← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 227

Sashe 7

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya ɗan dakata da yin maganar yana bin fuskokin kowannensu da kallo. Dukansu sun wani natsu suna bin shi da kallon suma, wasu da kallo mai cike da tuhuma, wasu kuma da kallo mai cike da tsantsar ƙauna. In faɗa maku gaskiya? Kowa ya ga GAT sai ya sake kallonsa, kyakkyawan dattijo ne ajin farko, fari tas tamkar ka taɓa jini ya fita, ga balain kwarjini da farin jini, dik in da ya je ana sonsa kuma ana haukar tsoronsa, fuskansa babu alamar wasa ko fara'a, amma a haka kowa son shi yake yi, yana da jajircewa matuƙa a kan aikinsa, idan ya wurgawa mutum waɗan nan dara-daran eyes ɗin nan nasa wlh sai ka ji fitsari ya kubce maka, eyes ɗinsa suna da zurfi da firgitarwa, gasu milk color mai ɗan duhu, kwayar kuma tiger brown, a shekaru zai iya kai 45 to 47 years haka, amma idan kuka gansa wlh ba zaku bashi even 30 yrs ba, yana da kyan jiki matuƙa, ga gashin kansa bakinkirin babu alamar furfura, ba dan na san shekarunsa na gaskiya ba da na ce karya ne bai wuci ɗan 25 ba! Saboda jajircewansa a kan aiki ya tara uban makiya da masoya, babu mai shege mashi gaba bai takesa ba, baya hawa tsarin kowa, sai dai a hau nasa!.

(WANI IRIN RAWA KUKE TINANIN ZAI TAKA A WANNAN LITTAFI BAYAN WANNAN YABO DA YA SHA DAGA GARENI?)

Cigaba ya yi da cewa. "Ina fatan samun sakamako mai kyau daga gare ku a wannan zama, lokacinku ya fara daga yanzu!". Yana kai karshen maganar ya koma ya zauna a saman kujerarsa.

Yana komawa ya zauna wani dakakken soja ya mike wanda akalla zai iya kai shekaru 40-45, fuskansa a É—aure tamau babu alamun wasa a tattare da shi, ga razani da kwarjini irin na sojoji a tattare da shi, BRIGADIER GENERAL AMEEZAN (BGA) shi ne sunan dake rubuce a gaban kakimsa. Mic dake gabansa ya kunna, sannan ya fara da cewa.

"A gaskiya a nawa ɓangaren an samu cigaba sosai, an samu nasara, mun kashe ƴan'ta'adda a cikin wannan satin a kalla sunkai talatin zuwa arba'in, sannan mun tashi guraren da suke zama, mun hana su zaman gari mun hanasu zaman daji, mun dai samu nasara sosai......". Ya ɗan dakata yana kallon fuskokin sauran sojojin, ya fahimci wasu suna kallon shi ne cike da tuhuma wasu kuma suna kallon shi cike da gasgata shi.

Bai damu ba ya cigaba da cewa. "Mun raka yan ta'adda a guje tamkar karnuka, mun hana su sukuni, babu abunda zamu ce sai dai godiya ga sojojin mu da suka sadaukar da rai domin bawa wannan kasa kariya, amma mun rasa sojoji a kalla zasu kai goma, ina jajanta wannan al'amari". Ya kai karshen magana tare da buÉ—e takardar dake gabansa, rahoto ne na shaidan aikin da yake ikrarin sanyi.

Tunda ya fara magana har ya kai karshe akwai wasu generals na sojoji guda biyu da ke zaune a gefensa, sai kallon juna suke suna sake kallon shi, da alamar shakku a kan fuskokinsu, amma babu wanda ya tankasa, dan babu wanda yake magana idan É—aya yana magana.

Gaban General of the army ya turo wannan rahoton nasa yana kara ji da kansa a matsayin sunyi aikin ƙwarai, sai ya koma ya zauna. Wani dakakken soja ne ya sake mikewa cike da nuna tsantsan jarumta. MAJOR GENERAL RAHEEL (MGR) shi ne sunan dake rubuce a gaban kakakinsa.

