← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 135 OF 227

Sashe 135

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Muryan nasa ya daki zuciyanta matuƙa, sai ta tsinci kanta da murmusawa kafin ya buɗe baki ya sanya mata a ciki, siririn murmushin da ta ƙara mashi kyau ya yi kafin ya ce. "You're so cutie, jiya na kwana mafarkinki, can you be my girlfriend please?". Ya kai karshe tare da ɗaukar chocolate ɗaya yasa a bakinsa....... Ai gabaɗaya ya goge mata hadda, ya ALLAH, ya haɗu, ta ko'ina, ga iya zallar madarar soyayya, ga salo mai ɗaukar hankali da shagwaɓa, kalamai masu narka zuciya, ya rabb.

Miƙewa ya yi, bai jira amsarta ba, ya ɗan sunkuyo kanta kaɗan, tamkar zai yi kissing ɗinta, ta ɗago kai suka kurawa juna idanu, muryanta na rawa tana ɗan kyafta idanu ta ce. "Yeah, why not?".

Wani irin musulmin ajiyar zuciya ya sauke tare da sumbatar forehead ɗinta. "I love you". Ya furta tare da miƙewa, ya juya ya nufi chair ɗinsa, bayansa ta bi da kallo tana jin wani irin daɗi a cikin ranta. A daidai lokacin Aisha da Rimsha suka shigo. Saita natsuwarta ta yi tare da karisa fito da small chop ɗinta.

A chair ɗin da uncle ya miƙe a kai Aisha ta zauna, ita kuma Rimsha ta jawo chair ɗinta zuwa kusa da Seraphina, ta hau fito da kular abincinta, tin bata gama fitarwa ba kamshi ya buɗe ko'ina a cikin class ɗin, mandi rice ce da ya ji nama da kayan kamshi, sai drinks da Ammie ta haɗa mata, dama ta ce a sanya mata a babban kula saboda tare da Seraphina zasu ci.

A natse suka fara cin abincin, Uncle ya zubawa É—an bakinta idanu tana kara narka mashi zuciya, ya mace a kaunarta. Ita ma dik bayan minti É—aya sai ta É—ago ya saci kallonsa, ya ALLAH, dik ya narka zuciyar baby cherry É—in daddy.

Bayan sun kammala cin abincin suka tattare komai, suka gyara komai, Rimsha na É—agowa ta ga Uncle na kallonsu, cike da kunya ta ce. "Sorry Uncle bamu ce ka zo mu ci ba"....... One side smilling ya saki tare da cewa. "Thank you dear".

Dik kunya ya kamasu basu ce mashi ya zo su ci ba, a haka aka dawo class suka cigaba da karatu. 1:30 daidai suka tashi school, fitowa suka yi ita da Rimsha, Aisha dake SS1B ma ta fito, su kuma SS1A suke. A ƙasar wata bishiya dake kusa da gate na garden ɗin makarantar suka tsaya. Rimsha ta ce. "Zamu ga waye za'a riga zuwa ɗauka, nasan Uncle Faryan ɗina yana hanya".

Ɗago kai Seraphina ta yi da nufin ta yi magana unexpected idanunta suka sauƙa a kansa, yana tsaye a kofar offince da yakasance mallakinsa, ya rungume hannaye a kirji, kallonta kawai yake yi. Suna haɗa idanu ya sakar mata ƙayataccen murmushi, tsintar kanta ta yi da mayar mashi da martanin murmushin.

Daidai lokacin motar Faryan ta shararo kan titin wajen, ya gaji da jiransu a parkin lot ya ce bari ya shigo cikin school ya dubata. Rimsha na hangosa ta yi gaggawar nufo motar, yana ganinta shi ma ya kashe tsayar da motar.

Kama hannun Seraphina ta yi tare da cewa. "Zo mu je ki gaisa da uncle É—ina kuma husband to be É—inki"...... Cike da shirirta ta ce. "Husband biyu zan haÉ—a kenan? Daddy and Uncle Faryan".

