← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 131 OF 227

Sashe 131

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tin ɗazun ƙoƙarin karyata kansa Aryan yake yi, yana ƙoƙarin tursasawa zuciyarsa ta yarda kamanni ne kawai ba wai murya bane iri guda, amma abinku da shaiɗan, ya hana mashi yarda da hakan, ya hana zuciyansa sukuni.............. Rage tsawonsa Lion ya yi, ya ɗauki Aryan cak ya saɓa a saman shoulder ɗinsa, kai tsaye room ɗinsu ya kaisa, a saman gado ya kwantar da shi, ya dawo parlo ya ɗauki laptop ɗinsa da waya.

A tsakiyar É—akin ya tsaya tare da cewa. "Vir goodnight, my heartbeat is not feeling well"........ Ai Aryan ya wuce bugawar zuciyar Lion, dan wani irin son da yake mashi baki ba zata iya faÉ—a ba, shiyasa wani lokaci yake ce mashi shi ne bugawan zuciyansa, idan babu shi zuciyansa ba zata buga ba!.

Vir dake zaune saman bed ne ya amsa da. "I want to see him". A sanyayye yake magana, wani haɗaɗɗen korean guy ne, fari kal tamkar madara, kuna ganinsa ba tambaya kun san korean ne, kyakkyawan gaske ne, lips ɗinsa purple color, while gashin gerarsa tamkar zasu haɗe gasu bakinkirin yana wani sheki, kashin kansa tamkar wanda aka kifawa huka, amma ya bayan wuya yana yana da ɗan tsawo har ƙasan wuyansa, ta gaban goshi kuma a daidai saitin gerarsa gashin ya tsaya, nasa ɓangaren shi ma ya haɗu.

Babban aminin su Leo ne tin na yarinta, yanzu haka wani Mission suke yi yasa yake ƙasan Russia baya tare da su, tsawon shekaru uku aikin zai ɗaukesa, yanzu saura mashi watanni biyu kawai ya dawo, a tare suke aiki, amma wannan aiki da ya tafi Lion ne ya tura shi, kuma aikin sirri ne, a gaba zaku san wani irin aiki ne, muje dai zuwa.

"No goodnight". Lion ya faÉ—a. Ba tare da ya jira amsar Vir ba ya katse video call É—in, ya kashe laptop É—in tare da É—aurawa a saman laptop table dake gefen bed É—insu. Saman bed É—in ya hau, ya riko hannun Aryan yana kallon kyakkyawan fuskansa da take cike taf da damuwa, kura mashi idanu Lion ya yi na Æ´an tsakanni kafin ya ce. "To much of pressure, all for what?". Ya faÉ—a yana É—aura É—ayan hannunsa a saman gashin kan Aryan.

Nisawa Aryan ya yi tare da riko hannun Lion sosai. "Bro give me sleeping pills or injection now". Ya faÉ—a a lokacin da ya ji kansa na barazanar tarwatsewa.

Sauƙa ƙasan bed ɗin Lion ya yi. Waje ya fita, jim kaɗan ya dawo hannunsa rike da sirinjin allura. Zuwa ya yi yai mashi, sannan ya fita zuwa mayar da alluran, kafin ya dawo Aryan ya yi barci. A maimakon ya kwanta yai barcin shi ma, sai ya zauna ya tofa wa guru da Aryan ɗin addu'ar barci, sannan ya sauƙo ƙasa.

Waje ya fito ya koma É—akin aikinsu dan ya binciki Aryan sosai, meyake damunsa? Meyasa ya gagara yin magana? Ya gagara yin barci sai da allura? Bugawar zuciyarta ta canza, meyafake faruwa?. Gara ya bincika da kansa ya gani.

After some times.

Aryan ne tsaye a parlon gidansu Seraphina, hannunsa rike da waya, yau ya yi balain kyau cikin hoodie farare tas, ya sanya hular kayan a kansa, daga ta ciki kuma ya sanya p-cap, ya zura hannu É—aya a cikin aljihu, É—ayan hannun yana pressing phone, sai tashi daddaÉ—ar kamshi yake yi.

