Sashe 192
Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cak Rimsha ta tsayar da kallonta a kan Seraphina, kana ganin idanunta zaka san tana cikin tsananin tashin hankali.... "Na ce ke baki son shi ne?". Seraphina ta sake tambaya.... Nan fa komai ya ɗaukewa Rimsha na ƴan dakiku, sai kuma ta ja dogon numfashi, muryanta a dashe ta ce. "Idan na ce bana son Uncle Aryan na yi karya, dan a koyaushe in zan yi addu'ar miji ina kwatance da irin qualities ɗinsa, amma dik wannan bashi bane, ni irinsa nike fata ba shi ba, kuma ban taɓa addu'ar mai halin mugunta irinsa ba, bana son halinsa, mugu ne sosai, tsoron kallon fuskansa nike sis, zuciyata bugawa take yi tana rawa muddin yana gida, ko ban haɗu da shi ba idan na ji ya zo gida hankalina in ya kai dubu tashi yake yi, wlh ni gara ace mutuwa na yi da ace na wayi gari na ji wannan bakin labari wai shi ne mijina".
Siririn tsaki Seraphina ta ja kafin ta ce. "Meyasa sai mai irin qualities ɗinsa kike addu'a? Ba ga shi ba? Kika sani ko addu'ar taki ce ALLAH ya amsa maki ta hanyar baki shi? Kika sani ko shi ne alkhairi a gareki? Kada ki bani kunya sis, is he not a man? And ke ba mace bace?"........ "Uhm, sis ba zaki gane bane, Uncle Aryan bakin mugu ne, ban tsanesa ba, amma na tsani halinsa matuƙa".
"Sai ki canza shi, ke ba mace bace? Ki canza shi da salonki, ki koya mashi dik irin halin da kike so ya zama, ki koya mashi ya zama mai taushi"...... Ganin Seraphina ba zata gane irin mugunta Aryan bane yasa ta kifa kanta a saman table kawai, ta fara rera sabon kuka.
Rungumeta Seraphina ta yi, ta dinga bata baki, da kyar ta samu ta yi shiru, ganin Rimsha fa ta rigata ta tsorata da Aryan, tana tsoronsa tamkar mutuwarta ne yasa Seraphina ta ce bari ta kyaleta zuwa wani ɗan lokaci sai ta ƙara bata shawari, yanzu ba zata taɓa fahimtarta ba.
Haka suka kasance har sauran ɗalibai da uncle suka shigo, ya fara karantar da su, sai dai dik abin da yake koya masu sam baya shiga kan Rimsha, tana nan cikin ƙuncinta, Seraphina ta yi ƙoƙarin kwantar mata da hankali, amma abin ya ci tura, dole kawai ta haƙura ta kyaleta zuwa su fita break, Uncle ɗan kwalisa kuwa sai satar kalle mana Cherry yake yi, yana son a tashi break ya zo ya faɗa mata ya yi kewarta.
A ɓangaren shi kuwa Aryan, yana isa gidan Abba bai iskosu ba, Abba da Faryan basa nan. Bai yi wa Ammie magana ba ya fita ya koma gidansu Lion.
-------------------------🔥
D--------O--------L
Manasa ce ta fara lura Arya bata cikin sansani, to da yake sun san halinta da son ruwa sai ta ce bari ta dubata a wajen ƙoramun nan kan ta zo ta yi breakfast. Fitowa ta yi da nufin ta je wajen. Bata yi wa kowa magana ba ta wuce. Tin daga nesa ta hango Arya kwance saman dutse, da sauri ta ƙarisa wajen tana ambatar sunanta.
Sai da ta taɓata ta gane ta suma ne. Hannu tasa cikin ruwan ta ɗebo, ta yayyafa mata a fuska. Dogon numfashi ta ja game da saukewa a hankali, slowly ta waro idanunta waje, sake sauke ajiyar zuciya ta yi kafin ta yunkura ta miƙe. Cike da mamaki Manassa ta ce. "Bloody lafiya kike sume a nan?".
