← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 227

Sashe 95

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni ban ce komai ba, amma shawara da kirana ga mata, dan girman ALLAH dik asibitin da zaki je, kome aka ce za'ayi maki ki É—auki waya ki kira É—an uwanki namiji, ya zo ya tsaya maki, duniya ba abin yarda bane, idan kina da wa ko kani ya tsaya a kanki dik abin da za'ayi a yi a gabansa, ba ruwanki da cewa mijinki da Æ´an uwansa suna nan, ke baki da Æ´an uwa ne? Idan ta kama an ce lallai sai an cire maki mahaifar ne to idan an cire ki ce su baki kayanki ki tafi da shi, kada ki yarda ki barshi a asibiti, ko sun ce maki jefar da shi zasu yi dan ciwo ne ki ce e su baki kayanki, wlh gara ki je ki tona rami a gidanki ki binnesa kina ganin ramin kullum akan ki bar masu, baki san me suke yi da shi ba, dik abin da aka yi da shi ba zai canza daga sunan mahaifarki bane!
Ban faÉ—a haka dan rashin yarda ya shiga tsakaninku da mazajenku ba! Ku yi hankali ne kawai, kada ki yarda da zuwa asibiti guda É—aya ana duba lafiyarki, idan an yi maki aiki ne bayan kin samu lafiya jeki wani asibitin daman a maki scanning ki tabbatar da lafiyarki, duniyar yau ta zarce dik yadda kuke tinanin, abin ya fi karfinmu ya fi karfin shuwagabannin AVARIS! Dan abin daga sama yake, ALLAH ne kawai zai iya dafa mana ya kawo mana karshen wannan musifa, amma hakan ba zai faru ba sai mun tashi tsaye, mu kare kanku sai mu nemi UBANGIJINMU da ya taimaka mana.

Gabaɗaya WS-HOSPITAL ina typing ɗin labarin ɓangaren ina kuka, wlh har cewa mahaifiyata na yi zan jingine labarin nan saboda tausayin dake cikinsa ya yi yawa, mamana ta ce idan na rubuta zata yi farinciki da hakan, kuma ta umarceni da kada na rage ko A daga cikun ilimi da sanin da ALLAH ya bani, ta ce in daure taimakon alumma zan yi, alƙalami ya fi takobi! ALLAH yana tare dani, ta kara mun kwarin gwiwa sosai, kullum idan ina typing part ɗin sai na ce mata ina jin kamar ba zan iya ba zan jingine labarin, ta ce ta sanni zan iya in dage! The thing is very touching heart, emotional, har tsoron shiga cikin labarin in zayyana komai nike ji! I need your prayers.

Mutanen AVARIS suna buƙatar addu'arku, yadda aka horasu da yunwa da wahalar nan kuna tunanin ba zasu karɓi wannan aiki gadan-gadan bane tin da kowa yana son lallai sai ya yi kuɗi? Matan AVARIS yanzu kuma sun shiga uku, mahaifarsu ya zama kuɗi, shikena a kuma, yanzu kowa asibiti ka leƙa za'a ce aiki ake mata, ALLAH ka shige mana gaba ka karemu daga dikkan wata musifa.

Wannan shi ne hanyar da su Dr James suke bi dan samun mahaifar mata, tin da kuma kuka ga sun tsuga mashi kuÉ—in har kimani miliyan tamanin a wajen sayensa fa to ku sani bakaramin abu suke yi da shi ba, ba karamin kuÉ—i suke samu ba, amma koma menene idan muka shiga cikin labarin zaku sani.

Yanzu sai kewaye duniya suke suna raba wannan buƙata tasu ta a kawo masu mahaifa zasu saya, nasan maza masu matattun zuciya tuni zasu karɓa, matanma wasu da basu san ciwon kansu ba da kansu zasu karɓi kuɗin, ni damuwata shi ne idan aka basu mahaifar abin da zasu yi da shi, kun dai san ba zasu zuba makudan kuɗi a ƙan karamin abu ba ko? Babba abu ne!.

---------------------------

Dr Kamal ne ya ce. "Yunwa ya cinye kowa ba dole su sayar ba, gwamnatin Avaris bata son biyan ma'aikatan lafiyar government hospital É—inta albashinsu, basa son sauke hakkinsu, kasar ga yunwa da wahala dole su sayar a".

Sipping na drink ɗinsa Dr Mark ya yi tare da cewa. "Basu da zaɓi ne, dole su sayar"....... Dr James dai rufe files ɗin ya yi tare da ɗauko wani file ɗin..... "Muna da contract har uku fa a shekarar nan, dole mu mayar da hankali, sannan batun project na PC ɗin nan, daga sama an hura mun wuta sosai, yakamata mu mayar da hankali, a nan da wattanni shidda zuwa takwas mu kammala project ɗin nan mu ci kuɗinsa"................... Miƙewa Dr Kamal ya yi tare da cewa. "We have to go to section D dan duba wancan project ɗin, yanzu ɗayar project ɗin nan zamu kammala, na bawa Maya document na aikin, 24h garesu, dan haka mu bar wannan zancen sai jibi idan mun samu feedback daga garesu".

Na'am suka yi da zancensa, ajiye cup na drink ɗinsa Dr Mark ya yi, kusan a tare suka miƙe suka fito ta kofar office na Dr James, daga nan suka fito izuwa section D. Suna tafiya a natse amma cikin zafin nama. Dik in da suka wuce sai nurses sun duƙa sun gaidasu.

Kai tsaye cikin section D suka shiga, rabuwa suka yi, suka fara kewaye a wajen suna duba dashen da suka yi! Suna bi suna É—aukar rahoto da kansu, komai na tafiya daidai, halittar da suka dasa cikin mahaifar har sun fara motsawa tamkar yaro na motsi a cikin uwa, karku manta sai da ya zama embyro suka dasa shi a cikin mahaifar.

