← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 227

Sashe 75

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

An basu data mai karfi dan satarwa, an saita wayoyinsu da na'urorin su Arya. Dikka waÉ—an nan abubuwa fa wannan shegen rucksack É—in nasu ya kwashesa, ga kayan sakawansu still a ciki, jakar ta cika dam, sai da aka sanya masu belt aka iya rufe jakar, ta yi mugun nauyi, amma a haka zasu É—auka a bayansu. Mazan fama ba, soja ba dik kai ba!.

A ɓangaren Manassa an zuba mata Individual first aid kit mai shaƙe da kayan farko na taimakon gaggawa, a cikin akwai irinsu bandages, tourniquet, hemostatic agent da sauransu dan ceto ran soja da gaggawa. Sannan an sanya mata combat medic kit, kayan aikin likita masu yawa sosai kuma masu amfani da za'a buƙata a gaggauce dan jinyar raunin filin daga ƙananan zuwa matsakaita a yayin mission.

Dikkansu an basu water bladder dan su samawa kansu ruwa a koma ina suke, kuma ruwan zai zama mai tsabta har su sha su yi abin da zasu yi. Dik an basu ƙananan sleeping system mai caji da rana dan in suna barci wani motsi ya zo komai nisan shi wannan ya ankarar da su. An basu entrenching tool na karfe wanda ake haɗa shi da notika, idan sun isa wajen da zasu kafa tantina suna iya haɗa shi, kamar shovel haka yake, dan su tona rami aka basu.

Sannan dikkansu an basu gas mask wasu kuma cbrn mask, mask ne dan kare numfashi daga iskar guba, iskar sinadarai ko biological hazards dake yanki, takan iya yuwuwa akwai gurɓacewar yanayi a in da suka nufa, wannan mask zai hanasu shaƙar gubar. Sannan an basu cbrn suit mai kama da jacket, yana kare gangar jikinsu daga iskan sinadarai ko gurɓacewar yanayi. An basu cbrn hands gloves, da kuma ear protection dan kare kunne daga ƙarar makami, suna sanya shi kada su rasa jinsu saboda karar bindigu.

Su Arya jami'an computer na musamman kuma an shirya masu compass & maps gps unit a laptops ɗinsu, kuma dik abin da aka basu mai caji da rana ne, dan shi rana a ko'ina akwaisa, lantarki kuwa kun san babu, shiyasa aka masu masu amfani da rana kamar solar kenan. Sannan an haɗa masu gps enabled devices, wannan zai taimaka masu wajen daidaita matsayi daga nesa sosai. An shirya masu na'urar hangen sama, ga su unmanned aerial vehicles, ƙananan drones dan hango sama daga nesa, ga portable drone controllers dan sarrafa uvn na waje.

Uwa uba an haɗa masu counter drone systems wanda zai iya gano drones na abokan gaba idan sun turo masu, su suna iya turawa abokan gaba ƙananan drone ɗinsu, su yi control ɗinsa ya je har in da miyagun suke, suna zaune a cikin tantin da suka kafa a sansani suna kallon dik wani motsin ƴan ta'adda a laptop ɗinsu suna kwasan bayanansu suna sanarwa sojojinsu. Kai an fa shirya masu kaya dayawa, sannan aka shirya masu ɗanyen abinci, su zasu girka kayansu da kansu, su Arya aka shirya masu laptops ɗinsu a cikin rucksack, sannan aka basu bututun iska saboda faɗawa kogi ko wani rami na ruwa.

Tambayana a nan shi ne, shin masu karatu sojijin ƙasarku haka ake basu kwararrun kayan aiki a lokacin da za'a turasu faɗa da wasu ƴan ta'adda? Ko iya bindiga kawai ake basu?.

Dikkansu suna sanye da uniform a jikinsu, har da su Arya yau an basu uniform, sun kuwa yi balain kyau, tamkar dan su aka yi kayan, sun kara kwarjini da firgita makiya.

