← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 211 OF 227

Sashe 211

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mu É—an koma baya kaÉ—an kafin mu cigaba. A É—azun bayan Aryan ya kammala waya da Seraphins ya bata izinin tafiya, da suka gama wannan rikici da Vir ya bar wajen room na Lion ya shiga. Babu kowa sai ya fita zuwa É—ayan room É—in, nan ya isko Lion tsaye yana shiri cikin tail coat fari tas, a gefen bed ya zauna yana faÉ—in. "Ina da tambaya".

Shiru Lion bai kulasa ba. A dake ya ce. "Wai wannan gida naka ne kai kaɗai ko namu?"...... Banza da shi Lion ya yi bai amsa ba. Ganin hakan yasa ya ce. "Ɓata bakina ma nike yi da na tsaya yin magana da kai a kan wannan issue, ina da right na yin abin da nike so a gidan nan, dan haka zan kawo sister ɗita wannan gida, ta zauna damu for some days, ba zata shiga harkarka ba, bama zata zo in da kake ba".

Tamkar babu Lion a ɗakin, ya cigaba da abin da yake yi, sai da ya kammala ne ya kalli in da Aryan yake. "Get ready to go to Dad's house now, there's something we need to check". Yana gama faɗa ya juya ya fice abinsa. Miƙewa Aryan ya yi, ya fito ya sanar da su Vir su shirya, sai ya dawo dan shiryawa.

After like 1 hour suka fito shirye cikin kaya iri É—aya, tamkar Æ´an huÉ—u. A main parlo suka iso Lion zaune, ya É—aura kafa É—aya bisa É—aya, ya É—aga kansa sama tamkar mai tinanin wani abin, ya yi shiru.

Ƙashin maƙogwaronsa Aryan ya ɗan taɓa kafin ya ce. "Let's go". Ba tare da ya yi magana ba, ya miƙe tsaye kafin ya waro jade eyes ɗinsa masu kama da sleeping eyes ɗin nan, yau sai ya yi kamar wanda yake cikin maye ma, dik yadda aka yi barci yake ji.

Jerawa suka yi zuwa main door na fita. Suka shiga elevator suka yi ƙasa, dik da suna sanye da wannan nose mask ɗin nasu na gado dik wanda ya gansu sai ya sake waigawa ya gansu, mazajen gaske.

*Jama'ar kirki littafin ZAKUNA BIYAR STEP 1 ya zo gangara, zamu shiga STEP 2 wanda shi ne ainahin labarin yake cikinsa, ZAKUNA BIYAR iya STEP 1 ne kawai free, daga STEP 2 zuwa karshe paid ne, 1k kacal yake, ki hanzarta making payment kada mu tafi mu barki, dan labarin bai ma fara ba, tarin ilmin, faÉ—akarwa, waazantarwa, wayar da kai, nishaÉ—antarwa dik yana cikin STEP 2, yanzu dik ba'ayi komai ba, STEP 1 dik sharar fagece, ainahin labarin yana gaba, in kin shirya makin payment ga account É—ina, 2308489938, Musa Fatima Zahra UBA bank. Sai ki turo mun evidence ta wannan number 08161390581. Mutanen Niger ku mun magana ta numberta sai in baku Nita É—in da zaku yi payment É—inku a ciki, idan kuma kati ce ku mun magana dai zan faÉ—a maku komai.*

Likes comments and share fisabilillah.

QUEEN OF SURPRISE ✍️🔥
🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥

PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.

For more information 08161390581 Whatsapp me only.

STEP 1🔥

2025-12-31.🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

No editing.💔

E_____________ 73 & 74

A harabar benen nasu suka tsaya, key ɗin wata dalleliyar mota Lion ya fitar daga aljihun coat ɗinsa. Miƙawa guru key ɗin ya yi, dikkansu da kallo suka bisa suna mamakin ganin yau da motarsa na ainahi zasu fita.

