← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 227

Sashe 122

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

The only Prince of RING OF POWER kenan........ Tin da ya sako kafarsa a step na jirgin nan ta koina aka fara kashe mashi pic. Manyan mutane dake tare gefe guda suna jiransa ne suka fara gyara tsayuwa dan ya fito su gaisa.

Sai dai tin da ya fito kansa a ƙasa, bai ɗago ba, yana wani irin taku cikin zafin jini, guards biyar ɗinsa suka take mashi baya suma cikin tsananin jarumta, kai tsaye wajen tsadadden motar dake fara tas a cikin jerin bakaken motocin dake fake dan shi ya nufa, gabaɗaya numbobin motar an rubuta PRINCE OF RING OF POWER a jiki, da alama mallakinsa ne kawai motocin, shi kaɗai akewa comboi.

A jikin motar ya tsaya tare da juyowa, har lokacin kansa a ƙasa, Prime Minister ne ya fara nufosa cike tsaro da girma, guards ɗinsa suna take mashi baya shi ma. A gaban Lion ya tsaya, hannu Lion ya bashi suka yi musabaha, sannan ya juya ya shiga motarsa, bayan Prime Minister bai sake gaisawa da kowa ba, kuma akwai manya sosai da suka halacci wajen saboda shi, ko meyasa yaki amsa masu?.

A jere motocin suka tashi, kai tsaye sai katafaren MASARAUTAR BARTHARUN wacce suke kira da RING OF POWER. Masarauta ce mai ɗimbin tarihi wacce ita ke juya Avaris a yau, su da saurata suke mulki ba siyasa kai tsaye ba. Kamar England, kunga suma da sarauta suke mulkar ƙasa, sarauta ce mai power a ƙasar. To haka Avaris ma, RING OF POWER ita ke da karfi a ƙasar fiye da politics.

Masarauta ce da dik wani jarumi ko mai mulki da ya fara mulkan Avaris daga cikinta ya fito, masarauta ce da ita ta kafa Avaris da kewayenta, masarauta ce da ita ta jagoranci mahaukatan mayakanta da basu É—auki rai a bakin komai ba suka yi faÉ—a suka kwatowa Avaris Æ´anci a hannun turawar mulkin mallaka, shiyasa masarautar take da karfi sosai, ita ta sama masu Æ´anci.

Kakan Lion namiji shi ya jagoranci mayakansa suka yi fito na fito da Burtaniya a lokacin yana matashi, shiyasa dik wanda ya fito daga wannan masarauta mutanen Avaris mugun girmama shi suke, ana ji da shi, to Lion shi ne the only magajin da masarautar take da shi, shi ne yarima mai jiran gado, Nirash bai san da su a duniya ba, kazalika suma basu san da shi ba, Lion dai shi ne yasan komai, kuma kunga na faÉ—a maku ya ki faÉ—awa Leo tarihin iyayensu.

Masarautar tana da balain girma, tana da fuskoki biyu da fadoji uku, tana da tarihin mayaka da dawakai, sune suka zo na biyu a duniya a masarautar dake da yawan dawakai da mayaka, su in zasu yi yaki a kan dawakai suke yi, suna da karfin masifa tamkar dawakan nasu, kakansu Lion har yanzu shi yake mulkar masarautar, kuma babansu Lion da Hussaininsa su biyu ya haifa a duniya, amma dik ya rasasu, tin suna raye ma suka bar masarautar.

Daddyn Lion zuciyar balai ne da shi, akwai saurin fushin masifa, baya É—aukar nonsense, baku ji shiyasa su Dr James suka ce sun ci bakar wahala kafin su samu damar kama shi ba? Mutun ne mai haÉ—ari, ya gaji jarumta daga mahaifinsa.

Saboda wannan zafin zuciya da ɗan banzan girman kai nasa ya ɗebesa suka yi faɗa da mahaifinsa, shi kuma mahaifin nasa ya yi amfani da power ɗinsa na mulki ya hukuntasa, ya jefasa a kurkukun masarautar tamkar ba ɗan sarki ba, ya ce sai daddyn Lion ya durkusa ƙasa a gabansa ya bashi hakuri, shi kuma daddyn Lion ɗin ya ce da ya bashi hakuri gwara ya sanya takobi ya datse wuyansa ko kuma ya rataye kansa.

Kafiyar bala'i daddyn Lion yake da shi, ga shegen zafin kai, aikuwa Iron Sovereign watau King ya ce shi kuma sai daddyn Lion ya ce mashi sorry, ya É—auki tsawon wata ana ganawa daddyn Lion É—in azaba, amma taurin zuciyarsa da taurin kansa tasa ya ce sai dai ya mutu a azaba amma ba zai bada hakuri ba. Da mahaifinsa ya ga haka yana tsoron rasa É—ansa sai ya fito da shi, ya ce ya koresa ya bar mashi masarauta cike da sa ran daddyn Lion zai bashi hakuri komai ya wuce.

A maimakon ya bada hakurin, sai ya ce tafi nono fari! Wlh yaki bada hakuri, ya gwammaci ya bar family da gatansa ya tafi saboda furta kalmar sorry kawai, ya ce ba'a mahaifi wanda zai bawa hakuri ba! Aka ce ɗan nagada ya fi ɗan na koya, shi ma kakansu Lion ɗin fa haka yake, a lokacin yakin kwato ƴanci da turawa da turawan suka kama shi, a kan ya basu hakuri ne ya gwammaci dik azaban da suka gana mashi, daga karshe duka datse mashi yatsun kafafu, amma dik da haka yaki bada hakuri, yasan halinsa kuma yake ƙoƙarin tursasa mahaifin su Lion da ya basa hakuri.

