← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 227

Sashe 64

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ai tana shiga ta tsaya turus tana kallon yadda Zaysh yake dukan kofar ɗakin amarya, dan ya shigo ne ya sameta a tsakar gida, a tinaninta ba zai shigo ba, tana ganinsa ta watsa da gudu sai cikin ɗaki, shi kuwa ya bi bayanta, yau sai ta faɗa mashi a yaushe ƴar uwansa take bin maza da ta ambata, cikin fushi ya koma baya ya take kofar tata da karfin gaske har sai da ta jinjiga tamkar zata ɓalle, ya koma baya zai sake duka na biyu ne Ummie ta shigo.

Da gudu ta yi kansa tana ƙoƙarin cewa ya dakata, sai dai ina, kafin ta iso ya sake kaiwa kofar duka a karo na biyu wanda ya sanya kofar rugujewa ya faɗa ta ciki. Gabaɗaya ya canza tamkar ba shi ba, a fusace ya dimfari cikin ɗakin, yana taku irin na mazan gaske.......

E kam yau akwai rikici a gidan comrade Faisal........😂

STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥

ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️
🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥

PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.

https://www.facebook.com/share/g/1EUXbqsDjP

STEP 1🔥

2025-11-19.🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E_____________16 & 17

Ihu amarya ta fara kurmawa, ta gudu cikin bedroom, cikin zafa ya bita ciki, tamkar babu hankali a kansa, ko da yake dama a irin wannan lokaci ba man kai suka cika ba na faɗa maku, dan a lokacin su kaɗai suka san ya suke jinsu, bare sun karɓi alluran karshe na fita horo, amarya tana tsakiyar dajin dake kewaye da zakuna, dan kuwa a kanta wannan allura zai fara aiki, kunga kuwa ita ai ta bar tarihi.

Duka ɗaya yai wa kofar bedroom ɗin nata ya ruguje, dan shi irin kofar wood ɗin nan ne. Ciki ya shiga, saman gado ta haye tana ihu. Aikuwa taka saman gadon ya yi da takalmarsa, tana ƙoƙarin gudu ya damki gashin kanta, dama ɗankwalinta ya cire tin da ta gudo ta baro parlo.

Tsabar razana da tashin hankali fitsari ta saki a zaninta a wajen. Ina ai bai san tana yi ba, waje ya jata da gashin kan nata, yana fitowa ya daddage ya buga mata kai da jikin bango kusa da É—akin nata. Wani irin azababben ihun da ta zunduma sai da gabaÉ—aya unguwar ta amsa.

Ummie fa ja da baya ta yi, dan wlh ta ji tsoron tinkararsa, ta ce ba shi bane, an canza mata shi, bata tashi sanin haÉ—arin soja ba sai yau, kun san shi fa soja ko kakinsa firgita zuciya yake yi bare shi da yake horon AZURE kuma sabon passing out daga bar two bama bar one ba, ai amarya sai sorry.

Da gudu Ummie ta nufi kofar gida dan ta buÉ—e jama'a su kawo masu É—auki, ita da kanin nata yau tsoron tinkararsa take yi. Tana buÉ—e kofar ta ga jama'a a tsaitsaye a kofar gidan, da sauri ta ce. "Jamilu ku zo ku taimaka mun kada ya kashe amarya!". Muryanta na rawa ta yiwa matasan unguwar magana.

Da gudu suka faɗo cikin gidan, daidai lokacin Zaynish ya kwashe kafafun amarya ta zube ƙasa kamar kayan wanki, kun san sojoji sun kware wajen iya kwashe kafafun mutane su zubar dasu a ƙasa.

Dik matashin da ya shigo da gudu yana ganin kalar uniform É—in sai ya ja wata uwar birki, ba É—an sanda ba ne bare a iya zuwa a sasanta, shi wannan daga nesa idan aka ga kakin kawai canza hanya ake yi in dai akwai tsama a tsakani. Matasa sun fi goma babu wanda ya iya karisawa wajen ya rikesa, wasu ma ai a miliyan suka juya da gudu suka bar gidan.

Makwabta mata da sun shigo sun ga mai dukan amarya zasu juya da gudu. Hankalin Ummie ya yi mugun tashi, ga shi ko kaÉ—an bata da zarrar iya zuwa ta kama shi, kuma ita kaÉ—ai ce in ta kama shi kun san ba zai kai mata duka ba, zai daure, amma ina ta tsorata.

Wannan shegiyar takalmar tasu yasa ya fara ball da amarya, daga karshe ya kwance wannan shagiyar tattauran belt É—in nasu, dukanta ya fara yi tamkar wanda aka saukarwa wahayin duka. Wani irin gigita Ummie ta yi, tsoronta kada ya yi kisan kai. Da sauri ta ce. "Jamilu dan ALLAH ku kama mun shi".

Wanda aka kira da Jamilu ne ya ce. "Aunty Ummie kina gani soja ne fa ba police ba, gaskiya ni ban shirya mutuwa ba"...... Da sauri na jefensa ya ce. "Kai ma kenan da kake matsayin abokin É—an banga, mu kuma mu ce me? Ai kawai sai dai mu ce ALLAH ya jikan amarya idan ta mutu, dama ta ishemu a layin nan".

Kuka hawaye bibbiyu Ummie take yi, da kyar ta iya cewa. "Ku kama shi ba zai yi maku komai ba, kanina ne, dan ALLAH ku dakatar da shi"...... Ai ina dik cikinsu babu wanda ya motsa bare su yi yunkurin kama shi...... Dukan ALLAH tsine uwar mai karya Zaynish ya yi wa amarya, farfashe mata jiki ta ko'ina
, har sai da yaga ta daina motsi, sannan ne ya dakata yana cigaba da huci.

