← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 218 OF 227

Sashe 218

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Turo baki ta yi. "Saboda daga bakinka ya fito yasa na sha, ba dan haka ba bana so, test na bakinka ya kara mashi daÉ—i da armashi shiyasa, amma ni nasan strawberry bashi da wani daÉ—i"..... Ai gabaÉ—aya sawa ta yi ya ji shi a wani yanayi, wai dan daga bakinsa ya fito, kai wannan yarinya sai shiru.

Miƙa mata ragowar ya yi yana faɗin. "Na hanaki shan milk baki ji ko?"...... "Kai daddy kai daddy, to ai wannan bashi da yawa, and ni ka faɗa mun meyasa ka ce in daina shan milk kaki". Ta faɗa tana miƙewa zaune. Kama hannunta ya yi ya damka mata ice cream ɗin kafin ya ce. "Gaba zaki san dalilin hanaki sha milk, yansu dai karɓi ice cream ɗinki ki shanye".

Make mashi kafaɗa ta yi. "A'a daddy, ni in dai ba na bakinka ba to ban so"..... Wani irin hararar kauna ya wurga mata kafin ya ce. "Wannan already ya taɓa bakin nawa, please my cherry ni bana shan zaƙi, karɓa ki sha kayanki"...... Har lokacin bata kula da rose dake gefensa ba, ta sake make mashi kafaɗa kan ba zata karɓa ba.

"Karɓa in baki wani gift". In a low way ya faɗa...... Tana turo baki ta karɓa tana kallonsa. "Close your eyes". Ya faɗa ta hanyar motsa laɓɓa kawai ba tare da fitar wani sauti ba. Da sauri ta datse violet eyes ɗinta. Rose ɗin ya fito da shi kafin ya ce. "Open your eyes".

Ai tana sauke kallonta a kan rose ɗin nan bata san lokacin da ta kai hannu ta karɓa ba, da sauri ta ɗan rungumesa tana murmushi. Raba jikinsu ya yi kafin ya ce. "Sha ice cream ɗinki bari mu je wajajen yawo sosai". Ya faɗa yaka ƙoƙarin tada motar.

A shagwaɓe ta ce. "Daddy ni kam ka bar kaini ko'ina mu je mu hau fly board please"........ Ɗan zaro mata idanu ya yi, sai kuma ya ce. "Fly board a daren nan? Baki tsoron ruwa ko?"........ Kai ta gyaɗa. "Yes daddy, ruwa is the most favorite thing da nafi so, please mana my gentle chaos". Ta marairace fuska tamkar zata sa mashi kuka. Zai yi magana ta rigasa, ta dinga mashi magiya har sai da ya aminta, haka ya juya kan motar suka koma beach na cikin CRYSTAL PALACE.

A in da ya faka motarsa É—azu yanzu ma ya faka, ya fito ita ma ta fito, yarinyar nan sanyi tamkar zai busar da ita amma take kiran su hau fly board. A bakin ruwan ya tsaya tare da kira guard dake tsaron wajen, ya ce su haÉ—a mashi flye board bari ya hau da matarsa.

Sun yi mamakin ganin da daren nan zasu hau, around 1:30 yanzu, amma basu da zaɓi ya wuci bin umarni, haka suka shirya mashi. Hannu yasa ya ɓalle botirin after dress na jikinta, ya zare rigar gabaɗaya, ya ce ta ɗaure gashin kanta da veil na rigar. Ba musu ta yi a hanzarce.

Hawa kan fly board ɗin ya yi, ya ɗaure kafarsa da kyau kafin ya miƙo mata hannu, kama hannunsa ta yi, ta hau ita ma ta gabansa, sai ta juya ta ƙanƙame shi ta baya, shi kuma ya riko waist ɗinta ta saman mazaunanta da kyau, ta ɗan ɗaga hannunta ɗaya sama tana murnushi, daɗi kamar ya kasheta.

Ni ban ma san ya zan kwatanta maku fly board ɗin nan da hausa ba, matsalata ban iya kwatance bane. Bari dai in gani ko zan iya, kada ku mun dariya. Yauwa fly board zaku gansa a cikin teku, masoya suna hawa su ta yawo a saman ruwa, kai wannan kwatance na rasa ta ya zan yi fa......... 💔😭😂

Haba juyi ya fara yi da ita a cikin ruwan, tin suna baki-bakin gadar beach ɗin har suka fara natsawa can tsakiyar ruwan, daɗi kamar ya kasheta, sai ma sun tashi sama sosai, sai ta ɗaga hannu tana ƴar ƙara, fatanta ta ganta a tsakiyar teku zata je garin da rana yake fitowa, ya ALLAH, a wannan rana ta san ko rintsawa ba zata yi ba.

Kara ƙanƙame shi da hannu ɗaya ta yi, tana cigaba da ɗaga ɗayan hannunta tana murmushi, shi kam kallo fine face ɗinta kawai yake yi, yana jin tamkar ya haɗe bakinsu, yadda suke a tsakiyar ruwan nan gasu a saman iska, iska mai daɗi sai kaɗa su yake yi, gabaɗaya ya canza mashi yanayin mood ɗinsa, ya shiga romantic way, yana ɗan lumshe ido.

Suna saman iska ta ce. "Daddy barci kake ji ne?". Da yake hasken dake baki-bakin gadan na haskasu sosai. Kai kwai ya iya girgiza mata alamar a'a, gabaÉ—aya ya rasa natsuwansa, barema yadda kirjinta ke haÉ—e da nasa. Hannunta da ta É—aga sama ta sauke game da É—aurawa a kan kyakkyawan cheek É—insa kafin ta ce. "Daddy naga eyes É—insa tamkar kana jin barci".

