← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 125 OF 227

Sashe 125

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Miƙewa zaune Abba ya yi, hakika ya kiɗima da jin zancen nan, sai da ya fara maimaita hasbiyallahu wani'imal wakil kafa goma sannan ya ce. "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, a zamanin nan na yanzu kawai ALLAH ne zai iya kare maka zuri'a, wannan wace iriyar musifa ce?".

Shiru suka É—an yi, can kuma Abba ya ce. "Aurar da ita ai ya zama dole ne, wannan musifa dole ai, sai ka shirya biyawa Vash É—in sadaki, wata biyu ma ta yi nisa, gara a aura mashi ita nan da sati guda, dama zai zo ya yi kwana biyu kafin su tafi next mission kaga komai zai tafi daidai".......... "Haka ne Abba, amma a bari nan da two months É—in". Aryan ya faÉ—a, so yake a ranar da za'a É—aura auren a haÉ—a da nasa shi da Cherrynsa, shiyasa yake son nan da 2 months.

Da farko Abba ya so ja, amma daga baya ya hakura ya bar batun, nan da wata biyu za'a yi bikin. Sosai Abba ya shiga damuwa, a daren ranar wlh bai rintsa ba, Aryan na fita Abban yasa aka kira mashi Rimsha, tana shigowa zata hau jikinsa ya ce ta zauna a ƙasa magana zasu yi, ai tana ganin yanayin fuskansa ta natsu tsit.

A ƙasa ta zauna, ta sha jinin jikinta, fuskansa babu alamar wasa ya ce. "Tambaya zan yi maki, ki faɗa mun tsakaninki da ALLAH"...... Cike da mamaki ta ɗago ta kallesa, bai taɓa yi mata magana irin haka ba, amma sai ta ce to zata bashi amsa tsakaninta da ALLAH.

Kai ya jinjina game da cewa. "Kin taɓa kwanciya da wani ɗa namiji ko kin taɓa da wata ɗiya mace?"...... A zabure ta zazzaro idanu a kansa, ganin ya kara murtuƙe fuska ne yasa ta yi ƙasa da kai game da cewa. "A'a Abba, ban taɓa wlh"..... "Ki mun bayani da kyau!". Ya faɗa in a harsh way, dan yana da mugun zafi, yanzu ne ma da tsufa tasa ya ɗan yi sanyi, amma da! Tab!......... Shiru ta ɗan yi kafin ta ce. "Wlh Abba ban taɓa aikata ko ɗaya daga ciki ba, amma roommate ɗinmu suna yi, classmates ɗinmu ma suna yi, ni da Seraphina ne bamu taɓa yi ba".

Tarar numfashinta ya yi da cewa. "Meyasa kuke wanka a tare a toilet ku dayawa matsayinku na matasan ƴan mata?"........ Jikinta ne ya soma rawa, cikin sanyin murya ta ce. "Abba wani lokaci ne idan mun yi lattin zuwa class muke wanka tare dan mu yi sauri, amma bayan haka ALLAH babu wani abin"...... Daga kalamanta yasan iya gaskiyarta take faɗe, dan haka sai ya ce ta tashi ta tafi ba tare da ya faɗa mata hukuncin da uncle ɗinta ya yanke kan aurar da ita ba...... Da sauri ta miƙe ta fito, a ransa ya ce yakamata ya fahimtar da Aryan cewa Rimsha bata taɓa aikatawa ba, dan ya kara tsanarta sosai, a bayanan da ya yi wa Abba ma ya yi kamar ya yarda ta taɓa aikatawa.

Abin da yasa Aryan ya ce ta taɓa aikatawa kuma shi ne, ya fahimci bayanin Seraphina a baibai, da ta ce mashi sister Aana ta ce ita kirjinta basu girma ba, ba zasu yi komai da ita ba, kirjin Rimsha ya fi nata girma, to shi ne yake tinanin kenan tin da na Rimsha yafi nata girma suna aikatawa da ita kenan ai, bai san ba haka bane, bai fahimta bane, shi ne har da ƙara tsananta zai aurar da ita.

