← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 153 OF 227

Sashe 153

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na uku a jinin jariri akwai erythropoietin, shi kuma sinadarin da ke taimakawa wajen samar da jan jini red blood cells, kun san jan jini daban yake, masu shi daban suke, da lafiya da karfi.

Na huɗu akwai fetal hemoglobin. Wannan nau'in haemoglobin ne da ke cikin jinin jariri, wanda ke da ƙarfin ɗaukar iskar oxygen fiye da na manya, idan ka yi amfani da maganin 3D hmmmm, karfi da lafiya kam a dai yi shiru kawai. Na biyar akwai alpha fetoprotein, wannan sinadari ne da ake samu a cikin jinin jariri, wanda ke sabonta garkuwar jiki, idan kin tsufa garkuwar jikinki ta raunata ta yadda kowani cuta zai iya yi maki shigar farad ɗaya, to wannan sinadari na sabonta garkuwar jiki, ki zama tamkar yara.

Na shidda akwai Interleukins & growth factors, waɗannan sinadarai ne dake ƙarfafa garkuwar jiki da kuma sabunta ƙwayoyin halitta. To su ne a jinin ɗan jariri wanda sai sun razana jaririn suke samo jikinsa ya sakarwa jininsa waɗan nan sinadaran ta yadda in sun marƙaɗa shi sun matso jinin zai zo ɗauke da sinadaran!.

To mu cigaba da bibiyar 3D yau mu ga abin da ya turewa buzu naɗi, amma kafin nan ina da tambaya! Mun gama jin na jini, to shi kuma ɓargon ƙashin fa? Me suke yi dashi? A gaskiya shi fitina da balainsa ya fi na jini, a hankali zamu iso garesa, zaku ji komai, haɗarinsa yawa ne da shi, shiyasa na ware mashi lokaci na musamman.

Bayan kamar 30 mins da kammala zuba sinadaran injin na mixing Dr Mark ya tsayar da injin, komai ya haɗe sosai. Dr Kamal ya ɗauko color ɗin da suke buƙata, white suka sanyawa haɗin, take da injin ya sake mixing komai ya zama fari tas tamkar farin fenti, ba zaku taɓa cewa akwai jini a ciki ba, Dr James ya ɗauko fm, sinadarin dake kashe ƙarnin jini da dik warin wasu sinadaran, ya zuba a ciki, suka ɗauko wani powder mai kamshin inabi da sauran kayan itatuwa suka zuba a ciki.

Injin ya sake mixing sosai kafin su sake kash injin. Sannan suka danna wani madanni, gabaɗaya farantin ya yi sama, ya juye maganin cikin wani abu tamkar ball, daga nan suka kunna wasu injuna dake gaba guda biyu kafin su kunna makunnin wannan ball ɗin. Nan take ball ɗin ya fara motsawa yana sama ya ɗan yi ƙasa.

Matsawa kaɗan suna yi izuwa karshen injinan suka tsaya, a wajen akwai wani katon baff a bakin karshen injunan. Sun rungumo hannayensu a saman kirji, idan suna aiki ba'a magana, babu wanda ya ce da wani ƙala, kowannensu yana lissafin kan yadda zasu ƙara inganta aikin nasu ne.

After 30 mins da tsayuwarsu a wajen sai ga bakin injin ya buɗe, you can't believe what i saw my people. Ya ALLAH, a jere drugs suka fara zubowa a cikin wannan baff ɗin, yadda kuka ga ake arranging magunguna a cikin saches ɗinsu, haka waɗan nan magunguna suka fito daga cikin injin, ko kasheki za'ayi idan ba'a gabanki aka haɗa wannan magani ba ba zaki taɓa cewa akwai jini da waɗan nan sinadaran a ciki ba, pure magunguna ne a ciki farare ƙal..... Kin taɓa jin maganin hana tsufa? mai da tsohuwa yarinya.

