← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 168 OF 227

Sashe 168

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannu Noor ya miƙa ya taɓo Vash yana faɗin. "Vash lafiya?"...... A ɗan firgice ya ɗago, nisawa ya ɗan yi tare da cewa. "Akwai matsala bro"...... Dikkansu dawo da hankalinsu a kansa suka yi, cikin sanyin murya Noor ya ce. "Matsalar me?"......... Wayansa Vash ya miƙo mashi kan ya duba ya ga matsalar.

Karɓa ya yi, suna cigaba da tafiya farinwata tankar ta fito sosai yanzu, hakan yasa ta ƙara haskaka masu hanya sosai. Fara bin chat ɗin Noor ya yi, wani waje ya yi murmushi, wani waje ya haɗe rai, har dai ya iso kan in da take cewa daren yau zata kashe Manassa, ya duba reply da Vash yai mata, na zunzurutun magiya da ban hakuri, ya damu sosai.

Hakan ne ya ɓatawa Noor rai, sai ya ce gaskiya ba zai iya barin Vash a cikin damuwa ba, dan haka zai faɗa mashi gaskiya, miƙa mashi wayan ya yi yana faɗin. "Aljanar zata kashe kanta kenan?".

Cike da mamaki Vash ya ce. "Me kake nufi?"....... "Manassa da ita kake wannan chat É—in ai, tin ranar na san da haka, na É—auka zata cigaba da zolayarka irin na masoya ne kawai shiyasa na rufa mata asiri, ban zaci zata jefaka a damuwa ba, tin da haka ne bari in faÉ—a maka ita ce".

Ina Vash bai yarda ba, sai ya fara girgiza kai alamar kai ba ita bace, a dake Noor ya ce bari in tabbatar maka. Wayansa ya fitar, ya kira number V, bugu ɗaya ta ɗauka, dama ta koma ɗakinsu ta ɗauki wayar. Tana ɗauka ta shagwaɓe murya da cewa. "My Romeo, har yanzu baka dawo ba".

Ai wani sabon feeling ɗinta ya ji, a sanyaya ya ce. "Ina dawowa yanzu, ina son ki mun wani abin ne yanzu"..... Ƙara shagwaɓe murya ta yi wajen cewa. "Me kenan?"......... "Jeki ari wayar Manassa yanzu, kada ki faɗa mata me zaki yi da ita, ki karɓo ki zo cikin tantina ke kaɗai akwai abin da zaki mun da shi"..

Da okey ta amsa tare da miƙewa ta fita, jim kaɗan ta dawo game da cewa. "Ga wayar a hannuna"....... Hannu ya miƙa ya karɓi wayar Vash kafin ya sanya wayansa a H-free ta yadda Vash zai ji komai kafin ya kaluɓo number Vash ɗin. "Shi ga contact ki saka wannan number da zan kira maki yanzu". Da okey ta amsa. A natse ta shiga.

Number Vash ya fara kira mata ta fara shigarwa kenan sai ta ce. "Akwai number a wayar, gata ta fito da saving my flower"....... ÆŠago idanu ya yi ya kalli Vash kafin ya ce. "Shiga Whatsapp É—inta ki nemo mun member". ....... Da sauri ta shiga, sai ta ce. "Number ce a sama, da ita take chat yanzu".

"Okey to shiga kan number ki yi clicking voice, a cikin voice É—in ki ce I am mrs Noor ya wadatar"....... A natse ta aiwatar da abin da ya ce, bata tambayesa me dalili ba, saboda tasan haka kawai ba zai tsaya wannan dogon magana ba.

"Na yi na tura". Ta faɗa.….... "Okey to goge voice ɗin yazama tamkar ma baki shiga kan chat ɗin ba". Da okey ta amsa kafin ya aiwatar da abin da ya ce, daga nan ya ce mata. "Je ki mayar mata da wayar, yanzu zan dawo ba jimawa, wait for me don't sleep"........ "Okey my Romeo, love you more"...... "Love you too". Kit ya kashe kiran tare da miƙawa Vash wayansa dan ya duba voice ɗin.

