← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 227

Sashe 109

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baku yi manakin yadda Maya da Zinta suke da tausayi ba? To daddyn Lion shi ne ubansu, uwarsu kuma sai ALLAH ne kaÉ—ai ya san daga gidan uwar wa Dr James ya kwaso kwayayenta ya haÉ—a ya kyankyashesu, amma dai koma kwayayen wace mace ya É—auko ya haÉ—a da sperm na daddyn Lion tabbas kwayayyen sun kasance special ne, dan tin da ya ce zai kyankyasawa kansa mata da magaji ai kunsan ba zai sanya ordinary eggs ba, dole special zai sanya.

A takaice dai plan na shirta mai karfi yadda zai mallaki Zinta, ya kuma dasa mata sperm na ubanta da eggs ɗinta ta haifa mashi magaji mai basirar daddyn Lion, amma wanna plan ɗin ya ɓoye ko su Dr Mark bai faɗa masu shirinsa ba, ya dai fake masu da cewa zai auri Zinta ne kawai dan tana da kyau, saboda daddyn su Lion kyakkyawa ne, so Zinta da Maya sun fi kiwa kyau a hospital ɗin, bai faɗa masu zai ɗebi sperm daga cikin na daddyn Lion da suka killace ya dasawa matar tasa idan ya aureta ba. Kai na ce akwai cakwakiya babba, dik mommynsu Lion ce silar komai, da bata karɓi kuɗi ta masu hanya sun kama daddyn Lion ba, da ba'a ɗebi sperm ɗinsa an ajiye ba.

Yanzu dai a taƙaice Zinta da Maya kannen Lion ne daga kyankyasar kwalba, sun haɗa uba, uwar ce dai ba'a san daga in da aka samo eggs ɗinta ba. Kai Dr James ya zarce shaiɗani wlh, wannan irin kaifin ƙwaƙwalwa da ɗan banza basirar, kuna ga wata plan na ban mamaki!.

ALLAH sarki shiyasa Maya da Zinta suke son junansu sosai, ashe ubansu É—aya, uwar ce dai bamu sani ba ko eggs É—in mace guda ne ko kuwa kowacce da uwarta!

"Ku daina yi mana maganar Muhammad a nan". Dr Mark ya faɗa tare da miƙewa, ya nufi hanyar fita yana faɗin zaman ya kare tin da za'a tuna baya, daga haka ya fice zuwa office ɗinsa. Su ma su Dr James ɗin fita suka yi kowannensu ya nufi office ɗinsa.

After some days da faruwar wannan abin. Sister Zinta and sister Maya ne zaune a ɗakin da suke haɗa Chemicals ɗin nasu, abin duniya dik ya ishesu, waɗan nan chemicals da sune haɗawa ya yi mugun tsaya masu a rai, sun gagara tursasa zuƙatansu su cigaba da aikin, sun kuma rasa ya zasu yi, dan basu isa su ce ba zasu yi wannan aik ba, ba mai ja da 3D, sannan ita Zinta zuciyarta ta mace a kan soyayyar Dr James, ba zata iya kin yin aiki idan ya sanyata ba.

Dik da basu san ne za'ayi da chemicals ɗin ba amma zuƙatansu sun yi muguwar karaya da tsorata, musamman sister Maya da ta fi Zinta rauni, wani lokaci ma idan tana aiki kuka sosai take yi, saboda haɗarurrukan chemicals ɗin sun zarce yadda kuke tinani, sai ta yi ta kuka tana jin kamar wasu za'a cutar, kamar abin sharri ne, ta rasa dai gane dalilin da yasa take kuka idan tana haɗawa.

Yanzu haka kuka take yi hawaye bibbiyu tana tace sabbin chemicals da aka shigo da su yanzu, masu haÉ—arin da suka fi na baya. Haka ta tacesu, ta cire masu karfin ciki, ta zare matattun ciki, sannan ta je ta haÉ—a cikin waÉ—an can chemicals da suka haÉ—a a cikin wani katon drom mai zurfi, ta zuba a ciki.

Tsayawa ta yi a kusa da drom É—in tana kallon yadda miyagun chemicals É—in suke juyawa a cikin drom É—in suna haÉ—ewa da juna. Sister Zinta ce ta matsa wajen, nata chemicals É—in da ta gama haÉ—awa ta juye a ciki, sannan ta ce. "Sister Maya lafiya?"....... "Sister Zintata hankalina ya gagara kwanciya a kan wannan aiki, ina jin tamkar sharri ne".

Dafata Zinta ta yi, juyowa Maya ta yi suka rungumi juna, Zinta ta ce. "Babu wani abu, yanzu bari in je office na Dr James in bashi report na yau sai in zo mu koma SECTION A mu tattauna a can ko?".......... Kai kawai Maya ta iya gyaÉ—a mata....... "Je ki kaiwa Dr Kamal naki rahoton kin ji? Mu haÉ—u a gate na SECTION A".

Nan ma kai kawai Maya ta gyaɗa mata. Raba jikinsu ta yi tare da wucewa ta ɗauki result na aikin yau, ta nufi waje cike da zumuɗin zata ga Dr James, yarinyar nan ta haukace a kansa sosai, ita ko iya ganin face ɗinsa ta yi ba ƙaramin daɗi take ji ba, bare ace ya yi mata magana, ooooo, kwanar farinciki take yi.

Hannunta rike da file ɗin ta shigo arear 3D office. Tin daga nesa sister Lazy ta hangota, da sauri ta mike ta tareta bata bari ta kariso kusa da office ɗin nasa ba. A gabanta ta tsaya tare da miƙa mata hannu tana faɗin. "Bani rahoton in kai mashi!". Babu wasa a tattare da ita ta faɗa.

