← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 188 OF 227

Sashe 188

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaune ya isko sister Maya a saman side sofa, tana karanta littafin nan na ɗazun, while sister Zinta na zaune a gefen bed sanye da rigar ɗazun, suna hira jefi-jefi. Ganinsa yasa sister Maya miƙewa tana faɗin. "Zan je cikin asibiti in duba babys ɗinmu, sai kin zo".

Zuwa ta yi ya raɓa shi ta fice. Tsayawa a tsakiyar ɗakin ya yi game da zubawa sister Zinta idanu. Da yake suna da kunya na jinin gado sai ta gagara iya ɗagowa ta kallesa, ta yi ƙasa da kai tana ɗan ɓoye fuska. Gentle ya tako in da take. A gabanta ya ɗan tsugunna, kyakyawawan hannayenta ya riko, ya zubawa face ɗinta idanu.

"Welcome sir". Ta faɗa can kasa...... "Are you okey now?"....... Kai ta jinjina mashi alamar e......... "Came on". Ya faɗa tare da ɗan miƙewa ya rungumeta yana ɗan shafa bayanta, hannayenta tasa ta yi hugging ɗinsa tightly. A tare suka sauke ajiyar zuciya, ya ɗan saketa tare da cewa. "Let me bath"....... "Should I help you?". Ta faɗa can ƙasa. Kai ya ɗan girgiza. "Ki huta ina zuwa".

Daga nan ya fara rage kayan jikinsa, yana yi yana ƙura mata ido, ita kuwa ta yi ƙasa da kai. Cire kayan ya yi, ya rage daga shi sai shorts, cikin toilet ya nufa. Nisawa ta yi tare da kwanciya tana jin sabon sonsa na shigarta.

----------- silent.

After some hours, zaune yake a saman bed ɗinsu, sanye da pjs ash color a jikinsa, ya tasa laptop a gabansa, while sister Zinta na kwance a gefensa, ta tada kai da cinyarsa, shi kuwa yana ta aiki, ya mata girki da kansa, ta ci ta ƙoshi, ya mata wanka da kansa, suka sanya kaya iri ɗaya, ya kwantar da ita, yana shafa kanta yana aikinsa har barci ya ɗauketa, watau wani irin so yake yi wa Zinta na wuce misali, ko motsawa ta yi har cikin ransa yake ji.

Video call ya danna a laptop É—in nasa, ringing ya fara yi, jim kaÉ—an aka É—auka. Wani kyakkyawan fuska ne ya bayyana a gaban screen É—in, kyakkyawan mutum ne, matashi ne da ba zai wuci 25 years ba, suna mugun kama da Dr James sosai, kamar an tsaga kara.

"Good evening bro". Dr James ya faɗa. "Evening ƙanina, ya aiki?". ............ Kai jama'a ƙaninsa kuma? Wannan matashin yana nufin ya fi Dr James shekaru? How? Wai kun gansa kuwa? Ɗan yaro fa, amma wai shi ne yayan Dr James? Abin da mamaki.

"Cool bro, ya naku aikin?"....…. "Muna da kai ai dole komai ya tafi daidai". Bro ya faɗa..... Kai ya ɗan jinjina yana murmushi kaɗan-kaɗan........ "Ya batun waɗan can kwarin?". Brother ya tambaya..... "They're ready, ko yanzu kuke da buƙata zaku samesu, amma ni bro ina son sanin me World system zata yi da waɗan nan kwari? Me zaku yi da shi?".

Siririn one side smiling brother ya saki kafin ya ce. "Wata ƙasa zamu ladabtar, sun kawo mana taurin kai da tsaurin ido ne, shiyasa muke san yi masu azaba ta wannan hanya, mu sakar masu kwarin da zasu cijesu suna sanya masu guba a jiki"...... "To shi kuma NEXAPOS-31 fa? Sai yaushe zaku yi amfani da ita?"........ Shiru brother ya ɗan yi. "A sabuwar gwamnati, sai gab zaɓe, amma kasan bamu da tabbas, idan aka ɓata mana rai a yau muna iya sakinta wa duniya, kawai dai mun fi son sai an yi zaɓene, idan aka samu sabuwar gwamnatin sai mu kiɗima hankalin duniya!".