Wannan mota dad da kansa ya saya masu su huɗun iri ɗaya, to tin bayan rasuwar dad ɗin suka rufe motocin, dik wani abin da zai sanya a gane suna da alaƙa da Haiza'an sai da uncle yasa suka ajiyesa, dalilin kenan da yasa basa fitowa da Hero, domin kowa ya ga wannan zaki sai ya gane zakin Haiza'an ne, dan wannan zaki ya shiga tarin dad dama duniya bakiɗaya, kuma a jikin Zakin a gaban goshinsa akwai rubutun sunan dad da aka yi mashi da wuta, shiyasa kowa ya gansa zai gane na dad ɗin ne, shiyasa ko waje basa leƙowa da shi, yana gida.

Sun yi mamakin ganin zasu fita da wannan mota, motocin nasu dik plate numbersu sunan Haiza'ans family ne a jikinsa, shiyasa suka jinginesu. Tin da suka ga Lion zai fita da wannan mota suka fahimci ya shirya fito na fito da duniya bakiɗaya kenan, lallai kuwa akwai kura, uncle da duniya ta ɗauke ya mutu yana ƙoƙarin tada tarzoma kenan, zai sanya IRON FIST su bayyana a duniya, zasu jingine aikin SSO kenan ko yaya? Ya Aryan zai yi da Seraphina da ta tsani IRON FIST? Me Khaiza'ans family zasu ce? Abba zai yarda da cewa Aryan shi ne Champion na IRON FIST?.

Fito da motar guru ya yi, Lion ya shiga gidan gaba, Aryan da Vir suka shiga gidan baya. Kai tsaye HEART OF CRYSTAL PALACE suka nufa. Tin daga kan securitys dake tsaron CRYSTAL PALACE har izuwa kan jama'ar dake ciki sai da suka zubawa motar nan ido, musamman suna Haiza'an dake gaban motar. Mota na farko kenan da dad ya fara sayawa Æ´an matasansa a lokacin.

Da yake gate É—in gidan dad automatic ce, suna isa gate É—in ta yi scanning motar, ganin babu abin haÉ—ari a ciki yasa gate É—in ta wangale masu kanta. Ciki suka kutsa, kai tsaye suka nufi marking lot, bayan sun paka motar kusan a yare suka fito.

Cikin main parlo suka nufa, a jere suke sanya kafafunsu a ƙasa suna ɗaukewa. Suna shiga main parlo suka rabu, kowannensu ya yi nasa hanyar. Kai tsaye cikin ɗakin dad ɗinsu Lion ya nufa, tin da dad ya rasu Lion bai taɓa shiga wani ɗaki a gidan ba face na daddyn nasu, ɗakin mom ɗinsu yana nan yadda ta barshi, bai taɓa shiga ba, baya sha'awar ganin ko kofar ɗakin bare ya shiga.

A saman bed É—in daddy ya jefa wayansa game da cire tail coat É—in jikinsa ya jefa kan gadon, ya bar iya long sleeve shirt na ciki, toilet ya shiga, jim kaÉ—an ya fito fuskanta da É—an danshin ruwa, balconyn daddy ya nufa, tsayawa ya yi yana kallon cikin CRYSTAL PALACE É—in, a hankali ya É—an lumshe idanu yana tina da idan ya shigo gidan da fuskan daddynsa yake fara cin karo yana tsaye a balcony, ko yana zaune a kan sofar dake wajen.

A hankali iska ta fara kaɗa shi tana kaɗa kitson dake kansa, sai ya ji wani irin daɗi na ratsa shi. Ya ɗan jima a tsaye a wajen kafin ya juyo ya dawo cikin ɗakin. Haka kawai yau ya ji yana sha'awar yi wa daddyn nasa bincike a ɗaki, abin da bai taɓa yi ba, dan kullum ya zo daga toilet sai gado kawai yake amfani da su.

