Sashe 93
Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jikinta dik ya mutu ta haÉ—a bluetooths É—in ta yi connecting É—insu da sautin nata, ta yadda suna kutsawa cikin daji ita kuma tana magana, ma'ana tana directing É—insu a kan hanya while tana ganin rahoton da drone É—inta ke É—auko mata.
Bluetooth uku ta ɗauka ta nufo shi, a natse ta miƙa mashi tare da cewa. "This is it". ....... Ba tare da ya ɗago ya kalleta ba ya karɓa ya juya, da gudu su Angelina suka fito dan ganinsu, sun sha mamakin ganin dikka mazan sun yi shirin yaki, suna rike da bindigu, babu alamar wasa a tattare da su, dik sun tsaya a layi sun yi shirin mutuwa ko rayuwa.
Miƙewa Noor and Zaynish bluetooth ɗin hannunsa ɗaiɗai Leo ya yi, shi kuma ya sanya ɗaya a kunnensa, cikin sirri yai mashi bayanin yadda zasu tafi, daga nan ya ce su shirya. V na tsaye tana kallon Noor da yake ƙoƙarin sanya bluetooth a kunne, ba zaka taɓa cewa shi bane, fuskan nan babu alamar wasa, lallai ya cika alkawarinsa da ya ɗauka na cewa ba zai bari soyayya ta ɗauke mashi hankali daga kan aiki ba, ko sallama bai zo sun yi ba, aikin dake gabansa kawai yasa kai.
Bayan ya kammala shirinsa tsab sai ya É—ago ya kalleta. Hannu ya É—aga yai mata alamar heart da shi, slowly ya motsa lips É—insa wajen cewa. "I love you". Ko kaÉ—an babu fara'a a kan fuskansa, yanzu ya tashi daga Romeo ya rikiÉ—a zuwa AZURE SOLDIER kuma member of DOL!. Kallon shi cike da fargaba kawai take yi, ta gagara iya mayar mashi da martanin love É—in da ya furta mata, ganin haka yasa ya É—auke kansa daga kallonta, dan kada ma ta raunata mashi zuciya.
Sojoji 20 suka tafi, suka bar 4 a tare da su Arya dan su basu tsaro, su V suna kallonsu har suka wuce cikin shirin yaki. Bayan sun ɓacewa ganinsu ne suka juya da nufin su koma cikin tantinansu sai Arya ta ji alamar kuka kamar kuma motsi ta can nesa da tantinsu. Cike da jarumta ta nufi wajen, tin daga nesa tana jiyo kukan tana bibiya har ta isa wajen, yana da nisa daga in da suke, sannan wajen bakin ruwan dake kusa da su ɗin nan ne amma ta can.
Tin daga nesa ta hango mutum a bakin ruwan zaune dirshan a ƙasa tana kuka. Da sauri ta karisa wajen, yarinya ce karama da bata wuci 10 years ba, kyakkyawar gaske, irin masu kiwon shanun nan ne. Arya ta ɗan ji tsoronta kaɗan, saboda bata zaci mutum bace, gata a tsakiyar dokar daji, gata kyakkyawa, sannan tana zaune kusa da ruwa tana kuka, sai ta zaci ƴar ruwa ce kawai.
Kamar zata juya, sai ta tina ba'a san sojoji da tsoro da sarewa ba, hakan yasa ta ji kwarin gwiwa, da sauri ta nufi yarinyar. A gabanta ta tsugunna tare da dafa shoulders É—inta, a sanyayye ta ce. "Why are crying? Where's your mom?".
ÆŠago kai yarinyar ta yi ta kalleta, sai da gaban Arya ya faÉ—i ganin a fusge yarinyar taso yi mata kama da Leo, amma kama ta jini haka ba ta fuska ba. Ni kam na ce Arya ko dai ko dai? Ko dik damuwa da shi ne yasa kike ganin masu kama da shi?.
