← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 227

Sashe 78

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Na shirya mashi, amma kin san idan na tina karatun aji na biyun da zamu shiga aka ce ya fi kowanne wahala gabana faɗuwa yake yi? Ina jin kamar ba zan iya ba, yanzu wannan karatun ma da ya muka kare? Wahala kan wahala"....... "Zaki iya ƴar uwata". Ta faɗa cike da ƙoƙarin kwarara mata gwiwa...... "Ina sa ran na iya sosai"....... Da haka suka cigaba da hira suna shirya chemical ɗin nan har suka kammala, sannan suka fito, a lokacin yamma ta kawo kai, karfe 5 suke tashi daga aiki sai su koma wajen kwanansu na ɗalibai, za su shiga class daga 7 na safe zuwa 1 na rana, da sun fito zasu wuce wajen practical, karatunsu ba kamar na sauran likitoci bane, su special ne, suna karatu ana haɗa masu da aiki kullum dan su kware.

Kamar yadda AZURE BARRACK take yaye jami'ai gifted haka WS-HOSPITAL take yaye likitocin da babu irinsu a duniya, mayun bincike mayun aiki tamkar ba Æ´an adam ba, a yanzu ba zaku gane komai ba, sai tafiya ta yi nisa damu a cikin WS-HOSPITAL zaku fahimci karatun! Mu je zuwa ku dai.

A lokacin da suka fito wajen lap ɗin almost 5:20, a gurguje suka yi shirin tashi, suka cire lap gown na jikinsu da hand glove ɗin, sannan suna shirya tsab. Dawowa wajen sashen su Dr James suka yi, a nan Sister Zinta ta ce. "Maya mu je ki rakani waiting room na Dr James".......... "Kin san halinsa ƙawata, shi baya son ya ce abu a saɓa mashi, ke kaɗai ya kira, idan ya ganmu tare ransa zai ɓaci, kinga hakan zai sa ma ki rasa damar da yake son baki, ba zan so ki rasa wannan dama ba, ki je ke kaɗai kin ji? Zan jiraki a section B".

Ta san maganar Maya gaskiya ce, ba'a mashi abin da bai ce ba, amma tana mugun tsoron zuwa ita kaÉ—ai ne, dan shakkarsu take ji. Cigaba da kwarara mata gwiwa Maya ta yi har ta yarda zata tafi ita kaÉ—ai, tamkar wacce kwai ya fashewa a ciki haka ta nufi waiting room É—in nasa dake gefen office É—insa, kafin ka shiga office É—insa kofar room É—in yana daga gefe. Ciki ta shiga bakinta a É—auke da excuse.

Babu kowa a ciki sai wani irin ni'imantaccen kamshi dake tashi, ga sanyin Ac dake buga ko'ina, sofa set set guda É—aya ne a cikin room É—in, a tsakiyar sofas É—in akwai wani lallausan Dubai rug a wajen, sai karamar dispenser, sai kuma wata karamar freezer daga gefe dan zuba drinks su yi sanyi, ga kuma wata karamar show glass mai É—auke da glass cups masu kyau kuma very luxury. ÆŠakin dai ya haÉ—u sosai.

A saman sofa ɗaya ta zauna, tin da suke basu taɓa shigowa sashen su Dr James ba, dan su aikinsu a wajen Chemicals yake, ta wannan ɓangare suka fi kwarewa, sai sun je aji biyu zasu koma sashen dabbobi, daga sashen dabobi dama sai babban sashe watau na su Dr James. Zaman good 30 mins ta yi, sai faman tinane-tinane take yi da kalle-kalle, ta yi tinani ya fi dubu kan dalilinsa na kiranta, amma ta rasa gane dalili, sai kawai ta yi shiru.