A fusace ya juyo da kallonsa a kan Ummie, haba ai a miliyan su Jamilu suka yanka kofar gida, sun ga zaki ya juyo, ka ji gudun karti wasu ta saman gini suka dira waje. Ita kanta Ummie kaÉ—an ya hana ta saki fitsari a in da take tsaye, ba dan tasan ciki É—aya suka kwanta ba, ko mai wuya ba zai cutar da ita ba da wlh babu abin da zai tsayar da ita itama, tuni zata gudu, amma ta daure ta tsaya.

Dimfarota ya yi tamkar wani mayinwacin zaki, a gabanta ya tsaya, with harsh voice ya ce. "Dama irin zaman da kike yi a gidan nan kenan? Meyasa baki sanar dani ba? Ina Faisal É—in yake? Sai ya faÉ—a mun idan jaka aka bashi ko ance mashi baki da gata ne!". Tashin sense, yau babu batun Yaya Faisal, Faisal kai tsaye, ba shakka da comrade Faisal na nan yau da shi ma ya gane ALLAH da girma yake.

Wani irin kerma da jikinta yake yi ne yasa ta gagara iya rike kanta, kasa ta durkushe tana cigaba da kallonsa har cikin ido, ta gagara bashi amsa. Tsawa ya daka mata da karfi wajen cewa. "Wacece wannan? Kuma ina Faisal É—in na ce? Sai sun faÉ—a mun a gidan uban waye kika bi maza? Idan basu faÉ—a mun sun bani shaida ba billahil lazi sai na lahira ya fisu jin daÉ—i".

Hannu bibbiyu tasa ta dafe kirjinta dake barazanar tarwatsewa, still kallonsa take yi ta gagara yin magana, allurar tasa ta motsa, baya iya fahimtar a wani hali take ciki bare ya sassauta mata murya, sai ma tsawa da ya sake daka mata tamkar zai kai mata duka, daga karshe ma yasa hannu ya miƙar da ita tsaye, yana cigaba da huci ya ce ta lissafa mashi masu ce mata tana bin baza, da alama wannan kalma ta fi komai ƙona mashi rai. Har lokacin baiwar ALLAH ta gagara yin magana.

Jama'a sun cika kofar gidan dam, amma kowa yana tsoron shigowa, wasu matasa ma aka samu suka kira Æ´an sanda. Mota biyu Æ´an sanda suka zo, take jiniya ya karaÉ—e umguwar, zaku ce yaki ake yi, jama'a an yi cirko-cirko.

Ƴan sanda biyar ne suka diro ƙasa daga bayan motocinsu, da farko sun tsaya a waje, sai su Jamilu suka faɗa masu ai kisan kai za'ayi a cikin gidan, hakan yasa suka danno kai ciki da gudun gaske, a lokacin shi kuma yana tsaye gaban Ummie ya titseyeta kan lallai ta faɗi masu mata ƙazafin zina, yau sai sun bashi hujja ko kuma dik su ci ubansu ne, ba zai ɗauki nonsense ba, yana matsayin position 3 a bar 2 ɗin za'a kawowa rainin wayau? Tab!.

Da gudu Æ´an sandan suka kewayesa suna faÉ—in ya natsu ko su harbesa har da É—aga bindigu su nunnuna shi. Nan fa su Jamilu suka dawo cikin gidan dan ganin gulma, da a basu kabari gara su bayar.

Ai a miliyan Ummie ta ware, sai kuma ta fara ƙoƙarin kare Zaynish ɗin, muryanta na rawa a fara ƙoƙarin cewa ƴan sandan su yi hakuri su je rigimace ta cikin gida. Bata kai ga yin magana bama wani ɗan sanda ya ce. "Madam bai yi maki komai ba ko?"........ Da kyar ta iya ƙoƙarin buɗe baki zata yi magana, amma ta gagara saboda rawar da jikinta yake yi.

Shi kuwa wani irin juyowa ya yi tamkar bujumin zaki, dikka Æ´an sandan sai da gabansu ya faÉ—i, baya suka É—an ja suna faÉ—in kada ya motsa. Kallon tsab ya yi masu kafin ya ce. "Your gun down!". A sigar bada umarni ya yi maganar, dan ya ga dik ya fi Æ´an sandan rank, dikkansu constables ne, ko soja dake bar one ya fisu rank bare shi da yake na uku a bar 2, ai ya wuci waÉ—an nan.

Jin yadda ya yi magana cikin bada umarni in a harsh way ne yasa suka ɗan ja baya, sun sha jinin jikinsu, slowly suka yi ƙasa da bindigunsu kamar yadda ya umarta. Ganin basu yi gardama ba sun yi biyayya ne yasa ya ɗan sauko ya yi masu bayanin waye shi, da sun yi gardama lallai da sun ɗanɗani karfin dukan hannun horon Azure yau, dan wlh yadda yake jin kansa tsab zai iya dukan zaratan maza 20 ko sama da haka, shi fa abokin balai ma yake nema yanzu ko zai sosa hannunsa dake mashi ƙaiƙayi, wai baku ga Vash a gida yana can yana ta faɗa da neman masifa bane? Ai haka suke bayan horo, dik su rikiɗe su zama wasu zakuna.

Ba karamin girgiza Æ´an sandan suka yi ba jin waye shi, sannan ya ce masu zasu iya tafiya babu ruwansu da case É—in nan. Sai a lokacin Ummie ta ce. "Ku yi hakuri kanina ne, faÉ—ar gida ne, ba wani abin zai mun ba". Tana magana dai idanunta a kansa sosai.
Chapter 64 · 0% Book details