Dikka sojojin ƴan uwansu suna wajen dan yin bankwana dasu, ta yiwu su dawo a raye ko kuma akasin haka, kowa zai ga ɗan uwansa na karshe ne a yanzu. Ummie bata zo ba, dan Zaysh ya ɓoye mata, ya ce mata dai zasu shiga wani aiki, zata iya kiran wayansa ta ji a kashe idan babu rana basu yi caji ba, amma dik in ya kunna waya zai kirata. A haka ya kyaleta, dan baya son ɗaga mata hankali.

Babban soldiers eagle aka kawo dan ɗaukarsu ya yi dropping ɗinsu a bakin dajin da zasu shiga mission na farko, idan ya saukesu a wajen sai su kutsa cikin daji da ƙafarsu. Suna ta ɗagawa ƴan uwansu hannu suka fara shiga jirgin a jere cikin tsari haɗe da ɗan pareti, da haka suka shige cikin jirgin suna kallon ƴan uwansu, Leo yana ta kallon Champion and Lion da guru dake tsaye a babban filin tashin jirgin AZURE, dikkansu suna sanye da nose mask, ga katuwar jacket da suka sanya, p-cap a ciki kafin su sanya hukar jacket ɗin, sun yi kyau kam matuƙa.

Sai da jirgin su Leo ya ɗaga sannan IRON FIST suka bar barrack ɗin, suka koma hotel da suka sauƙa, ba yau zasu koma ba, dan akwai binciken da suka zo yi dan tabbatar da wata gaskiya da basu faɗi ba, so zasu ɗan yi kwana biyu a nan.

Daddy Noor ma sai da ya ga tashin jirginsu sannan ya koma gidan GAT ya hau shirin komawa US.

Su V da suka zo tafiya sai da zuciyarsu ta ɗan kaɗa, dan basu taɓa tafiya aiki ba kun sani, dole su ɗan tsorata, amma Arya yarinyar nan tamkar babu zuciya a kirjinta sai dutse, ko kaɗan bata tsorata ba, sai ma cewa da ta yi su yi sauri su tafi, dan ita ma ta shiryawa mutuwa, bata da tsoro ko kaɗan yarinyar, ita dai V ta ji kwarin gwiwa ne kawai a waje ɗaya shi ne Noor yana tare da ita, tasan dik wuya zai tsaya mata.

Manassa and Angelina kam ba'a magana, ita Manassa komai normal ne, baka gane tana farinciki ko bata yi, kamar Vash take, komai daidai ne, ko su mutu ko su rayu dik daidai ne, ita kuwa Angelina har da guntun hawayenta, wai na kewar daddynta ne hawayen, kuma karya ne, zuciyarta ne ya fara karaya, ta ji tsoron su mutu, dama a cikinsu dik ita ce mai tsoro gaskiya fiye da Manassa, tana da saurin karaya, karfin hali ai sai Arya, balai, yarinyar nan ko mutuwa ake yi ba zata fasa abin da ta sanya a gaba ba, ita ta gado daddynta sak, dan kafin ya taka matakin GAT ai sai da taurin zuciya da jajircewa, to ita dai da kwarin gwiwarta suka nufi can.

Jama'a an iso in da nike son mu iso, sojojinmu sun tafi Mission, yanzu zamu shiga ainahin labarin ZAKUNA BIYAR, yanzu zamu isa ga ainahin jigon labarin, masu hawan jini, masu low bp ayi hakuri da abin da alkalamina zai rubuta a wannan karon, na san fore sure zuƙata zasu kaɗa, hankula zasu tashi, amma amin afuwa, ilimi da farkar da al'umma nike burin yi! Sannan zan so wannan ɓangare dana kira da jigon labarin nan kada ku tsallake waje ko ɗaya, da daɗi da ba daɗi dik ku yi hakuri ku karanta, dan amfananku ne, ba karamin amfani zai yi maku ba!! Muje zuwa kan jigon labarinmu a yanzu!.

