← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 227

Sashe 72

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shirinsu na biyu shi ne, mind control & neuro weaponry, fasahar sarrafa hankalin mutane, a baya ba na ce za'a sace bayananku ba? Idan aka gama sacewa sai a fara project kan yadda za'a fara sarrafa hankulan mutane, za'a fara sarrafa mutum daga nesa ta hanyar microwave, EMF, ko chip a kwakwalwa, sauya maku tunani, saka tsoro ko ƙiyayya cikin mutane dan ɗora su akan tafarki ba daidai ba, ku yi ta tsanar juna kuna kashe juna, kuma ko ya za'ayi maku bayani ba zaku fahimci kowa ba, dan abin da aka cusawa kwakwalwarku kenan ku tsani ƴan uwanku, ku ta kisa babu gaira babu dalili, ba zaku taɓa sanin cewa ana amfani da ƙwaƙwalwarku ake cusa maku tsanar juna da son kashe mutane ba, ku dai gaku nan ne kawai zaku ta kisa, kuna sace ƴan uwanku, babu tausayi babu imani!.

Project ɗinsu na uku shi ne, kashe hanyar abinci, bayar da abinci da ruwa da magani marasa kyau a ɓoye, nan gaba kaɗan aiki zai yanke, makarantu babu, asibiti ba za'a ɗauki ma'aikata ba, babu aikin yi dai a taƙaice, hakan zai sa al'umma su koma kan harkar noma da kiwo, dole su koma sana'ar hannu, shiyasa WORLD SYSTEM ta fara kashe ɓangaren sana'ar hannun ba tare da kowa ya sani ba, zasu baku iri mai gurɓata ƙasar noma da muhalli su ce ya fi kyau ku shuka, da zarar kun fara shukasa shikenan ya kashe naku irin, ko kun shuka naku ba zai fito ba, a lokacin da zasu fito da addininsu guda ɗaya wa duniya zasu ce ku yi imani da shi ko su hanaku abincin nomawa, dama irin da kuke shukawa nasu waye ne? Ko ku yi masu biyayya ko yunwa ta kasheku! Baku da mafita, kuma ga shi su nasu irin bashi da ƴaƴa bare idan kun shuka ku sake shukawa, sau ɗaya zaku shuka, idan zaku sake wani sai dai ku saya daga wajensu. In banda munafurci me na kashe ƴaƴan irin nasu idan ba wani munafurci suka shirya maku ba?.

Makiyaya ma ba'a barku a baya ba, yanzu haka WOLRD SYSTEM tana ƙoƙarin kirkirar namar da za'a dinga haɗawa da technology pmh, zasu ce maku wannan nama yafi, zasu yaudareku ku karɓesa, zasu yi maku saukinsa, ku kuma zaku so banza, daga nan ku zubar da batun kiwata naku dabbobin, zasu rabaku da dabobinku ta hanyar kashe wasu, su ƙone wasu, su sace wasu, daga karshe su hanaku namansu da suke sayar maku a sauki da aka kirkiresa da technology ne ba namar da ALLAH ya bamu ba, dole idan kuna son nama ku yi biyayya a garesu. Wannan abu bata shafi musulmi ko kirista ba, mai kuɗi ko talaka, zaku sha mamaki a lokacin da masu kuɗin da kansu zasu fara nadamar bautawa waɗan can tsinannun, dan kwantan ɓauna suke yi masu a yanzu, babu wanda zai iya gane hakan.