Banza da Manassa ta yi, ta miƙe ta kwashi kayanta ta nufi cikin sansaninsu. Shiru Manassa ta ɗan yi tana mamakin halin Arya sosai. Juyawa ta yi tana kallon koramar dake zubo da ruwa daga sama. Daga bayanta ta ji ance. "What are you doing here?".
Ko bata juyo ba tasan muryan, a natse ta amsa da. "Waiting for my special person"........ "Are you sure?". Vash ya faɗa yana ƙarisowa in da take...... "Very sure". Ta faɗa game da juyo da kallonta a kansa. Nisawa ya ɗan yi, cikin zafa ya haye kan dutsen. A gefenta ya zauna suna fuskantar ruwan, hira mai cike da respect ɗin juna suka fara yi, bai fito da soyayyarta a fili ya bayyana ba, ya dai biye mata yana bata amsar tambayoyi. Ita kuma tana tinanin da sun koma sansani ta ɗauki wayarta zata mashi aljanar da ta saba ta ce taga ya kula wata a bakin ruwa.
Mu ɗan yi baya kaɗan a ɓangarensu Leo. A lokacin da suka kammala breakfast, team 1 dik suka haɗu a tantin Leo, sai suka kwance mutanen da suka zo da su jiya. Sun yi mamakin ganin fuskokin mutanen, fuskoki mai cike da kamala da mutunci. Vash da Noor ne suka caje jikinsu kaff.
Abin da suka gani ya yi matuƙar gigitasu, ID card nasu, ya tabbata navy ne, ya rabb, sojojin ruwa ne da wannan aika-aikan, no wonder suka iya faɗa irin na soja, ashe dik ɗaya ne. Kallon juna team 1 suka yi, cike da takaici Noor ya ce. "Wannan wani irin cin amanar ƙasa ne? Wani irin zalunci ne wannan? Ya ake son al'umma su yi da ransu?".
Zaynish ya amsa da. "Dama ai dik abin da ya shigo kasar nan in ma mai kyau ko mara kyau to da sa hannun sojojin ruwan dake kan aiki, ba ta yadda za'ayi wani abu ya keta bakin ruwa ya shiga cikin ƙasa basu sani ba, hakan ba zai yiwu ba, suna sane da komai!".
Shiru Leo bai yi magana ba, saboda tsananin takaici, wai ace da jami'ai ake haɗa bakin wajen yin wannan ɓarna.
Can Leo ya ce. "Ku karɓo mana alluran barci daga wajen Manassa, ko kuzo da ita ta zo tai masu, zuwa dare zamu san hukuncin da zamu yanke masu".
Vash ne ya ce. "Amma yakamata ace mu ajiyesu har su farfaɗo sai mu tambayi su waye suka basu aikin?"........ Shiru Leo ya ɗan yi, sai kuma ya girgiza kai. "Ba zasu faɗa maku ba, dan suma basu san wanene ainahin mai ɓarnar ba, suna karɓar umarni ne kawai daga sama kuma cikin waya, dan haka babu wani amfanin neman information a wajensu"......... Noor ya ce. "Su ɗin karnukan farauta ne kawai".
Sun gamsu da waɗan nan kalamai na Leo, dan haka sai suka yarda da shawaransa, a kan haka suka tsayar da matsaya, daga nan suka rufe babin zancen suka ɗauko maganar shirya plan kan yadda zasu je wajen wannan hayaƙi su duba menene.
