← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 227

Sashe 30

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nisawa Leo ya yi jin labarin, a ransa yake mamakin jin sunan Fayruz Zaheeran, tabbas ya taɓa jin wannan suna, amma a ina? Ya mance, gefe guda kuma mamaki yake yi jin cewa Noor ya fi to ne daga CRYSTAL PALACE, like wow, waje ɗaya suke, dan shi ma Leo daga can yake, suna gini guda amma basu san juna ba. Da ya tuna suna gini guda sai ya ce kila a nan ya taɓa jin sunan Fayruz Zaheeran ɗin, lokaci guda kuma ya sake tunawa ashe fa suke da mallakin STARS BODY LUSH, zai iya yiwuwa ma a jikin mansu ya ga sunan.

Jin labarinsa yasa ya ji tausayinsa matuƙa, sai ya guduri niyyar taimaka mashi da gaske, a farko ya fara bashi horo ne saboda kansa ya daina sanyasu ɗaukar last, yanzu kuma zai bashi horo ne a matsayinsa na maraya ya tsaya ya karfafa kansa. Tin daga wannan rana Leo ya fara horar da Noor horo ta musamman, ya ja shi a jiki sosai, su Zaynish sai mamaki suke yi yadda aka yi Leo yake jan Noor a jiki har suna magana, sun kuma yi mamakin yadda aka yi Noor yanzu baya faɗuwa a horo, yana kokari sosai.

Sai ma da Leo ya zaunar da shi, ya nusasshesa cewa lallai ya tsaya tsayin daka ya zama namiji, kada ya biyewa shirme, kada ya manta mahaifinsa shi kaɗai ya mallaka namiji, shi kaɗai ya kwallafa rai a kansa, kada ya zubawa daddynsa ƙasa a ido, ya tsaya ya jajirce ko dan ƴan uwansa mata dake gida. Irin waɗan nan kalamai Leo ya dinga yi mashi, har ya sanya Noor ya ji wani irin karfi da kwarin gwiwa ya lulluɓesa, cikin ƙasa da wata guda gabaɗaya Noor ya canza, ba zaku taɓa cewa shi bane, ya zama jajirtacce, dik in da Leo ya sanya kafafunsa Noor ma zai sanya nasa, sun zama very close brothers!.

-------------------🔥

A yanzu sun kai watanni uku a GIDAN SOJA, sun tsaya tsayin daka suna karɓar horo babu wasa, manyan generals sun yi matuƙar sanya idanunsu a kan room 1 ɗin nan sosai, saboda jajircewa da baiwa irin nasu, yanzu ba iya Noor kawai ba, gabaɗaya ɗakin training ɗin dare suke yi, saboda su bada mamaki! Amma su Zaysh Leo yana basu horon dare ne dan kada su ja team na su ya rinƙa faɗuwa, Noor kuwa a yanzu yana bashi ne a matsayin Brother!. E akwai case.

Yau takama Monday, 5:30 bayan sun yi sallar asuba, tsaye suke a hall da suka saba tsayawa, gabaɗaya matasan idan kuka gansu a yanzu sun canza, dikkansu jikinsu ya karɓi horo wuta-wuta, dik sun murɗe sun fara zama mazajen gaske, musamman team 1 dake satar hanya su yi horon dare, jikinsu ya fi na kowa murɗewa, shi kam Leo baa magana, dama jikinsa da horo ya zo AZURE, yana gym, yanzu ya zo ya kara wuta-wuta, ai idan kuka gansa sai ka sha jinin jikinka.

Yanzu fa sun saba da Captain sosai, yana mugun son waɗan nan matasa, ya hora yara dayawa, bai taɓa jin wasu a ransa irin su ba!.

Cike da takun jarumta ya iso wajen, kamewa suka yi suka sara mashi tamkar yadda suka saba. Saman stage ya haye, ba tare da ɓata lokaci ba ya ce. "1, 2, 3 start!" Cikin ɗaga murya.

Yana cewa start suka buÉ—i baki game da É—aga murya suka fara rera taken GIDAN SOJA...... "We march through fire, through storm and rain, with steel in heart, we bear the pain, for land and honor, we stand so tall, United as one, well never fall. Oh, we rise, we fight, we stand as one, through darkest nights, til battle's won. With fearless hearts, our banners wave, We are the strong, we are the brave! Our boots leave echoes on the ground, A thunderous beat, a mighty sound. No chains can break the will we hold, Our spirit fierce, our hearts like gold. Through blood and dust, through fire and war, we march ahead, forevermore. For freedom's call, for justice true, Our oath is strong, we'll see it through. Oh, we rise, we fight, we stand as one, through darkest nights, til battle's won, with fearless hearts, our banners wave, we are the strong, we are the brave!".

Bayan sun kammala rera taken nasu, ƙasa Captain ya sauƙa, jagoranci ya yi masu zuwa gym, dan yanzu kowacce safiyarsu tana farawa ne da gym kafin komai. Yana zuwa ba ɓata lokacin suka fara, a yanzu 500 push-ups suke yi in less than 15 mins, 500 sit-ups 300 burpees, kuma cikin zafin nama ba nuna kasala ko gajiya.

Room 1 suna yi ma suna tafawa da juna, Captain ya ga sabon salo, dan kuwa idan suna yi sai su ce É—aya ya hau bayan É—aya, Leo ya É—auki Noor a gadan bayansa, Zaysh ya É—au Vash a gadan bayansa, watau yi haka ma ba wata wahala sai sun É—auki abu mai nauyi. Dik Generals na sojojin nan sun shiga mamaki sosai gaskiya, musamman a kan canzawan Noor lokaci guda, hakan yasa suka tsananta sanya masu ido sosai.

