← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 227

Sashe 92

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko sau É—aya Leo bai É—ago ya kalleta ba, ya shige cikin ruwan abinsa, sai dai bai tsaya ta kusa da ita ba, saboda ita tana tsoron can tsakiyar ruwa, ta baki-baki ta tsaya, shi kuma wajen yai mashi kaÉ—an tin da ruwan ko waish É—insa bata kai ba.

Can ya shiga har sai da ya kai in da ruwan ta zo daidai kirjinsa. Gagara motsawa Arya ta yi tamkar wacce ta sume, slowly ta juyo bayanta ta ɗan saci kallonsa. Wankansa yake yi cikin kwanciyar hankali, kirjinta dake barazanar tarwatsewa ta dafe tare da jan dogon numfashi kafin ta furzar a hankali, a idanunta kawai ta fara kallon irin yadda ya cire rigar a gabanta, ya ilahi, ita kanta ta shaida Leo ya haɗu matuƙa, jikinsa tamkar madara, ba tabo ba ciwo sai wannan tsage na gerar tasa da ta ƙara mashi kyau sosai.

A takaice sai da ya yi wankansa ya fito, ya mayar da bathrobe É—insa ya bar wajen sannan ta samu salamar dawowa cikin hayyacinta, a lokacin ta É—an iya samun motsawa, jikinta dik a mace, ta ji ba zata iya cigaba da wankar ba, sai kawai ta fito ita ma. Ganinsa dik ya kashe mata jiki, da kyar ta mayar da kayanta ta nufi É—akinsu.

Nan ta isko su Angelina dikkansu a ciki suna ƙoƙarin shiryawa cikin kayan aiki, sun yi wanka a tantunan da suka kafa. Da ganinta suka nufeta suna tambayar lafiya? Dan sun ganta tamkar wacce kwai ya fashewa a ciki ne.

A takaice ta ce masu babu komai, sannan ta wuce ta É—auki uniform É—inta, a gurguje ta hau shiryawa, while Angelina and V sun kammala shiri har sun fito da laptop É—insu dan yin aikin da ya kawosu.

Tactical trouser and tactical t-shirts Arya tasa, kayan sun yi mugun yi mata kyau, ta goge gashin kanta dake zubar da ruwa, ta shirya tsab tare da zube perfume É—inta na kamfanin STAR LADIES BODY LUSH, sannan ta nufi wajen laptop É—inta.

Ita kuma Manassa miƙewa ta yi ta nufo waje dan ba aikinta bane yanzu, tana da free time..... Sosai suka dukufa a kan aikinsu na tsawon good 30 mins, V tana duba ta kudanci, Angelina ta kudu maso gabans, Arya ta yamma maso kudu. Idan a aikin computer ne jama'a to a barwa Arya kayanta, cikin ƙankanin lokaci ta gano motsi a wajen, sannan ta yi amfani da sound-d ɗin jikin drone da ta tura dan jiyo menene a wajen, ta sanya katan Bluetooth ɗinta a kunnuwanta dan ta ji me ake cewa da kyau.

Magana ta ji na mutane, amma bata iya ganinsu, sannan maganar bata iya fita sosai, amma confirm ƴan adam ne suke magana a wajen. A natse ya zare Bluetooth ɗin daga kunnenta, ta ɗaura saman table da laptop ɗin nasu yake, sannan ta miƙe ta fito waje.

Kirjinta na bugawa da karfi ta isa wajen tantin su Leo, daga bakin kofa ta tsaya, yanzu dai taki shiga Æ´ar kaniya, tana tsoron sake ganin abin da ta gani jiya da kuma É—azun. Sara mashi ta yi game da cewa. "Sir akwai karin haske".