Tsoronta yasa Zinta ta miƙa mata hannayenta suna ƴan kerma. Fisga ta yi da karfi tare da juyawa tana cokala wannan takalmin nata mai uban tsawo ta nufi office ɗin nasa. Idanun sister Zinta ne ya cicciko tab da kwallah, ta ɗan turo baki kafin ta juya cike da takaicin yau bata kallesa ba, ɗazun da safe ma da zata kai mashi rahoton wani chemicals cikin wanda suka kawo ya faɗi kwalbar ta fashe ya zube su sake kawo irinsa Lazy ta hanata shiga, sai dai ta karɓi rahoton da ta rubutan ta shigar mata da shi, ta kuma karɓo amsar ta dawo mata da shi, abin ya yi mugun bata takaici.

Tsaye sister Lazy ta isko Dr James a tsakiyar office É—insa yana kokarin haÉ—e takardun dake kan table É—insa, sun tashi kenan, yana tattare rahotonni masu muhimmanci saboda in ya natsu a gidansa cikin dare ya dubasu.

Cikin wani irin karuwan yanga da yauni tana wani kwas-kwas ta shigo office ɗin. A gabansa ta tsaya tare da miƙa mashi result ɗin, tana wani karairaya ta ce. "Should I escort you?"....... Shiru bai yi mata magana ba, bai ma ɗago ya kalleta ba, sai da ya gama shan kamshinsa kafin yasa hannu ya karɓi takardan hannun nata. Ɗan duba takardan ya yi, a natse ya ce. "Ina mai wannan aiki ɗin da ba zata kawo rahotonta da kanta ba?".

Ɗan tsuke fuska ta yi, sai kuma ta ce. "Ban san meyasa bata son shigowa office ɗinka ba, amma ranar na ji tana cewa da ta shiga office ɗinka gara ta shiga cikin wuta, shiyasa idan ta zo take bani result ɗin ta ce in miƙa maka, ni dik tinanina ma kai kake cewa ta bani in baka ai". ......... Shiru ya yi bai sake yin magana ba, sai dai ya miƙo mata result ɗin alamar ba zai karɓa ba, idan kuma bai karɓa ya sanya hannu ba to fa aikin sister Zinta na yau an yi cancel ɗinsa, idan dama aikin 30 days zata yi to sai ta kara maimaita wannan aiki da aka yi cancel ya zamana kenan 31 days zata yi.

Abin ya yi mugun yi wa sister Lazy daÉ—i na yadda ta ga ta lalata mata aikinta na yau, cike da yanga ta juya ta fita. Kai tsaye room na su sister Zinta ta nufa, tana wani irin makirin murmushi.

Tana zuwa ta iskosu a ɗaki, isowarsu kenan suna ƙoƙarin cire kaya zasu shiga wanka. Jefawa sister Zinta file ɗin a kan fuskanta ta yi tare da cewa. "Ya soke aikin yau! Kuma ya ce dik in kika zo kawo mashi rahoto ki ajiye a PA office". (Office na PA office ɗinta kenan, kunga ta samu damar kullum ta dinga ɓata mata aiki, tana shirga mata karya a wajen Dr James har ya fusata ya fara hukuntata.

Cike da tashin hankali ta É—auki file É—in, tamkar zata yi kuka ta ce. "Meyasa ya soke aikin? Akwai in da na yi mistake ne? Ko dai akwai abin da yakamata in saka wanda ban saka bane? Aunty Lazy please help ki basa hakuri, zan sake duba komai in gyara".

Dogon tsaki Lazy ta ja tare da juyawa ta fita, tana fita Zinta tasa kuka tana faɗin ta shiga uku, dan tasan idan ya soke aiki fa mutum ya shiga uku, bayan sake aikin sai ya bashi hukunci mai tsanani. Jikinta na rawa ta ce. "Sister Maya me abin yi?"........ Maya da gabaɗaya jikinta ya yi mangaribar jemage ne ta amsa da. "Ina ganin mu yi wanka sai mu je gidansa ki bashi hakuri, ki ƙara gyara rahoton, ki duba da kyau ko akwai in da baki yi daidai ba".

Na'am ta yi da wannan shawara, cikin rawar jiki ta buÉ—e file É—in ta zaro paper, a gefen gadonsu ta zauna ta hau dubawa a natse. Ita kuma Maya ta wuce cikin toilet dan yin wanka.

Me kuke tinanin zai faru? Cakwakiyar asibitin nan dayawa take!.

STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥

ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️
🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥

PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.

STEP 1🔥

2025-12-3.🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E_____________ 36 & 37

Har Maya ta kammala wanka ta fito Zinta bata ga wani mistake ba a wannan result ɗin da ta duba, miƙawa Maya ta yi game da cewa. "Sister tayani dubawa ko dai ban gani da kyau ba, bari nima in yi wanka in fito". Karɓa sister Maya ta yi, ta ɗaura saman bed kafin ta wuce ta hau shiryawa.

Da alama daddynsu Leo ne yake da irin design na idanun nan nasu mai shegen kyau da É—aukar hankali wanda a hausance ake cewa mai idon shinkafa, zaku ga idanun yana da tsawo kamar shinkafa a kwance, ga shi ya É—an yi kamar zanen kifi, kuma idanun a buÉ—e suke manya-manyan, na su Maya farare kal-kal, amma nasu bai yi kalar sanyi watau jade eyes sosai kamar nasu Lion ba, su idan nasu ya É—an yi duhu kaÉ—an, while na su Lion yana da haske jade É—in.
Chapter 109 · 0% Book details