A hanzarce ya karɓa, aikuwa yana dubawa ita ce, tabbas ba aljana bace Manassa ce, aikuwa ya ce zai yi mata tsiya shi ma, ba zai bari ta gane ya gane ita ba aljana ba ce, su cigaba da tafiya haka, ranar da zai damketa yana nan zuwa, zata san ta taɓo jinin Champion na IRON FIST, yadda ta dinga bashi wahala yana magiya ba zai kyaleta haka ba.

Daidai lokacin suka isa bakin tekun nan amma ta can nesa da tantinsu, wani ɓangare ne da ake sauƙe ƙaya, amma ba ainahin in da ake sauƙe kayan bane, nan wani gefe ne kamar na sirri wanda ba kowa yasan ana sauƙe kaya a wajen ba, watau idan jiragen ruwan suka kusa isowa madakata in da ake sauƙe ƙaya, sai su ratse hanya, su ratso gefe can nesa daga in da ake sauƙe ƙaya, sai su dakata a wannan waje, kuma jiragen ruwa basa wannan ratsen sai tsakar dare, suna tsara tafiyarsu yadda sai dare zasu kusa isa madaka in da ake sauƙe ƙaya.

Tin da suka doso wajen wasu mahaukatan karnika suka fara haushi da karfi-karfi, alamar securitys dogs ne, waɗan da aka horar da su dan gadi, kun san su dik yadda suka ji motsi sai sun yi haushi. Aikuwa suna wannan haushin wasu kartin maza suka fara firfitowa daga cikin jiragen ruwan dake faffake a bakin ruwa, wasu ma ba'a sauƙe lodin kayan dake kansu ba.

Maza ne mada karti da a ƙallah zasu kai 30, dikkansu yawancinsu babu riga a cikinsu, suna murɗe sosai, dama kun san tsaron irin wannan waje sai masu rai da lafiya game da jini a jiki ake baiwa, dan kome zai zo su iya tarewa.

Hannayensu rike da gabza-gabzan torchlight masu masifar haske, suna wani bubbuɗewa suka fito da nufin su ga su wanene?......... Ganin haka yasa Leo ya ce. "Is time for game"...... Yana faɗar haka tin bai rufe baki ba Noor ya diro ƙasa daga bayan nasa. Da gudun gaske suka dare suka rabu.

Dik suka kama wajen ɓuya, wasu suka ɓuya bayan kwantainars, wasu kuma bayan jiragen ruwa. Haske ko'ina waɗan nan karti suka fara yi suna wani irin numfashi irin na gardawa. Kewaye lungu da saƙo suka fara yi da haske, while dik in da suka yo sai sojojin AZURE sun kauce sun ƙara ɓuya.

Wani shirgegen ƙato ne ya zo ya wuce saitin in da Noor ya laɓe, ya wuce gaba yana haske-haskensa. Ai yana wucewa Noor ya fito, dik da baya jin kuzari a jikinsa, haka ya bi bayan mutumin, yana zuwa ya sanya hannunsa ya shaƙo wuyan mutumin ta baya, ya matse da hannu ɗaya tare da sanya ɗayan hannun ya toshe mashi baki.

Fafutuka ya fara yi yana neman yadda zai kwaci kansa, sa dai ina, renon AZURE ba wasa ba, sai da Noor ya kaisa ƙasa, sai da Noor ɗin ya tabbatar baya numfashi, sannan ya sakesa tare da karɓar light ɗin hannunsa, ya kasheta game da turata cikin aljihu kafin ya damƙi ƙafar mutumin, ya ja shi a ƙasa tamkar kayan wanki, bakin ruwa ya kaisa ya jefar sannan ya dawo ya laɓe.