To waɗan nan magunguna ba komai bane face magungunan mai da tsohuwa yarinya, maganin gyaran jiki, skin ɗinki ya zama irin na waɗan can na kwana, maganin glowing, lightning, glass skin da sauransu, zai sabonta maki halitta cikin ƙanƙanin lokaci. Shiyasa basa karɓar sperm da eggs na munana sai kyawawan mutane, dan dik wanda ya sha maganin ya zama yaro, ya kuma yi kyau sosai, shiyasa dik nurses dake cikin wannan asibitin suke da mugun kyau, dan sperm and eggs na kyawawan gaske ake ɗaukowa! Fatan yanzu kun gane dalilin da yasa dole sai na kyawawa!.

To ina matan littafin nan masu shan maganin gyaran jiki? Masu shan maganin ƙarin haske, su skin care manya! To koma dai me ga abin da kike sha nan, mu munga komai, munga dik abin da 3D suke haɗawa, dan haka mu bamu a wannan layin na su glowing, ko ya kuka ce mutanen kirki?..... Watau ni kaina ina kiɗimewa idan na tina abin da suke haɗawa da wannan ɓargon ƙashin jariran fa, mun dai ji na jini, ko ya na ɓargo da kuma shi kansa garin ƙashin da tsoƙa ɗika yake? Yanzu shikenan jarirai guda biyar ɗin nan sun tafi har abada? Haka zasu cigaba da salwantar da rayuwan jarirai? Suna niƙasu tamkar masara! Tamkar ba rai bane da su? Wannan wace iriyar balai ce, rai fa, su ɗauka su saka cikin inji ya niƙa ya fitar masu da jini daban, garin tsoka da ƙashi daban, ɓargon cikin ƙashi daban, rai fa, ran ma na jaririn da bai ji ba bai gani ba, bai san komai ba, la haula wala ƙuwata illah billah, allahumma ajirni fi musibatin, wannan musifa ina zamu tsaya da ita? Ba dole jama'a su dinga ganin tashin hankali da musifu ba, ace ƴan ɗan adam akewa wannan ɗibar albarka, ya ALLAH.

Bayan magungunan sun gama zuba ne 3D dikka suka É—ebo ruwa a boket duka zuba cikin farantin da ya haÉ—a maganin da farko, sannan suka kunnasa, farantin ya yi sama, ruwan ya zuba cikin ball, daga nan suka sake tsayawa a gefe. After 30 mins sai ga magunguna da basu kai ka farko ba sun fara fitowa, watau marasa karfi sosai aka yi yanzu da É—aurayar inji.

Waɗan nan marasa karfi sosai ɗin sai kun sha sosai yake biyan buƙata, kuma shi ne mai arha daidai talakawa!. A baff daban marasa karfin suka zuba, dan da na farko ya gama fitowa sun janye baff ɗin gefe, sai suka sanya wani.

Bayan komai ya gama fita sai suka haɗa karfi suka cicciɓi baff ɗin magani mai karfin suka fito dashi wajen ɗakin, suka koma suka ɗauko mara karfin suna fito da shi waje. (Ni na rasa ma wani irin suna zan baiwa wannan ɗaki saboda musifar dake cikinsa, kai ya ALLAH. To bari dai mu bashi sunan ɗakin niƙa jariran, tin da babban abin da suke yi a ciki kenan.

A wajen ɗakin niƙa jariran suka dire baff dikka biyu ɗin, magunguan yana dayawa, ga baff ɗin da girma, sai da suka yi da gaske suka iya ɗauka. Suna ajiyewa Dr Mark ya kira guards madaka karti su uku suka zo suka ɗauki baff ɗin, amma kafin su ƙirasu sai da suka rufe kofar ɗakin niƙa jariran da matakan tsaronsu na wutar lantarki, babu wani mahaluki da yake shiga masu wannan ɗaki, su kaɗai suke shiga, saboda su kaɗai suka san ɓarnar da suke yi a ciki.

Bayan guards ɗin suka bi izuwa wani katafaren ɗaki mai girman gaske, kwalayen magunguna ne cike a cikin ɗakin, a nan guards ɗin suka sauƙe baff ɗin dikka biyu, akwai ma'aikata mutum 10 a ciki, aikinsu kawai shi ne shirya magungunan a cikin kwalaye ƙanana kafin a shiryasu cikin manyan cartons.