"To amma bro kwanaki ka ce mun kuna shirin canza yanayin duniya bakiɗaya, kuna shirin extreme climate crisis, kun saka na kirkiro maku kwayoyin cutar da zasu sanya mutane mugun zazzaɓi mai tsananin karfi da zafi, kuma mun fitar maku da kwayar cutar, amma baka sake magana a kai ba".

Kai brother ya ɗan jinjina. "Already wannan magani naka ya isha ga al'ummar duniya, sai dai yana cikin asibitoci musamman asibitocin gwamnati, ba mun yi amfani da kwali da kalar maganin da gwamnati take rabawa kyauta ne ai, ka kwashe asalin ingantattun magungunar, ka shigar da namu, kasan mutane da son banza, tin da an ce na kyauta ne zasu dinga karɓa suna sha, basu san shawowa kansu suke yi ba, to tuni har maganin ya fara bazuwa".

One side smile Dr James ya saki kafin ya ce. "Naga wasu likitocin sayar da maganin kyautar ma suke yi ai suna karɓar kuɗaɗe". ......... "Basu san marasa kyau ɗin bane ai, sun zage su wai zasu cuci mutane, gwamnati ta bada kyauta su kuma suna sayarwa". Brother ya faɗa.

"Business kan business ba". Dr James ya faɗa........ Nisawa brother ya yi kafin ya ce. "Mu samu damar canza yanayin duniya shi zai bamu damar yin abubuwa dayawa".....… Dr James ya ce. "Ni kam ya batun ambaliyar da kuke ƙoƙarin kirkirawa waɗan can manyan ƙasashe uku dake ƙoƙarin bijire maku ɗin ne? Ka ce zaku hasasa masu ambaliyar da zai haifar da rugujewar tattalin arziki, zaku fasa manyan dams a sirrance, bayan ambaliya zaku tsokani fararen ƙasar da ke ƙarƙashin ƙasa ku haifar masu da girgizan ƙasa, zaku yawaita ambaliya a duniya, kuma zaku yawaita girgizar kasa, a lokacin kuma ga fari, hakan zai sanya yunwa ya zautar da al'umma, ya batun wannan aiki?".

(ALLAH sarki wannan magana ta tina mun da ambaliyar Maiduguri, mutanen barno muna kara miƙo jaje, ALLAH ya jiƙan waɗan da suka rigamu gidan gaskiya.)

"Aikin yana nan, kasan mu yanzu matsalarmu shi ne mu san yadda zamu yi mu kashe aikin hannu a cikin al'umma, kasan nan gaba kaɗan zamu ƙwace kowani irin aiki daga hannun al'umma, za'a rasa aikin yi, talauci da taadanci zai ƙaru, idan aka rasa aikin yi dole ƴan zaman banza su ƙaru, hakan zai sanya matasa su faɗa harkar shaye-shaye da daba". Ya ɗan nisa tare da cigaba da cewa.

"Zamu iya kwace kowani irin aiki, yanzu muna shirin kashe karatun boko, baya ga shi zamu kashe kasuwanni ta hanyar kawo masu sauƙin tsaro, mu haɗasu da na'urar da zaka ajiye a shago ba sai mutum ya zauna maka ba, mutum zai iya damfararka amma naura ba damfara, hakan zai sanya su yarda da na'urorinmu sosai dan suna ganin sauƙi ne ya samu, daga nan kasuwannin za'a daina ɗaukar matasa zaman shago, a koma masuwancin media da naura, mu kirkiro robot masu dawo da sauran ayyuka a kasuwa, kaga mun kashe kasuwa, ɗan adam baya buƙatar aiki a cikinta".