To abu na gaba shi ne, geoengineering, gine-ginen masana'antu dake kwanto ɓaraka wa duniya bakiɗaya, zasu yi gwanjo na jirage da ke fitar da hayaki, zasu kirkirosu ne su sayar da su a arha, jiragen su yawaita, a daina hawa motoci sosai, amma abin da baku sani ba shi ne waɗan nan jirage da zarar sun tashi sama canza yanayin sama suke yi, suna bada chemtrails a sama dan canza yanayi, wannan yanayi shi zai ƙirƙiro fari, ambaliya, da kuma girgizar ƙasa masu girma a jere a jere, wannan fasaha ce ta cikin geo weaponry, ta haka ruwa zai ɗauke a yankuna, koguna su ƙafe, rashin ruwa rashin abinci, dik abin da kuke zato ya wuce nan........ My people a koda yaushe, ko bana raye idan kun tina da Princess Teema or Star Lady ku mun addu'a, sannan ina rokon da ku tayani addu'ar samun damar kammala rubuta wannan littafi.

Aryan na kammala karanta wannan bayanai Lion ya sake turo mashi wasu kamar haka. A dik cikin ƙasashen dake duniya AVARIS ce kasar da ta fi cancanta a garesu su fara aiwatar da wannan project ɗin, kasar tana da dik abin da suke buƙata, shiyasa suka sanyawa ƙasar ido, fitinar yau daban ta gobe daban, kuma abin mamakin shi ne manya masu gudanar da wannan tsari cikin barisa da hangen nesan mafiya yawa daga cikinsu ƴan Avaris ɗin ne, saboda ƙasa ce dake da tarin ƴan baiwa, suke basu tsari da abin da ya dace. Yanzu dole mu fara aiki a kan Avaris kafin mu cinwa WORLD SYSTEM.

Ɗago kai Aryan ya yi bayan ya kammala karanta wannan jawabi, sai ya ce. "Bro i saw one message this morning cewa an samu sabbin ƴan ta'adda da suka fito a kasar Avaris two days ago, ƴan ta'adda ne masu haɗarin da suka fi waɗan da suke cikin ƙasar a yanzu". Ya yi magana dikkansu shi da guru kallonsu a kan Lion suna jiran jin me zai ce, ni kaina ina jiran jin me Lion zai ce, dan nasan zancensa gaskiya ce zai faɗa, fasa kwai zai yi.

STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥

ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️
🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥

PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.

https://www.facebook.com/share/g/1EUXbqsDjP

STEP 1🔥

2025-11-21.🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E_____________20 & 21

Lion bai yi magana ba for almost 5 mins, sannan yai masu dropping messages na bayanai a computers É—insu. Sun san bayayin dogon magana, dikkansu basa tsawaita magana, amma na Lion and guru is worst, magana ta minti É—aya ba zasu iya yin bayani ba, sun gwammaci zaman typing su tura ba magana ba, shi Champion idan ta kama yana daurewa ya yi magana har na mintuna biyu.

Already sun saba dama dik abin da suka tambaya a rubuce yake turo masu amsa, suma a rubuce suke tura tambaya, sai basu wani damu ba, a natse suka buÉ—e message É—in kamar haka.

"Kun taɓa ganin yadda ƴan ta'adda suke fitowa dan kansu kawai ne? Ƴan ta'adda! Wasu jama'a ce da ake kirkirarsu musamman dan a fitinawa al'umma, kun taɓa tambayar kanku ina iyaye da ƴan uwan waɗan nan ƴan ta'adda? Kun taɓa tambayar kanku meyasa ƴan ta'adda suke da horo kan sanin makamai tamkar yadda sojoji suka sani? Za'ayi musayan wuta da ƴan ta'adda da sojoji, idan bullet ɗinsu ya kare a ƙasa da minti ɗaya suke sake sanya bullets a bindigunsu tamkar yadda aka horar da sojoji sanya bullets a bindingu cikin gaggawa, kun taɓa tambayar kanku ya aka yi suka iya dikka wannan? Ko dai a kullum kuna rigingimu tsakaninku da ƴan uwan da kuke tare da su cewa sune ke kasheku?".