Sun tsara nan da kwanaki biyu zasu je su duba menene a wannan waje, kan wannan matsaya suka tsaya, sai Leo ya ce su fita su ɗan yi kewaye a arear wajen ko akwai wani abin da zasu samu. Zaynish da Vash suka fita, shi ne Vash ya tsaya wajen Manassa a bakin ruwa, while Zaynish ya tafi bakin babban tekun nan dan saka idanu, shi ya damu sosai da yadda ake shigo da gurɓatattun kaya, a cewarsa bai ga anfanin hukumar sojan ruwa ba, a rana idan ka tsaya a bakin tekun nan sai ka ga jiragen ruwa sama da 10 sun iso, wasu suna nesa, wasu sun juya, to yanzu sun san wasu daga cikin abubuwan da ake shigo dasu, yakamata su san abubuwan da ake fitarwa.
Tamkar Zaynish ya shiga cikin zuciyar Leo, in baku manta ba Leo yana yawan tsayawa a bakin tekun nan, to kullum tunaninsa me ake fitarwa cikin waɗan nan manya-manyan jiragen ruwan? Ina ake kai abin da ake fitarwa? Wasu lokutan yana ganin tankokin man fetur ne, wasu tankokin da rigister gwamnati, wasu kuma yana zargi babu, wasu kuma na ƴan kasuwa ne, dik bama wannan ba, manyan containers da ake fita da su kullum me a cikinsu? Kullum yana wannan tunani, shi ne ya tsara su je su fara binciko me ake shigo da shi kafin ya tsara binciko me ake fita da shi. Leo yana da kishin ƙasa da kishin kai sosai.
Zaynish and Vash suna fita Leo ya ware gashin kansa, ya ɗauko comb ya miƙawa Noor, karɓa Noor ya yi ya fara taje mashi gashin, abinku da renon mata, take Noor ya tsara mashi kitaon balba masu balain kyau, ya zuba mashi mayukan gashi a kai, sai kamshi gashib take yi, ta ƙara zama golden white sosai.
Yana tsaka tara jelar kitson ya ɗaure ne ya ce. "Bro kaki ka faɗa mun zanen me a bayan wuyanka, ina son sani, kuma kasan me?"....... Kai Leo ya girgiza alamar aa... "Waɗan nan zane suna mun kaman na sansu a wani waje, ina jin kamar zanen password na wani abin ne da na taɓa sani, kaman kuma zanen wani tambari". Ya faɗa daidai lokacin da ya gama ɗaure mashi jelar kitson, sai yasa hannu a saman lallausan fatan bayan wuyan Leo ɗin, ya fara shafa zanen yana son tina a ina ya san shi.
"Yadda ka ga zanen nan haka nima na gansa, na sha faɗa maka ban san na menene bane, ban ma taɓa ganin zanen me bane, ni da kawai ana ce mun a bayan wuyana akwai zane kamar tabo, kamar da wuta aka yi mun, to ban sani ba". Leo ya faɗa game da juyo, har ga ALLAH bai san zanen me bane, shi dai kawai ana ce mashi akwai zane a wuyansa, bai taɓa gani ba, kuma bai taɓa sha'awar ya gani ɗin ba.
Miƙewa ya yi game da ɗaukar belt ɗinsa, ya sanya a jikinsa da kyau, a wannan lokaci Manassa ta shigo da allura, Noor ya nuna mata mutanen, zata masu alluran Leo ya ce. "Na awa nawa ne?".
Cike da gimamawa ta ce. "Awanni 12 sir Zaynish ya ce mun". Jinjina kai ya yi alamar haka ne, Noor ya taimaka mata ta yi masu alluran, sannan ta fita. Ƙarisa shiryawa Leo ya yi, suka fita a tare da Noor, suka kutsa cikin daji, suna tafiya suna hira, suka yi nisa da sansaninsu, daga ta bayan sansaninsu can suka isa bakin ruwa, a nan suka zazzauna saman wasu manyan duwatsu dake kewaye da wajen, ga wasu bishiyoyi dake kaɗa iska mai daɗi kuma mai sanyi, Leo ya ɗibi wasu duwatsu ƙanana yana jefawa a cikin ruwa one by one suna hira.