Sashe 115
Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A cikin ƙasa da mintuna 10 suka lallasa ƴan ta'addan nan, wasu ko motsi basa yi. Noor ne ya ce. "Waɗan nan ɗaukarsu ma ai aiki ne, jibesu fa, ƙazaman banza"....... Leo da ya ɗauko bindigarsa yana ƙoƙarin gyarata ne ya ce. "Babu in da zamu kaisu, dik harbesu a nan zamu yi, idan ma an gane mun kashesu sai mu ce a musayar wuta ne by mistake, kada ku wuce kama ƴan ta'adda biyu mu koma da su, suma dan ana buƙatar bayanai daga bakinsu ne, amma dik saura ku harbe shegu!".
Na'am da wannan shawara suka yi, Zaynish ne ya fara saita bindigarsa ya dinga binsu one by one da suke baje a ƙasa yana fasa kansu da bindigar tasa, babu tausayi bare imani. To a irin haka ina soja zai yi tausayi? Ai aikin soja ba dik kai ba, tin yana gani ana kashewa a gabansa har ya fara kashewa da kansa, ya kashe ya kara kashewa, tin yana kashewa yana tausayi zuciyarsa na ɗan rawa, har ya dawo kisa ta zame mashi jiki, ya saba, zai ɗauki bindiga ya harbi rai kamar ya harbi tsuntsu, ba zai damu ba, ba zai ji komai ba!. JINJINA GA DIK WANI KAKI NA SOJA!.
Bayan sun kashesu tsab Leo ya wuce gaba, tsalle Noor ya daka ya ɗale bayan Leo ɗin, cikin shagwaɓa ya ce. "Bro na gaji, ba zan iya tafiya da kafafuna ba, ka goyani har zuwa wajen sansaninmu my Juliet ta mun massage"....... Hannu Leo yasa ya gyara shi a bayan nasa da kyau, ya tallabosa suka cigaba da tafiya kafin ya ce. "ALLAH ya shirya mun kai".
Zaynish ne ya daki kafaɗar Noor tare da cewa. "Ba zaka canza hali ba!"....... Turo baki ya yi tare da saƙalo wuyan Leo, ya kwantar da kansa a bayan wuyan Leo ɗin yana hararan Zaynish kafin ya amsa da. "Bafa zan canza ba!".
Leo dai bai sake yi masu magana ba, yana ta cigaba da tafiya abinsa, ya rataye bindigarsa a gefen shoulder ɗinsa. Noor dake kwance yana zuba masu shagwaɓa ne ya zabura ya sauƙa daga bayan Leo, tsayawa cak shiru suka yi, take suka ɗauke nunfashinsu suka daina yi. Nan suka ji alamar numfashin mutane biyu daga gefensu.
Tsalle Noor ya yi ya sake hayewa bayan Leo tare da gyara bindigarsa, kafin su Zaynish su gano masu numfashin ya saita ya yi harbi biyu a wajen sunkurun ciyayin dake kusa da su, already ya ga ƴan ta'addan dama. Yana sake harbi biyun nan ya komar da kansa a bayan wuyan Leo ya kwanta yana turo baki da shagwaɓa tamkar bashi ya gama harbi yanzu ba, ya wani rukunkume Leo, kamar zai yi kuka ya ce.
"I miss my Juliet over, nasan yanzu tana can tana kukan rashina .......". Bai karisa maganar ba ya dakata tare da É—aga bindigarsa ya saita gabansu ya yi harbi. A tinaninsa alamar da ya gani ta mutum É—aya ne a wajen, sai dai yana harbin ta samu mutum É—aya shi kuma É—aya ya fito da gudun gaske, kafin su harbesa ya iso in da suke.
Kan su juya ya yanka Zaynish da wukar dake hannunsa. Da karfi Leo ya juyo da Noor dake bayansa, Noor ya saita bindiga ya harbi ɗan ta'adda ya faɗi mushe. Cikin zafin jini Noor ya sauƙo ƙasa daga bayan Leo, da sauri ya zo ya rike Zaysh yana faɗin sorry.