Bayan sun kammala push-up Captain ya sanyasu yin 200 squats da kaya a bayansu, wannan horo ana yi masu ne yadda zasu kware wajen iya É—aukan Æ´an uwansu a lokacin wahala, misali idan an harbi wani soja zasu iya É—aukansa a bayan wuyan ko a kafaÉ—a ba tare da sun gaji ba, kun gane ai?

Haka suka kwashi 1 hour ana koya masu yadda zasu gudu da koda gawar Æ´an uwansu ne a filin yaki, aka dinga sanyasu É—aukan kayayyaki masu nauyi, shiyasa zaku ga soja zai iya É—aukar mutum dik girmansa a kafaÉ—a ba tare da gajiya ba, to sun saba, su yaku-yakunsu ma É—aukan juna suke dik girmansu su É—aura a bayan wuya kamar sun É—auki kwali tsabar azaban horon ya bi jiki!.

Bayan sun kammala wannan, wajen breakfast suka nufa, kamar kullum aka raba masu abinci, cikin natsuwa suka ci, yanzu an rage masu lokacin cin abinci, daga 30 mins zuwa 15 mins, dole ka kammala a 15 mins in ba haka ba ka ƙoshi, saboda horonsu yanzu ya ninku sosai shiyasa aka rage lokutan da basu da amfani sosai aka kara masu kan horo.

Bayan kammala breakfast Captain ya É—aukesu zuwa wajen da zasu yi pain endurance test, ko kaÉ—an babu alamar gajiya a tattare da su, Leo da Noor sun haÉ—a kai, Vash and Zaysh sun haÉ—a kai.

A wannan horo an sa su sun zauna a ƙasa ba tare da wani ya motsa ba na tsawon awa ɗaya, suna riƙe da bindigogi masu nauyi. Idan wani ya kuskura ya motsa, sai team nasu su fara daga farko. Ga ruwan da ake watsa masu daga sama dik dan kara masu azaba, ga nauyi bindiga, ba damar motsawa ko kaɗan, ko hannunka zai yanke saboda nauyi dole ka jure. A yau ne su Noor suka ga amfanin push-up da suke yi, dan shi ya karfafa masu hannayensu har suka iya ɗaukar bindigogin nan ba tare da sun motsa ba!

Team nasu ita ce ta farko a fita wannan horo da nasara, sun yi murna, amma fa an ci kwakwa, É—aukar bindiga mai cike da harsashe ba dik kai ba!. WaÉ—an da suka faÉ—i aka sanyasu suka fara daga farko, waÉ—an da suka yi nasara kuma aka É—aukesu zuwa wajen da zasu yi JUMPING FROM HEIGHT. Wahala kenan!

Wajen wani katanga mai tsawon mita 20 aka kaisu, Captain ya ce suna da 10 mins dole su ko yi hawa katangar nan da gudu su tsallaka shi su dira ta baya!.

Wai baku mamakin yadda sojoji suka iya dirowa daga wajaje masu tsawo? Shiga gida ta katanga baya basu wahala dik tsawonta, hakazalika zaku ga tun motocinsu bai gama tsayawa ba sun iya dirowa ƙasa da gudu, sun kuma iya hawa bene ta hanyar kakkama gini ba ta staircase ko kofa ba, to ga horon da ya koya masu irin wanna, dole su haye wannan katanga su dira. Dik wanda bai yi a kan lokaci ba kun san zai sake ne!.

Ganin katangar da kyau Leo ya yi, a nan ya fahimci su Noor ba zasu iya ba, dan haka sai ya ce da Noor ya koma baya ya zo da gudu ya taka tafukan hannunsa da ya haÉ—a waje guda sai ya yi tsalle ya kama saman katangar ya haura sama. Captain dai yana tsaye yana kallonsu, dan a wannan waje basirarsu ta kwacesu ne, dole su koyi kowacce dabara su yi tsallaka kafin 10 mins.

Ɗaure belt ɗin wandonsa da kyau Noor ya yi, baya-baya ya yi, da gudun gaske ya zo, cikin zafin nama Leo ya sanya gwiwansa ɗaya a ƙasa, sannan ya haɗe tafukan hannunsa cikin na juna. Noor yana zuwa ya taka tafukan nasa Leo ya taimaka mashi ta hanyar tayasa ɗaga kafafun nasa, ya yi tsalle ya damki katangar. Cikin zafa ya haye tare da rike waist ɗinsa yana mai da nunfashi, saura sojojin sai faman gwadawa suke yi babu wanda ya iya, Noor shi ne na farko da ya fara hawa.

Miƙewa Leo ya yi tare da komawa baya, cikin zafa ya zo da gudun gaske, ya taka tsakiyar katangar tare da kara karfin tsallensa ya damki sama. Haurawa ya yi ya samu Noor, bai ko kalli in da saura suke ba ya kama hannun Noor suka dira ta baya. Nan fa dayawan sojoji suka fara ɗaukar salon Leo, sai su zo da gudu su taka tsakiyar katangar su kama sama su haye.

Captain yana mamakin irin baiwar Leo, kullum shi yake kawo masu salo na musamman, har ta kai in suka je wajen sabon horo suna jiran Leo ya fara, da ya yi kowa zai É—auki salonsa. Zaysh, Unays, Vash and Juraiz matashin dake É—akinsu Unays, su ne suka yi na biyun haye katangar, Juraiz jajirtaccen matashi ne, shi ma É—an Naija ne, ya fito daga Kano ta dabo tumbin gwiwa, kun san kanawa dik abin da suka yi niyyar yi sai sun yi ne, kowa sai ya jirasu! Dan haka Juraiz ba baya ba!
Chapter 30 · 0% Book details