Madan ce ta fito, a mutunce suka gaisa kafin ta wuce cikin kitchen. Yana tsaye a wajen Aunty Safiyya ma ta fito, gaisuwa ita ma ta É—aga mashi, dikkansu ba tare da ya É—ago ya kallesu ba ya amsa, amma all they're movement yana sane da shi, kallonsu ne kawai bayayi.

Wucewa ta yi ta bi bayan Madam ita ma, still yana tsaye Aisha ta fito sanye da uniform, sket baki zuwa gwiwa, da riga fari mai dogon hannu, sai socks farare kal-kal, gashin kanta a É—aure gida biyu, ta sanya mashi ribon, tana rike da school back É—inta.

Har ƙasa ta durkusa ta gaida shi, ita ma ba tare da ya ga in da take ba ya amsa, miƙewa ta yi ta koma saman sofa ta zauna, a daidai wannan lokaci sai da Suhana ta fito, sanye take da kayan barcin da suka fitar da surar jikinta, ta ji mugun daɗin ganin Aryan a tsaye, a tinaninta zata ja ra'ayinsa da surar jikinta ne, dan ALLAH yai mata halitta mai kyau ba karya, ta yi zubin shahararrun karuwai masu yin surgery su cike nan da can ɗin nan, sai dai ita bana surgery ɗin bane, kyauta ce daga ALLAH, goodbye and welcome dik a cike masha ALLAH.

Sai dai bata san IRON FIST jikin mace ba shi ne a gabansu ba, idan sun yi ra'ayi matan da suka ninkata a komai zasu samu, kai in suna so kowacce dare da irin matan da zasu kwana, amma wannan ba ita bace É—abiarsu ba, su da maza da mata dik kallon abu guda suke masu, dik kyan mace da wani surarta wlh basu kallonta kamar mace, tamkar namiji suke kallonta saboda tin ainahi basu sanya abin a ransu ba, sun cirewa kansu feeling da sauransu.

Ko Seraphina da Aryan yake kauna soyayyar tsakani da ALLAH yake yi mata ba dan surarta ba, saboda ya fara son Seraphina ne tin babu komai a kirjinta, tin tana JSS1, kawai jinin É—an uwansa ne yasa yake sonta a farko, daga nan ta rikiÉ—a izuwa soyayya, amma bayan haka wlh dik kyan surarki tamkar bango haka suke ganinki.

A gabansa ta tsaya, tana wani yauki da yanga ta É—aga mashi gaisuwa. Shiru babu alamar ya ga wata halitta wai Suhana a wajen. A daidai wannan lokaci Seraphina ta fito sanye da uniform irin na jikin Aisha, da alama makaranta guda ya sanyasu.

Matsawa Suhana ta yi tana ƙoƙarin ɗaura hannunta a saman nasa tana faɗin. "Meyasa baka son amsani ne? Ko kana tsoron faɗawa so......". Bata iya karisarwa ba ta ɗauke wuta ɗiff saboda wani marin da ya ɗauke fuskanta da shi!.

Take ya sulale ta baje a ƙasa bata numfashi, yarinya ta sha marin IRON FIST, ALLAH yasa idan kika farfaɗo kada ki rasa kunnuwanki ki daina ji gabaɗaya, dan ba karya kin sha irin marin wanda IRON FIST suke yi wa maza! Kin maru ba karya.

Sosai Seraphina ta razana, da gudu ta juya ta koma cikin É—aki jikinta na kerma, dan ita ta san dukan Aryan, abin ba'a cewa komai. Bayanta ya bi cikin zafin nama, dama lokaci na kurewa ita kaÉ—ai suke jira. 7:20 ta yi.

Zaune ya iskota a gefen gado tana hawaye without any reason. Cike da mamaki ya ce. "Are you okay?". Zabura tai ta miƙe tsaye, jikinta na kerma ta ce. "Daddy please don't slap me, i promise you that ba zan sake yin laifi ba, for give me". A ruɗe take maganar, ga hawaye tamkar an buɗe tap.