Suna nufarsa Rimsha ta ce. "A'a ba wani daddy, ki manta da daddyn nan naki please, ni dama bana son shi tin da kika ce ya cika faÉ—a da sanya dokoki, idan kika bari ya aureki wahala zaki sha, gara ki manta da shi ki so Uncle É—ina, Uncle Faryan zai baki soyayya, zai kula dake, zai maki dik abin da kike so, ga shi Uncle Faryan kyakkyawa kaman mugun Uncle Aryan É—ina, da uncle Aryan ba mugu bane, da yana kula mata da shi zan yi maki fatan ki aura, amma bakin mugu ne, baya kula mata, ALLAH ki so Uncle Faryan yana kama da uncle Aryan, ki shigo cikin zuri'armu, nasan kema zaki so zama cikin familynmu, idan kika auri Uncle Faryan kullum muna tare". Ta kai karshen maganar daidai lokacin da suka isa wajen motar.

Hakika kalaman Rimsha sun fara tasiri a ranta, musamman yadda ta ce idan ta auri Uncle Faryan zasu kasance a tare, tana son Rimsha sosai, tana son zama da ita, ko dan su kasance gida É—aya zata auri Faryan, zasu zama Æ´an uwan gaske.

Sauƙe glass na motar Faryan yai, a natse ya ce. "Tauraruwa mai haske, kin kara kyau sosai"....... "Good afternoon Uncle Faryan". Ta faɗa a ɗan shagwaɓe tana turo baki....... Idanunsa a kan nata eyes ɗin ya ce. "Afternoon my princess, ya school? Hope komai daidai?".

Kai ta gyaÉ—a mashi alamar e kafin ta ja baya, Rimsha ta shiga gidan gaba na motar tana murmushi....... "Uncle daddyn Seraphina bai zo ba, ko zamu yi dropping a gida?". Cewar Rimsha.

Da sauri ya ce why not, su shigo ya saukesu. Da sauri ita ma Rimsha ta fito ta koma baya, Aisha ta shiga gidan baya, Seraphina ta shigo gidan gaba. Tada motar ya yi suka nufi side ma benen su Seraphina, suna tafiya yana ta jan Seraphina da hira har suka isa. Yana parking Rimsha ta kalli Seraphina, a sanyayye ta ce. "My star lady, kada ki manta idan kika yarda da uncle Faryan zamu kasance tare na har abada, zaki shigo cikin zuriarmu, zamu je school tare, shopping tare, mu ci abinci tare, komai tare zamu dinga yi".

Sosai waɗan nan kalamai suka yi tasiri a zuciyarta, sai take jin ta aminta da Faryan, amma kuma shi Aryan kada ku manta soyayyar tin yarinta tai mashi, pure soyayya kenan, hakika idan zata so Faryan yanzu sai dai dan kalaman da Rimsha ke yi mata, shi kuma Aryan sonsa yana ƙasan zuciyanta ne wanda ba zata iya haɗa shi da kowa ba, amma yanzu yarinta yasa ba zata iya banbantawa ba, a halin yanzu kowanne a cikinsu zata iya cewa tana so, amma kowanne da dalilin son nasa except daddy Aryan da pure love da babu dalili take mashi.

Zata so Uncle ne kawai dan irin kulawa da kuma nuna soyayya da yake mata, kunga su IRON FIST basu iya soyayya ba, daddy Aryan bai iya dik waɗan nan tausasawa ba, sai bada umarni ya iya, ko ta ce tana son abi sai dai ya kaita ta zaɓa, ya biya kuɗi, ba irin kyautar masoyan nan, ba kalamai irin na Uncle, shi dai umarni.

Jinjina kai ta yi tare da cewa. "Zan yi tinani". Tana faÉ—a ta buÉ—e kofar motar ta fita. Da sauri Faryan ya buÉ—e shi ma ya fito. Zata wuce ya ambaci sunanta, juyo da kallonta a kansa ta yi. Wucewa Aisha ta yi ta basu waje.