Nisawa ya ɗan yi game da juya fly board ɗin suka nufi bakin beach ɗin, dan tana neman jefasa cikin wani al'amari, gara ma kawai su sauƙa. Kukan shagwaɓa ta saka mashi tare da cewa. "Daddy kada ka saukeni yanzu"........ Ko sannu bai iya ce mata ba, wasa ya kare, sauketa ya yi shi ma ya sauka. Ya kama hannunta sai cikin mota, sai kuka take yi yai banza da ita.

Da gudun gaske ya tada motar suka nufi benensu. Yana tsai da motar ya fita game da fito da kayan da suka yi shopping, ya kama hannunta sai cikin elevator. Suna haurawa ɗaki ya wuce da ita, bai yi mata magana ba ya ajiye mata kayanta ya nufi waje. Yana fita ya rufe kofar fita gida nasu, ba mai iya sake fita ko shiga. Daga nan ya wuce benensu yana jin cikinsa wajen mararsa na murɗa mashi sosai. Ita kuwa ta zauna a bakin gado tana cigaba da kukan shagwaɓarta har da cewa daga yau ba zata sake kula shi ba.

A hankali ta kwanta kan gadon tana ta faman kunkuni har barci ya saceta a wajen.

Shi kuwa Aryan gida ya koma, zaune ya isko Lion a tsakiyar bed yana rike da laptop yana bibiyar su guru da suka fita aiki yau, ya sanya bluetooth a kunne suna magana da juna.

Ai Aryan na shiga ya haye gado ya kwanta ba tare da ya yi wa Lion magana ba. Ya kwanta ruff da ciki yana dafe mararsa da hannu É—aya, serious ciwo marar tasa take mashi, in ta murÉ—a sai ya datse idanunsa.

Kallo ɗaya Lion yai mashi ya ɗauke kansa, ya cigaba da abin da yake yi na ƙoƙarin kwatantawa su Vir location da containers ɗin suke..... Tsabar yarda da kansu da IRON FIST suka yi babu bindiga babu wuƙa a hannunsu, daga su sai key ɗin motar da suke driving guru and Vir suka tafi. Kuma cikin daji can border da ƙasar suka kutsa.

Tin da suka sako hancin motarsu cikin wannan dajin suke sharara gudu, guru yake driving dan dik cikinsu ya fisu iya mota sosai, Vir ya kwantar da kansa a jikin kujerar mota yana danna waya, hankalinsu a kwance mutanen nan, tamkar basu san cewa waje mai haÉ—ari zasu shiga ba.

Jikin motarsu ta gaba akwai camera, ta wannan Camera Lion yake kallon kan hanyar da suke a laptop ɗin gabansa.......... Suna dab da isa wajen containers ɗin ɗaya daga cikin motocin da suka ɗauko container ɗin driver ɗin ya zare kansa daga layin da motocin suka jeru su 5 suna ƙoƙarin shigowa cikin ƙasar.

Canza hanya wannan container ta yi, kuma ba kowa bane driver ɗin wanna mota face Dr Mark, in baku manta ba ai ya fito da kwari cikin mota mai ɗaukar container. To tin shigowarsu Vir wannan dajin Camera da 3D suka sanya a kofofin shige da fice na dajin ta nuna masu cewa mota ta shigo, da Dr James ya bibiyi su Vir sai ya gane motar jami'ai ne, dan da motarsu na SSO suka fito sakamakon kada ma ƴan sanda su taresu a hanya su ɓata masu lokacin.

Ganewa da Dr James ya yi cewa jami'ai ne dik da bai san su waye ne a cikin motar ba, sai ya ce kira Dr Mark a waya, ya ce mashi ya canza hanya akwai matsala a wajen, to shi ne ya zame kansa daga cikinsu. Tsabar 3D sun shahara dik wasu dajukan da suke bi dan aikata ɓarnarsu a hanyar shige da fice sun sanya Camera dan gudun raja irin ta yau, watau ko an so kama su ba zasu kamu ba, Dr James munafuki yana tsaye gaban computer yana kallon komai yana baiwa Dr Mark information kamar dai yanzu.

Robar ruwa Vir ya ɗauko, ya fasa ya ɗaɗɗakawa cikinsa rabi sannan ya rufe sauran. A daidai lokacin suka yi kiciɓus da containers ɗin, da karfi direbobin dake jan motocin containers ɗin suka ja birki har motar karshe ta daki wacce ke kusa da ita. Horn suka fara dannawa su Vir cike da takaicin tare masu hanya da suka yi.

Kashe motar guru ya yi, suka ɗan kalli juna, Vir ya ƙara kwantar da kansa a jikin kujerar motar, basu yi alamar zasu motsa daga in da suke ba.

Ganin haka yasa driver ɗin container gaba ya buɗe ya diro ƙasa, wani shirgegen kato da shi, ga tsawo ga ƙiba, jikinsa a murɗe sosai kamar ɗan dambe, yana wani nishi tamkar wanda ya yi gudu. Cikin takun dake nuna namijin gaske ne ya nufi motar su Vir.

Sake kallon juna suka yi kafin su buÉ—e kofar motocin a tare su fito, lokacin chaskalewa ya yi. Wannan driver na zuwa ya dunkule hannu zai kaiwa guru punch a fuska, ai cikin zafa guru ya rike hannunsa. Vir ya daka tsalle ta kan motar ya kai mashi wani bahagon punch a bayan kunne, Vir bahago ne kaman Lion, sun fi amfani da hannun hagu sama da dama.
Chapter 218 · 0% Book details