A kaifafe ya fara magana kamar haka. "Gaskiya ne BGA, ana samun cigaba sosai a ɓangaren tsaro saɓanin baya, a nawa yankunan da nake wakilta an samu nasarori da dama, mun kama ƴan ta'adda sun kai goma sha biyu, muna fatan mu cigaba da samun nasara haka har mu karar da su". Shima ya kai karshen maganarsa tare da buɗe takardun dake gabansa na rahoton shaidan abinda ya fada ya turata izuwa ga GAT.

1 by 1 haka gabaÉ—aya sauran sojojin suka mike sukai jawabansu. Sai soja guda É—aya ne bai tashi ba, wani kyakkyawan matashin soja da akalla zai kai shekaru talatin da uku zuwa da biyar a duniya, fari tas da shi, kyakkyawan gaske.

Yana zaune shiru yana binsu da ido saboda shi sabo ne a karin girman, satin da ya wuce ya taka matsayin irin nasu bisa ga jajircewa da kokarinsa, karfi da aikinsa ya bashi wannan matsayi, so bai fara aiki ba tukuna, cikin satin nan zai fara aiki shiyasa bai bada rahoton shi ba.

Tattara dukkan bayanansu GAT ya yi sannan ya mike ya rufe masu taron a zuwan zai duba rahotannin nasu sannan kuma zai zurfafa bincike saboda tabbatar da gaskiya suke faɗa ko ba haka ba, a bayaninsa na rufe taron ya kara masu karfin gwiwa, ya nuna musu su kara jajircewa dan tabbatar da tsaron wannan ƙasa, ya ja kunnensu sosai ya kuma tsawatar musu a kan su tsaya suyi aiki, su kawo karshen ƴan ta'adda, ya kwarara musu gwiwa sosai sannan ya rufe musu taro da addu'a irin tasa.

Bayan rufe taron shi ya fara fita kafin dukkan sauran sojojin su rufa mishi baya. Suna fitowa BGA ya tsaya gaban ƴan jaridu domin basu rahoton abin da suka tattauna a yanzu, ya sanar da su cewa ana kara samun nasara ɓangaren tsaro, sannan ya kara da cewa an yi nasarar kama wasu daga cikin ƴan ta'adda, daga karshe ya rufe masu da cewa ƙasarsu ta kusa tsabtata daga datti ƴan ta'adda, sun kusa kawo karshen ta'addanci da duk wani tada kayan baya, yana masu albishir da za'a samu zaman lafiya mai ɗorewa, ransu fansa ne a kan wannan ƙasa.
Yana gama zuba musu kalaman nasa da kowani ɗan ƙasa yake fatan ji, sannan ya wuce zuwa office ɗinsa dake bene hawa na 4 kusa da office ɗin GAT, ya yi amfani da elevator dan haurawa sama. Sauran Generals duka kowanne ya wuce nasa office. Su kuma ƴan jaridu suka fita suka sanar da al'umma halin da tsaron kasar take ciki. (A gaske haka tsarin yake, haka ƴan jaridu ke yawon faɗa mana halin da ƙasa ke ciki bayan manyan sun faɗa masu son ransu, uhm a wannan karon komai zan rubuta shi ne yadda yake In Sha ALLAH, sai ɗan gyara dan armashin labarin da kuma jin daɗin masu karatu!.)

-------------------------🔥

A gefe guda kuma an kammala yiwa dukkan matasan sojojin nan allura, nan captain ya bukaci da kowa ya wuce ɗakinsa dan ya huta alluran tabi jiki, za su fara karɓan horo cikin kankanin lokaci.

Cikin natsuwa suka fara watsewa É—aya bayan É—aya suka nufi inda ya kasance É—akunansa suke.