Da hannu yarinyar tai mata nuni da wani jarka na ruwanta da take É—eba, ta zo É—eba ne ya kwace ya faÉ—a cikin ruwan, ita kuma tana tsoron shiga, shi ne ta zauna ta hau kuka. Kallon jarkan ruwan nasu Arya ta yi, ta fahimci yarinyar bata jin turanci, a ranta ta ce to wace yare yarinyar take ji?.
Ganin bata da lokacin ɓatawa wajen buƙatar gane yaren yarinyar ne tin da ga su Leo sun tafi kuma dole zasu buƙaci information daga wajenta, sai ta yi saurin miƙewa, cikin zafin nama ta faɗa cikin ruwan, iyo ta yi har izuwa in da jarkan yake, ta fito da shi tare da zuwa ta miƙawa yarinyar, sai da ta miƙar da ita, dik da yakansance yarinyar jikinta dik datti Arya bata kyamaceta ba, ta sanya hannu ta kakkaɓe mata jiki sannan ta ce to ta tafi.
Alama yarinyar tai mata da cewa zata ɗebi ruwa kafin ta tafi, karɓar jarkar Arya ta yi, ta cika mata da ruwa sannan ta ɗaura mata a kai, ta ce ta tafi. Wucewa ta yi tana waigo Arya, ita ma tsayuwa ta yi tana kallonta har ta kurewa ganinta, mamaki Arya take yi ta yadda aka yi mutane ke rayuwa a wannan dajin! Ganin yarinyar ta tafi yasa ita ma ta wuce da sauri ta koma wajen tantinsu.
Canza kayan jikinta ta yi, sai tambayarta ina ta je ta jike su V suke yi, amma bata kula kowa ba, ta canza kaya ta zo ta hau kan aikinta, watau Arya tana da kyakkyawar zuciya, kawai halinta ne a haka na rashin son shiga mutane da ware kai, rashin son hayaniya da É—auke kai a abu ga tsiwa da riko, amma batu na kirki a zuciya yake, kuma zuciyarta tas yake a kan hakan.
Ita kuwa V sai ƙoƙarin kiran Noor take yi, ta manta basa zuwa farmaki da waya, dik wayoyinsu na tantunansu, daga su sai bullets and gun suka tafi. Angelina na ta faman kallon hotunan da tai wa su Unays ɗazun, while Manassa ta yi shiru tana tinanin guy ɗin da suka haɗu da shi ɗazun da ta je yin brush.
Tana tafiya tana waige-waige kawai ta ci karo da shi, baya ya ja tare da kura mata idanu kafin ya ce mata ita ɗin kyakkyawa ce. Shiru bata mashi magana ba, ta matsa gefe ta cigaba da goge bakinta, unexpected daga bayanta ta ji ya zuro hannu ya karɓi brush ɗin, goge mata bakin ya dinga yi har sai da hakwaranta suka fita. Juyawa ta yi ta ɗan turesa ganin ba zai daina goge mata bakin ba.
Ta ɗaure fuska tamau kafin ta ce. "Waye ya baka izinin ka taɓani ko wani abin nawa?". ........ Yana kallon kyakkyawan face ɗinta ya amsa da. "No body, haɗuwarki ce kawai sila, kuma ai gaba nike dake a wajen aiki, kinga ba sai kin bani izinin yin abu ba, ni ne ma zan baki izini!!"...... Harara ta dallah mashi kafin ta ce. "Kasan wacece ni kuwa da kake maganar gaba kake dani a aiki?!".
"Soja ce ke kamar ni, ke jami'ar computer ni kuma jami'in bindiga, that's all"......... "Haka kake tinani?!"..... Ta faÉ—a a fusace. Kai ya gyaÉ—a mata alamar kwarai haka yake tinani. Screen light na wayarta ta kunna tare da juya mashi. Ai yana kallon hoton kan wallpaper É—inta bai san lokacin da ya saki brush na hannunsa ba.