Bari in ɗan yi maku karin haske a wannan waje kafin mu wuce gaba dan kada ruɗewar tai maku yawa, naga dayawa sun fara ruɗewa tin ba'a je komai ba, to zan buɗe maku haske kaɗan. Nasan kun fahimci cewa waɗan nan kwayaye da suka dasa a cikin mahaifa a page ɗin jiya kun fahimta yara aka dasa, to yara suke kyankyasa da waɗan nan mahaifa, suna haɗa sperm na ɗah namiji da kwayayen mace su kyankyashe yara. Sai dai kuma idan suka kyankyashe waɗan nan jarirai basa wuce watanni uku a wannan asibiti, wasu jariran a ranar da aka fito dasu daga cikin mahaifar a ranar ba'a sake ganinsu, wasu suna kai wata ɗaya a wajen, wasu suna kai wata biyu har su fara wayau suna shan madara maimaikon nonon uwa, amma basa taɓa haura wata uku iya wuya, kuma abin mamaki kullum suna cikin kyankyasan yaran ne, dik wata suna cire kwan halittar mace ai kun gani, to me suke yi da uban yawan jariran da suke kyankyasar nan? Ina ake kaisu?.

Baku yi mamakin yadda na ce maku nurses na asibitin dik shekarunsu ɗaya ba, watau 18 years ba? To ai dik ta wannan hanya aka kyankyashesu, suka renesu, suka basu ilimin likitanci, sannan waɗan nan ƴan mata da ake cire kwan haihuwarsu dik wata ku sani suma a nan aka kyankyashesu musamman aka killacesu dan a rinƙa cire kwayayyensu.

Na ji wasu readers suna cewa basu da hankali suka yarda ana cire masu kyan haihuwa, to jama'a a lafa haka nan, suma Æ´aÆ´an kwalbar haihuwa ce da aka kyankyasa ba Æ´aÆ´an mama da baba ba, basu da kowa sai ALLAH, suna dai da azzaluman ubanunsu da suke bada sperm É—insu a kyankyashesu, dik namijin da zai bada sperm É—insa a wanna harka shi ne babban azzalumi kwai ba zai bada yaro ba sai an haÉ—a da sperm, to masu bada sperm nasu sun fi kowa laifi, su suna can suna jin daÉ—i cewa maniyinsa ma saya ake yi a basu kuÉ—aÉ—e, a yaudaresa da cewa ai man shafawa ake yi da maniyin, su yarda su yi ta sayarwa, basu san bataliyar Æ´aÆ´a ake kyankyasa masu ba.

Sannan dole zaku ga nurses É—in suna É—an kamanceceniya, kada ku manta a jikin matan nan dai na page É—in jiya ake ciro kwayayyen halittarsu, gara maniyin na maza daban-daban ne, amma kunga ana iya ciro kwai goma a jikin mace É—aya, kunga yara goma kenan! Dole wasu su yi kamanceceniya.

Karin wani haske a wannan asibitin, basa kyankyasan mata sai maza, basu cika amfani da sperm mara karfi sosai ba sai idan an basu contracts kan kyankyasar yara mata, amma dik maza suke kyankyasa, waÉ—an nan nurses É—in kawai suka kyankyasawa kansu mata, dan ba zasu yarda su kyankyashi maza su renesu ba, dan maza zasu iya basu matsala, mace halitta ce mai rauni, dik a turban da suka É—aurata zata bi ne, musamman idan bata san komai ba.

Amma dani daku dik mun san idan suka kyankyashi maza suka renesu, suka masu ilimin likitanci to fa idan idanunsu ya buÉ—e suna iya cin ubansu ne, shiyasa suka ki yarda su É—auki maza, so a takaice basa kyankyansan yara mata sai maza, kansu kawai suka kyankyawa matar nan dake masu aiki, fatan yanzu kun gane?.

Yauwa karin wani haske, daga waje wani likita baya zuwa aiki a wannan hospital ɗin, wannan amsar tambayar readers ne, in kara maku haske, babu wani mutum daga waje dake shigowa wannan hospital ɗin, ko sperm suka saya a waje ake ciniki, a ƙasa daban ma ake ciniki, in sun saya su waɗan na. 3D ɗin ne zasu fita su ɗauko sperm ɗin su kawo, dan haka wani daga waje baya shigowa, iya waɗan nan 3D ɗin ne kawai ke aiki a asibitin babu wani likita, fatan kun gane?. Mu je zuwa.

Sun jima suna kewaye a wajen, sai da suka tabbatar jariransu suna nan lafiya, suna samun rayuwa daidai da cikin uwarsu, sannan suka fito, kai tsaye office É—insu suka koma, dan shiryawa wannan babban project da manyan duniya suka basu aiki a kai mai suna P-C. WANI PROJECT NE WANNAN? SHI NE AINAHIN LABARIN JAMA'A.

A gefe guda kuwa sister Lazy tana can tana kuka kan abin da Dr James yai mata, ya koreta a gaban sister Zinta, wannan abu ya tsaya mata a rai matuƙa.

To mu leƙa CRYSTAL PALACE mu dawo, na fi son a kowani page ku dinga jin halin da kowani ɓangare yake ciki ko ba yawa ne!.

--------------------------🔥

CRYSTAL PALACE.

Can tsakiyar dare Aryan da ya gagara barci ne ya fito ya nufi room da yake zaton guru na ciki. Ya kuwa same shi zaune daman dadduma yana sallah. A gefen bed ya zauna yana jiransa yana har ya idar, miƙewa ya yi bayan ya kammala addu'a ya nufi Aryan ɗin.
Chapter 95 · 0% Book details