← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 190 OF 227

Sashe 190

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Mu je lokacin sallah ya yi". Vir ya faÉ—a. A tare suka fito zuwa other rooms na floor É—in, dan su yi gaggawar shirin zuwa masallaci. Yau dai kafin su shirya Lion ya tafi, sai a lokacin kuma ya faÉ—owa Aryan ashe bai yi sallah la'asar ba, hakan yasa ya ce su je zai yi sallah a gida bayan ya biya bashin wanda ake binsa.

Vir da guru suka wuce suka bi bayan Lion. Shi kuma Aryan ya shinfiÉ—a dadduma ya tada sallah a gida.

After 3 hours.

*Jama'ar kirki littafin ZAKUNA BIYAR STEP 1 ya zo gangara, zamu shiga STEP 2 wanda shi ne ainahin labarin yake cikinsa, ZAKUNA BIYAR iya STEP 1 ne kawai free, daga STEP 2 zuwa karshe paid ne, 1k kacal yake, ki hanzarta making payment kada mu tafi mu barki, dan labarin bai ma fara ba, tarin ilmin, faÉ—akarwa, waazantarwa, wayar da kai, nishaÉ—antarwa dik yana cikin STEP 2, yanzu dik ba'ayi komai ba, STEP 1 dik sharar fagece, ainahin labarin yana gaba, in kin shirya makin payment ga account É—ina, 2308489938, Musa Fatima Zahra UBA bank. Sai ki turo mun evidence ta wannan number 08161390581*

Likes comments and share fisabilillah.

QUEEN OF SURPRISE ✍️🔥

ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️

🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥

PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.

For more information 08161390581 Whatsapp me only.

STEP 1🔥

2025-12-24.🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E_____________ 63 & 64

After 3 hours.

Zaune suke a saman chair na dining, dinner suke yi a natse, babu wanda ya ce da ɗan uwansa ƙala, dik kuma suna kallon abin dake gabansu face Lion dake kallon waya kuma yana dinner.

After some minutes suka kammala dinner, kusan a tare suka ajiye spoons, basa da yawan cin abinci, kai suna iya 24h basu ci abinci ba, kuma basu damuwa, idan sun zo ci É—an kaÉ—an suke ci su tattare sauran.

Suna ajiye spoons Lion ya miƙe, cikin room ɗinsu ya shige, bayansa suka bi da kallo har ya shige, Vir ya ce. "Yau Lion ya koma sak daddy, sarautar ta motsa har damu ma yi za'ayi"......... Aryan ya ce. "Ai da sauki ma tin da uncle ne ya taɓosa, kasan uncle kuma ba yadda muka iya da shi, sai dai mu ɓata rai a cikin zuciya".

Miƙewa guru ya yi yana faɗin. "Ina zuwa, ina da aiki"...... "Aikin me?". Vir ya faɗa yana miƙewa shi ma..... "Aiki kan malaman secondary school da Champion ya haɗani da su". Ya faɗa tare da shigewa cikin ɗakinsu. Kallon Aryan Vir ya yi. "Me malamai kuma suka yi?".

Tamke fuska Aryan ya ƙara yi game da miƙewa tsaye, cike da takaici ya bashi labarin dik abin da ya faru kan Seraphina da kuma Rimsha, shi ne yasa guru ya yi mashi bincike kan daga ina matsalar ta samo asali, dan ya ji ƙishin-ƙishin cewa da sa hannun gwamnati, to yana son tabbatarwa kafin ya ɗauki mataki, shiyasa guru yake aikin sirri a kai. Shiru Vir ya yi, can kuma ya ce. "You mean ɗiyar Dr Hushaima tana raye?".

