← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 126 OF 227

Sashe 126

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannu Aryan ya ɗaura a kan zakin yana ɗan shafasa alamar rareashi, guru kuma ya fara shafa ƙasan wuyan zakin. Harara Lion ya dallawa zakin irin ka daɗe baka yi fushi ba, sun ɓata ne yau, ta kwaɓe masu.

Gurnani da karfi zakin ya yi irin zamu haÉ—u ne, zaka zo nemana wani lokaci. Lion bai dena hararansa ba yasa hannu zai kai mashi wata marin Aryan ya tare yana faÉ—in. "Kaga kada ka takurawa bawan ALLAH, ka ce kai haka kake wannan hali, bawan ALLAH bai maka komai ba ka nemi kuntata mashi, ka manta amanarsa aka bamu ne?".

Hararansu dikkansu Lion ya yi kafin ya matsa ya sauƙa ƙasa izuwa room na aikinsu, dan ya duba meyasa ake ta samin cases a kan cire mahaifa this year, me ake yi da su ne? And me yake jawo lalacewar mahaifar da za'a dinga cewa mata mahaifarki ya lalace sai an cire! Meyasa mace ta yi haihuwa ɗaya biyu wata ma har uku dik da kanta take haihuwa sai na kwanakin nan ne za'a dinga cewa ba zata iya haihuwa da kanta ba sai an mata aiki? Yanzu abin is getting out of sense, ya fara zama ruwan dare, ko'ina koken da jama'a suke yi kenan, so yakama IRON FIST su shiga wannan case ɗin su dakatar da koma menene ake shirin yi!.

While Aryan ya kalli guru kafin ya ce. "Murnar me kake yi?". Ƙara ɗaure fuska ya yi kafin ya amsa da. "Wasu banks na ƴan damfara ne suka kwashe kuɗin mutane zasu gudu, ina hawa media yanzu naga batun, al'umma sai kuka suke yi, shi ne na datsi tsaron banking, na fasa security ɗinsu, na sakewa al'umma kuɗinsu har ma da ƙari da na kwaso daga account na CEO na banking, na zubawa kowa ƙari ya fantama, yanzu koya banking zasu yi dan su dakatar da kuɗin al'ummar dake wannan banking ba zai yiwu ba, dan na sanyawa bakin tsaro nawa na kaina".

Aryan ya tari numfashinsa da cewa. "Ka ce kawai ka kwace banking, to ALLAH yai maka albarka, ai naga kwana biyun nan suna tinanin IRON FIST ta yi sanyi shi ne suka fara dawo da damfara da cutar mutane, dole mu koma bakin aiki dan kakkaɓe gurɓatattu, ni yanzu ma akwai in da zan je, sai 3 na dare zan dawo". ......... Guru da yasan hali sai ya ce. "Kada ka masu kisan sauki, ka gana masu azaba kafin kashesu".

Kashe mashi ido É—aya Aryan ya yi alamar ya gano komai, sannan ya wuce ya bi bayan Lion. Bayansa guru ya bi kafin zakinsu ya rufa masu baya da gudu. A É—akin aikinsu suka isko Lion yana bincike, a kusa da shi Aryan ya tsaya, sai da ya manna mashi sumbata a cheek kafin ya sanar da shi zai fita sai karfe 3 na dare zai dawo. Kai kawai Lion ya jinjina ba tare da ya yi magana ba. Wucewa ya yi izuwa room É—insu dan ya shirya. While shi ma guru ya bi bayan Aryan dan ya tayasa shiryawa, Lion kuma ya cigaba da aikinsa cikin kwanciyar hankali da natsuwa.

-------------------------------🔥

AZURE.🔥

A maimakon ta fara bashi labari sai ta shige jikinsa, ta lafe tana zuba mashi shagwaɓa. Hannu ya tura cikin gashin kanta, ya warware kullin da tai wa gashin, ya watsa har saman bayanta zuwa mazaunanta, bayanta ya cigaba da shafawa yana biyewa shirirtarta.