Ta gaji da zama da zuba idon ganin shigowarsa, amma shiru, sai a lokacin da cire tsammani, ta shiga wata tinanin, ta manta da zai shigo sai ta ji an turo kofar room ɗin. Tin daga ƙasa ta fara kallonsa, yana sanye da sportswear ba kayan aiki ba, da alama ya ɗan jima da tashi aiki, still fuskansa da nose mask, and ya ɗaura jacket a kan kayan saboda wani irin fitinannen sanyin da ake zubawa, kafarsa sanye da ankel socks and crops farare.

Ai yana shigowa ta miƙe tsaye a wani irin slow tana kallonsa, kowani motsi nasa a kan idanunta. Dr James irin mazan nan ne masu burge mata da shiga rai, ga shi da salo ɗan gaye.

A saman sofa ya kariso ya zauna, sai da ya ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya, ya gama shan kamshinsa kafin ya ce. "Get out of my office!". A ɗan kaifafe ya faɗa, saboda ya ji haushin yadda ta kara 30 mins a kan lokacin da ya bata, shiyasa bai shigo da takardun da zai bata ɗin bama, ya ga lokacin da ta shigo ɗakin ta Camerar dake ɗakin, karfe 5:30 ta shigo, shi kuma 5 yasan suke tashi, kuma 5 ya ce ta zo ta same shi, shi ne zata ɓata mashi lokaci, ba zai ɗauki wannan iskanci ba.

Tsoro da shakkarsa yasa bata yi ƙoƙarin bashi hakuri ba, da sauri ta wuce ta fita. Tana fitowa suka ci karo da sister Lazy dake ƙoƙarin shiga office ɗinsa hannunta rike da tarin files na manyan ayyuka dana rahotannin dabbobi.

Tana ganin sister Zinta ta fito daga waiting room ɗinsa ta dakata tare da juyowa gareta, sai dai kafin tai mata magana Zinta ta wuce da gudu tana ƙoƙarin toshe bakinta saboda wani irin kukan da yake shirin kubce mata, ta ji zafin rasa wannan dama, tin bata wuci 16 years ba take dakon wannan dama, shekara biyu kenan tana aiki tukuru dan ta samu attention ɗinsa, yau ta samu amma ta sake rasawa, dole ta ji zafin wannan abu.

Da gudu ta nufi in da zata samu Maya. Zaune ta iskota rike da wani littafi tana dubawa. Da gudu ta zo ta ja hannunta tana faɗin. "Sister mu je"..... Maya na shirin tambayarta lafiya, amma ganin tana kuka yasa ta fasa tambayar tata tare da miƙewa kawai ta bi bayanta. Da gudu suka wuce sashen kwanan ɗalibai dake can nesa da lap ɗin, kuma shi ne section A a wajen, na ce maku sashe 5 ne a cikin wajen, sashen kwanan ɗaliban lafiya shi ne section A, sashen dabbobi shi ne section B, sashen chemical shi ne section C, akwai section D da section E wanda labari bai isar damu wajen ba bare mu san me a cikinsu.

Da gudu suka koma hostel É—insu. Ita kuwa sister Lazy da sauri ta shigar da takardun office na Dr, jikinta har tsuma yake wajen yin gaggawar fitowa ta bi bayan sister Zinta dan ta je ta ji me ya haÉ—ata da Dr James da har zata shiga waiting room É—insa kuma ta fito tana kuka, ko dai akwai abin da yai mata ne?.

Kai tsaye sashen kwanan ɗalibai Lazy ta nufa, sai huci take yi, dan a duniya idan ana son aga fushinta wata ta raɓo Dr James, a cewarta zata iya kisa a kansa.

A lokacin da ta shiga room ɗinsh suna zaune sister Zinta na faɗawa Maya abin da ya faru sai ganin Lazy a kansu suka yi, cike da tsoro suka mimmiƙe tsaye, ɗaure fuska tamau Lazy ta yi, in a harsh way ta ce. "Ke me ya kaiki room na Dr James?"....... Tsuru-tsuru da idanu Maya ta yi, dan akwaita da tsoro sosai, gara ma sister Zinta da ɗam kwarin zuciyarta.

