← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 227

Sashe 15

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

To a haka dai suka rayu har Ummie ta zama budurwa. Da yake suna da balain kyau kamar Æ´aÆ´an larabawa hakan yasa samari suka fara tururwar zuwa neman aurenta. A lokacin bata yarda ta kula kowa ba, ta cigaba da karatun islamiyarta har ta zama Ameera a islamiyar tasu, malamin ya É—auketa tana karantarwa a wajen dik wata yana biyanta kamar 5k a kuÉ—in Naija. Da wannan 5k É—in take amfani ta haÉ—a da É—an aikatau na mutane da wanki a gida da takewa mutane, ta haÉ—a kuÉ—in ta sanya Zaynash makarantar boko dake É—an babban gari kusa da su, ta ce ya yi karatu zai taimaka masu a rayuwa tin da shi namiji ne.

Zaynash yana primary 4 a school uncle ɗinsu kanin babansu ya zo garin ganin gida bayan tsawon shekaru. Ya jajanta halin da suke ciki, ya kuma yaba da ƙoƙari irin na Ummie, daga nan ya ce zai tafi da su birni su yi rayuwa a can. Bai yi ƙasa a gwiwa wajen ɗaukarsu su koma can ba, suna zuwa can kuma wani fitina ta tashi ta tsaya na matarsa, ta ce waɗan nan ƴan kauye ba za su zauna mata a gida ba, an yi juyin duniyar nan taki yarda, a na haka kakansu ta faɗi ta rasu, dalilin kenan da yasa matar tasa ta hakura su Ummie suka zauna, imani ya ɗan shigeta ganin mutuwar tsohuwar a gabanta.

Su Ummie sun yi zaman shekara ɗaya a gidan amma cikin rashin daɗi da takura, ga kuntatawa da Auntyn tasu matar kawun nasu take masu, dik ta sallami ƴan aikinta su Ummie suka zama masu mata bauta, sun ci kwakwa matuƙa kafin kanin Auntyn tasu da ya dawo daga bautar ƙasa ya ga Ummie ya ce shi fa ya yi mata, yaga tsantsar kyau, Auntyn tasu ta so hana auren amma ALLAH ya yi sai anyi, Ummie ta auri wannan bawan ALLAH. To shi ma dai ba wani kuɗi yake da shi ba, yawon neman aiki yake yi, ɗan makaranta ne.

A lokacin Zaynash ya kammala primary, dan zuwansa babban gari ya cigaba da karatu, uncle ɗinsu ne yake biya mashi kuɗin makaranta. In taƙaice maku labari har yanzu Ummie tana cikin talauci da kunci ga takurar dangin miji musamman wannan Aunty tasu, dik ta shafe mata bakin fenti a family shi ne yasa basa sonta ko kaɗa. A lokacin da Zaynash ya kammala secondary school sai ya ce shi makarantar sojoji zai tafi, ya zaɓi hakan ne kuma bisa ra'ayin Ummie, tana son ya zama babban soja dan kawo karshen ta'addancin dake faruwa, saboda ƴan bindiga ne suka kashe iyayensu, suka shiga har gida suka yi masu rashin mutunci, sannan suka yi garkuwa da su, da ba kuɗin fansa shi ne suka kashesu suka baiwa karnika gawarwakinsu.

In kara takaice maku yanzu auren Ummie da mijinta shekara biyu kenan, bata taɓa haihuwa ba, hakan yasa dangin mijin suka kara sakota a gaba, zagi da cin mutunci kala-kala suke yi mata, kannensa da Auntynsu matar uncle ɗinsu sun hanata shan iska, da ta yi magana ace juya bata haihuwa. Dalilin kenan da yasa Zaynash ya kara mai da hankali dan ya zama babban soja ya ga ya fitar da Ummie daga cikin kuncin da take a ciki, yana balain son ƴar uwarsa kamar yadda take mutuwar son shi. Dama da zai zo GIDA SOJA uncle ɗinsa ne ya yi mashi komai, amma sai da ya sayar da gidansu na kauye da konarsu, sannan ya cika ya kawosa nan, dan AZURE ba dik kai ba, makaranta ce na ɗan wane da wane, uncle ɗinsu ya kashe makudan kuɗaɗɗe kafin Zaynash ya samu wannan makaranta, and da kyar Auntynsu ta bari uncle ɗin nasu ya yi mashi komai ɗin, ita kuma Ummie kuɗi kimanin 50k a kuɗin Naija ta bashi, wannan dalilin yasa ya baya son kawo mata abin da zai ɗaga mata hankali, ya yi alkawarin daurewa dan ya ga ya cinwa narasa. Amma fa bai tsammaci haka GIDAN SOJA yake da wahalar gaske ba. A TAKAICE KENAN RAYUWAR ZAYNASH, DAN HAKA DIK YADDA ZAKU GA YANA GASA DA SAURAN YARA DAN YA ZO NA FARKO KADA KU GA LAIFINSA, BURINSA NE HAKAN DAN TSAMO ƳAR UWARSA DAGA WAHALA, SHIYASA YA DAGE!!.

-------------------------🔥

Ya jima sosai zaune a wajen kafin ya miƙe tare da kashe wayar tasa, sannan ya dawo cikin ɗakin. Still dai idanun Leo biyu yana karance-karance da nazartan makaman da aka koyar da su yau. Ko ɗago kai bai yi ya kalli Zaynash ba, yana cigaba da abin da yake yi. Shi kuma Zaynash sai kallonsa yake yi har ya isa saman bed ɗinsa, ya kwanta tare da jawo bargo zuciyansa cike da tinanin yadda zai rayu a GIDAN SOJA. Ya so ya ɗan yi karatun abin da aka koya masu ɗazun kafin ya yi barci, sai dai ina, gajiyar wahalar da suka yi tasa barci ta yi awon gaba da shi. Shi kuwa Leo ya yi karatu har 1 na dare, kafin ya miƙe ya ɗauro alwala, ya zo ya yi nafilfilinsa, daga karshe ya rufe da shafa'i da witiri kafin ya kwanta dan ɗan rintsawa shi ma!.

