← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 227

Sashe 96

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A kusa da shi ya zauna tare da cewa. "Brother lafiya?"..... Kai Aryan ya girgiza alamar a'a ba lafiya, amma bai yi magana ba, guru yasan me matsalar, basa iya kwana cikin fushin juna, idan sun yi faÉ—a kasa barci dikkansu suke yi, su yi ta faman kumbure-kumbure amma ba zasu iya bawa juna hakuri ba.

Shiru room É—in ya yi, can Aryan ya ce. "Brother Lion bai ji ciwo ba ko?"...... Wani irin kallo guru ya wurga mashi kafin ya ce. "Yana second room jeka duba". Siririn tsaki ya ja tare da gyarawa ta kwanta a gadon na guru. Shiru guru ya É—an yi yana tunanin yanzu Lion ya bar É—akinsa fa, shi ma tin da ya farfarÉ—o daga alluran ya gagara yin barci, shi ne ya zo wajen guru, ya fake da cewa Aryan bai ji ciwo ba ko? Guru da iskanci sai ya ce mashi ya je ya duba, shi ne yaki zuwa ya koma room É—insa, yanzu haka yana tsaye a tsakiyar É—akin, yana son zuwa duba Aryan ya ga yana lafiya bai ji ciwo baz amma girman kansu da nuna isa ya hanasa, ga abin a ransa ta hanasa sakat.

Shiru Aryan ya kwanta, zuciyansa ya gagara daurewa, sai ya miƙe game da cewa. "Mu je in duba ko ya ji ciwo"............. Hararansa guru ya yi game da cewa. "Ku dai kuka sani". Ya faɗa tare da bin bayansa suka fito waje.

ÆŠakin da Lion yake suka shiga, yana jin sun turo kofa ya juyo da sauri, ai yana ganin Aryan wani irin sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin kuma ya É—aure fuska. "What brought you here?". Ya faÉ—a har da nuna irin bai damu da su É—in nan ba..... Banza da shi Aryan ya yi tare da wucewa ya kwanta a gado yana satar kallonsa, shi kuma guru ya shigo ya hau tausan Lion É—in. Da yake abin da yake so kenan su yi sulhu sai ya yi saurin hakura, da haka suka wuce saman gado in da Aryan yake, babu wanda ya ce da É—an uwan uppan, suka kwanta shiru, ba jimawa barci ya kwashesu.

Washegari suna sun mance da sun yi faÉ—a, suka koma kamar da, a tare suka yi sallar asuba kamar yadda suka saba, suka dawo, wanka kowannensu ya yi suka sanya hoodie iri É—aya fari tas, sannan suka faÉ—a É—akin aikinsu dan tsawaita bincike kan AVARIS.

A gaban computers ɗinsu suka zauna, Lion ne ya ɗauki cube yana jujjuyawa yana ƙoƙarin haɗawa. Su Aryan dake kokarin duba aikinsu ne suka samu sakon binciken Lion da ya tura masu.

Buɗe saƙon suka yi, a natse suka fara karantawa, batu ne kan dalilin da yasa ake ta faman tashe-tashen hankula a arewacin AVARIS, dik jerin tattalin arzikin da arawacin ta mallaka ya rubuto masu ajere, albarkatun ƙasa sama da 28 arewacin AVARIS ta mallaka, ciki har da uranium da ake haɗa su nuclear, arzikin gold, fetur, coal tantalite, tin, granite, asbestos graphite nickel, dik arewacin kasar tana da shi, ma'adanai masu balain tsada, batu ake na makaman nuclear fa, arzikin da manyan ƙasashe basu da shi, shiyasa abin yaiwa Avaris yawa wai shege da hauka.

Bayan sun karanta sun gama ne guru ya ce. "To tin da ma'adinan sun yi wa kasar yawa, shuwagabanninta basu iya amfanar da ƙasar da ita ba why not ba zamu shiga siyasar kasar ba? Ma'ana mu tsayar da waɗan da za su iya kwato ƙasar daga hannun ƴan sarin da ta faɗa?".

Cigaba da jujjuya cube É—in Lion ya yi tare da cewa. "That's impossible!". Ya faÉ—a idanunsa a kan Aryan da gabaÉ—aya ya mayar da hankalinsa a kan waya, his attention isn't there. Yana can yana kallon Seraphina dake ta faman neman hotonsa da ta É—auka jiya dan ta turawa Rimsha, a tinaninta she's smart, bata san da IRON FIST take tare ba, yama za'ayi ta É—auki hotonsa ba zai sani bane? Ko da yake bata san gabaÉ—ayanta ma a tafin hannunsa take ba, wai ita ma ta yi wayau.
"Rimsha i didn't see this pic, but why not ki turo mun pic na uncle É—in naki, idan shi ne zan gane ai". Ta yi typing ta tura mata. Shi dai Aryan ganin gudun ruwansu kawai yake yi, yana son jin karshen wasan......... "Seraphina you are out of your sense! Uncle Aryan É—in ne zan samu pic É—insa? Don't you that ni makiyarsa ce? Idan yana waje ma bana fitowa". Ta turo mata amsa.