Hannu tasa ta goge hawayen dake zuba mata, cikin girmamawa ta ce. "Shi ne yai inviting ɗina zuwa wajen........". Bata iya karisa maganar ba sakamakon wani bahagon marin da Lazy ta sauke mata, cikin fushi ta ce. "Ke har kin isa Dr James yai inviting ɗinki zuwa wajensa? Wacece ke? Dame kike taƙama?".

Note, yauwa na ji kuna cewa dikka malaman asibitin nan kamanninsu É—aya, ba haka na ce ba, ce maku ma yi suna É—an kamanceceniya, amma kowacce da irin halittarta da kuma yanayin kamanminta, kyan fuskarta da kyan jikinta, ko yanayin hasken skit É—insu ya bambamta, kawai dai shekarunsu ne dikkansu É—aya watau 18 years, in da suke kamanceceniya kuma shi ne yanayin jiki, Æ´an caras-cas dasu zubin Æ´ar tsana na ce maki.

Dafe kuncinta sister Zinta ta yi, idanunta suka kara kawo ruwa sosai, bata da bakin iya ramawa saboda sister Lazy a karkashin office ɗinsu Dr James take, dole ne su yi mata biyya. Zazzaro fararen idanunta Maya ta yi, tana son ja da baya sister Lazy ta cakumo wuyar rigarta, cikin faɗa ta ce. "Kece kike zugata ta shiga gonata ko? An faɗa maku Dr James mara aji ne shi da zai kula irinku? This should be the first and last da zan sake ganinku a arear da yake, ku ba a section B kuke aiki bama? Me ya kaiku side ɗinsu?!". Ta faɗa tana shaƙe mata wuya.

Gagara amsa mata suka yi, cakumo wuyar rigar Zinta ma ta yi, tsabar mugunta ta haÉ—a kansu ta gwara da juna kafin ta ce. "Dik wacce ta sake shiga gonata sai na lahira ya fita jin daÉ—i!".

Su kuwa tsabar tsoronta babu wacce ta iya koda kara ne, dik da sun ji zafin buga masu kai É—in da ta yi, amma suka shanye har sai da ta gama zazzaga masu jajjagen balain nata, ta kwashi kafafunta mai kama da na sauro ta nufi waje fuuuuu, sannan ne suka zazzauna a gefen bed É—insu tare da rushewa da kuka a tare. Sai da suka yi mai isarsu suna luguiguita gaban goshinsu, sannan ne suka yi shiru, suka rungumi juna cike da takaici da danasanin zuwa side É—insu Dr James.

Almost 30 mins suna a haka kafin su miƙe zuwa toilet ɗinsu, abinku da ɗaliban lafiya, ko'ina a cikin toilet ɗin nasu tsab-tsab har sheki yake yi, fuska suka wanke a wajen wash hand base, sannan suka fito, saman gado suna koma, kowacce ta fito da littafanta ta fara nazari kan Chemicals da suke karanta a yanzu, babu wacce ta sake cewa ƴar uwarta uppan suka shiga karatu.

Ita kuwa Aunty masifatu kanwar jarabatu watau sister Lazy kai tsaye room ɗin Dr James ta nufa tana ta wani uban huci, ran ƴan mata ya ɓaci.

TO MY PEOPLE ME KUKE TINANI A WANNAN ƁANGARE? MU JE ZUWA!.

CRYSTAL PALACE.🔥

Zaune Seraphina take a saman gadonta, tana rike da waya tana dannawa, ta shiga world live a wayar tana dudduba labaran duniya dan jin me yake gudana. Lokaci guda ta zunduma ihu tare da miƙewa tsaye.

Da gudu Madam da É—iyarta Aisha suka shigo dan jin meyasamu Seraphina take ihu kuma, a tsakiyar gado suka iskota tana murmushi ta kurawa waya ido, cikin kiÉ—ina Madam ta ce. "Babyn daddynta lafiya? Wannan ihun fa?".
Chapter 78 · 0% Book details