← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 161 OF 227

Sashe 161

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙara rumgumeta Manassa ta yi, tana murmushi ta ce. "Ke wanenen wannan?. Shi ne baki taɓa faɗa mun ba?"..... Murmushi ita ma ta ɗan yi. "Hmmmm ya haɗu over, shi ma fa soja ne, hoooooo Manassa i love him from the button of my heart, everything about him is special, his movement, his speech, his walking, his energy, his looking, the way he's working, the way he's praying har yasa na ji ina sha'awar addinin da suke yi, baki ga idan suna addininsu ina fita in tsaya ina ganinsu ba? Everyday shi ne yake tsayawa right side na sir Nirash idan zasu yi addini, i love his natsuwa over".

Kara zazzare idanu Manassa ta yi, tana É—age gera ta ce. "You mean sir Zaynish?"........... GyaÉ—a kai ta yi sama alamar yeah shi fa....... Manassa ta ce. "Yeah, sir Zaynish karshen haÉ—uwa ne shi ma, especially his hair, African hair É—insa akwai É—aukar hankali, yana da yawa kuma ya cika kansa"...... Jama'a kunsan gashi buzaye ai, akwai kyau, ashe kalle mana gashin Zaynish namu suke yi.

Angelina zata yi magana Arya dake fama da aiki ne ta rigasu da cewa. "Rubbish! Ku ba zaku daina ɓata lokacinku a kan maza ba ko? Ba za ku kama abin dake gabanku ba ko?"........ Harararta Angelina ta yi. "To tin da ke baki da lokacinsu sai aka ce maki muma haka ne? Mu muna son maza, especially kyawawa, ina son sir Zaynish, a kansa zan iya komai, abeg maintain word and mind your business!". Ta kai karshe tana murguɗa mata baki.

Kunsan Arya da karfin hali, hata ɗaukar raini, aikuwa tana juyowa ta kaiwa bakin Angelina bugu da karfi wanda sai da tasa ta saki karar da bata taɓa zatan zata yi ba. Ai a miliyan ta miƙe ta yi kan Arya, da sauri Arya ma ta miƙe tana faɗin. "Zaki sa hannunki a jikina ne?".

Angelina bata yi magana ba, tana zuwa ta damketa da faɗa, suka fara kokawa da karfi tamkar basu san juna ba, kome suka samu bugawa juna suke yi, da sauri Manassa ta taso ta fara ƙoƙarin rabasu, amma abin ya ci tura, hakan yasa ta fita da gudu sai ɗakin Leo, ta ce su zo su raba mata su Angelina suna faɗa.

A lokacin suna tsaka da tattaunawa kan wannan tafiya da zasu yi. Leo ne ya ce Vash ya je ya rabasu kuma ya kawo mashi su nan. Miƙewa ya yi, Manassa ta yi gaba ya rufa mata baya, har lokacin faɗa suke yi sosai, Arya ta jiwa Angelina ciwo a baki na punch ɗin da ta dinga kai mata.

Yana zuwa ya damkesu da hannu É—aiÉ—ai ya rabasu, sai huci dikkansu biyu suke yi. ....... "Dik ku je sir Nirash yana kiranku". Vash ya faÉ—a a dake. Siririn tsaki Arya ta ja tare da wucewa gaba kafin Angelie ta rufa mata baya, V dai tana ta barcinta.

Juyawa shi ma ya yi zai fita, a sanyayye V ta ce. "Sir Arvash"....... Tsayawa yai tare da juyowa, kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauke kansa........ Cike da zolaya ta ce. "A ranar da muka fara haɗuwa ka ce kana sona, nai maka kyau, amma yanzu meyasa ko magana baka mun? Ko kallona baka son yi?". Ƴar ƙaniyar yarinya, tafa san meyasa yake dik wannan, na farko ta ce mashi ita ƴar GAT ne, kunga ko a nan ɓangaren soja tafi karfinsa, na biyu ga aljanar da take mashi, aljanar tasa ta ce in ya kula wata mace sai ta kashe macen, kunga kuwa ba zai so a kasheta ba ai.

Amma hakika nin gaskiya Vash yana son Manassa, irin sosai É—in nan, kawai dai waÉ—an nan iya shege biyun da ta yi mashi ne yasa ya ja baya.

"Da farko da na ce ina sonki ma wasa nike yi, shi ne kawai!". Ya kai karshe tare da yunkurawa zai juya....... "Ban yarda wasa kake yi ba, dan na ce ni Æ´ar GAT shi ne zaka gujeni? Ba zaka iya fuskantar kowani haÉ—ari a kan macen da kake so ba? Kai ba soja bane"........ Dakatawa ya yi, slowly ya É—ago eyes É—insa a kanta, lallai tayi gaskiya, yakamata ya fuskanci kowani irin haÉ—ari ne a kan soyayyarsa, bai kamata ya janye dan GAT ba, to amma ita aljannar kuma fa? Idan ya ce zai iya ja da GAT zai iya ja da aljanar da baya kallo ne? To ace shi musulmi ne ya riki ayoyin ALLAH, ita Manassa idan ya fara soyayya da ita aljanar ta zo mata me zata karanta ta tsira tin da ba addini ne da ita ba?.

Ganin ya yi shiru ne yasa ta ce. "Kasan ba zaka iya sona da gaske bane kasa na fara sonka? Ka cutar da zuciyata? Haka addinin naka ya koyar ka cutar da mutum?"......... Nisawa ya yi tare da ɗago da idanunsa sosai a kanta. Rasa me zai ce mata ya yi, sai kawai ya juya zai fita. Kukan munafurci ta fashe mashi da shi, har da tsuggunawa ƙasa.