4:30 ASUBA.

Wannan busa ta jiya ita ta tada su, sun sha mamakin ganin yau ma Leo idanunsa biyu yana zaune a tsakiyar gado yana duba waya. Tambayar kansu suka shiga yi wai shi wannan baya barci ne?. Basu san yanayi ba, amma tin 4 yake farkawa, kuma sai 1 yake kwanciya, barcin 3h yake yi.

Da wani irin ciwon jiki Vash ya farka, ga in da aka zane shi jiya ya yi ruÉ—u-ruÉ—u ya kumbura, idaninsa jajir, jikinsa dik babu kwari. Da kyar ma ya iya tashi, intently ya diro kasan bed É—insa, cikin wani irin matsanancin hali ya nufi toilet ba tare da ya yi wa kowa magana ba, shi kaÉ—ai ya san me yake ji.

Dirowa ƙasa Zaysh ya yi ya nufi toilet shi ma, jikinsa dik tai tsami. Noor kam komawa ya yi ya kwanta, har da kukan shi jikinsa ciwo yake yi mashi, dan haka wlh ba zai iya tashi ba. Wanka su Zaysh suka yi tare da fitowa suka shirya. Leo already ya yi wanka ya shirya, dan tim 4 ya tashi, yanzu kuma 4:30, wannan 30 mins sun ɗaukesa shiryawa.

Bayan sun kammala shiri ne Vash ya ce bari ya tashi Noor. Zaysh dake ƙoƙarin ɗaure jakansa ya ce. "Ka kyalesa ba, zai tashi da kansa ne"....... "No brother, kasan halinsa, bari in tashesa kada a mashi duka"........ Cigaba da abin da yake yi Zaysh yai bai sake yin magana ba.

Slowly Leo yai switch off na wayarsa tare da ajiyeta a saman bed ɗin, ya ɗauko littafin karatun makamansa na jiya ya diro ƙasa da shi, jakansa ya buɗe tare da mai da book ɗin, sannan ya shinfiɗa bed ɗinsa da kyau, ya naɗe bargonsa, ya ɗauko army p-cap sabuwa daga cikin jakan ya sanya a kansa, daga nan ya nufi waje ba tare da ya kalli in da suke ba.

Da kallo suka bishi har ya fita. Vash ya ce. "Awww ashe fita ta kofa yake yi, all though ɓacewa yake yi"........ Harararsa Zaysh yai tare da cewa. "Baka da hankali, dama fita yake yi mana, wani hanya yake bi shi ne abin mamakin". Ya kai karshe tare da karisa ɗaure jakan nasa, ya ciro biscuit guda ɗaya, sannan ya nufi waje.

"Wait for me". Vash ya faɗa yana nufar bed na Noor. "Yi sauri". Cewar Zaysh da ya tsaya ta waje a bakin door...... Yana tsaye a wajen sai ga makwaɓcinsu Unays ya dawo zai shiga cikin ɗaki da gudunsa. Binsa da kallo sosai ya yi, a nan ya fahimci dik yadda aka yi daga wajen motsa jiki yake, watau dan ya zo na farko a daren ma baya barci? Fita yake hora kansa? Tab lallai ya fisu zalama wannan, kai kai kai, ya zo da sabon salo fa.

Shiru ya yi yana tinani anya shi ma ba zai fara hora kansa ba kuwa? Da daddare idan kowa yai barci. A daidai lokacin Vash ya dafasa tare da cewa. "Let's go, Noor yaki tashi"....... "I already told you that ba zai tashi ba, just leave him, bodynsa zai faÉ—a mashi".

Vash yana da tausayi ne sosai, sai ya É—an yi jim, fuska da alamar tausayi ya ce. "But bai kamata mu kyalesa ba ai"..,........ "Saboda kai ne ubansa?". Zaysh ya faÉ—a. Da sauri Vash ya girgiza kai. "No, amma a nan we're brothers, mun zama Æ´an uwa tin da babu iyaye".

Gaba Zaysh ya yi tare da cewa. "Ai sai ka tsaya kada ka tafi tin da Noor bai farka ba, kai waye ma ya ce maka a gidan soja lokacin horo ana taimako ne? Ko da yake kai sabon zuwa ne, bari ka fara gogewa a nan ne ina ga in ka taimaki wani aka baka horon da sai ka kwanci mutuwa zaka gane me nike nufi". Yana tafiya yake wannan magana. Da sauri Vash ya rufa mashi baya zuciyansa cike da tausayin Noor.

Kai tsaye masallaci suka nufa, a lokacin har an kira sallah, ana shirin tada kabbara ma.
Bayan sun yi sallah sun fito, kowannensu sai miƙa yake yi, saboda wahalar da aka sha jiya, jiki dik tsami, daga masu cewa wash, sai masu cewa ash, sai kuma masu cewa bayana, abinku da farin shiga.

A gabansu Captain ya tsaya cikin tsantsar jarumta da nuna dakan jiya ne shi, cikin kakkaifar murya ya ce. "1, 2, 3 start!" Cikin É—aga murya.
Chapter 15 · 0% Book details