Sashe 204
Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da okey ta amsa mashi, daga haka suka yi sallama, ya shiga gallery É—insa, hotunanta ya fitar ya fara kallon yana tina yarintarsa, lallai Aunty Ummie ita ce komai É—insa, tai mashi komai, a rana sai ta kirasa sau biyar ko mantawa bata yi, ga hidimar shago dana gida, amma baya sanya ta manta da shi, kome ta É—auka zata kai baki sai ta tina shi, ta ce shin shi ya ci ko bai ci ba? Yana samun irin abin da take ci ko baya samu? Dik ta damu.
Ya jima yana kallon hotonta kafin ya ɗan nisa, unexpected wayan nasa ya kubce ya faɗi ƙasa a gabansa. Da sauri Angelina ta ɗauko mashi wayan, kurawa hoton da yake kallo ɗin ido ta yi. Bata san lokaci da ta ce. "Wow, she's so beautiful"........ Slowly ya ɗago kallonsa a kanta wanda tin da ta zauna a wajen ko sau ɗaya bai ganta ba, har cikin ransa ya ji daɗin yadda ta furta words kan hoton.
Murmushi ta ɗan yi game da miƙo mashi wayar tana faɗin. "Is she your sister?". Ta faɗa tana mai da kallonta a kansa......... Bai amsa mata ba, kuma bai karɓi wayar ba. Bata damu da bai amsa ba ta sake cewa. "You look alike, amma tafika kyau saboda ta fika hasken fata, and ta fika big-big eyes, wow ta yi kyau sosai, anya ba zan cewa daddyna ya auro mana ita ba? Ta yi kyau sosai, na ji ina sonta".
Har cikin ransa ya ji Angelina ta burgesa, dik wacce zata so Aunty Ummie, hakika zata sace zuciyansa. Ganin bai karɓi wayar bane yasa ta zaci ya ji haushin abin da ta yi ne, sai a lokacin ta tina ashe oganta ne, taɓa wayansa ba da izininsa bama ta yi laifi, da sauri ta ce. "Sorry sir, it can't happen again". Ta faɗa tana sake miƙo mashi wayar, cikin muryar girmamawa tai maganar.
Hannu yasa ya karɓa yana ɗauke kallonsa daga kanta. Ƙasa ta yi da kai, haka kawai sai ta ji murmushi ya kubce mata ganin yau ɗaya ya ɗaga ido ya kalleta, abin da bai taɓa yi a, ba zata mance wannan rana ba, kuma haka kawai har cikin ranta ta ji Aunty Ummie ta shiga ranta, ta yi matuƙar burgeta, har ta ji cewa lallai tana son yin magana da ita. Zanen heart ta yi a ƙasa tare da zana dogon kifiya a tsakiyar heart ɗin kafin ta yi rubutu da yaren daddynta a saman heart ɗin, a ƙasa kuma da turanci ta rubuta. "Zuciyata ta makance kan mutum ɗaya, ta rufe ruff kan mutum ɗaya, bana ji, kuma bana ganin kowa sai shi, shi kaɗai ne zaɓina, shikaɗai nike gani in ji daɗi, i love you forever and ever"...... Ta gama rubutun tare da miƙewa ta bar wajen, ta koma kusa da Manassa ta zauna zuciyarta cike tab da tsananin begensa, tana fatan ace ya ga wannan zane.
Shi kuwa cigaba da dannar wayansa ya yi ba tare da ya sake É—agowa ya kalli in da take bama bare ta ji sanyi a ranta.
-------------------
Tsaye Lion yake a tsakiyar room ɗinsa rike da rigar pjs ɗinsa daya cire, ya kunna light bolb da suka ɗaura a saman tantin wanda ke amfani da solar, haske ya gauraye ko'ina a cikin ɗakin, yana ƙoƙarin ɓalle botiran rigan zai sanya a jikinsa ya fita.
Bakinta a É—auke da excuse Arya ta shigo cikin tantin rike da hannun yarinyar nan, zata fita ne yarinyar ta ce sam ita ba zata zauna a É—akin ita kaÉ—ai ba, shi ne Arya ta kamata suka taho tare.
Sake hannunta Arya ta yi game da kamewa ta sarawa Lion tana ɗan yin ƙasa da kai, gabanta sai faɗuwa yake yi na ganin kyakkyawan kakkarfar surar jikinsa, his sixpack was so Masha ALLAH, dole nema ya tafi da tinanin dik wacce ta gansa, gabaɗaya sai ta nemi natsuwarta ta rasa, ai a miliyan ta ɗauke kallonta daga kansa game da sauƙe hannun nata ƙasa.
"Sir akwai abin da yakamata ka zo ka gani, dan bayani da baki ba zai yiwu ba". A dake ta faÉ—a cikin girmamawa. Kai ya jinjina ba tare da ya yi magana ba. Sake sara mashi ta yi kafin ta kama hannun Jehan su nufi waje tana É—an waigosa. Cikin tantinsu suka koma, ta zauna a gaban laptop É—inta game da cewa Jehan ta zauna a saman electric mattress É—insu.
Hayewa kai Jehan ta yi tana kallon Arya cike da so, tana son Arya sosai.... Cigaba da abin da take yi Arya ta yi, ita kaɗai a cikin tantin, su V dik suna wajen wutar da suka kunna. After 5mins da kiransa sai ga shi ya shigo sanye da pjs ɗin da yake rike da shi ɗazun, hannunsa rike da wayansa yana pressing, da alama saƙo yake rubutawa.