Yana tsaye a tsakiyar ɗakin yana rike da wayar da ya kara a kunne alamar waya yake yi, amma shi ma maganansa irin na IRON FIST ne, ba zaka taɓa cewa yana magana ba, can ƙasa cikin sanyin murya tamkar baya motsa lips. Tsayawa ta yi daga wajen tana satar kallonsa har ya kammala wayan, yana sanye da kaya irin nata sak, shi ma tactical trouser and t-shirt ya sanya, da yake ya fita haske sosai kuma launin kayan nasu duhu ne sai ya fi yi mashi kyau, shi shi ya yi wa kayan kyau, ita kuma kayan ne suka yi mata kyau.

Ita dai har yau tana mamakin kitson dake kansa, kuma mugun kara mashi kyau yake yi, sai ma idan ya sakesu, wlh ba karamin kyau yake yi ba, amma yafi yawan tara jelar kitson ya É—aure, idan kunga ya sakesu to yana cikin yanayi mai daÉ—i ne suma zai barsu su shana.

Bayan ya kammala wayan ne ya nufo waje, hakan yasa ta bashi hanya da sauri, a wannan karon ita ta wuce gaba ya rufa mata baya. A gaban laptop É—inta ta zauna tare da É—auko Bluetooth É—in nata ta mayar kunne, hannunta É—aya naa kan mouse na laptop É—in, É—ayan hannunta kuma yana gefen table É—in.

Ciki Leo ya shigo wanda yasa su V kara natsuwa sosai. A gaban laptop ɗin nata ya tsaya, ta bayanta kenan, ɗan sunkuyowa kanta kaɗan ta gefen shoulder ɗinta ya yi a ƙoƙarinsa na son hango motsin dake wajen. Ai jin yadda ya sunkuyo kanta har tana jin sauƙar numfashinsa a jikinta ne yasa gabaɗaya ta birkice ta rasa natsuwarta, har wani ɗan kerma yatsun kafafunta suke yi.

Shi kuwa ko kaɗan bai kawo komai ba, sai ma hannu da ya miƙa ya ciro Bluetooth na kunnen nata ya sanya a nasa kunnen dan ya ji sautin dake fitowa. A lokacin da ya sanya hannu zai cire Bluetooth ɗin nan dogayen yatsunsa suka taɓata sai da ta ji wani irin shock, shi kam bai ji komai ba, to a bakin aiki yake, dik wani tinaninsa da lissafinsa game da hankalinsa ya tafi a kan laptop ɗin, bai mashi ma kamar macece take zaune a wajen ba.

Jin sautin baya fita sosai da ya sanya Bluetooth ɗin ne yasa ya ɗaura hannunsa a kansa mouse ɗin da hannunta ke kai da nufin ya gyara sautin, bai ma lura da hannunta a wajen ba. Saura kaɗan ta saki fitsa a wando saboda razana na jin skin ɗinsa ya taɓata, da sauri ta zame hannunta tana jan wani irin dogon numfashi.

Bai san tana yi ba, ƙoƙarin clearing na voice ɗin ya shiga yi yana sauke mata numfashinsa mai ɗumi a gefen wuyanta, gabaɗaya ya rikita baiwar ALLAH shi bai san tana yi ba...... Ya nemi clear na laptop ɗin sama da ƙasa bai gani ba, hakan yasa ya ɗan juyo da kallonsa a kanta kaɗan. "Ina clearing voice and rash ɗinki?". In a cool way ya faɗa.

Daidai lokacin ita ma ta juyo da kallonta a kansa saboda yadda cool voice ɗinsa ya ratsa kunnuwanta ya yi mugun tafiya da ita, sai ta ji tamkar yana romantic mood ko kuma shagwaɓa yake yi mata, alhalin ba haka bane, kunnuwanta ne kawai ke jiyo mata hakan.

Zuba mashi idanu ta yi, ta manta ya tambayeta ta gagara yin magana..... "Are you okey?". Ya faɗa yana zare kallonsa daga kanta, waɗan nan jade eyes ɗin nasa masu kalar sanyi sun kara rikitata, sai da ta haɗiyi wani irin yawu gwad kafin ta iya amsa mashi da. "Bari in fitar maka dasu". Dama ta ɓoyesu ne a wani waje saboda V dake addaba mata da clearing na wakokin soyayya..

