← Book details Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 227

Sashe 33

Zakuna Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rufewa ta yi ta matsa kusa da manyan, da kyar ta kwantar da guda É—aya ta buÉ—e, kayyakin sakawa ne masu bala'in kyau da tsada. Abinku da yarinta, tuni ta fara murna tana jin daÉ—i tin ma ba'a ce mata nata bane. Wani haÉ—aÉ—É—en top white ta ciro, sai ta É—auko ash jeans. Tuni ta hau shiri a cikinsu, a wajen ta shirya tsab, kayan sun yi mugun yi mata kyau kuma. Sai murna take yi ta É—auko É—ayar echolac É—in zata buÉ—e kekan ta ji wani irin gurnani mai firgitarwa.

A miliyan ta ɗago kanta, a daidai lokacin wani ƙosasshen bujumin zaki ya sanyi kansa cikin parlon cikin tafiyar ƙasaita. Ai wani irin ihu da ta kurma tare da zabura ta miƙe tsaye, hakan yasa Zakin juyuwa da gabaɗaya jikinsa da kallonsa a kanta, suka ga juna ido cikin ido.

Haba wani irin zunduma ihu ta yi tare da watsawa a guje ta bazama ba tare da tasan in da ta nufa ba. Ai da gudun gaske zakin ya rufa mata baya shi ma. Bata san in da ta nufa ba, bata san ya aka yi na sai tsintar kanta ta yi cikin wani É—aki. Tsayuwa ta yi a tsakiyan É—akin tana faman waige-waige, daidai lokacin zakin ya bango door ya shigo É—akin da gudun gaske shi ma.

Ihu ta zunduma, lokaci guda kuma ta ɗauke wuta diff, ta sulale ƙasa a wajen. Da gudu zakin ya yi kanta, daga bayansa ta cikin ɗakin wata murya ta ce. "Hero, come here". Da karfi zakin ya juya, ɗakin irin dogayen ɗakin nan ne, ba faɗi sosai sai tsawo.

Cikin zafin jini zakin ya yi kan wanda ya kirasa. Wannan mutumin ne dai da ya É—auko yarinyar daga hospital, zaune yake a saman sofa, wasu rantsastsun sofa set ne a cikin room É—in, a kusa da sofar akwai wani curtains masu shegen kyau launin dark ash da kamar sun raba É—akin biyu. Guys É—in su biyu ne suke zaune suna fuskantar juna, dikkansu kuma face É—insu sanye da nose mask, hoodie baka ce a jikinsu, sun sanya hular kayan, da alama tattaunawa suke yi.

Jin motsin shigowarta yasa suka kai kallonsu a kanta. Nasan kuna son sanin su waye waɗan nan mutane! To a taƙaice bari in faɗa maku, waɗan nan shahararrun terrorist kuma gangsters ne da duniya ke haukar nemansu, but babu wanda ya san ainahin fuskansu, sunansu da ɓarnarsu kawai ake ji, su uku ne a team guda, ko muryansu babu wanda ya taɓa ji, IRON FIST shi ne takensu, dik in da suka aikata wani shahararren laifi sai sun bar tambarin IRON FIST mai ɗauke da hoton kan zaki, wannan tambari duniya ta rika makama wajen nemansu, an zana tambarin nan a ƙasashe daban-daban ya fi a kirga da nemansu, amma har yau an kasa fitar da ainahin zanen IRON FIRST na gaskiya, dan akwai wajen da suke covering in zasu bar tambarin. An yi binciken duniyar nan an gagara kamasu, to mutanen da wani lokaci basa zuwa aikata abu da kansu, suna daga ɗaki a gaban computer zasu yi abin da zasu yi. Dik kuma idan zasu fita aikata laifi suna da mask na team ɗinsu da suke sanyawa, mutane ne da basu da tsoro bama su santa ba, tsabar yarda da kai zasu iya shiga waje kai tsaye su aikata laifi ba tare da bindiga ko wuƙa ba! Ga bala'in saiti a fagen harbi, idan suka so kashe mutum tazarar mitoci a tsakaninsu suna iya harbinsa kuma ya same shi, suna iya harbin mutum a cikin mota mai tsananin gudu tsabar kwarewa, mutane ne dake amfani da ƙwaƙwalwa fiye da jami'an gwamnati, shiyasa aka gagara kamasu, tsawon shekaru an gagara gane dalilinsu na aikata manyan laifuka, kuma babu ƙasar da suka bari, dik karfin tsaronku suka yi ra'ayi shiga suke yi, da wayar mutum da ba nasu ba ma suna iya karɓa su datsi tsaron wasu tsabar kwarewa da yarda da kai, haɗarinsu ya zarce yadda ɗan adam zai iya tinani, suna da salon kisan mutum na musamman wanda dik wanda ya ga wannan kisa yasan su suka aikata shi, a shekarun baya su ne suka yi wa shugaban Amurka wani irin mummunar kisa suka kifar da gwamnatinsa, kowa kuma yasan su ne, amma an rasa hanyar kamasu, ku duba tsaro irin na shugaban ƙasa, amma suka shiga ta karkashin ƙasa suka kashesa suka fito, kwarewarsu yasa basa barin makama komai ƙanƙantarta idan suka aikata laifi!