A tare wasu matasan sojoji su uku suka nufi inda ya kasance É—akinsu, suna tafiya ne a natse kasancewar yau suka fara sanin juna a assembly hall, da alama dukkansu sunyi maraba da juna, daga yanayin yadda suke tafiya za ka fahimci cewa lallai sun fahimci juna.

Room number 1 shi ne É—akin da suka shiga, dik da kasancewar sun san babu kowa a ciki, hakan bai hana É—aya daga cikinsu daka sallama ba. Sai dai ga mamakinsu kuwa suna sanya kai a cikin É—akin suka yi arba da mutum a tsaye a tsakiyar É—akin. Sun yi matukar mamakin ganinsa dik da cewa sun san mutane huÉ—u ne a kowani É—aki, amma sai suka kawar da mamakinsu su ka karaso ciki.

Ɗaki ne na matasan sojoji, gadaje ne guda huɗu a ciki, akwai komai na bukata, kowane ɗaki akwai toilet nasa a ciki, toilet guda biyu, gadon nasu irin sama da kasa nan ne, irin gadon ƴan boarding school, ya yi kyau sosai gadon, kowane gado yana shimfiɗe da zanin gado da bargo na lulluɓa, duka kalan uniform nasu na sojoji ne, ga karamin freezer. (Kada ku manta ba wai iya makarantar soja bane kawai a wajen, fili ne na yaye kwararrun jami'an da manyan kasashe suka aminta da kwakwalwarsu, waje ne na yaye gifted a ɓangaren kwakwalwa, karfafa a ɓangaren jiki, zaku gane nufina idan tafiya ta yi nisa, amma kafin nan me kuke tinani a wannan gida na soja? Ya ɗakunan kwanciya na sojijin kasarku yake? Irin na AZURE BARRACK ne?.)

Wannan matashi dake tsaye yana goye ne da katan jakansu irin na sojoji a bayansa, da alama kayansa ne a ciki, hannunsa rike da takarda yar karama kaman yana karantawa, kansa sanye da army p-cap.

Kusan a tare waÉ—annan matasa 3 da NOORIEL, ARVASH da ZAYNASH, kusan a tare suka yi mishi sannu, sai dai ga mamakinsu bai amsa su ba.

Kallon juna sukayi cike da mamaki, dan dukansu a lokacin da suka fara gabatarwa da juna kai a assembly hall lokaci guda suka sake suka amsa wa juna kasancewar sun san ba su da kowa a nan, kuma wlh jininsu yai mugun haɗuwa cikin ƙanƙanin lokaci tin kafin ma su gane ɗaki ɗaya suke kuma rukuni ɗaya zasu karɓo horo, amma how comes shi suke mishi magana ya ƙi amsa musu?.

NOORIEL ne ya gagara hakura da alama shi yana da zalama da son mutane sosai, karisawa gaban matashi ya yi, ya tsaya suna fuskantar juna, cikin É—an nuna alamar rashin jin daÉ—in amsa musu da bai yi ba ya ce. "Amma dai ba ka ji mu bane muna yi maka magana baka amsa ba ko?".

Babu alamar gayen zai tanka mishi, sai ma raɓawa gefensa da yayi ya wuce, a saman gadon da ya kasance ita kaɗai ce a cikin ɗakin saura biyu duka ɗaya kan ɗaya ne, ita kaɗai ce babu na biyu akanta. A samanta ya ɗaura takardan dake hannunsa, sannan ya kwakkwance igiyar jakar dake bayansa tare da sakko da ita, ya ɗaura jakar itama a saman gado, bai ko kalli in da suke ba. Abin ya basu mamaki sosai, sun san cewa a lokacin da suka zo wannan barrack ɗin, sun ajiye jakunkunansu a ɗakin, ba suje assembly hall da su ba, amma shi kaman bai yarda da su ba, da jakarsa ya tafi.

Sororo NOORIEL ya tsaya ya saki baki yana kallonsa cike da mamaki, basu tsammace hakan ba. Shi kuwa yana ajiye jakarsa ya cire p-cap dake kansa.
Chapter 7 · 0% Book details