Sashe 65
Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ganin tsananin kamanninsu na buzayen nan ne yasa suka yarda ƙaninta ne, dan dik wanda ya ganta ya gansa, dan ma dai shi wannan gashin nasu ma buzaye ya cika mashi kai sosai, yasa fuskansa ta ɗan rame, amma dik da hakan kamanninsu sosai.
Da sauri ƴan sandan suka karɓi umarni tin da sama da su yake, da gudu suka fice a gidan, sam basu lura da an sumar da amarya ba, su a zatonsu iya Ummie ce kawai. Ai suna fita su Jamilu suka bi bayansu, dan tsoron kada Zaynish ya bi ta kansu.
Suna fita Ummie ta yi ta mazan kama hannun Zaysh ɗin tin da taga ya ɗan sauƙo, shi ma sai a lokacin alluran ta ɗan sauƙa ya iya ganin firgicin dake kan fuskanta, ɗan rungomo shoulder ɗinta ya yi tare da cewa. "Sorry Ummie, wannan firgita dik na mecece?".
Ai da sauri ta rumgumesa ganin dama ya samu ya ɗan sauƙo, sabbin hawaye ne suka fara wanke mata fuska, da kyar ta iya cewa ya je ɗaki dan ALLAH ya basu dama ta kira jama'a a kai amarya asibiti, zai yi mata gardama ta ce. "Zaynish ALLAH idan ka mun gardama zuciyata zata iya bugawa, ka je ɗaki dan ALLAH".
Ganin yadda ta firgita sosai ne yasa ya hakura ya wuce cikin room É—insa, da sauri ta É—auko wayarta ta kunna, number Faisal É—in ta kira. Bugu É—aya ya É—auka, da yake bai san me yakefaruwa ba sai ya ce. "My Æ´ar aljanna yanzu nike son kiranki in ji kun iso ne, dik kewarki ta dameni".
Da kyar ya iya danne kukanta, ta harhaɗo natsuwa tare da girmamawa a garesa kafin ta fara faɗa mashi abin dake faruwa, bata ɓoye mashi komai ba. Fusata ya yi, ya fara yi mata faɗa da cewa dama amarya na jifarta da kalmar mazinaciya shi ne bata taɓa faɗa mashi ba? Meyasa dik rashin kunyar da amarya take yi mata take ɓoyewa bata faɗa mashi?.
Shiru ta yi tana sauraron faɗar tasa har ya kammala, sannan ne ta ce. "Ka yi hakuri, ban son haɗaka faɗa da matarka ce, amma ka yafe mun mijina"..... Shiru shi ma ya ɗan yi kafin ya ce. "Zaynish ya mun daidai, dan ko ni ne hukuncin da zan yi mata kenan, na sha faɗa mata tai maki biyayya, dan ita ƙaƙaba mun ita aka yi, ke kuma ni na ganki na ce ina so, kuna da bambanci, idan tana son zaman lafiya dani ta girmamaki, watau shi ne idan na fita take maki abin da take so ko? To ku kyaleta a wajen babu wani asibiti da za'a kaita!". Cikin faɗa da iya gaskiyansa yake maganar.
Ummie baiwar ALLAH ba zata iya É—auke kai ba'a kai amarya asibiti ba, da sauri ta hau rokonsa kan ya yi hakuri a kaita. Da kyar ya yarda, sannan ya ce bari ya kira kannensa da kannenta su zo su É—auketa.
Cike da mamaki ta ce. "Kai ka yi nisa ne da ba zaka zo ka kaita ba?"..... A natse ya ce. "Bana garin ne, na je tsakanin Adamawa da Taraba". ...... Zazzaro ido ta yi kafin ta ce. "Ma ka je yi can?".