Drawers na wajen mirror ya buɗe, babu komai a ciki, rufesu ya yi ya nufi wajen closet na daddy, kusa da wani tangamemen wardrobe ya tsaya, komai yana nan yadda yake, kayan daddy dik baa taɓa komai ba tamkar yana raye.

Nisawa Lion ya É—an yi, hannu ya kai zai buÉ—e wannan wardrobe É—in, sai taki buÉ—ewa, zuba mata idanu kaÉ—an ya yi, nan ya fahimci haÉ—e take da na'urori, sai da password zata buÉ—e. ÆŠan É—age kafaÉ—unsa ya yi alamar anyway, sai ya wuce drawer ta gaba. Hannu ya kai jikinta take ta buÉ—e kanta. Wasu tsala-tsalan tail coat masu masifa tsada ne a shirye a ciki, a jikin hanger aka shiryasu tamkar mai shi yana raye.

Kallo É—aya ya yi masu ya É—an É—auke kai, har zai wuce kuma sai ya lura ai ba iya faÉ—in wardrobe É—in ba kenan, tana da zurfi amma a wajen da su coat É—in nan suke ya yi kaÉ—an ace iya zurfinta kenan, what's behind?. Bai yi wani dogon tinani a kai ba ya matsa gaba, dan bai son ciwon kai, saboda yana tinanin dik kaya ne a cike a cikin ko'ina, dan yasan halin daddyn nasa É—an kwalisa ne, gadon É—aukar wanka suka yi.

Wucewa gaba ya yi, ya dinga yawo a wajen, ko wucewa ya zo yi kusa da wardrobe in dai ta É—an yi scanning É—insa sai kofar ta buÉ—e, bai damu ya dudduba me a ciki ba, wasu drawers É—in ma takardu ne a cike a ciki ba kaya ba, amma bai mai da hankalinsa ba, wucewa kawai yake yi.

A cikin ransa ya ce. "Ina computer dad? Da wannan computer yake controlling HAIZA'ANS AIRLINE da sauran abubunsa"....... Kada ku manta na ce maku computer hannun Dr James ita ce computer dad.

Fitowa daga wajen ya yi, ya dawo tsakiyar É—akin. Yana tsayawa sai ga Vir ya shigo yana faÉ—in. "Nan ka yo?"..... Bai yi magana ba, ya dai bi Vir da ido. Saman gadon dad Vir ya zauna yana cigaba da kallon Lion É—in.

Aryan kuwa kai tsaye room na mom ya nufa, domin kuwa ya jima yana son zuwa room ɗinta ya yi bincike, amma bai samu dama ba, abubuwa sun masu yawa, kafin su kammala wannan wannan zai sako kai, ko lokacin kansu basu da shi........ Yana tura kofar yana da kura ta buɗesa, dan kuwa ana gyara ko'ina a gidan banda ɗakin nan, Lion ya hana a taɓa ko kofar ne, shiyasa uban yana da kura ya buɗe koina.

Kamar Aryan zai juya sai kuma ya daure ya fara tattare yanar yana shiga ciki, dik in da ya taka sai shaidar kafansa ya bayyana saboda kura da ta yi yawa.

Gadonta, drawers komai yana nan yadda ta fita ta bari, har bedsheet baa taɓa ba. Ɗan girgiza kai Aryan ya yi game da cewa. "Sai an share room ɗin nan an gyara zan dawo, dattin ya yi yawa". Ya faɗa game da ƙoƙarin juyawa zai fita.

Idanunsa ne suka sauƙa a kan gadonta, ya ga alamar tudu a bakin gadon, alamar wani abin ne da kura ta rufe sosai, kamar ba zai je wajen ba, sai kuma ya daure ya karisa. Hannunsa yasa ya zaƙulo abin dake wajen, kura ya zama tamkar ƙasa mai laushi aka zuba a wajen.
Chapter 211 · 0% Book details