Dawowa Seraph ta yi, a kusa da shi ta tsaya, tana kallon face ɗinsa ta ce. "Uncle gani"...... Ajiyar zuciya ya ɗan sauƙe kafin ya ce. "Nasan Rimsha ta faɗa maki ina sonki, haƙiƙa haka ne, ina sonki kuma ina fatan in ɗaukeki zuwa cikin zuriarmu, please kada ki ce a'a".

Shiru ta yi tana tinanin kalaman Madam dake ce mata dik wanda ya ganta sai ya zaci wata babba ce, sai a É—auka 16 years take da shi, yanzu kowani namiji mai lafiya ya ganta sai ya sake ganinta, samari zasu yi tururuwan zuwa wajenta, dan haka ta kula sosai, a wannan lokacin komai zai iya faruwa da ita, wannan lokacin shi ne lokaci mafi haÉ—ari ga rayuwar É—iya mace, kada wasu kalaman soyayya su kwasheta ta faÉ—a cikin wani rayuwa, su nan turawa ne, ba ruwansu da sex after marriage, su before marriage suke yi, dik wani dokokin musulunci ba binsa suke yi ba, dan haka ta rike mutuncinta, kada ta kuskura ta bari wani namiji ya shiga gonar da ba nasa ba.

WaÉ—an nan kalamai ma Madam sun ratsa zuciyarta, hakika yanzu ta fara gasgata Madam, dan yadda ta ga kowa in ya ganta ya ce yana so, lallai ba shakka haka ne, suna mata kallon babba ne, alhalin 13 years kawai take da shi.

Juyawa ta yi ba tare da ta yi wa Faryan magana ba, ta wuce cikin room da zai sadata da elevator ɗinsu. Bayanta ya bi da kallo yana jin tamkar ya mallakawa kansa ita. Sai da ta ƙurewa ganinsa sannan ya shiga mota suka bar wajen.

Tana shiga gida ita kuma room É—inta ta wuce, wayarta ta É—auko ta hau kiran number Aryan tin kafin ta cire uniform, tana shigowa gida shi ne a ranta. Ga mamakinta sai ta ji wayansa a kashe, ta É—an shiga damuwa na jin wayar a kashe, amma ta ajiye wayar ta hau cire uniform.

A lokacin shi kuwa yana can yana barcin huce wannan zazzafar zuciyar, kuma koda idanunsa biyu ma ba zai É—auki kiranta ba kuma ba zai je É—aukota ba sai dai ta dawo da kanta, dan yau har ita haushinta yake ji, dik ya tsani kowa, Abba ya kara rikita mana zuciya da kwakwalwarsa, yana son mai da mana da shi ruwa mun samu mun kwatosa daga dokokin IRON FIST na babu mata a tsarinsu da kyar!.

Wanka ta yi, ta canza kaya, pjs ta sanya dan shan iska, ta fito parlo dan yin lunch, a nan ta isko Aisha zaune saman dinning, zama ta yi, masu aiki suka zuba mata abinci, sai suka fara ci a tare.

-------------------------🔥

Tafiya take yi tana Æ´an waige-waige, bata ji motsin kowa ba sai ji ta yi kanta ya bugu da bayan mutum. Da sauri ta É—ago da kallonta dan ganin wanene? Daidai lokacin shi ma ya juyo slowly dan ya ga waye ya bugesa.

4 eyes suka yi da juna, wani irin yawu mai wuyar wucewa ta haÉ—iya, ya ALLAH, sai ta tina ranar da ta fara ganinsa a school É—insu, ranar da ta matsa dab da shi irin na yau, ita kaÉ—ai tasan me ta gani wannan rana.

Wani irin kallo mai kama da kina da hankali kuwa Leo ya wurga mata kafin ya ɗan ɗauke kansa yana ƙara ɗaure fuska. Ɗaure fuska tamau ita ma ta yi, a ɗan ƙule ta ce. "Nan wajen tsayuwa ne da zaka tsayawa mutane a hanya?".
Chapter 135 · 0% Book details