A daidai lokacin shi ma Zaynish ya muɗe wuyan wani da ya zo ta kusa da shi, aikuwa yana dab zai haskasa Zaysh ya yi kukan kura ya danke wuyansa, ya murɗe ya karyeta. Yana karyewa Noor ya sake damke wani, shi ma murɗe mashi wuya ya yi ya karya. A tare Leo da Zaynish suka damki wasu biyun, dikkansu murɗe masu wuya suka yi suka karya. Daidai lokacin shi ma Vash ya damƙi wani shirgegen ƙato, ya murɗe mashi wuya.

Faɗar ta koma yaƙin sunkuru, suka dinga yi masu ɗauki ɗaiɗai har sai da suka kashesu tas, sannan suka kutsa cikin kwantainars ɗin. Har lokacin karnukan suna haushi, sun bi dik wanda suka kashe sun ɗauke torchlight ɗinsa sun kashe. Nufar in da suka ɗaure karnukan a jikin wata bishiya Leo ya yi, ya je da nufin ya kashe karnukan, amma sai ya ga suna da mugun kyau sosai, irin manya-manyan karnukan nan ne masu tulin gashi a jiki, ga su farare tas, hakan yasa suka burgesa, su biyu ne, ɗaya gashin jikinsa har yana jan ƙasa, ɗaya kuma bai ƙarisa kai na wancan ba, bujumaye da su tamkar zakuna.

Shafa kawunansu ya yi, hakan yasa suka yi shiru, sai ya wuce ya kyalesu da nufin idan sun gama abin da ya kawosu zai kwance karnukan su wuce da su.

Gaban wani ƙaton kwantaina suka tsaya, hannu Leo ya sanya wajen jikin container, sai ya ga alamar gari-gari. Tsanin dake jikin container ya kama ya hau, Noor na rike da light yana haska mashi, ya haye zuwa wajen da aka sanya sarƙa aka ɗaure container sosai. Ƙasa ya sauƙo, suka shiga cikin wata jirgin ruwa, a nan ya samu almakashin tsinka sarƙa.

Dawowa ya yi, Noor na haska mashi haske ya sake hayewa sama, karfi yasa ya datse sarkar, sannan ya sauƙo, Zaynish da Noor suka haɗu suka buɗe marfin container. Dallah light a ciki suka yi. Kaya ne shirye a cikin kwalaye, an shiryasu datsan-datsan. Leo ya ce Zaynish ya sauƙo da kwali ɗaya su gani.

Ba musu ya sauƙo da shi, suka farka bakin suka buɗe. A tare suka ɗago suka kalli juna, wasu irin sinadarai ne na haɗa ƙananan boma-bomai, shegen tsada ne da waɗan nan sinadaran. Kai kawai Leo ya jinjina, bai yi magana ba, ya ɗauki almakashin ya matsa zuwa container na gaba, ya datse sarkar da aka rufeta. Zaynish da Vash suka buɗe marfin, while Noor yana ƙoƙarin rufe kwalin sinadarin boma-boman nan, a matsayinsu na sojoji dik wannan karatu sun san shi, hmmmmm su suka san me aka shirya a wajen, shiyasa kuka ga Leo ya girgiza kai kawai.

Suna buɗe container na biyun kuwa kwalayen drugs ne a cike a ciki. Leo ya ce Vash ya sauƙo da kwali ɗaya. Da sauri ya sauƙo da shi. Buɗe kwalin suka yi, wasu irin magunguna ne wanda aka ɓuye ainahin manufar drugs ɗin, aka ɓuye ainahin daga ina suke, a jikin kwalin maganin an rubuta made in Avaris, amma sai ga shi sun kama maganin a bakin tekun shigo da shi ƙasar, kunga kenan dama daga waje ake shigo da su aka ɓoyewa ƴan Avaris gaskiya, aka ce a ƙasar ake haɗa masu.
Chapter 168 · 0% Book details