Saman haÉ—aÉ—É—un chairs da aka tanada masu suka zauna, suka zuba idanu suna kallon yadda ma'aikatan nan ke aiki da jikinsu wajen ganin sun shirya komai yadda yakamata a kan lokaci. Suna sanya magunguna marasa karfi a kwali daban, mai launin white and ratsin ash, su muma magunguna masu karfi kwalinsu farine tas.

Sai around 10 na dare 3D suka je suka yi wanka, suka shirya cikin shiga iri ɗaya, white pj's, basu ko ci abinci ba suka dawo ɗakin aiki. A lokacin ma'aikatan sun shirya cartons 20 na masu karfi, 10 na marasa karfi, kowani carton kuma yana ɗaukar kwali ƙanana na maganin guda 25. Umarni Dr James ya baiwa guards uku da su fitar masu da cartons 30 ɗin dikka da aka shirya waje.

Cikin ƙanƙanin lokacin suka fitar da shi suka ajiye a tsakiyar SECTION E ɗin, sannan suka koma bakin aikinsu. Wayansa Dr James ya ɗauka, password na tsaron lantarki dake jikin wani kofa dake fuskantarsu ya cire. Yana cire password ɗin shocking na wajen ya mutu, tangameme kofar karfen dake wajen ya wangale kansa.

Da kansu 3D suka fara jidan kwalayen drugs ɗin suna shigarwa cikin wannan ɗakin. Cikin ƙasa da 10 mins suka kammala, a lokacin 12 na dare ya yi.

Bayan sun kammala shigar da komai kaf, sai suka rufe kansu a cikin É—akin, suna rufewa lantarkin wajen ta kawo, shocking ya dawo, dik wanda yakuskura ya zo jikin kofar bushewa zai yi, dan wasu irin mahaukatan shocking ne a wajen.

Wuta na kawowa ɗakin naga wani haɗaɗɗen katafaren ɗaki ne, ga sofa set, AC, TV, tamkar office na wani hamshaƙin muƙamin gwamnati, komai na cikin ɗaki fari ne tas, an zuba maƙudan kuɗaɗɗe ba karya, ya ALLAH. Dr Kamal and Dr Mark ne suka wuce suka yi zamansu a saman sofas ɗin.

Shi kuwa Dr James wayarsa ya shiga latsawa kamar na 5 mins, sai ga pop dake ɗakin ta gefen hagu ya fara motsawa, jim kaɗan wajen ya buɗe tamkar kofa, sai ga tsani an juro da shi ciki. Miƙewa su Dr Mark suka yi, suka fara jidan kwalayen drugs ɗin suna haura tsanin, kowannensu kwali bibbiyu yake ɗauka su haye tsanin.

Suna hayewa hudawa suka yi cikin wani ɗaki wanda babu komai a cikinsa, tamkar store ne, empty yake, a nan suke shirya magungunan. A cikin ɗakin wani babban likita dake sanya cikin kayan aikinsa ne a tsaye, ya rungume hannayensa a kirji yana kallonsu suna shigo da drugs ɗin. Wannan likitan shi ya zuro masu tsanin, shi Dr James ya turawa saƙon sun iso, shi ne ya buɗe wajen ya sako masu tsani dan su haura.

Wai kun san tsadar magungunan kuwa? To ko shugaban ƙasa ba na kowani ƙasa ne yake iya jurar sayen maganin dik bayan wata ɗaya yana sha ba, suna da tsada, dan kwali ɗaya ƙarami mai ɗauke da drugs ƴaƴa kwara 6 kawai ya kai 1M, in dai kana son mai da kanka yaro matashi kuwa dole ka dinga sha dik tsadarsa. Amma ai kunga sun yi marasa karfi sosai watau ɗaurayar inji, waɗan nan basu da tsada sosai, carton ɗaya baya wuce 100k, kunga a karton kuma kwali 25 ne a ciki, zai kama kowani kwali 4k kenan, kunga shi da sauƙi a kan masu karfi.
Chapter 153 · 0% Book details