Hannu ta tura ta baya ta rungumesa sosai, cikin shagwaɓa ta ce. "My Romeo yaushe zamu yi first night ɗinmu"........ Idanunsa ya ɗan ɗaga sama, sai kuma ya ce. "Ba'a gidan nan ba, a gidanmu ko a wajen Mission".

"Why not a gidan nan?". Ta tambaya tana ɗago kai, kunsan Angelina ta ɓata ta da kalle kallen banza, sannan yanzu ta gama kallon video ɗin in baku manta ba, gabaɗaya cike take da feeling shiyasa take mashi waɗan nan surutan da bata san tana yi ba.

Matso da face ɗinsa dab ita ya yi, tamkar zai haɗe bakinsu sai kuma ya dakata game da cewa. "Kina buƙatata ne? Kina buƙatar mijinki?". A shagwaɓe sosai ya yi magana....... Ɗan lumshe idanu ta yi tare da sake warosu a kansa. Slowly ta gyaɗa mashi kai alamar e tana buƙata. Tongue ɗinsa ya fitar ya ɗan lashi lips ɗinta da suka ciza kala saboda yanayin da take ciki.

"Na fiki buƙata, amma ba'a gidan nan ba"..... Cikin wani irin murya tamkar ƴar maye ta ce. "Kana tsoron daddy ne?"........ Kai ya girgiza mata alamar a'a kafin ya ce. "Bana son yin dis virgin ɗinki a gidanku ne kawai, na fi son a gidanmu ko a wani waje". ...... "Why?". Ta faɗa tana saƙalo wuyansa ta ƙara shigewa jininsa sosai.

Yana É—an lumshe idanunsa da suka yi jajir da su ya amsa da. "Haka kawai, zan fi jin daÉ—i da samun peace of mind"........ Nisawa ta yi kafin ta matsa ta haÉ—e bakinsu. Kissing É—insa ta fara yi in a romantic way. Moving hannunsa ya yi from her waist to her back. ÆŠan tallabota ya yi tare da juyawa, ya kwantar da ita a saman sofar kafin yai mata runfa da buÉ—aÉ—É—iyar kirjinsa.

Wani irin hot kiss ya shiga bata, cikin dabara ya sake moving hands ɗinsa izuwa saman botiran sleeping dress ɗinta. Ɓallesu yai ya cire, sai ya ɗan raba jikinsu tare da zame ɗan bakinsa daga nata. Ɗan lumshe idanu yai tare da sake warosu a kan tula-tulanta dake tamkar an bura balo-balo.

Da kyar ya iya ce mata. "Where's your bra?"... Kashe mashi ido ɗaya ta yi before ta amsa da. "Bana sanyawa da daddare"....... Hannu ɗaya ya kai ya shafi tula-tulan nata, cikin tsananin shgawaɓa in a romantic mood and voice ya ce. "Ohhhhh sh**** my Juliet, now all this is mine?". Yana wani lumshe idanu ya faɗa.

Ɗan turo mashi baki ta yi kafin ta amsa da. "Yeah is yours"........ Kwantowa kanta kaɗan ya yi, baya son taɓata sosai saboda baya son yi mata komai a gidansu, shi ganinta kawai ya zo yi ya koma cikin barrack. A gefen wuyarta ya kwantar da kansa, yana shaƙar kamahin shampoo ɗinta na kamfaninsu mai kwantar da hankali, ya ɗaura hannunsa ɗaya a kan tula-tulan nata, yana shafawa a hankali yana ɗan lasan wuyanta.

Gabaɗaya ya kara kiɗimata ga shi babu alamar zai yi abin da take so, juyawa ta yi ta kara shiga jikinsa sosai. Da ɗan karfi ya furta wash saboda yadda ya ji kirjinsa a jikinsa, ya ALLAH. Daurewa ya yi, ya rungumeta ba tare da ya sake taɓa wani abin daga jikinta ba, a hankali ya dinga shafa bayanta zuwa mazaunanta har barci ɓarawo ya saceta.