A wajen damtsen hannu yai mashi wani irin wawan yanka da ta shiga sosai. Rigar jikinsa Noor ya cire tare da sanya karfi ya yageta, ya kama hannun Zaysh ya ɗaure mashi dan su samu jinin ya taƙaita zuba, saboda ba karamin jini ne yake zuba daga wajen ba, kunga daga yaki ya fito, ya jijjiga jininsa sosai, dole jini ya zuba a wannan yanka sosai.
Ɗaure mashi gam ya yi, sannan Leo ya ɗaukesa a bayan wuya suka cigaba da tafiya. Abin like wow, suna tafiya Leo and Noor suna hira kuma suna kashe ƴan ta'addan dake gudowa daga wajen sassaninsu in da sojojinsu ke ɓarin wuta, suna tsarewa su nemi wajen ɓuya, da sun fito zasu ci karo da su Leo, sai su harbesu, kuma ko a jikinsu basu tashi hankali ba, a natse suke tafiya suna hiransu.
In takaice maku labari sai da suka kwana suka wuni suna musayar wuta, Vash da ya sha harbi a kafa Leo ya umarci wani soja ɗaya da ya ɗaukesa ya mayar da shi sansaninsu surgeon devissio watau my surgeon lioness Manassa ta dubasa ta ceto rayuwansa kada a tsaya ɓata lokaci bullet ɗin ta yi ɓarna, komai na iya faruwa idan aka barshi ya jima, yana ma iya rasa kafarsa yazama sai an yanke mashi kafar nasa, shiyasa Leo ya ce a mayar da shi sansanisu da wuri dan basu san adadin lokacin da zasu ɗauka a wannan ɓarin wutar ba.
To a haka suka kwana suka wuni babu cin abinci babu ruwan sha, musayar wuta kawai suke yi, har sai da suka tabbatar komai a arear ya daina motsi, sun kashe dikkan ƴan ta'addan sannan suka fara shiga lungu da saƙo na sansanin ƴan ta'addan suna dubawa ko akwai waɗan da suka ɓuya, su kamosu su masu yankar rago.
Basu bar mutun ko É—aya da rai ba sai guda biyun da suka harba a kafa, da ogansu da wani, su kawai suka bari da rai dan su mayar da su barrack.
A ɓangaren su Arya kuwa, kamar yadda su Leo suka kwana suka wuni musayar wuta suma haka suka kwana suka wuni musayar hawaye, sun shiga damuwa, ko abinci basu ci ba, sun zauna jugum-jugum har zuwa lokacin da sojan can ya dawo da Vash ɗauke a saman wuyansa. Da gudu su Arya suka fito jin cewa ga soja ya dawo ɗauke da wani soja.
Ai ba wanda ya kai Manassa kiÉ—ima da ganin Vash aka harba, domin kuwa shi ne mutumin da ta haÉ—u da shi a safiyar ranar da zasu tafi bakin daga. Ai bata san lokacin da ta kurma ihu ta yi kansa tana tambayar me ya same shi ba?.
Da gudu wani soja ya shiga cikin tantinsu ya ɗauko wani tampol ya zo ya shinfiɗa a ƙasa a wajen. Shinfiɗe Vash a kai sojan ya yi, a lokacin ko motsi Vash baya yi, ya suma kuma ya rasa jini. Kansa Manassa ta yi, tsabar ta ruɗe ma ta manta da cewa ita ce surgeon ɗinsu.
Arya kuwa, da gudu ta shiga cikin ɗaki ta ɗauko jakar Manassa. A gaban Vash ta zo da gudu ta zube gwiwowinta, zuge zip na jakar ta yi, gabaɗaya ta zazzage abin dake ciki a ƙasa tsabar kiɗima. Sai a lokacin Manassa ta farga da ashe ita ce surgeon ɗinsu, ai cikin zafin nama ta kwaso kayan aiki irinsu scapel, jikinta na kerma, tana hawaye ta fara ƙoƙarin ceto kafarsa.