Miƙewa Seraphina ta yi, zarya ta fara yi a cikin ɗakin tana tinanin yadda aka yi hoton daddyn nata ya goge a wayar, ta san dai ta ɗaukesa

Unexpected Aryan ya ji an kwace wayansa, a zabure ya É—ago kai, four eyes suka yi da Lion dake tsaye a kansa. Wani irin harara Aryan ya dallah mashi kafin ya ce. "Give me phone malam, ka wani tsaya mun a kai kamar sojan gona". Cike da fargaban kada Lion ya duba wayar ya yi maganar.

Juya gaban screen na wayar Lion É—in ya yi dan ya ga me ya É—aukewa Aryan hankali suna irin wannan zama kan mission É—insu mai muhimmanci, ai yana juyo da wayar sai..........

Likes comments and share fisabilillah.

STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥 For more information 08161390581 Whatsapp me only.

ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️
🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥

PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.

STEP 1🔥

2025-11-28🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E_____________30 & 31

Juya gaban screen na wayar Lion É—in ya yi dan ya ga me ya É—aukewa Aryan hankali suna irin wannan zama kan mission É—insu mai muhimmanci, ai yana juyo da wayar sai ga call É—in Abba ya shigo. GabaÉ—aya hankalin Aryan ya gama tashi, baya son su sake yin faÉ—a irin ta jiya, amma kuma ba zai iya jurar Lion ya yi taking wani mad reaction a kan tsakaninsa da Seraphina ba, to Abba ya kira ya raba gardama.

Miƙo mashi wayar Lion ya yi yana hararansa da wannan jade cool eyes ɗin nasa, kai ka ce Leo ne a wajen saboda tsananin kamanninsu, girman idanunsu ma ɗaya.

Sai da Aryan ya sauke wani musulmin ajiyar zuciya kafin ya karɓi wayar, ganin Abba ne yasa ya kara natsuwa tare da picking up, a H-free ya sanya wayar, cikin sanyin murya ya ce. "Assalamu alaikum Abba"........ "Waalaikumussalam"..... "Good morning Abba".

Shiru Abba ya ɗan yi kafin ya ce. "Stop everything you're doing and come, I want to see you"....... Kallon juna Lion da Aryan suka yi kafin Aryan ya ce. "Abba lafiya dai ko?"......... Daga gefen Abba Faryan ɗan Auta ya riga Abba da cewa. "Yah Aryan wlh kada ka dawo, aure Abba zai je neman maka, wai zai kaimu gidan matan........". Ɗiff muryan Faryan ta ɗauke, da alama toshe mashi baki Abba ya yi, dan yasan idan Aryan ya ji wlh ba zai koma ba, sun fara wasan ɓuya kenan, haka suka yi a baya, ya taɓa ce mashi zasu je wani gida neman mashi mata, Aryan ya ki dawowa, sai da ta shari watatti takwas bai taka gidan ba, ko sun kira wayansa baya ɗauka, wayar Faryan kawai yake ɗauka ya ji ya gida suke, sai da Abba ya ce an bar maganar sannan ne komai ya gyaru, to wannan karon so yake ya damki Aryan ga shi ga shi suna kallon juna kafin ya umarcesa ta yadda ba zai iya bijirewa ba. Sai dai da alama Faryan ya ɓata komai.

Kuma a tsarin Abba da zarar an je an tambayo auren a wannan lokacin ake ɗaurawa, shi baya jeka ka dawo, ana bashi aure za'a ɗaura a wajen, baya bari wai bari yaran su fahimci juna, ya ce zasu fahimta a gidan aurensu, shi yake yin komai, shi dai a bashi yarinya kawai, da zarar anbashi ko tsinken iyayenta baya karɓa, sai dai ma ya basu sadaki mai tsoka, daga nan a ɗaura su ɗauko yarinya su kawota cikin family, kayan ɗaki da kayan sakawa dik zata samesu a gidan mijin, yanzu dama suna zuwa gidansu Aunty Lisa in an basu zai ɗaura masu aure ne kawai su dawo da matansu.

Jama'a kunji wani ta'addancin zuciya irin na Abba? Wannan ai ɗanyen ta'addancin zuciya ne whichs mu IRON FIST family ba zamu yarda ba ko ya kuka ce my people? Ba zamu yarda ayi wa Champion namu auren dole ba! Dole mu yi ruwa mu yi tsaki, ku zo mu je mu yi kanenen mu yi uwa mu yi makarɓiya mu taya Champion namu kwatar ƴancinsa, kada mu bari kanmu ya yi marfi, dan ma dai Abba ne sai mu ɗan raga mashi, amma ba zamu yarda ba.

Ai Aryan yana jin jawabin Faryn ya katse kiran, sai ya kira number Faryan ɗin dan ya ji ainahin meke going. Yana kira bugu ɗaya aka ɗaga, a sanyayye ya ce. "Faryan what's going on? Me Abba yake shiryawa?"....... Unexpected ya ji muryan Abba ya ce. "Abin da kake tinani shi nike shiryawa, na baka 2 hours yanzu in ganka kada raina ya ɓaci".
Chapter 96 · 0% Book details