Bai yi magana ba, ya dai jinjina kai. Da sauri ta kai hannunta saman nasa dake kan mouse na laptop É—in da tinanin idan ta É—aura hannunta ai zai cire nasa, sai ta ga akasin haka, domin kuwa hankalinsa ya tafi kan cikin kungurmin dajin da drone da V ta tura yake É—auko masu video, ya mayar da kallonsa kan laptop na V, ko kaÉ—an bai ji hannun Arya a kan nasa ba.

Ita kuwa jin É—umin hannunsa yasa ta mance me zata yi, unexpected ta tsinci kanta da fara shafa skin É—in nasa da golden hair kalar na kansa ke kwance a hannun nasa luff. Jin ana shafa mashi hannu ne yasa ya dawo da kallonsa a kan hannun nasa, da sauri ya juyo da kallonsa a kanta wanda ya yi daidai da ta juyo dan ta saci kallonsa ita ma.

Ganin angry face ɗinsa mai rikitar wannan, ga waɗan man jade eyes ɗin nasa ne yasa ta ji a take natsuwarta ta dawo, har ɗan ɗauke wuta ta yi kafin ya sha jinin jikinta, da sauri ta ɗauke kallonta daga kansa tare da fara ƙoƙarin cire hannunta a kan mouse ɗin, sai ta ga ya rigata cirewa. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta haɗiyi yawu mai wuyar wucewa gwab, sannan ta fara kokarin aikinta.

Bayan ta fitar masa ta ɗauke hannunta ya mai da nasa ya shiga ciki, har yanzu dai jikinta na ɗan rawa, amma ta daure har ya gama abin da yake yi, ta yi mamakin ganin yadda ya kware a computer, har ta ji kamar ta yi bincike a kansa! Me ya haɗa shi da computer da zai iya sarrafata har haka?. Tana can tana tinaninta shi ya kammala abin da zai yi har ya fita waje, da sauri ta miƙe ta nufi kofa dan ta sami damar binsa da kallo, an kuwa yi haka, ta zuba mashi idanu har ya shiga cikin tantinsa.

Su Angelina dai sai kallonta suke yi a sace, sun sha mamakinta. A fili ta ce STERIOUS, MYSTERIOUS, watau sterious mutumin da ba'a iya fahimta, mai ɓoyayyen hali kenan, ta gagara fahimtar a sahun mutane kirki zata sanya shi ne ko a na banza, shiyasa kawai ta bashi wannan suna STERIOUS.

Su Angelina dai suna ta kallonta, ta É—an jima a tsaya a wajen kafin ta juyo ta dawo ciki, ta zauna a gaban laptop É—inta tana cigaba da bibiyar abin, ta sanya Bluetooth a kunnenta, nan ta ji Leo ya gyara sautin maganar na fita sosai, lallai Æ´an ta'addan ne a wajen, ga shi suna magana cikin farinciki da shanawa.

Tana ƙoƙarin yin magana kenan sai ji ta yi Leo dake tsaye a bakin kofa ya ce. "Ki haɗa ƙananan bluetooth ɗin dik ki miƙo mun".......… Da sauri ta ɗago ta kallesa, ya shirya cikin kayan yaki, waist ɗinsa ɗaure da bullets cover, yana kokarin gyara bindigar hannunsa. Sai da ta ji faɗuwar gaba, take ta ji tsoron su je su mutu a can ya kamata, ita da take cewa zata dinga basu wrong information idan sun tafi yaki sai ga ta cikin tsoron kada su je basu dawo ba, watau ita imani da tausayi a zuciya take ba'a kan fuska ba, ɗaure fuska ba shi ke gwada rashin imanin mutum ba.
Chapter 92 · 0% Book details