Ƙarisowa in da take ya yi, ya ciro hankey daga aljihunsa, hawayen ya goge mata tare da damƙa mata hankey ɗin a hannu, sannan ya riko hannunta suka fito parlo ba tare da ya yi magana ba. Duƙawa ya yi ya ɗauki bag ɗinta da ta jefar a ƙasa ta gudu, ya nufi waje da ita.

Da sauri Aisha ta taso ta rufa mashi baya suka bar Suhana a baje a sume. Ganin ba dukanta zai yi bane yasa ta saki jiki, ta ƙanƙame hannunsa tana sauke ajiyar zuciya. Bai ce mata ko ƙala ba har suka shiga cikin mota, haka bai ce mata ko kala ba har suka nufi haɗaɗɗen school na cikin CRYSTAL PALACE ɗin.

A parking lot na wajen ya tsayar da motar, da sauri Aisha ta fita ta basu waje, É—an É—aure fuska ya yi, on a serious note ya kara ja mata kunne a kan karatu, ba ruwanta da kowa, banda abubuwan da ya hanata, daga karshe ya ce mata. "Kinga yanzu ni mijinki ne, idan kika kuskura kika yi shirmen da kika yi a junior set É—in nan zaki shiga wuta ne, kuma dakuwa zaki yi ne a hannuna, dan yanzu ni kaÉ—ai nike da mallaki kuma da iko dake!".

"Daddy dama yanzu ka zama mijina?". Tana murmushi ta faÉ—a. Hararar kauna ya É—an wurga mata kafin ya ce. "Bar shiririta, ki yi karatu sosai, ni mijinki ne mana yanzu, kinga yau ce first day É—inki a school É—in nan, dan haka ki yi karatu sosai"....... Wani irin daÉ—in da ta ji ne yasa ta faÉ—o jikinsa. ÆŠan É—aure fuska yai tare da cewa. "Tashi mun a jiki bari in ta fi"......... "Kai daddy kai fa ka ce sai ka zama miji zan dinga kwanciya a jikinka, to yanzu ba ka zama ba?".

Nisawa ya ɗan yi. "Haka ne, to yanzu dai tashi ki wuce kada lokaci ya kure".... Wai shi ya faɗa mata shi mijinta ne dan kada ta yi shirmen da ta yi a baya, kun ji kuma ta yadda ta fassara shi yansu kuma, kai shi dai yana cikin alkhairi dumu-dumu, Seraphina sai shirin ALLAH, rashin uwa babban musifa ce, ga rashin karatun addini, ai fin haka ma zata aikata, jama'a uwa rahama ce, rahamar da babu biyunta, a kullum ina ƙara faɗa maku, uwa number one ce!! Idan babu ita a rayuwar bawa hakika sai kunga banbancin rayuwarsa da waɗan da suke da uwar.

Tana murmushi ta ɗago kai. Sumbata ya mannawa cheeks ɗinta tare da cewa. "Ki yi karatu sosai"....... Da okey ta amsa, miƙewa daga jikinsa ta yi, sumbatar ita ma ta manna mashi kafin ta buɗe kofa ta fito. Tana fita ta rufe kofar kenan sai ga motar Faryan ya kawo Rimsha.

Ai cikin zafin nama Aryan ya tada motarsa ya bar wajen da gudu, dan ALLAH yasa motarsa na gidan Abba daban, motarsa na IRON FIST daban, so ba zasu ganesa ba. Ita kuwa Seraphina zata wuce Rimsha ya sauke glass ta kwala mata kira tin basu gama parking ba. Ai tana juyowa taga Rimsha bata san lokacin da ta dawo wajen motar da gudu ba.

Faryan tin bai yi parking ba idanunsa a kanta, yana kashe motar ya riga Rimsha fitowa. Cikin sanyin murya da salon soyayyarta ya fara yaba kyan da uniform É—in yai mata. Sosai ta dinga murmushi tana faÉ—in uncle Faryan na gode.
Chapter 131 · 0% Book details