Ajiyar zuciya ya sauke tare da gyara mata kwanciya, ya zareta daga jikinsa kafin ya miƙe, ya sauƙo ƙasa, a gaban sofar ya tsuguna game da sanya hannu ya rufe mata botiran da ya buɗe, sumbatar ɗan bakinta ya yi kafin ya miƙe, cak ya ɗauketa sai saman shoulder ɗinsa.

Waje ya fito da ita, dik sojojin dake gidan basu lura da shi ba, da yake bq yana ta baya ne, so ta kofar kitchen da ya huda ta bayan ya bi izuwa cikin parlo. Nan ya isko Aunty Lisa tsaye shiru tamkar mai tinanin wani abin, ga alamar damuwa a kan face É—inta.

A saman sofa ya shinfiÉ—e V kafin ya dawo kusa da Aunty ya tsaya, sai da ya ja dogon hancinta, yana wani lumshe idanu saboda bai wastsake ba ya ce. "Lafiya kike tsaye a nan haka?".

Ɗago da eyes ɗinta irin nasa ta yi, kallo ɗaya tai mashi ta ɗauke kai tare da cewa. "Ango har an gama cin amarcin ne?". ....... Ɗan shagwaɓe fuska ya yi. "Kai Aunty ki bari, my Juliet special ce, a special time and place zan yi abin da ya dace, yanzu dai faɗa mun menene yake damunki?".

Tamkar zata yi kuka ta ce. "Our pleasure ina cikin damuwa"..... ÆŠan zazzare eyes É—insa a kanta ya yi kafin ya ce. "Wani irin damuwa kuma?"....... Hannunsa ta ja suka fito parlo ta kofar baya wajen kitchen, suka tsaya ta wajen tank na ruwan gidan, cikin sanyin murya ta ce. "Damuwata guda biyu ne"....... "Okey I'm listening".

"Na farko ina fargaban yaran honey ba zaku karɓeni a matsayin uwa ba, musamman Arya, dan ya faɗa mun sau da dama yana yunkurin yin aure su Arya suna hanawa, baya son ɓacin ransu saboda maraicinsu, shiyasa ya ce kada in faɗa masu cewa ni matarsa ce, yanzu dai ƴar ɓuya muke yi da su, ko ɗakinsa bana zuwa sai sun yi barci, hakan yana damuna".

Zuba mata idanu kawai ya yi yana mamakinta ita ɗinma tukunan......... "Damuwata ta biyu shi ne, a fannin aikina na gano wani waje da ake safaran yara mata ƙanana ana kaisu ana ɓuyewa, sai a dinga kaiwa manyan shuwagabanninsu suna lalata da su a gidajen shaƙatawarsu da manyan hotels a nan AVARIS, wannan abu ya yi matuƙar ɗaga mun hankali, amma na rasa yadda zan fito da maganar, dan manya daga cikin ƙasar nan ta AVARIS suna da sa hannu a wannan al'amarin, na ji ina tsoron yin magana".

Tin da ta fara wannan magana jikinsa ya fara tsuma, É—an rintse idanunsa ya yi, ya sake warosu a kanta, ai take ya wastsake daga mayen da V ta sanya shi, a dake ya ce. "Wani irin lalata ne wannan? Ai wannan ba abin ayi shiru bane, ba kina da evidance ba?"....... Kai ta gyaÉ—a mashi da sauri alamar e.

Hannu ya miƙa ya riko shoulders ɗinta, cike da jarumta ya ce. "Rayuwar yaran da basu ji ba basu gani, yaran da basu san komai ba, rayuwarsu zaki taimaka, buɗe wannan sirri wa duniya tamkar taimakon al'umma ne, please aunty kada ki ji tsoron kowa, ki fitar da sirrin kuma ki takurawa GAT da ya bawa sojojinmu umarni su tarwatsa wannan waje su ceto yaran nan da ake kawalcinsu zuwa manyan hotels da manyan wajen shaƙatawa, mu muna gab da tafiya MISSION, ba lallai su yarda su turamu wajen ba, amma naso ace mu aka tura".
Chapter 126 · 0% Book details