In takaici maku labarin dalilin kenan da yasa daddyn Lion ya komawa US da zama, daga bayan Husaininsa ya ji ba zai iya zama ba, ya rufa mashi baya, dan kamar chewing gum suke! Mahaifiyarsu ta yi ta baiwa Iron Sovereign hakuri kan wai ta bada hakuri madadin ɗan nata, ya yafe mashi, amma sai ya ce yana son ɗansa da bakinsa ya furta wanda kuma shi kansa yasan abu ne da ba zai taɓa yiwuwa ba.

Har daddyn Lion ya koma ga ALLAH bai taɓa furtawa wani kalmar sorry ba, kuma tin da ya bar masarautar bai sake waiwayarsu ba saboda bala'in zuciya, sai wani lokaci da mahaifiyarsa bata da lafiya, a lokacin Lion yana da 5 years a duniya, shi ne ya ɗauko shi suka zo, bai je in da Iron Sovereign yake ba, ya duba mamarsa kawai ya bar masarautar abinsa. KUN JI TARIHIN DADDYN LION A TAƘAICE KO?.

To Lion ya zo masarautar sau uku bayan babansa ya bar duniya, É—aya tare da su Aryan ya zo, biyun shi kaÉ—ai, kuma dik yana zuwa ne saboda kakarsa da ita kaÉ—ai ta taimaki mahaifinsa, lokacin da mahaifin Lion ya bar masarautar granny É—in tasu ce kawai ta É—ebi gwala-gwalai É—inta ta bashi, ta ce ya je ya saidasu ya rayu cikin farinciki da walwala, shiyasa dik abin da Lion yake yi idan granny ta yi kira zai amsa, yanzu ma ita ta kirasa kan ya zo.

And mahaifinsa kafin ya rasu ya faɗa mashi ya kula mashi da mahaifiyarsa, kullum maganarta kawai yake yi, ita kaɗai ta tsaya mashi, ita ɗin uwa ce da kowa zai yi burin samun irinta, so shiyasa Lion yake tare da ita. Abin da yasa baya zuwa wajen kakansa namiji kuma, kakan nasa ya ce ba zai karɓi Lion a matsayin magaji ba har sai ya zo ya durkusa a gabansa ya bashi hakuri, watau ya yi abin da babansa bai yi ba kenan, idan ya yi haka zai karɓesa a matsayin magaji.

Shi kuwa Lion ya fuskanci kakan nasa ido da ido ya ce waye ya ce mashi shi Zayra'an yana neman a karɓesa a matsayin magaji? Baya da buƙatar sarauta a rayuwarsa, kai family ma kanta baya buƙata bare wata sarauta, wlh shi Zayra'an da ya bada hakuri, da ya furta kalmar sorry gwara ya kashe kansa. Babbar magana, King ya ga wanda ya fi daddyn Lion izza da isa, watau dik da yasan kashe kai ba kyau amma da ya bada hakuri gwara ya kashe kan nasa.

To shi ne suka raba jaha da Iron Sovereign ɗin, saboda ya ce ba zai bada hakuri ba, shiyasa kuma kuka ga Lion ya tsani kalmar sorry, ya ce ba zai taɓa furtawa ba! Kuma waɗan da suke tare da shi ma ba zasu furta ba, yanzu ko kashe Leo zaku yi ba zai taɓa ce maku sorry ba, sun ce da zu furta wannan kalma gara a kashesu! Tin da a kan kalmar aka kori babansu daga dangi, to ba zasu furta ba!......... E to akwai kura, mah people me kuke tinani ne wai?.

Tin da suka danno hancin motocinsu cikin katafaren gate na farko na masarautar na fara ganin wasu irin kyawawan mutane masu cikar kyau da haiba, sai dai fa mutanen suna da abin al'ajabi, dik wanda zaku kallah a cikin masarautar yana sanye ne da wata iriyar shiga ta ban mamaki, wasu irin king tail coat suke sanya da. Kuma abin mamaki mazan masarautar su suke yin kitso, mata kuma sai su É—aure gashin kansu gida biyu su sako jelar ta saman kafaÉ—a.

Ashe ga daga in da su Lion suka gado kitso a kai, daga wajen daddynsu suka gada, shi kuma daddyn nasu kunga daga nan Masarautar ya girma da shi kenan, al'adarsu ce, dole maza suna kitso mai shegen kyau, sai su É—aure jelar gashin su yi tuntu da shi. Wasu kuma kitso baya wuce dogaye kwara uku suke yi, sai su yi amfani da kitson su É—aure gashinsu da shi su yi tuntu, style na kitso dai kala-kala, kuma da yake gashinsu yana da tsantsi da kyau, baki da sheki ba karamin kyau kitso yake yi masu ba!

A kaf masarautar babu mai golden hair sai Lion, kada ku manta shi ma a wajen mom É—insu da ta fito daga kabilar Pamira ya gado golden hair ba daga wajen daddynsu ba. So shi kaÉ—ai ne mai kalar wannan gashi, shiyasa ya kara fita daban a cikin daban na mutanen masarautar. Yana da causin dayawa, da sauran Æ´aÆ´an Æ´an uwan Iron Sovereign, amma dai shi kaÉ—ai ne magaji.

(Kun san me? Mutanen Ring Of Power nan sun tuna mun da mutane Birnin Black World na littafina na RAWANI ZALINCI! Mutane Big Bro Black Tiger namu, su kuma irin shigar Annabi Isa suke yi, amma su basa kitso a kai, su kuma wannan masarauta maza da kitso ita ce al'ada, mata kuma da tara gashin a É—aure! Wlh sun tuna mun Black Tiger É—inmu na amana!.)
Chapter 122 · 0% Book details