"Wani abokina ne ya ce mu je haƙar gold a wajen, ya ce ana samun alkhairi sosai a wajen, akwai sabon wajen da aka gano yake da gold a wajen, to shi ne na ce bari in jarraba tin da aiki ya gagara samuwa, ki tayani da addu'a ƴar aljanna, ki mun addu'a in yi farar tafiya"..... Dik da bata so tafiyar ba dan tasan yadda ake mutuwa a wajen harkar gold ga wahala, amma hakan bai hana ta daure ta zuba mashi addu'a sosai ba, ya ji daɗi ya dinga amsawa da amin, sai da ya zuba mata kalaman kauna sosai, sannan suka yi sallama yana faɗa mata zai turo kannen amarya yanzu, kuma yana umartanta da ta shige ɗaki yanzu, sannan ta gaida mashi da kaninsa Zaynish ta kuma bashi hakuri da abin da ya faru.
Da okey ta amsa tare da yi mashi fatan alkhairi, daga haka suka yi sallama ya katse kiran, gagara komawa É—aki ta yi, haka ta samu fili a wajen ta zauna har lokacin da Æ´an uwan amarya suka zo suka É—auketa, basu yi wa kowa magana ba, dan already Faisal ya faÉ—a masu cewa akwai zaki jarumin jarumai a gidan, su kula su kuma haÉ—e malaman jikinsu waje guda, idan ba haka ba jikinsu ya faÉ—a masu ma, shiyasa basu yi magana da kowa ba suka É—auketa suka fita, hegiya ta ji maza ta sume.
Ita kuma Ummie da aka tafi da amarya sai ta bi bayan Zaysh izuwa ɗakinsa dake gidan, kuma yana ma da ɗaki a gidan uncle ɗinsa, kawai Ummie ta matsa mashi su sauƙa a gidanta da safe sai suje gidan uncle ɗin ne, baya son zama a gidanta yanzu da ya kara girma, a da dai lafiya lou ya zauna lokacin yana yaro.
Zaune ta iskosa yana danna waya, ya sanya sim card É—insa ta nan gida Naija, da alama wani abin yake son yi. A kusa da shi ta zauna zata fara magana kenan taga yasa waya a kunne, cikin sanyin murya suka gaisa da uncle É—in nasa, sannan ya faÉ—i mashi ya dawo, sun iso lafiya. Watau Zaysh É—an halak ne na gasken-gaske, dik da halin da matar uncle É—insu ta jefasu a ciki hakan bai hana shi yana yabawa uncle É—in nasa kuma yana kara gode mashi ba, and kome zai yi sai ya fara sanar mashi kafin ya yi, tamkar uba haka ya É—aukesa dan yasan ba laifinsa bane, ba shi ya muzguna masu ba, matarsa ce ta yi komai.
Bayan sun gama gaisawa da uncle sun yi sallama ne ya miƙe tsaye, da sauri Ummie ta rike hannunsa tare da cewa. "Ina zaka je?"....... A taƙaice ya amsa da. "Wanka". Sakesa ta yi tare da miƙewa tana faɗin ya zauna bari ta haɗa mashi ruwa. Da a'a ya amsa mata, ya kara da cewa ita da bata da lafiya, ta zauna shi bari ya haɗa da kansa tin da shi ai ba bakon gidan bane.
Zama ta yi tana sauke numfashi a hankali-hankali, shi kuma ya fito ya É—ebi ruwa a bokiti ya wuce toilet dan ya yi wanka.
-------------------------🔥
C-P.
Basu dawo gidan ba sai da suka yi sallar ishai, sannan suka shigo. One by one suka tsala wanka, suka shirya cikin sleeping dress iri guda, sannan suka shiga É—akin aikinsu.
A gaban computers ɗinsu suka zauna, Lion ne ya kunna wani video na zanga-zanga da ake yi a ƙasar AVARIS, natsuwa dik suka yi suna kallon video mai tsawon mintuna 33, sai da suka gama kallo tsab sannan ya tsayar da video tare da cireta gabaɗaya.