Wani dogon note ya sake tura masu kamar haka a kasan wannan. "Terrorists! Kalma ce wacce aka kirkira, ƴar ta'addan dake Avaris waɗan da ake ta ikirarin sun addabi al'umma dikkansu kauyawa ne, dakikai ne da basu taɓa shiga class ba, ya aka yi suka iya karatun sanin makamai karatun da ya fi kowanne wahala? Sanin ita kanta bindiga ba karamin wahala bace, ya aka yi suka san dikka wannan? Ya aka yi suke da bindigun da suka fi na sojijin Avaris karfi da sabonta? Ta ina suke samo makamai masu karfi da kayan aiki tamkar jami'ai? Sun fi wasu jami'an ma kayan aiki in gantattu! Why?"

Amsa, a bayan kowani ɗan ta'adda ko ɓarawon daji akwai manyan dake bashi umarni kuma dake koya mashi aikin ta'addanci, ƙalilan ne daga cikin ƴan ta'addan suka fito daga kasar Avaris ɗin, kalilan ɗin kuma jahilan ciki aka kwasa game da yi masu karya da sunan jahadi suke yi wa musulunci, da rashin iliminsu aka yi amfani wajen sanyasu aikata abin da suke yi! Amma ainahin ƴan ta'addan idanu baya ganinsu, mutane ne da aka kirkiresu, tsawon shekaru aka horasu, mutane ne da basu da wani dangi bare su san daɗi dangi har su ji tausayi, basu da iyaye, su kawai an kirkiresu ne saboda taaddaci da kashewa, shiyasa ba zasu ji tausayin kowa ba, ba zaku taɓa gane kan wannan rigima a yanzu ba, sai bincike ya natsa damu cikin WORLD SYSTEM komai ya yi nisa zaku gane mecece ainahin ta'addanci, su waye ainahin ƴan ta'addan da ake dangatawa da musulmai alhalin basu ma da addini kwata-kwata, dik wanda yake matsayin member na wannan taaddancin bashi da addini wlh! Ko kiristoci na kwarai basa kisa haka ɗai, saboda sun karanta Annabi Isa ya haramta!.

Tin da suka gama karantawa suka natsu tsit suna nazartar kalaman Lion, dik abin da ya faɗa gaskiya ce, ba yadda za'ayi ace rana tsaka ƴan ta'adda su bayyana a waje, su kori jama'a a kauyuka su kwacesa su zauna, lallai tsawon shekaru ake ɗauka wajen horasu a kan hakan, tamkar yadda ake hora sojoji, idan an gama horasu sai su bayyana, ba ƴan ƙasar Avaris bane, bakin haure ne, wlh ainahin ƴan ta'addan ba ƴan kasar bane! Suna amfani da ƴan ƙasar ƙalilan daga cikin jahilan da sukaki karatu ne, sai su fake a bayansu suna taddancin, ƴan kasan da ake yi wa kallon ƴan ta'adda lallai karnukan farautar jiga-jigan dake laɓe a bayansu ne, manyan basu fitowa fili su yi aiki kai tsaye ne saboda gudun aga banbancin launin fata da sauyin harshe, shiyasa suna gefe suna koyawa karnukan farautar tasu ɓarna, ban da haka dakikin da bai je makaranta ba yaushe yake iya magana da correct English? Baku taɓa jin ƴan ta'addan suna turanci ba ko? To iyayen gidansu dake koya masu harbi da bindiga da sauransu turanci kawai suka iya! Dole su koyi turanci na magana yau da kullum.

(Can naga wani É—an ta'adda a media yana video yana cewa we have a lot of informance everywhere, I said eyeee this guy hear English well-well, he pass me da na yi FGC makarantar da ba'a magana da kowacce yare a cikinta sai turanci, ashe ni dik shirme na iya, ga wani a kwana can ya kware ba tare da zaman class ba. ALLAH kai mana kyakkyawan karshe, ba lallai a yanzu ku gane in da na dosa ba, saboda tushe nake son É—auko maku, but keep reading, zaku gane sosai a gaba!)
Chapter 72 · 0% Book details