Cak ya dakata tare da juyowa, ya ALLAH, zuciyansa na sonta, ba zai iya wucewa ya barta tana kuka ba, dawowa ya yi, a gabanta ya tsugguna tare da sanya hannu ya ɗago haɓarta, suna fuskantar juna, hankey ɗinsu na sojoji ya fitar, a natse ya goge mata hawayen munafurcin da ta ƙaƙalo, cikin sanyin murya ya ce. "Sorry, amma a halin yanzu ba zan iya baki amsoshinki ba, tabbas ba karya bane ina sonki, amma ba zan iya soyayya dake yanzu ba, ba kaina nike jiyewa ba, ke nike jiyewa, so please ki bani lokaci zan nemo mafita". Yana kai karshe ya miƙe ya fita.

Ai yana fita ta miƙe tsaye, ta rike waist ɗinta ta fara tikar rawar da babu kiɗa, haka take so dama, ta yi ta wahalar da shi, ita tana da imanin cewa dik abin da namiji ya same shi a sauƙaƙe baya taɓa ɗaukansa da daraja, shiyasa take son sai ta ganawa zuciyar Vash namu azaba kafin ta bada kai, a zahiri gata Manassa kuma tana sonsa, a baɗini gata aljana da ta haramta mashi son kowa. Kai yaran GAT sai shirin ALLAH.

Sai da ta yi rawarta mai isarta, sannan ta ɗauko wayarta, ta hau rubuta mashi saƙon cewa a madubin ganinta na aljanu ta ga ya kula wata yarinya yau, lallai ya sani dik abin da ya faru da wannan yarinya shi ne sila, ya shirya ba zata bar wannan yarinya ba, ai ta faɗa mashi dik macen da ya kula sai ta kasheta. Tana gama rubuta mashi ta tura sai ta hau cigaba da taka rawarta tana nishaɗi.

A can kuwa Leo ya baiwa Arya da Angelina punishment na frog jump, saboda baya son irin wannan É—abia, ace suna Æ´an uwa kuma suna faÉ—a, ba zai É—auki wannan iskaci a team É—insa ba. Abin ku da soja a cikin ruwan sama ya sanyasu tsallen kwaÉ—on fa, ga dukan ruwa ga wahala.

Dikkansu sai da suka yi frog jump 100 suna kewaye tantunansu su sake dawowa, abinku da renon AZURE basu nuna wahala ko gajiya ba, amma sun ji a jikinsu kasancewar a cikin ruwan sama ne hakan ta faru. Dalilin wannan wahalar da Angelina da ya Leo ya yi ne yasa Unays ya ƙara ƙullatansa, ya ce ba zai kyalesa ba sai ya ɗauka mata fansa.

After some hours, garin ya yi shiru, iska mai sanyi ya sauƙa saboda ruwan da aka sha, dajin ya ƙara kyau da zama kore shar, ruwan sama ya ɗauke ɗiff, matasan sojojin da suka yi sallar magrib da ishai sun hura wuta suna zaune ƙarƙashin bishiya suna hira suna shan ɗumi, dik suna sanye da army jacket da takalmar aikinsu, while team 1 suna cikin ɗaki a zaune suna tsara yadda komai zai tafi, suna tsara a daren nan zasu saci jiki akwai in da zasu je su duba wani abu. Sojojin dake masu girki sun girka sun gama, sun zubawa kowa a plate, sojojin dake kewaye da wutan da suka kunna suna cin abincinsu.

While su Arya ma suna cin nasu abincin a É—aki, amma V kwance take saman gado, ta yi wanka tana sanye da sleeping dress É—inta masu kyau, taki cin abinci, idanunta har sun kumbura saboda kuka, tana kudundune a cikin army blanket É—insu. Sai rarrashinta Angelina take yi, amma taki tasowa ta ci abincin.

Daga karshe dole suka kyaleta, dan sun san hali. Fitowa Angelina ta yi hannunta rike da abincinta, ta nufi in da matasan sojojin nan suke zazzaune, daidai lokacin Zaynish and Vash suka iso wajen. Sai kallon Zaynish Angelina take yi, amma shi bai san da zamanta ma a wajen ba, yana zuwa yai zamansa a kusa da wutar tare da fito da wayansa, take sojojin wajen dik suka miƙe suka sara mashi har ita Angelina ɗin, sai da ya jinjina masu kai sannan suka koma suka zauna.

Wayansa Zaynish ya ya É—an fara latsawa, da alama shi fa su Angelina basu mashi bama, ba ruwansa da su.

Ya mayar da hankali kan abinda yake yi kawai, a daidai lokacin Aunty Ummi ta kirasa, miƙewa yai ya bar wajen, bayansa Angelina ta bi da kallo, sai magana Unays yake yi mata amma bata tanka ba, cikin sanyin murya ya ce. "Nai maki message baki mun reply ba".

Ƙasa ta yi da kai, a ɗan daƙike ta amsa da. "Banga saƙon bane"...... Nisawa ya yi tare da ƙara matsawa kusa da ita, ya fara janta da hira, ƙasa ta yi da kai, bata ƙara bi ta kansa ba ta hau cin abincinta a natse.

A can gefe kuwa, Leo da Noor ne zaune a cikin ɗakinsu suna cin abinci, Noor ya ce. "Bro zan je in ɗauki Juliet ɗita, ba zan iya cigaba da fushi ba"........ Abinci Leo ya ɗebo a spoon mai zafi sosai ya dannawa Noor ɗin a cikin baki ba tare da ya yi magana. Da sauri Noor ya fito da abincin yana buɗe bakin ta sha iska saboda zafi, akwai zafi sosai, ta ƙona mashi baki matuƙa.
Chapter 161 · 0% Book details