Kai ya jinjina alamar e. "Where's she?". Kara tamkar fuska Aryan ya yi. "Kasan tin asali Dr da Lion basa shiri ai, ba zai bar Seraphina a kusa da shi ba".... Tamke fuska shi ma Vir ya yi kafin ya ce. "Ya za'ayi Dr ta yi shiri da Lion bayan azzaluma ce, ta cuce shi ta cutar damu, ai ko ni bana goyan bayan ya taimakawa Dr, amma kuma ina goyan bayan ya taimakawa rayuwar Seraphina tin da ita bata da laifin komai, laifin wani baya shafar wani ai".

Ɗan rage tsawonsa Aryan ya yi, ya dafa table ɗin gabansa, soyaya ta rufe mashi idanu, baya son laifin Dr sam, a ɗan dake ya ce. "Wace hujjace ta tabbatar maku cewa Dr tana da laifi? Vir ka daina bin bayan Lion a lokacin da baka da hujja a hannu"...... Kada ku manta sarai Aryan yasan biyan Dr akayi maƙudan kuɗaɗɗe, ya ga alert ɗin a wayarta, amma in baku manta ba ya ɓoye maganar alert ɗin bai sanarwa Lion ba, kunji yana son kareta saboda yana son Seraphina.

"Lion bai taɓa hasashen banza ba, bai taɓa yanke hukunci ba tare da ilmi da dogon nazari ba! Dik hukuncin da ya yanke zallar gaskiyarsa ce a kai, dan haka Dr tana da sa hannu a kashe big brother, in ba haka ba meyasa taki buɗe mashi kofa a lokacin da muka sanar da ita rayuwansa na cikin haɗari? Kada ka manta dik iyayenmu sun rasu, manyan brothers ɗinmu dik an kashesu! Saura mu kaɗai muka rage, big brother shi ya tsaya mana bayan uncle, taya kake tinanin ba zamu ji zafin mutuwansa ba?". Har yana ɗan huci ya kai karshen maganar. Nasan kowa ya matsu ya ji tarihinsu, to kada ku damu, zaku ji komai dallah-dallah, ku kara hakuri saura kaɗan.

Shiru Aryan ya yi, hakika yasan sun azabtu a kashe big brother da aka yi, sun kai zuciya nesa ne, amma ba dan haka ba, ALLAH ne kaɗai yasan ɓarnar da za'ayi, shi kansa karfin hali ne yake son gwadawa na kare Dr, ban da haka ai yasan babu hanyar da ya gwada tana da gaskiya.

Ganin ya yi shiru ne yasa Vir sake cewa. "Ga shi a dalilinmu an kashe daddyn Vash, daddyn Rimsha, daddyn Humaira, daddyn Seraphina, all because of IRON FIST, amma still yanzu kana son Lion ya amsa cewa zai fito tamkar yadda dad ya yi? Kana son mu sake rasa uncle ne? Kada ka manta duniya dik ta É—auka cewa Hussain ya mutu, baya raye, so kake allura ta tono garma?".

Sai a lokacin Aryan ya samu kwarin gwiwar yin magana, nisawa ya ɗan yi game da cewa. "Uncle ba zai taɓa yin abin da zai cutar damu ba, kada ka manta shi ya umarci da mu ɓoye kanmu a farko, sannan shi ya renemu a irin wannan siga domin mu girma mu ɗauki fansa, ka taɓa tinanin meyasa uncle ya zaɓemu bayan muna da brothers dikkanmu? Ka taɓa tinanin meyasa iyayenmu dik basu renemu da kansu ba suka haɗawa Uncle mu? Suka miƙawa uncle yai mana irin wannan reno?".

Nisawa Vir ya yi, a wannan gaɓa Aryan yana da gaskiya, amma dik da haka akwai buƙatar ƙara lokaci kafin su bayyanawa duniya kansu da manufarsu, a natse ya ce. "Even do! Yakamata mu ƙarisa wasu abubuwan da muka fara a ɓoye kada a rusa mana su". Cikin wannan sanyin murna nasa Vir ya faɗa...... "Da wannan dan wannan, but......"......... "But what?". Yana hararansa ya tari numfashinsa.