Kai Dr James ya jinjina alamar haka ne. Cigaba brother ya yi da cewa. "Muna da hanyar kashe dik ayyukan mutane, asibitoci dik zamu kashe aikinsu, yanzu damuwarmu ɗaya ce, shi ne aikin hannu, musamman noma da kiwo, so gara noma yanzu mun ɗauko irin da zamu tarwatsa rayuwar nomarsu da shi, har ma wannan plan ɗin ya isa ga al'umma, to shi kuma kiwo shiyasa muka baka project na ƙirƙirar yadda zamu fara haɗa nama a lab dan mu kashe kiwo a duniya, dik wani aiki zamu kwacesa daga hannun al'umma, zamu azabtar dasu da yunwa ta yadda a lokacin da zamu fito da addinin da muke shiryawar nan dole al'umma su karɓeta, idan basu karɓeta ba yunwa ne zai kashesu".

Bari in ɗan yi maku karin haske. Suna da damar kashe dik ayyukan mutane, a nan gaba kaɗan dik wani aiki zai kwace daga hannun mutane, asibitoci zasu dawo na'urorin artificial intelligence ne zasuna aiki, kasuwanni ma haka, zasu rikita komai, kuma ba nan da nisa bane, gaba kaɗan ne zasu aikata hakan. Kun san meyasa suke dikka wannan? Suna son jigatar da al'ummar duniya ne, a yanzu ai basa iya juya duniya gabaɗaya, akwai ƙasashen da suka bijire masu, to wannan abin da suke shiryawa zai sanya ko'ina a duniya ya girgiza, idan yunwa ta yi yawa, a wannan lokacin da kowa yake neman mafita, zasu fito da wannan addini nasu guda ɗayan da suke son duniya ta koma binta, zasu ce ku karɓi wannan addini ku samu jin daɗi rayuwa ko kuma ku mutu da yunwa da wahala.

A lokacin wahala ta kai wahala, za'ayi ambaliya dayawa, fari da girgizan ƙasa, ga canjin yanayin sararin samaniya dake iya haifar da faɗuwar jiragen sama, ga cutar da 3D suke kirakiranwa duniya, jama'a basu da mafita a wannan lokaci, wuya zai sa su mance ALLAH, wasu zasu yi imani da wannan addini, yayin da wasu zasu ce ba zasu yarda ba ko zasu mutu.

Jama'a a wannan tafiya aikin hannu ne kawai WS ba zasu iya kwacewa mutane kai tsaye ba, wannan dole su lallaɓaku su sanya aikin hannunku ya zama yana karkashin sarrafarsu, ta yadda ko noma zaku yi dole ku nemi irin yin noma daga wajensu, ko nama zaku ci dole daga wajensu ne, suna son ganin sun mayar da komai naku karkashin ikonsu ta yadda zasu dinga binsu kuna rokonsu, su kuma su faɗa maku buƙatarsu, ko ku bi ko yunwa ta kasheku. To jama'a shawarata a gareku shi ne ku rike sa'naarku ta hannu, ba dan wani abu ba da na ce ku dakatar da karatu ku rike sana'arku domin ku samu saukin wannan yanayi da suke shirin jefa al'umma a ciki, kada ku yarda a sana'arku ta hannu a kawo maku wani abu da sunan cigaba ne ku karɓa ku yi amfani da ita, hmmmmm, kassaraku suke son yi, su damkeku a hannu gam, su samu damar mayar da duniya na bin addini guda ɗaya, a haka zasu cika burinsu na cure duniya su fitar mata da shugaba guda ɗaya da zai rinƙa juyata. Na kara baku shawarar ku rike sana'ar hannunku, ita kaɗai ce ba zasu iya kasheta ta sauƙi ba!.

-------------------

"Jinjina bro, aikinku yana kyau, na matsu in ga an saki NEXAPOX-31 É—in nan dan inga yadda zata yiwa duniya, na jima ban ji kukan jama'a ba, ina son in ga suna kuka har da na jini". A cewar Dr James.
Chapter 188 · 0% Book details