon gashi, gata da kyan jiki, sanye take da arabian dress, ta yi rolling kanta da veil alamar musulma ce. Tana ɗaura dara-daran eyes ɗinta a kan Seraph ta ji yarinyar ta yi mugun tafiya da imaninta, gata kyakkyawar gaske. Ai cikin azama ta karisa gareta.

Director ne ya miƙe ya bar wajen, ya koma saman kujeransa, ita kuma Madam ta zauna kusa da Seraph tare da riko hannunta tana ƙoƙarin tambayarta sunanta kenan director ya katseta, a natse ya fara bata bayanin wacece Seraph, watau marainiya ce da bata da uwa kuma bata da uba, dan haka ta kula da ita. Sosai Madam Rohisha ta ji kalamansa, ta kuma yi alkawarin ɗaukar Seraph a matsayin ƴar cikinta, daga nan ta kama hannunta, ta ja mata echolac ɗinta da ɗayar hannunta, sai ta ce Seraph ta ɗauki dakarta, daga nan suka fice izuwa side na mata, watau wajen kwanansu kenan!.

Farko kenan a rayuwar Seraph a school, dan haka zan yi labarin ne bisa ɓangare biyu, idan na waiwayo wajen Seraph to muna baya ne in da take rayuwa a school, idan na koma wajensu Leo muna gaba ne kafin in yi skipping, kun gane ai?.

STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥

ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️
🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥

PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.

https://www.facebook.com/share/g/1EUXbqsDjP

STEP 1________🔥

12-11-2025.🔥

FIVE LIONS, FIVE MISSIONS, ACTION, DEATH OR LIFE, ADVENTURE, BRAIN GAMES, REDRESS, A BREATHTAKING LOVE THAT STEALS THE HEART AWAY.♥️🔥

E_____________11

Ɗakin da yakasance mallakin ɗaliban aji biyu Madam ta kaita, tin da suka shiga Seraph ke faman kallon ɗakin kamar ta ga wani abin daga wata duniya. Bed guda huɗu ne a cikin ɗakin, uku yara na kwance a kai, ɗaya babu kowa. A nan Madam Rohisha ta kaita, sannan ta kira dikkan ƴan'matan dake kwance a saman gadonsu kan su zo ga bakuwa sun yi. Su ukun dik suka sauƙo, ƴan yara ne da basu wuci Seraph ɗin ba.

A wajen gadon suka zazzauna suna kallon Madam cike da kulawa, ita ma cike da kulawa ta ce. "Wannan bakuwa ce, ku kula da ita sosai, Aana kinga kin fi su girma ko? Ki kula da su"...... Wacce aka kira da Aana yarinya ce da zata iya kai 13 years, su kuma kun ga a lokacin 9 to 10 suke, ba'a cika 10 ciff ba.

Kama hannun wata kyakkyawar yarinya Madam ta yi, ita ma ba zata wuci 11 years ba, cikin sanyin murya ta ce. "Rimsha, wannan ita ma kamar ke take, she don't have anyone, bata da Father and Mother, take care of her kin ji? Ki kwarara mata gwiwa". Da sauri Rimsha ta É—ago kai, dan ta san zafin rashin iyaye, mahaifinta ya rasu, mahaifiyarta babu wanda yasan in da take, a hannun kakanninta take rayuwa sai uncles É—inta da suka tsani ganinta.
Chapter 45 · 0% Book details