Ɗan ja baya daga kusa da ita ya yi, with do respect ya ce. "Sorry madam". Ya ganta tare da daddynsu ne da su Arya, shi ne ya kiɗime haka, ya ga GAT. Harara ta dallah mashi tare da miƙa mashi hannu kan ya bata brush ɗinta, da sauri ya duƙa ya ɗauko ya miƙa mata, karɓa ta yi ta wuce ta nufi hanyar shiga room ɗinsu. Sai dab zata shiga ɗakin ne ta juyo ta saci kallonsa, ya yi mugun tafiya da imaninta, amma tin da yana tsoron daddynta sai ta yi ya ja mashi rai da barazana kafin ta sake da shi.
A TINANINKU DA WAYE TA HAÆŠU?.
To su Leo sai dai mu ce ALLAH ya tsare ya maido mana da ku gida lafiya, ya baku iko a kan waɗan nan ƴan ta'addan, su Arya ALLAH ya dafa maku ku naɗi information na komai da taka tsantsan ba tare da ƴan ta'addan sun gano drone na camerarku ba, ku naɗi komai ku bawa su Leo namu a kan lokaci kuma daidai ta yadda zasu yi aiki cikin hikima da kwarewa!. Kun ji halin da ƴan team DOL suke ko? To mu leƙa asibiti kafin mu wuce CP.
--------------------------🔥
WS-HOSPITAL.💔🥲
Zaune Maya ta isko Dr Kamal yana aiki a desktop computer dake gabansa, idanunsa sanye da eyes care, ga dikkan alamu ba aikin wasa yake yi ba, ya dukufa haikam.
Excuse tai mashi har sai da ta jira ya bata izinin shigowa bayan ta wuce PA É—insa kenan. A saman visitor chair ta zauna, cikin girmamawa ta ce. "Good morning sir"....... Bai amsa ba, hasali bai ma É—ago ba, yana cigaba kawai da aikinsa. Shiru ta zuba ido tana kallon irin haÉ—uwar office É—in nan, komai na cikin office É—in luxury one ne, ga wani haÉ—aÉ—É—en kamshi dake tashi.
Zaman good 30 mins ta yi kafin ya ɗauke idanunsa daga kan computer ya mai da shi gabaɗaya a kanta, slowly ya zame hannnunsa daga kan keyboard na computer kafin ya cire eyes protection dake idanunsa. Sai da ya cire ta fahimci ita yake kallo, ƙara natsuwa ta yi game da yin ƙasa da kai, tana jin kirjinta na dukan uku-uku.
"Maya". Ya ambaci sunanta can ƙasa. Da sauri ta ɗago kai. "Good evening sir". Dan sai a yanzu ta tina ashe yamma ce ma ba safiya ba. Bai amsa gaisuwar ba sai ya fito da wasu tulin takardu ya tura mata gabanta, sannan ya ɗauki pen ya miƙo mata. "Sign here". Ya faɗa in a low waye sosai.
Da yake suna shakkarsu da tsoronsu, bata tsaya tambayar document na menene bane kawai ta karɓi pen ɗin ta hau signing, paper dake ciki dikka ya dinga buɗe mata tana signing. Sai da ta kammala sannan ya ɗauko wani document ya miƙa mata. "Wannan shi ne project da kika yi signing na kin karɓa a yanzu, 24 hours gareki ki karanta document ɗin nan jibi da safe za'a fara project ɗin, so a yanzu kin dawo karkashin office ɗin nan da aiki, kina iya tafiya".
Cikin girmamawa ta amsa tare da karɓar document ɗin sannan ta miƙe ta fito cike da farincikin ta baro side na chemical ta koma side na manyam 3D da kowa ke tsoro......... Da kallon ƙasan ido ya bita har ta fita, wayansa ya ɗauka, rubutu yai short kafin ya ajiye wayar, ya miƙe ya buɗe door dake cikin office ɗin, a tinanina toilet ne a wajen, sai da ya shiga naga wajen ya sha banban.