Ko a gida suke zaku samesu da nose mask, mutane ne kuma masu fuskoki da dama, saboda kwarewa basa amfani da fuska guda, kazalika yau zaku gansu da ido blue, gobe violet, jibi ash, suna iya canza komai nasu a lokaci guda, ainahin suffansu ne dai baya taɓa bayyana, dik kalar da suke canzawa na boge ne, basu taɓa fita da ainahin face ɗinsu ba, takan iya yiwuwa yanzu da suke cikin gidan ma fuskan boge ce, dan ba'a gane masu! Mutane ne basu da shaukin komai sai kisan kai da tada zaune tsaye! Basu da uwa basu da uba a wannan gida, su uku suke rayuwa! Kuma wani abin mamaki ɗaya daga cikinsu baya wani jimawa a tare da su, yana da yawan tafiye-tafiye, idan ya yi sati ɗaya da su, zai iya tafiya ya je ya yi sati a wani waje, ko suna da iyaye to sun ɓoye iyayen a wani waje ne suke rayuwa su kaɗai a nan, dukiyar da suka mallaka ALLAH ne kaɗai yasan adadinta. A takaice su waye su kenan, saura bayani zaku ji daga baya.

Yanzu haka wanda Dr ta taimaka yana kwance a gadon asibiti, wanda ya É—auko Seraph yarinyar Dr kuma babban amininsa ne, dama na faÉ—a maku su uku ne, to yanzu su biyun ne a nan, shi wancan yana gadon jinya, dan ya rasa jini na wuce misali. IRON FIRST basa magana, basa bari a ji muryansu sai su da junansu, shiyasa guy É—in can bai tanka Seraph ba!........ Watau akwai wani cakwakiya dake gaban a book É—in nan! Hmmm!

-------------------🔥

Da gudu Hero ya bar kanta ya isa wajensu. Da hannu ya nuna mashi kusa da shi, kallon juna suka yi, É—ayan ya ce. "Champion who is this girl?". ....... Kallon in da take ta wutsiyar ido ya yi kafin ya amsa da. "I don't know her. It's FT said I should bring her home, treat her well, give her everything she needs, but I must not let her see him again or even know that he is in the house when he recovers and returns, baya son sake ganinta kuma baya son ita ma ta sake ganinsa, kawai in kula da ita".

Shiru guy É—in ya É—an yi, kamar ba zai sake yin magana ba sai ku ma ya ce. "Amma hakan ba zai ja mana matsala ba?"........ "Na yi tinanin hakan, but yarinyar bata da kowa, amma zan bashi shawarar ya kaita boarding school".... Jinjina kai guy É—in ya yi alamar shawarar ta yi kenan. Da haka suka cigaba da hiransu cikin yaren da ni na fassara maku, ba turanci suke yi ba, sannan maganarsu sam bata fita sosai bare a iya gane voice É—insu saboda nose mask da suka sanya!.......... Ba su sake bin ta kan Seraph ba!

Hmmmm akwaita kuwa! Yau kuma ta nan na faÉ—a ni Princess Teema!. To fatan dai kuna biye dani mu warware komai a tare!.

STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥

ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️
🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥

PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.

https://www.facebook.com/share/g/1EUXbqsDjP

STEP 1________🔥

7-11-2025.🔥

FIVE LIONS, FIVE MISSIONS, ACTION, DEATH OR LIFE, ADVENTURE, BRAIN GAMES, REDRESS, A BREATHTAKING LOVE THAT STEALS THE HEART AWAY.♥️🔥

E_____________8

Sun jima a wajen suna zaune, magana kuwa sai su fi mintina 20 babu wanda ya ce ƙala, can su ɗan yi hira, su sake yin shiru. A haka suka shari awanni uku a wajen, kafin Champion ya miƙe tsaye, dik in da kuke neman dakakkun jaruman maza waɗan nan sun kai, tsananin hora kansu suke yi fiye da yadda ake hora sojoji, dik saboda kwarewarsu, su basa yi wa ƙananan ƙungiyoyin ƴan ta'adda aiki, basu ma karɓar aiki a garaje, sai an yi saa, kuma wani lokaci fa har gwamnati suke yi wa aiki ba tare da gwamnatin tasan su ne IRON FIST ba.

Akwai wani lokaci da wani daga cikin gwamna a Avaris ya nemi taimakonsu through wani abokinsa, ya basu kwangilar kashe wani sarki, a wannan ɓangare and sansu ne da fuskan ƴan Korea, dan abokin nasa ma ce mashi ya yi akwai wasu ƴan Korea manyan terrorists zasu yi wannan aiki. Mutun ɗaya ne daga cikinsu ya shiga Avaris ya kashe wannan sarki kuma ya fita ya dawo, tamkar wasu aljanu, dan haka fuskokinsu a duniya yana da yawa matuƙa! Su kaɗai suka san ainahin kamanninsu sai kuma alƙalamina!.

Miƙewa ɗayan ma ya yi, kamar zai yi magana sai kuma ya fasa, ya buɗe curtains dake wajen ya shige. Shi kuma Campaion in da Seraph take ya kariso, yana zuwa yasa hannu ɗaya ya damki wuyan rigarta. Sama ya ɗagata sai kan shoulder ɗinsa. Ya nufi waje da ita. Hero zai biyosa ya nuna mashi hanya ya bi ɗayan guy ɗin, dan yasa idan ya biyota za'a samu matsala in ta farka.

Kai tsaye room É—inta ya nufa. Yana tura door É—in ya tsaya kaman wani gumki, a cikin duhu ya hau jujjuya ash eyes É—insa da bani da tabbacin kwayar idanun gaskiya ce, dan na faÉ—a maku a baya komai nasu na boge ne!.

Takawa ya yi a natse ya isa gaban light control dake manne kusa da bed, wajen da low light. Wutar É—akin ya kunna, gabaÉ—aya haske ya gauraye ko'ina, a saman bed ya jefa Seraph tare da nufar toilet É—inta. Jim kaÉ—an ya dawo hannunsa É—auke da bowl, a gaban bed É—in ya tsaya. A maimakon ya shafa mata ruwan a natse, sai ya kwarara mata shi a kan fuska!.
Chapter 33 · 0% Book details