-----------------W-S-Hospital🔥

Cikin wajen tamkar ba'a duniya take ba, ta ko'ina glasses ne da wutar lantarki, zaku rantse da ALLAH dik lantarki duniya a nan wajen ake karar da shi, ko da sunan wasa wuta bata motsawa a wannan waje bare a É—auke, jikin bangon ainahin wajen kakkafar bango ce da zaku yi zaton samudawan da ne suka gina shi ba mutane ba, dan gini ne da aka yi su da duwatsu masu karfi sosai. Amma daga ciki ko'ina na glass ne, ga kayan zamani ta ko'ina. A dunkule kenan, mu kara kutsawa ciki dan ganin meke going.

Ƙofofin wajen masu ƙarfi ne sosai haɗe da kimiyar tsaro na zamani mai ban mamaki, suna amfani da fasahar tsaro mai ƙarfi, tare da makullai na lantarki, akwai wani sashen ma da babu wanda yake iya shiga sai mutane uku, dan wajen door ɗin kuna taɓawa shocking ne a jikin, sai dai a ga mutum ya ƙandare in ya taɓa.

A gefe guda ga wani side tamkar fagen kwaje-kwaje na hospital haka aka yisa, dan ga É—akuna da beds dayawa a side É—in, kowani É—aki da dalilin hasasarsa a wajen. A wani side É—in kuma É—akuna ne masu kyau da gadaje masu rai da lafiya na majinyata, ta kowani kusurwa akwai CCTV, a saman bene kuma akwai wani É—aki mai cike da computer dan kula da cameras dake ta ko'ina.

Hospital ɗin yakasance da ɓangarori guda biyar, kai tsaye mu je ɗayan ɓangaren.

Wajen cike yake da glass, dik ɗakunan wajen glass wall ne, filin cike yake da dabbobi kala-kala masu haɗarin gaske, dabobin da idanu bai taɓa ganin irinsu ba, kowacce dabba tana cikin glass tamkar a gidan zoo, ga manya-manyan macizai, kunama, kifaye, kai harta cinnaka akwai wajensu, suna cikin glass, side ɗinsu yana da mugun girma sosai, kuma dik cike yake da waɗan nan dabbobi. Ɓangarorin hospital ɗin nan kowanne da abin da ya kunsa, ba zan fayyace maku me a ciki gabaɗay ba, sai tafiya ta yi tafiya, dan haka mu je zuwa, kun dai ji ɓangare na farko na dabbobi ne kawai!.

Akwai nurses dayawa a hospital É—in, amma dikka mata ne babu namiji ko É—aya, sai dai dik nurse da zaku gani a wajen sai kun kalleta kun sake kallo, babu munana a wannan waje, ga su da zubin Æ´ar tsana, sirara ga shape, farare tas-tas da su, rigarsu na aiki guntaye ne zuwa tsala-tsalan cinyoyinsu masu kama da madara saboda hasken jikinsu, suna da hakin gashin mai shegen kyau wanda suka É—auresa a tsakiyar kai, kansu da hular aikinsu, ga su da tsabtar balai, komai nasu cikin tsantsar kula da natsuwa suke yi, one thing about them, dik wata malamar asibit dake wannan Hospital É—in shekarunta É—aya da sauran, dikkansu they're age mate, babu wacce ta girmi wata a cikinsu, kuma dikkansu yanzu 18 years suke da shi, sannan abin da zai baku mamaki dayawa daga cikinsu suna É—an kamanceceniya da juna, wasu ma ida ka gansu zaka zaci twins ne, sannan sun kai su 40 a hospital É—in.

Abin da mamaki ko? Ace shekarunsu su 40 ko sama da haka dikka ɗaya, sannan dikkansu mata ne ba maza tamkar dama zaɓosu aka yi, kai ko zaɓosu aka yi sai haka!.
Chapter 75 · 0% Book details