← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 213 OF 227

Sashe 213

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

KuÉ—in rigar ya je ya biya suka nufi waje, suna fita ya rungumo shoulder É—inta tare da rage tsawonsa, a dan kunnenta ya ce. "Yau fa kin yi kyau over, anya ba zan aureki kawai ba? Na fara jin gajiya a kan wannan shamakin dake tsakaninmu, gara in cire hijabin ta hanyar halatta abin"........ Da sauri ta É—ago kai, cike da farinciki ta ce. "Daddy ka aure É—in kawai, kada ka jira komai".

Dogon hancinta ya ja. "Kafin na yi aure dole akwai tsari, sai na bi wasu hanyoyi shiyasa, but lokaci kaÉ—an ne ya rage, and yanzu akwai very important abubuwa sosai dake taso mana"...... Yana tina tarzomar da zata tashi ne bayan bayyanar IRON FIST a cikin CRYSTAL PALACE, yasan duniya dik sai ta tsaya cak, akwai kura, wannan dalilin yasa ma bai fara batun auren ba, ga shi yana da tafiya a gabansa mai muhimmanci.

Turo baki ta ɗan yi ta zura hannunta ta baya ta zagayo da shi har ta wajen flat tummy ɗinsa. A haka suka sauƙo ƙasa. Shopping na ƙasa ya shiga da ita. Kaya sosai ya fara loda mata, bathrobe da sukai mata gajarta na gidan nan dik ya ɗauka mata masu tsawo, ya sai mata abayas sosai, dan yana son ta dinga rufe jikinta.

Ita ma zagewa ta yi sai shopping take yi, har da É—aukar breziya dozen biyu, gani take ta zama Æ´an'mata yanzu, musamman da ake ce mata in an ganta kamar mai 16 years, shikenan tana jin kanta ta kai can.

Suna tsaka da shopping suna hiran soyayyarsu ne wata mace siririya mai zubin taliyar bua tai masu hello. Kallo ɗaya Aryan yai mata ya ɗauke kai, ita kuwa Seraphina ta fara kallonta daga sama har ƙasa, gata ƴar siririya sai kuma ta ɗauko wasu karuwan kaya, jeans and top ta labka a jiki, ta tara gashin kai a tsakiya ta ɗaure, ta sako jelar gaba, idanunta dara-dara, to a ajiye maganar adawa a gefe kyakkyawar gaske ce sosai, fara tas da ita, sai dai bata da welcome bare kuma goodbye, a shafe take kamar namiji da zani, amma kyan fuska kam akwai shi sosai.

Ta kwamo wani uban high heel tamkar wacce ke shirin zuwa taɓa duniyar wata. Yarinyar irin classic lady ɗin nan da boko ya bugasu, wayayyu fiye da misalin nan, a shekaru zata iya kai 25 haka, a nan CRYSTAL PALACE ɗin take, ƴar wani tsohon ƙusa ne na siyasa a ƙasar, dukiya ta yi mubaya'a, suna haya a CP.

Seraphina baki abin magana, da ta kare mata kallo sai ta ce. "Wannan fa? Ke babu mirror a gidanku ne?"....... A tinanin yarinyar Seraphina sister ɗin Aryan ce ganinta ƴar karama, sai bata amsa mata ba, ta ɗan matsa dab da Aryan, cikin wani karuwan murya dake maƙale ta ce. "Hii handsome, wajenka na zo, one minute please".

Aikuwa nan Seraphina ta ce ba'a haifi mutum ba, da sauri ta matsa kusa da angon nata, ta tamke fuska kafin ta bi yarinyar da wani matsiyacin kallo. Aryan dai tamkar ba da shi aka yi magana ba, ya yi banza da yarinyar.

Seraphina dan ta gwadawa yarinyar ita ma A ce sai ta ce. "My gentle chaos mu tafi wajen lotion in zaɓa, daga nan ya isa mu wuce". A shagwaɓe ta faɗa tana riko hannunsa. Tsayar da kallonsa a kanta ya yi, ta marairace fuska tana turo baki.

"Kin fasa sayen vest ɗin ne?". Ya faɗa can ƙasa. Kai ya jinjina mashi. "Yanzu na fasa, sai wani lokaci, kawai ka zo mu tafi". Ta ƙara kankame hannunsa. Ɗan rungumo shoulder ɗinta ya yi game da cewa mu je. Zame jikinta ta yi daga nasa ta tsugunna a ƙasa, tamkar zata yi kuka ta ce. "Ni ka ɗaukeni".

Waist ɗinsa ya riko da hannayensa dikka biyu, ya sauke ajiyar zuciya kafin ya rage tsawonsa, ya ɗauketa cak tamkar ƴar baby, hannayenta tasa ta saƙalo wuyansa kafin ta kwantar da kanta a gefen lion chest ɗinsa. Wucewa da ita ya yi, sun zo dab zasu wuce yarinyar Seraphina ta fidda tongue ɗinta tai mata gwalo, Seraph ta ji haushin yadda yarinyar ta yi banza da ita ta nufi Aryan ne, ta zage sai ta mashi magana, shi ne ta gwada mata capacity ɗinta.

Ai tsaye yarinyar ta yi tana ganin ikon god, babyn daddy ta goge mata hadda gabaɗaya. Da suka je wajen lotion zai sauƙeta ƙasa ta ce ina bata san wannan ba, wai sai dai ya riketa ta zaɓi abin da take so, ta ƙara ƙanƙame shi game da kwantar da kanta luff sosai. Uhm soyayya ai dole ya yi abin da take so dan kada ranta ya ɓaci.