Kwana tinane-tinane Abba ya yi, ya yi nadamar turata boarding school tana É—iya mace, a zamanin yanzu da komai ya lalacen nan, gaskiya ya yi babban kuskure. Wannan damuwa ta hanasa rintsawa, washegari da sassafe ya haÉ—a kan Faryan da Harleen ya ce su rakasa benen kusa da su aje batun nemowa Aryan da Harleen auren Aunty Lusi da Aunty Luna, dan fa bai manta da zancen ba.

Faryan ɗan auta kam ba ta shi ake yi ba, shi ance da sauran shi, basu san shi yana can yana ƙoƙarin sace zuciyar Baby Cherry bloom ɗin Aryan ba, ya samu numberta wajen Rimsha, jiya sun kwana chatting while Aryan sun kwana aikin IRON FIST, bai bi ta kan wayar Seraphina ba bare yasan abin da suke tattaunawa, ita kuwa tana nan Faryan ya tsarata son ransa, ya zuba mata kalaman da ta dinga murmushi har ta yi barci fuska ɗauke da murmushi. ....... Hmmmm ga shi da Aryan da Faryan sun fi shaƙuwa da juna, Aryan ya fi kaunar Faryan fiye da Harleen, akwai case kenan.

Faryan sai dariya yake yi yana murna za'ayi wa Harleen auren dole, baya murnar za'ayi wa Aryan auren dole, amma yana murnar na Harleen, dan dama yana son a kuntatawa Harleen ko dan kuntatawa Rimsha da yake yi.

Shiga ta mutunci suka yi, Abba thobe and bisht ya sanya, ya naɗa rawani, while Harleen and Faryan tail coat suka sanya. Kai tsaye suka nufi benensu Noor, sai haɗe rai Harleen yake yi. Ko da suka je daddyn Noor baya nan, amma sun samu uncle da su Aunty Luna, kuma sun karɓesu hannu bibbiyu saboda kirkinsu, yadda suka mutuntasu yasa Abba ya ji ya ƙara kwaɗayin su haɗa zuri'a, musamman yadda Aunty Luna ta gwada masu kulawa, da kanta ta kawo masu ruwa da abin taɓawa, ta zauna tana ta kula da su, uncle ɗin Noor ma akwai kirki da son mutane.

Ya zauna kusa da Abba sai jansu da hira yake yi, musamman ma da ya ji ai maƙotansu ne, sai ya saki jiki da su sosai, ya girmama Abba sosai, ba ƙaramin daɗi Abba ya ji ba, hakan yasa ya furta buƙatarsa ga uncle kai tsaye. Aikuwa cike da murna uncle ya ce ai wannan ba wani abu bane, dan suna addini daban-daban ba zai hana su auratayya ba matuƙar su Aunty Luna suna so, bari yayansa ya dawo zasu yi magana, zasu tattauna, kada Abba ya wani damu zai ji amsa mai daɗi.

Sosai Abba ya ƙara girmana dattakunsu, ya yi matuƙar farinciki, ya masu godiya sannan ya ce idan ba damuwa Aunty Luna su gaisa da Harleen, fuska ɗauke da fara'a ta ce ba komai, ta miƙe ta fita zuwa balcony, kin bin bayanta Harleen ya yi har sai da Abba ya ce. "Ka je tana jiranka".

Sannan ya miƙe yana haɗe rai ya fito balcony ɗin. Tana tsaye tana kallon cikin CP ya ƙariso wajen. Bai ce mata sannu ba sai da ita ta ce mashi. "Hy". Sannan ne ya amsa game da ce mata. "Well-done". Daga haka bai sake magana ba, har suka ɗauki 20 mins a wajen, sannan ya wuce ya dawo parlo, ga mamakinsa sai bai samu su Abba a wajen ba, sun koma gida.