"What are you thinking?". Lion ya faɗa tare da kunna wata recorder. Shiru dikkansu suka yi na a ƙallah 2 mins, sannan guru ya ce. "Batu ne a kan rashin tsaron dake Avaris ko?"....... Kai kawai Lion ya ɗan girgiza alamar a'a kallonsa a kan Champion da ya shiga duniyar tinani na daban.
"Yakamata mu sanya ido a kan Avaris sosai, saboda rashin tsaro ya yi yawa, wahala da yunwa sun yawaita, abin mamakin kuma kasar Avaris ita ce ta uku a dukiya da karfin tattalin arziki da albarkatun ƙasa, meyasa kuma take zuwa matsayin sahu na gaba a yunwa, wahala, rashin tsaro, ma'aikata babu albashi, sojoji ba'a biyansu yadda yakamata, dik duniya babu barrack ɗin da ya kai AZURE yaye ɗalibai masu kaifi, fikira da basira, ga horo na musamman da ko ba bindiga zasu iya gwabza yaki, to amma meyasa sojojin basa iya kama ƴan ta'addan? Meyasa komai yake tafiya a juye?". Guru ne ya faɗa cike da damuwa sosai a ransa.
Champion ne ya ce. "Babu wani abin da yake tafiya a juye guru, komai a daidai yake tafiya cikin tsarinsu, sai dai Æ´an kasar ne suke ganin kamar komai a juye masu yake saboda an juya tunanin kwakwalensu". Ya faÉ—a without looking at them, da alama yana jinsu amma ba dikkan hankalinsa bane a kansu.
One thing, da guru da Lion suna da alaƙa mai karfe da AVARIS and AZURE BARRACK shiyasa suke damuwa da ƙasar sosai, kullum aikinsu a kan shawo kan matsalar kasar ne, dan Avaris tana daga cikin top ten ƙasa masu shan bakar wahala a duniya, kuma tana cikin top ten na ƙasashe masu karfin tattalin arziki da albarkatun ƙasa da ruwa, to me matsalar? Abin da kowa ya gagara ganewa kenan, amma alƙalamina zai faɗa maku me matsalar!.
"Zancenka gaskiya ne Champion, amma a tinaninka meyasa Avaris tana da yelwar arziki, ga wadataccen noma, idan ka duba a kididdigar da muka yi suna iya noma abincin da ƙasar zata iya ci ba tare da sun ji yunwa ba, meyasa suke fitowa neman abinci? Manoman dake noma suna fama da yunwa da bakar wahala, meyasa?". Cewar guru.... A wannan karon Champion baya tare da su, so bai ma ji tambayar ba.
Shiru ne ya biyo baya for almost 5 mins, dama shi Lion kullum a karshe yake magana, sai ya gama jin dik abin da zasu faÉ—, ya gama jin ra'ayin kowa kafin ya faÉ—i nasa É—aya tamkar da dubu. Kamar dai ni Princess Teema, sai na gama jin ra'ayin kowa nike faÉ—ar tawa ra'ayin a karshe!.
Jin room ɗin ya yi shiru ne yasa guru yasa hannu zai taɓa Champion Lion ya dakatar da shi tare da cewa. "Wannan abu ne da yake a tsare! Idan har aka bar Avaris da wadataccen abinci, suka ci suka ƙoshi to the next thing abin da zasu fara yi shi ne nemawa kansu da ƙasarsu cigaba wanda hakan zai haifarwa da WORLD SYSTEM damuwa". Ya ɗan dakata kafin ya cigaba da cewa. "Kasan a duniya yanzu babu ƙasar dake da haziƙan mutane kuma ƴan baiwa irin kasar Avaris, sun san cewa idan jama'ar kasar suka farka to dik duniya sai sun jira, shiyasa suke kashesu da yunwa dan ma kada su samu kwarin gwiwar yin wani tinani bayan na abinci".
Cike da rashin fahimta guru ya ce. "To amma ta ya za'ayi a shiryawa babbar ƙasa irin wannan wahala da yunwa?".