Da yake Arya tana da ilimi a kan aikin na Manassa sai ta taimaka mata. Wani abu da Arya, tana da mugun tausayi ne yarinyar, idan ta ga wani a cikin wani hali tana rasa hankalinta gabaÉ—aya, ba ruwanta da koma waye, kawai idan ta ga mutum a damuwa zata tsaya mashi ne sai in da karfinta ya kare. Yanzu haka ta tsaya tsayin daka a kan Vash har zai da ta ga ya fita daga haÉ—ari, sannan ta samu damar jan dogon numfashi, sai ta koma babin tinanin sterious É—in nata.
Ganin Vash ya fita daga haɗari ne yasa kowa ya hau sauke ajiyar zuciya, musulman cikinsu suna ta Alhamdllh. Ita kuwa Arya matsawa dab da shi ta yi, hannunta har yana rawa wajen sanyawa ta ɓalle botiran rigar jikinsa, tsabar an shiga tashin hankali basu lura da uban gumin da yake haɗawa ba.
Buɗe gabar rigar ta yi, ta ɗauko kwalin wani drugs a cikin kayan aikin surgeon Manassa, ta yage kwalin, ta cire drugs ɗin ciki ta hau yi mashi fifita tana addu'ar Leo ɗinta ya dawo lafiya, dan tin da ta ga Vash da rauni ta ƙara karaya.
Ita kuwa V tana barcin safe a lokacin, daren jiya bata rintsa ba, sai yanzu take barci. Angelina na ganin abin dake faruwa ta dannawa daddynsu kira tana ruwan hawaye....... A lokacin da kiran ya shiga yana tsaye a tsakiyar ɗaki rike da waist ɗin Aunty Lisa dake kokarin ɗaure mashi maɓallan uniform ɗinsa, a taƙaice dai tana shirya shi zai fita office.
Ya tallabo waist ɗinta ta baya wajen mazaunanta, suna kallon juna ido cikin ido cike da tsantsar so da kauna, sai murmushi take yi. Sumbata ya bata a cheek ɗinta kafin ya ce. "Miƙo mun wayata ana kira". Da sauri ta juyar da kallonta zuwa saman bed ɗinsu dake shinfiɗe da tsadaddun bed sheet, ga wani fitinannen kamshi dake tashi.
Watau auren nan ya karɓesu fa, dikkansu suna kula da juna, Aunty Lisa ta kara kyau matuƙa, har wani murjewa skin ɗinta ya ƙara yi, while shi ma daddy GAT hakan ce, har wani sheki skin ɗinsa yake yi, ga kumatu da ya yi, hankulansu a kwance, yana nuna mata soyayya matuƙa, ita ma tana nuna mashi.
Yanzu haka ya cika alkawarinsa na sama mata aikin jaridar da ta kwallafa rai a kai, idan ya fita aiki ita ma zata fita nata aikin, amma tana riga shi dawowa.
Ɗauko wayar ta yi ta miƙo mashi. Ganin Angelina ke kira yasa ya katse kiran ya kirata. Aunty Lisa na ƙoƙarin juyawa ta bar wajen ya kamota da ɗayan hannunsa a lokacin da yake cewa. "My daughter be patient please, meyakefaruwa?"........… Tana goge hawayenta ta faɗa mashi an harbi sojansu ɗaya ne.
To abinku da soja, ko a jikinsa, wace iriyar mutuwa ce basu gani ba, sai kawai ya yi ƙoƙarin kwarara mata gwiwa, ya tunatar da ita cewa sun rigada sun yafe rayuwa ne kafin su fara wannan aiki? Ai rayu ba wata aba bace su a wajensu, so ta daina damuwa. Tina mata da komai da ya yi ne yasa ta shanye kukan, ta kwarara zuciyarta tare da yi mashi godiya.