Siririn tsaki ya ja tare da bin bayansu, ita kuwa Aunty Luna ko a jikinta, sai ma son shi da ta ji ya shigeta, dan tana son namiji miskili, bata san wannan ba iya miskili bane, É—an duniya ne.

A ɓangaren shi kuwa Aryan, yana barin gidan Abba ya koma wajen Lion. A lokacin Lion ya dawo daga Ring Of Power, yana tsaye a balcony sanye da pj's farare ƙal, ya saki kitson dake kansa wanda suka ƙasa mashi matuƙar kyau, hannunsa rike da cup of americano yana sha, ya zura hannu guda cikin aljihu, yana kallon yadda CRYSTAL PALACE ke a cikin dare, yana da matuƙar kyau da ɗaukar hankali, haske ta ko'ina tamkar rana, wani irin ni'imantaccen iska na kaɗawa a hankali-hankali wanda ke kaɗa kitson kansa suna motsawa, iskan gwanin daɗi.

Wajen sky blue light ne, hakan ta ƙara fito da tsantsar kyan fuskansa, waɗan nan jade eyes ɗin nasa sun kara wani irin cool sun ciza, zaku ce barci yake ji, in baku manta ba shi da Leo idanunsa sun yi zubin sleeping eyes ai, to da yake yanzu yana cikin kwaciyar hankali sai idanun suka ƙara zama sak sleeping eyes sosai, pink lips ɗin nan nasa ya ciza kala matuƙa, yana ɗan ciza laɓɓan nasa a hankali alamar yana tinanin wani abin.

Aryan ya É—an jima yana kallon haÉ—uwar Lion, da dai ya ga bafa zai gaji da kallon kyan nan nasa ba sai ya kariso wajen, a kusa da shi ya tsaya, hannu yasa ya fara tattare kitson dake kan nasa, yana tarawa wajen guda kafin ya ce. "What a special day today! My man yana cikin farinciki"....... Aryan ya san idan Lion yana cikin farinciki ne yake sake kitson kansa a watse.

Shiru babu alamar Lion zai yi magana. ÆŠaure mashi gashin Aryan ya yi game da cewa. "Yakamata mu binciki meyasa ake cire mahaifar mata a asibitoci a hankalin yanzu? The case is getting out of hand, anywhere ka juya wannan magana ake yi, i think there is something behind all this".

Kai Lion ya ɗan jinjina ba tare da ya yi magana ba, hannu Arya ya miƙa ya karɓi Americanon dake hannunsa, sipping ya ɗan yi tare da cirewa, ya nisa before ya ce. "A Avaris abin yafi worst! But why, meyasa dik wata musifa a wannan ƙasar tafi yawaita kuma mutanen cikinta suka fi shan wahala".

Sai da Lion ya ɗauki good 2 mins kafin in a cool way ya amsa da. "Saboda Avaris tana da mutane irin IRON FIST"........ Watau saboda tana da mutane ƴan baiwa, masu hazaƙa da basira, waɗan da idan suka samu dama a ƙasa da kwanaki suna iya saita duniya bakiɗaya ba iya Avaris ba, shiyasa ake dakushesu, ake hanasu motsi bare su ci ribar baiwar da ALLAH yai masu.

Jinjina kai Aryan ya yi, zai sake yin magana guru ya hauro wajen da juggling, alamar yana cikin farinciki, cike da murna yai hugging na Lion kafin ya sake shi yai hugging na Aryan, daidau lokacin Zakinsu ma ya hauro da gudu yana wani numfashi alamar yana farinciki shi ma.

Kai tsaye jikin takwaransa watau Lion zaki ya nufa, sai hayesa Lion ya ja baya yana ɗan marin fuskan zakin, ya ɗaure fuska kafin ya ɗaga mashi hannu alamar kada ya hau mashi jiki....... Hannu zakin ya ɗaga ko in ce kafafunsa na gaba, ya ɗaga duka biyu ya fara gurnani alamar Lion ya ɓata mashi rai.
Chapter 125 · 0% Book details