Ya kuwa biya mata, a haka ta karisa sauran shopping É—in, wai dan fa yarinyar ta ji haushi ne yasa ta ce kada ya sauketa, a haka zasu yi shopping, dik in da suka gifta yarinyar ta ganta kwance a kirjinsa. Kai Seraphina duniya, kishi da wanga É—iya ai balai ne, iya kirsa da kisisina.

Har da shafa arab hair É—in Aryan ta bayan wuyansa tana É—an turo baki. Shi kam bai kawo komai a ransa ba, kawai dan ya faranta mata yake yi. Bayan sun kammala shopping sai ya É—auketa suka yi bakin beach dake cikin CRYSTAL PALACE É—in, a lokacin dare ya fara yi, karfe 11 ta yi.

Suna parking a wajen sai ga kiran Lion. Picking ya yi game da karawa a kunne, shiru ya É—an yi yana sauraron Lion É—in, after like 20 second sai ya ce. "Kawai ku yi dinner É—in, sai can dare zan shigo".

BuÉ—e baki Seraphina ta yi zata yi magana ya yi gaggawar rufe mata da hannunsa yana É—an zare mata idanu. Kai ya jinjina kafin ya ce. "Zan kula". Daga haka ya ciro wayar ya katse. Zai É—auke hannunsa daga kan É—an bakin nata ta yi saurin kamawa ta sumbacesa kafin ta ce. "Daddy da waye kake waya?".

BuÉ—e kofar motar ya yi, ya fito ba tare da ya amsa mata ba, sai kuma ya ce. "Wait for me bari in maki oder abincin dare a wancan CRYSTAL RESTAURANT É—in". Bai jira amsarta ba ya wuce ya nufi wani haÉ—aÉ—É—en É—an karamin restaurant dake wajen.

Fitowa ita ma ta yi, ta tsaya a jikin motar game da takure jikinta waje guda, wani irin sanyi na bugata, akwai sanyi sosai.

Jikinta na rawa, ta so komawa cikin motar amma babu dama, dan tana fita motar ta rufe kanta, bata san yadda ake buɗeta ba. Unexpected idanunta suka sauƙa a kan beach na wajen, ya ALLAH, zazzare idanunta a kan ruwan ta yi, bata san lokacin da ta raba jikinta da jikin motar ba, da gudu ta karisa wajen tekun tana kallon fitilun dake wajen, ga hasken wata na haska ruwan.

Rufe idanu ta yi ta sake buÉ—ewa, a fili ta ce. "Wajen ya haÉ—u, yaushe zan samu cikar burina na keta cikin teku a jirgin ruwa in je kasar da rana take fara fitowa? Wayyo sea".

Lokaci guda wani iska mai sanyi ya busata, hakan yasa ta yi gaggawar takure jikinta waje guda, hannunta suka fara rawa, tana son kallon ruwan kuma tana son komawa wajen motar ta laɓe kada sanyi yai mata illah.

Shiru ta takure a wajen tana ganin haÉ—uwar ruwan. Unexpected daga bayanta ta ji an É—aura mata abu a saman shoulder, kamshin perfume É—insa yasa ta gane shi ne. Da sauri ta juyo ta faÉ—a jikinsa, ya rufeta da suit É—insa da ya cire, ya gyara mata da kyau, dama suit É—in ya É—aura mata a shoulder É—inta.

Zuro hannayenta ta bayansa ta yi, ta yi tighting ɗinsa sosai tana faɗin. "Daddy yaushe zaka ɗaukeni mu ratsa teku mu je kasar da rana yake fitowa ta cikin jirgin ruwa?"...... Can ƙasa ya ce. "Very soon, after our marriage". Ɗago kanta ta yi, suka ɗan zubawa juna ido, sai kuma ya rabata da jikinsa game da sanya mata suit ɗin nasa. Ya kama hannayenta suka nufi wajen haɗaɗɗun kujerun da aka tanada kusa da beach ɗin dan cin abinci.

A nan suka zauna saman kujerun dake kallon juna, ya zuba mata ido yana jin tamkar ya mallaketa ya gama, a daidai lokacin kuwa Abba na can suna plan da Ammie kan a cikin satin nan zai kawo ziyara gidansu Seraphina, Ammie ta bada goyon baya É—ari bisa É—ari saboda dama Seraphina ta shiga ranta.

Sai shagwaɓa take zuba mashi tana ƙarawa, shi kuwa yana ta biya mata, a wannan dare ya shirya masu abubuwa dayawa, dan har wajen CP zasu fita.

Ƙayattatun abinci aka kawo masu wajen, da kansa ya dinga ciyar da ita, sai santi take yi tana karawa, sai da ya cika mata ciki tab, sannan ya ci ɗan kaɗan, ya tashi ya kama hannunta suka nufi cikin mota, daga nan suka nufi ainahin main gate na CP ɗin, sai murna take yi yau zata fita waje, shi kuwa sai farinciki yake yi na ganin tana murna.

------------------------------🔥

D-------O--------L🔥

Around 1 na rana, bayan sun yi sallar azahar sun yi lunch, suka zauna Noor yana ɗaukar karatu wajen Leo, while Zaynish ya haɗa kayansa ya nufi bakin ruwa dan yin wankin kakinsa, ya ce ba zai iya baiwa ƙananan sojoji su yi mashi ba, saboda shi in mutum ne yai mashi wanki yana ganin baya fita, ya fi so ya yi da kansa.

Vash yana zaune a kan wani dutse yana shan mangoron da sojojinsu suka ciro a wata bishiya da ta nuna gwanin ban sha'awa.

A can kuwa, Arya da su Angelina suna É—aki, Manassa na zaune gefen mattress rike da drink a cup a hannunta tana sha, while Angelina na rike da laptop, yanzu ta mayar da hankali kan aiki sosai, saboda Zaysh baya É—aukar wasa.
Chapter 213 · 0% Book details