A dab saitinta ta baya ya ɗan tsaya, sai da ya kammala rubuta saƙon da yake yi ya tura sannan ya sunkuyo kanta game da maido da kallonsa kan laptop ɗin.
Kallon 1 minute ya yi wa laptop ɗin sai kuma ya kai hannunsa sama mouse ɗinta, already hannunta na kai. Ai wani irin yanayin da ta ji ya ziyarce a lokacin da skin ɗinsa ya taɓata ba zai misiltu ba, da sauri ta janye hannunta tana sauke numfashi a hankali-hankali, ga daddaɗar kamshin perfume ɗinsa na kamfanin su Noor dake ta faman tashin kofofin hancinta.
"Wannan ina ne?". Ya faɗa a natse yana mai da kallonsa kan face ɗinsa, ta tsare ƙashin wuyan nan nasa da kallo. Ɗan ɗauke kallonta ta yi game da cewa. "Jiya V ta tura drone mai ɗan girma wajen ne sai suka harbesa, shi ne na tura ƙarami ɗazun dan in ga me yake ɓoye. Waɗan nan mutane sune abin dake wajen".
Cike da mamaki Leo ya sake mai da kallonsa kansu. Wajen tamkar rana, wutar lantarki zaku zaci rana ne, tantuna ne dayawa a kafe a wajen, wlh ya fi sansanin soja haÉ—uwa, ga wayarin na wutar lantarki da aka yi, amma su sojoji an basu kaya masu amfani sa solar, a wani sashe na wajen mutanen ma gini ne na É—aki da block da sementi, ta ko'ina matasa ne suke yawo rike da muggan makamai masu rai da lafiyan da babu irinsu a hannun sojoji. Abin mamaki kuma wlh dik matasan nan yara ne da basu kai 20 years ba, suna sanye da rawani a fuska da jallaniya a jikinsu, wasu kuma da irin pakistan riga da wandon nan, sai sha'aninsu suke yi a wajen tamkar a cikin gari.
Riƙaƙƙun ƴan ta'adda ne dake arewacin ƙasar waɗan da suka samu lasisi a ta'addanci, waɗan da manyan ƙasar ke ɗaure masu gindi, suke jin tamkar sun fi karfin kowa da kowa.
Motsa done É—in Leo ya yi, ya fara controlling É—insa yana bin sassan wajen, ta ko'ina matasa ne ke shawagi, a kallah zasu kai matasa 300 kam. GabaÉ—aya mamaki ya hana Leo yin dogon tinani a kansu, mai da kallonsa a kan kilomita nawa ne tsakaninsu da mutanen ya yi, a gaskiya suna da nisa sosai.
Cigaba da kutsawa lungu da saƙo na wajen ya yi, fili ne mai girman gaske, tamkar gari, ga lunguna da wajajen ɓoya ba adadi. Juya akalar drone ɗin Leo ya yi ya nufi wani wajen wanda ya ga lantarki yafi yawaita a wajen dan yaga menene. Bolb na wuta ya yawaita a wannan waje. Tura drone ɗin ciki ya yi dan yaga menene.
Ya ilahi ya lillahi, ai Leo bai san lokacin da ya zabura ya miƙe tsaye daga sunkuyon da yake ba. Jama'a, ta'addaci ya yi mugun karfi a arewacin kasar fiye da yadda kuke zato, wannan ɗakin cike yake tab da computers masu inganci, karfin intanet dake wannan waje kusan za'a ce yafi na cikin gari karfi, ashe shiyasa suka iya gano drone na farko suka harbesa, lallai ƴan ƙasa sun yi mugun sake ta'addaci ya yi girman da in ba ALLAH ba babu mai iya kwatarsu.
Wannan abu ya yi matuƙar gigita Leo, kuma ƴan ta'addan aka horar kan sanin computer da iya sarrafata. TO WAYE YA HORAR DA SU A WANNAN FANNI?.
A wannan waje suna da likitocinsu, suna da masu yi masu girki, suna da dik wani abin da ɗan adam zai buƙata dan more rayuwa, dik yadda kuke tinaninsu wlh sun zarce hakan, wannan shi ne ainahin taddacin arewacin ƙasar ba wata rufa-rufa ko sakayawa, ƴan ta'addan suna rayuwar jin daɗi da ƴanci fiye da ƴan ƙasa, abinci available, ga likita, kuma kullum ƙara yawa suke yi, ga karfin internet da aka ja masu har cikin wannan kungurmin dajin, shiyasa zasu kafa waya su yi video son ransu, su saki baya slow na network saboda karfin intanet na kasar rabi dik su aka baiwa, idan sun tashi zuwa yin ta'addaci sai su tura kalilan daga cikinsu da su matsa daga in da suke zuwa gaba ta bakin fita cikin gari su kafa wasu tantunan, sai su yi shiri su shiga gari, su kashe na kashewa su kwashi na kwasa, su dawo dasu sansanin da suka kafa, bayan kwanaki biyu in komai ya lafa su zaɓi waɗan da aka tsara masu kan ba yanzu zasu sakesu ba, su kutsa dasu cikin daji su kaisu babban sassani wajen babban shugabansu.