Hararansa Aryan É—in ma ya yi game da cewa. "You want to push me against the wall"........ Hannunsa Vir yakama suka nufi cikin É—akin Lion ba tare da ya sake magana ba. Nan suka isko Lion kwance saman gado, ya É—aura hannunsa É—aya a kansa, É—ayan hannunsa a kan cikinsa, guru na sanye da bathrobe, da alama daga wanka ya fito, yana tsaye tsakiyar É—akin suna fuskantar juna da Lion.

Cikin zolaya guru ya ce. "Wai meyasa kake kallona ne?". Yana kallon Lion ya yi maganar. Aryan ne ya amsa da. "Yaga alama ce a jikinka mana". Vir ya amsa da. "Ba dole ya dinga ganinka ba É—an autan IRON FIST".

Wucewa closet ɗinsu guru ya yi, bai sake yin magana ba, su kuwa Vir ya shiga toilet dan yin wanka, Arya ya zauna gefen Lion tare da riko hannun Lion ɗin, cike da kulawa ya ce. "Bro please a huce haka, talk to us, Uncle fa ya tafi". Tamkar babu Lion a wajen. In takaice maku har suka yi barci Lion bai furta word ba, tamkar wanda aka ɗinkewa baki, yana dai binsu da ido, har suka gaji da magiyar ya yi masu magana suka kyalesa, dama sun san wlh in dai ya yi wannan shiru kome za'ayi ba zai yi magana ba, sai san da yaga dama, ba'a saka shi kuma ba'a hana shi, ganin damansa kawai yake bi, amma dik da haka suna gwada lallaɓa shi da yi mashi magana idan ya fara wannan shirun dik da sun san ba zai amsa ba.

A haka suka kwanta barci, kuma shi ya tashi ya sake binsu da tofin addu'a dik da yaki kulasu, can dare around 1 ya tashi ya É—auro alwala, ya haye kan dadduma ya fara gabatar da sallah, bashi ya sake kwanciya ba sai around 4, ya kwanta zuwa 5 ya tashi ya nufi shirin zuwa masallaci, a tare suke sallar dare kullum, yau sun gaji ne yasa suka kasa tashi, kuma basu yi barci da wuri ba, suna ta hiran yaushe gamo da Vir.

Sai da ya yi shirin sallah ne ya zo ya tashesu, Aryan ne ya fara farkawa, a gaggauce suka shirya suka fita izuwa masallacin cikin CRYSTAL PALACE É—in.

Bayan idar da sallah sun zauna a masallaci, suka yi karatun Alkur'ani mai girma, suka kuma yi askar, a nan ne Lion ya nemi zaɓin ALLAH kan ya koma gidan daddynsa ne ko kuma ya zauna a gidansa? Ya yi addu'a ya roki zaɓin ALLAH sannan ya barwa ALLAH komai, daga nan suka miƙe suka nufi komawa gida.

A nan ne Aryan ya zame daga cikinsu ya gudu wajen Seraphina. A lokacin da ya shigo room ɗin ya iskota tana ƙoƙarin jan zip na sket ɗin uniform ɗinta ta baya. Hannunta dake rike da zip ɗin ya kama game da ɗan jan sket ɗin sama, ya gyara zura rigarta ciki da suke yi, ya saita waist ɗinta kafin ya ja mata zip ɗin sama.

Nisawa ta É—an yi game da juyowa tana faÉ—in. "Good morning my gentle chaos". Tana murmushi ta faÉ—a....... "Morning my cherry, how's your night?".... "Cool and you daddy?". Hannayenta ya riko game da amsa mata da. "Super cool cherry"........ Tana É—an murmushin one side ta ce. "Ka ci abincin jiya?". ALLAH sarki soyayya, da wannan zance na yana jin yunwa a ranta ta kwana.
Chapter 190 · 0% Book details